Join Our WhatsApp Group

DIJE KARANGIYA Complete Hausa Novel Document by DIJE KARANGIYA


DIJE KARANGIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 142948



DIJE KARANGIYA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 13, Apr 2023

Author: Hadiza D Auta ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : TAURARI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 09032685442

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 736.51 kb

File Type: txt

Views: 2651+

Download: 1870+

Last download: 1 day ago

Description/Story: *💣💣DIJE K'ARANGIGIYA💣💣*




*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*




*ALHMDLLH ALLAH DA YA NUNA MANI WANNAN RANA HAKA MA NA GODEWA ALLAH DA HAR YA ARA MANI LOKACI YA BANI RAI DA LAFIYAR DA ZAN SAKE DORA ALKALAMINA DA SABON LITTAFINA MAI SUNA DIJE K'ARANGIYA, SAI DAI GAJEREN LABARI NE MAI CIKE DA BARKWANCI DA NISHADANTARWA HADI DA ILMANTARWA DUKA, MASOYANA A DUK INDA KUKE INA ALFAKHARI DA KU HAR MA DA MAKIYAN DUKA D/AUTA TANA GODIYA👍🏻*



*LITTAFIN DIJE K'ARANGIYA SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA UWA MA BA DA MAMA BAYA GOYA MARAYUN ALLAH, UBANGIJI YA K'ARA MAKI LAFIYA YA JA MANA DA NISAN KWANANKI INA SONKI SOSAI MUMMYTA ALLAH YA KAREKI DA SHARRIN MUTUM DA SHARRIN SHEDAN ALLAH YA SAKA MAKI DA GIDAN ALJANNAH KO ALJANNAR TA CEN CEN KOLOLUWA I LOVE YOU SO SO MUCH MUMMYTA💋💋💋👍🏻*





*Lamba ta 1*



Tafe suke su biyar kowacensu kanta d'auke da daurin ciyawar da suka debowa dabbobinsu, kowace karkashin ciyawar da ganwo a kanta sunyi d'ana tafe suke akan siririyar hanyar da ta ratsa ciyayi suna tafe suna ta firarsu suna dariya, sai dai wadda ke gabansu duka wadda tana tafe da Yar bulalarta a hannu tana dukan ciyawar da ke gefe gefen hanya tayi wata kuwwa ta fara waka tana cewa.

"ku saura ku ji Yau fa in naga dama"

Dukansu Suka had'a baki da kalar wakar da tayi wajen fad'in cewa

"Dije k'arangiya yau kuma wacce kika k'ullo?"

Wadda aka kira da Dijen ta yi tsalle har sai da ciyawarta ta so fad'uwa ta tare da sauri cikin wakar tace,.

"Rumfar mai gari yau nike so mu je mu tarwatsa"

Hansai ta zaro Ido waje bakinta yana rawa tace,. "WALLAHI nikam Dije babu ruwana haka kawai mu je mu d'auki alhakin mutane a banz......"

Dije cikin zafin nama ta kaiwa bakinta faka tace, "ware anan tun kafin yau Inna Meramu ta yi maki tuwon k'asa, kuma WALLAHI kika kuskura na ji kin fad'i maganarnan sai na darje maki baki yayi jini"

Sanin halin yasa Hansai ta yi saurin yanke hanyar ta barsu anan tana yi tana waigen Dije don kar ta biyota ta jibgeta a banza, don ta santa sarai wannan k'aramin aikinta ne, Dijen ta kalli sauran abokan nata ta ajiye ciyawarta ganin haka yasa dukansu suka ajiye tasu, Dije ta saka bulalar dake hannunta ta daki d'aya daga cikin kawayen nata tace,

"Ke kuma Lanti in kinsan cewa bak'in halinki zaki nuna har kisa a gano Shirinmu ba gaske bane ba to ki tafi gida kawai zamu k'araso"

Lanti jikinta yana rawa ta marairece tace,. "A yi dani kawai ba Zan bari a gano ba"

Dije ta kalli sauran ta kyalkyale da dariya sannan ta janyo kansu ta had'e waje d'aya ta fara rada masu kus kus a kunne, gaba d'aya suka tuntsure da dariya Mune tana dariya ta ce,.

"Har na hango yanda maigari zai ....."

Dije ta yi saurin buge mata baki tace,. "To tonanna tonamu aji tun kafin muje cikin garin"

Aiko ba shiri Mune ta yi gum tana fiki fiki da ido daga nan Dijen tace da kowa ya shirya da sunje bakin garin zasu fara shirinsu, aiko Suka k'ara d'aukar ciyawarsu Suka dora akai suna tafe suna dariya har daf da shiga cikin garin Suka fara koyon K'ugin kukan Kura sannan dukansu suka ciccire talkaminsu suka sagala a hannuwa Dije ta fara dafe ciyawarta ta zankara aguje tana K'ugin kura tana kuwwa tana fad'in

"wayyoo Kura! kura a garinmu ku yo agaji gata nan shigowa garin daf take damu ta kusa k'araso"

Aiko sauran kawayenta suma Suka dafe mata baya suna K'ugin suna ihun ga kura nan ta shigo gari, Mutane tun da suka fahimci abunda suke fad'a Suka fara gudun ceton Rai Dije da kawayenta aguje har fadar Mai Garin don tun daga nesa da Suka jiyo sautin kukan Kuran suka natsu musamman da suka ji abunda take fad'a sai ga dandalin ya fara watsewa, saboda ganin yanda suke gudu a bala'e suna haki suka Fara gasgata lamarin, sai mutum biyu aka bari a wajen sai ko ga su sun k'araso tana haki tace da su

"Mai Gari Mahaukaciyar Kura a garinmu yau gata cen har ta fara cin wasu a farkon gari da alama ma tana gaf da karasowa nan muma dakyar mukasha"

Maigarin ya zaro Ido waje yace,. "Ke Dije kinsan nasan halinki ko? To Wallahi......"

Kafin ya k'arasa sai ga wani aguje ya nufosu Yana fad'in "Kura! kura! Maigari"

Aiko Mai Gari ya zabura ya zankara aguje dafe da rawaninshi sai dai Yana gaf da shiga gidanshi ne wani kwatami ya jashi yayi luuu sai jinshi kake Tim! A k'asa rawani yayi gabas hula tayi yamma, sai ga Maigari da fasa wata arniyar k'ara ya mike cikin zafin nama ya fad'a gidanshi ko kallon rawanin da hular bai yi ba sai ihu yake yi yana fad'in,. "Kowa yayi ta kanshi Rana ta b'aci yau maza bisa kanmu".

Dije da sauran kawayenta da suke labe jikin k'aton iccen da ke k'ofar gidan Wanda anan Maigarin da mutaneshi suke Shan iska, sai k'ugin kukan kurar suke yi ganin kowa ya shige yasa suka fito suna ta tuntsura dariya musamman da suka hango wani dattijo aguje ya dafe keya sai gudun ceton Rai yake yi ya shige gidanshi kudum ya dantse k'ofa.

Daga nan bakin Gidan Maigarin Dije tace kowa tayi gida aiko kowacensu ta nufi gidansu Dije tana tafe tana dariyar keta idan ta hango wasu da gudu ta sake yin k'ugin kurar itama ta dafe ciyawarta aguje tana cewa

"Gatanan WALLAHI taci mutum biyar a farkon gari"

Aiko Mutane sai su k'ara d'aga k'afa da haka har ta kai gida sai dai tana Kai k'ofar gidan ta ga gidan a rufe gam! Wata dariya ta sake zubo mata, ta Kai kallonta ga wani gida da su ke makota da juna nan ma rufe yake gam sai da tayi dariyarta mai lasisi sannan ta fara buga kyauren Gidansu tana sake koyon kugin kurar a haukace tana fad'in

"Baffah ka bud'e Kura zata cenyeni a arha"

Sai gashi ko taji an bude k'ofar da sauri ya fisgota da k'arfi har sai da ciyawar ta fad'i ya turata ciki ya sake dantse k'ofar yana haki ya janyota har cikin Gidan yace,

"Maza shiga d'akin innarki ku b'oye Ni idan har ta shigo gidan ta canyeni ku sai ku tsira illah iyaka ku bini da addu'a"

Dije ta tuntsure da dariya saboda ganin yanda Baffan yake ta zaro Ido yana dubin k'ofar hanyar fita Gidan, aiko sai ga Kukan akuya a k'ofar gidan tana meeh! meeh! A guje Baffa ya zankara da gudu yayi hanyar d'akinshi yana fad'in

"Salamun k'aulan min rabbir'rahim shikenan tamu ta k'are yau shahada zallah a garin K'IRIU"

Har ya fad'a d'akinshi zai rufo ya waigo ganin Dije tsaye tana k'unshe dariyarta, cikin d'aga murya yace

"Uban me kike anan da ba zaki b'oye ba ke?......"

Jin sautin kuwwa a makotansu yasa Baffa ya kullo k'ofar garam ya Fara salati iya karfinshi, Dije ta k'araso jikin k'ofar tace

"WALLAHI Baffa ba wata kura ka kwantar da hankalinka"

Ganin yaki budewa ne kuma bai daina Salatin ba yasa ta nufi k'ofar gidan ta bud'e kyauren aiko sai ga Yar akuyarta a k'ofar gidan ta dawo kiyo ashe itace take kuka, ta rik'o igiyarta ta janyota har cikin Gidan ta je bakin k'ofar d'akin Innarta tace

"Inna ki bud'e ba wata kura WALLAHI duk k'arya ne"

Jin sautin kukan akuyar yasa Innar zaro Ido daga cen d'akin tace

"Dije kina Nan ko ta fara cenyeki"

Dije dafe cikinta tana dariyar fitar hankali cikin dariyar tace,. "Akuyata ce Inna ki fito ma ki gani da idonki"

Innar ta d'aga murya tace,. "WALLAHI in har kin ganni Lahira to kaini aka yi amman ba dai ace inje da kafafuna ba"

Baffa jin dariyarta ta yi yawa yasa ya zaci ko kukane take yi ya d'an bud'e k'ofar d'akinshi kad'an ya dan lek'o da idonshi d'aya jikinshi sai rawa yake yi yana makyarkyatar tsoro, aiko sai ga Dije ya hango kwance dafe da ciki tana dariyar keta.

Ya bud'e d'akin duka ya lek'o kanshi yace,. "Wai ke me yasa kike ja'ira yanzu ke duk wannan tashin hankali da kowa yake ciki ke dariya ma kika samu damar yi? To WALLAHI ki sani da ta shigo gidan da ke zata fara cin karo don Ni kafin ma infito cetonki kin zama Jan nama"

Dije ta rufe bakinta da dariyar da ta sub'uce mata tace, "WALLAHI Baffah k'arya ce kawai ake yi ba wata kura su Mune ne kawai Suka shirya komi"

Baffah ya zaro Ido ya fito d'akin duka yace

"Su Mune ? Ko dai su ke? To WALLAHI in dai har da gaske karya ce kuka shirya wannan karon ba ruwana da rigimar da kika janyowa kanki don ki sani ......"


Kafin ya k'arasa maganar sai gashi ko ya jiyo sautin haushin mutane a k'ofar gidan anata hayaniya, ana dad'i

"Yau Kam ya zama Dole a garemu mu d'auki mataki akan yarinyar nan"

Dije ta zabura da sauri tana rabon Ido ta Kai kallonta ga bishiyar itaciyar da ke tsakiyar gidan nasu, ta yi wurin aguje ta yi tsul ta haye saman itaciyar sai gata da kaiwa cen koli ta lafe luf tana sauraren jin irin matakin da za'a d'auka akanta yau kuma, don ita kanta tasan yau Kam ta tarowa kanta aradu da fad'i.




Dandano daga labarin Dije k'arangiya labarin barkwanci ne Mai cike da nishantarwa hadi da ilimantarwa a fakaice.





Akafta🤾🏻‍♂️






D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*




*Rangadi lalle Dije k'arangiya ta cafko jama'a Alhmdllh Ina godiya sosai Wallahi naji dad'in ruwan comments dinku akan book d'ina Alkhairin ALLAH ya Kai maku a ko'ina kuke fad'in duniyar nan luv u all💋*




*Lamba ta 2*



Baffah ya bi bishiyar da kallo cike takaicin ka haifi mutum baka haifi halinshi ba ya nufi k'ofar Gidan, sai dai ganin cincirindon mutane fal a k'ofar Gidan nashi kowane da abun dukanshi sai muzurai suke yi yasa shi dawowa da sauri yana sauke numfashin mai cike da tsantsar tashin hankali, aiko suka fara cewa

"Malam Buba ka fito da ita tun kafin mu shigo da kanmu mu janyota don kuwa Maigarin ne da kanshi yake nemanka tare da tijararriyar d'iyar taku"

Malam Buba ya fara had'a hannu waje d'aya yana fad'in,. "Don girman Allah ayi hak'uri da halin Dije yanzu haka Ni har yanzu ma ban ganta ba don ko Gida bata dawo ba"

Wani katoton bafaden Maigari ranshi a b'ace yace,. "Zaka fito da ita taje ta karb'i hukunci Koko sai mun shiga da kanmu mun fito da ita?"

Malam Buba ya marairece yace, "Ku yi hakuri don ALLAH duk da dai ni har yanzu ma bansan laifin da ta yi maku ba"

Bafaden ya zabura Kamar ya daki Baffah yace, "Yanzu duk guje gujen zuwan Kura da ake yi a garin nan kana nufin baka sani ba? To Bari kaji yanzu haka Uwardakin Maigari ta karye Kuma duk a sanadin yarka Dije, don haka Maigari ya bada umurnin a d'auko masa ita ko a raye ko a mace domin a ladaftar da ita"

Yana k'are maganar Baffah ya zaro Ido yace, "Don girman ALLAH kuyi hakuri amman Dije bata dawo gidan nan ba, idan kuma baku amince da maganata ba ku shiga na baku dama ku fito da ita"

Aiko kafin ma ya karasa maganar suka tureshi suka fad'a Gidan, Kai tsaye suka dinga neman Dije lungu da sak'o na gidan ganin d'akin Inna a rufe yasa suka zaci tana ciki, Aiko k'aton bafaden ya saka k'afa ya buge kyauren Inna da ke rakub'e tana salati don ta zaci ko Kurar ce ta shigo Gidan mutane suka biyota ana neman hanyar kamata, jin an bugo k'ofar yasa Inna rafka salati tace

"Wayyo Uwata wayyo Ubana zan biku ba tare da guzurina ba, wayyo ALLAHna ka taimakeni Kura zata yi man tsiya"

Inna ta make cen karkashin gadon bononta inda ta b'oye sai ihu take kwarmawa, jin motsin shigowar mutum yasa ta k'ara sautinta tana fad'in

"Yihhuuu Jama'a ku yo agaji tun kafin ta k'araso ta Kai mani wawa"

Baffah ya duk'o da kanshi ta karkashin Gadon inda yake jin sautinta, Inna tana had'a ido da kanshi ta zaci Kan kurar ne ta saka k'afa ta halbo wata fanteka dake ke karkashin gadon sai a fuskar Baffah, a zabure ya d'ago ranshi a b'ace yace

"Ke Mahaukaciya fito haka nan ba wata kura yarki ce ta janyo masifar don haka ga Maigari nan ya aiko a kamota"

INNA cikin wani sabon firgici tace

"Da gaske???"

A kufule Baffah yace,

"Karyar da na saba yi maki ce yau na k'ara kwatawa"

INNA cikin rawar jiki ta lallaba tana ture kwanukan da ta shige cikinsu ta samu ta fito, da kyar ganin Baffan baya d'akin yasa ta fito tsakar gidan, aiko sai gata da yin arba da mutane cike da gidan nasu Mata da Maza, cike da tsananin rudu tace

"Na shigesu jama'a Lafiya?"

Wata Yar tsohuwa tace,. "Ina fa Lafiya Dije ta janyo anyita jin raunuka a gari duk a sanadin rashin mutuncinta, ki je ki fito da ita tun kafin Maigari ya sa a d'auki hukunci akanku, daman ance d'ankuka Mai jawa Uwarshi jifa, to yau dai ta sake janyo maku abunda yafi na kullum"

Baffah cikin takaici yace, Na gaya maku bata gidan amman kunki amincewa"

Aiko daga cen saman itaciyar Dije ta kai iya wuya sai jin suka yi tace,. "Barsu Baffahna idan ma sunki amincewa su kasheni idan na sauko"

Aiko gaba d'aya suka d'aga Kai suna kallon bishiyar cike da tanbabar a'ina maganar take fitowa, Dije ta kurawa tsohuwar Ido tana maka mata harara tace,. "WALLAHI da kin cikani ta kanki zan diro Uwar tsugudidin tsiya"

Aiko a lokacin suka tabbatar da ashe ma saman itaciyar ta b'oye, Bafaden ya zo gaban bishiyar yace

"Ki sauko salun alun tun kafin a sare itaciyar duka ki fado ki kakkarye"

Dije ta yi saurin fad'in

"Yasin ba zan sauko ba duk Mai son in sauko ya hawo ya sauko dani, amman kusani duk Wanda yayi wautar hawa bishiyar nan to ina maku albishir ba zai sauko da Ido d'aya ba, don kuwa sai nasa aljanina ya zuke idon muga ta tsiya"

Aiko jikin kowa yayi sanyi saboda sanin halin wacece Dijen da hatsabibancinta, daga nan aka fara shawarar wa zai hau ya sauko da ita? Aka Kai karshe akan Baffahnta ya hau ya sauko da ita, ganin gidan sai k'ara dinkewa yake yi da mutane yasa shi yanke shawarar hawa ya sauko da ita ko don a samu rangwamen hukuncin da za'a yanke mata.

Aiko ya kama bishiyar zai hau kenan Dije tace,. "Jira in sauko Baffah ai dai Raina a hannun ALLAH yake duk cikinsu Babu mai ikon kasheni"

Baffah yace,. "Sauko a hankali to ai duk ke kika jawo komi muna zaman zamanmu kika d'auko muna abun magana"

Dije ta fara saukowa a...


Read / Download DIJE KARANGIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album