Join Our WhatsApp Group

A WANI GIDA Complete Hausa Novel Document by A WANI GIDA


A WANI GIDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28608



A WANI GIDA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 29, Jul 2023

Author: Nabila Rabi'u Zango ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 313.2 kb

File Type: txt

Views: 1248+

Download: 343+

Last download: 3 days ago

Description/Story: 🏡A WANI GIDA🏡


LABARI /RUBUTAWA
KHADIJA S. SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)


GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, wanda shiya aiko Annabi MUHAMMAD (SAW) da shiriya. Allah ya shiryemu baki daya ameen.


SADAUKARWA
Na sadaukar da dukkan wannan littafi ga al’ummar misulmai baki d’aya.

JINJINA👍👍👍
Jinjina gareku mahaifana, Inamai addu, ar Allah yarabamu lafiya ya saka muku da alkairi ameen.

TA DABAN CE😘😘
Aunty Ameena Khabir kina qaran qwarin gwiwa, Allah yaraya iyalanki.


GABATARWA
Wannan labari qirqirarren labari ne, banyishi dan ko wata ba, na yishi da fadakar, ilimantar, nishadantar, tsoratar da al’umma inason idanan kaga abinda yadace kayi qoqarin aikatawa domin gobenka, abinda nai ba dai dai ba kayi qoqarin gyaramin saboda na qaru wasu ma su qaru, Nagode🤝.


🏡A WANI GIDA🏡

🅿️1️⃣

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN QAI.



”Kai!.....Nidai naga ta kaina,kullum neman hanyar da zan samu farin cikin rayuwa nake amma inaa kullum baqin ciki ke kusantata nikam yazanyi ne naji dad’i?”

Hajiya NAFI ce taketa zance ita kad’ai kai idan baka luraba saikace ita da wani takeyi ba ita d’aya ba,miqewa tayi tafara zagaye d’akin tana bin ko’ina da kallo tare da yamutsa fuska tana jan dogon tsaki.

”Hajiya ! Hajiya!! ”kira ya doki cikin kunnuwanta aikam arazane ta juyo tana kallon me kirannata.

”Tsssummmmm, Har me zaki bani kike qwalamin wannan kiran? Ko kinmanta da yanayin danake ciki ne kikazo ki kuma d’agamin hankali?”

”A’a hajiya ba haka...”

”Rufamin baki bahaka bane me? idan ba haka bane tomenene? HAFSA tinbayauba na lura da take-takenki gaba d’aya kuma wallahi munkusa musa qafar wando d’aya dani dake tsuummmm”
Hajiya tayi tsaki sannan tafice tabar falon gaba d’aya.

”Ikon Allah! Lallai naga alamar nima saina tashi tsaye agidannan idan bahakaba to naga alamar Hajiya saita takani nikuma abinda bazan d’auka ba kenan”
Hafsa ta fad’a tare da miqewa itama tafice afalon.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Dad’ina dake LUBA bakya ganewa kullum idan anmiki karatu bakya d’auka kinta inda-inda kamar wadda taiwa sarki qarya”

”Haba HABI kema kinsan kaina yana ja sosai kawai dai kedince kullum abinda zaki zowa da mutum daban kinga dole kansa ya kulle ”

Luba ta bawa Habi amsa.

”Salamu alaikum!”
”Waalaikissalam”
Suka hada baki wajan amsa sallamar,Luba ce tamiqe da sauri tana fad’in,
”Lale Lale yarona sannu da zuwa yimaza kaje kace LARAI ta baka abincinka kaji”

”Tom mama ”
Yaron yafada yana fita sam baima kula da Habi da take zaune ba yau ficewarsa.
”Lallai Luba yaronnan yayi saurin girma tabd’i,uhummm koba Haneef baneba?”

”Uhummn kedai bari Habi wallahi ni kaina abin yanzu yafara bani tsoro,tin ana fad’a ina qaryatawa yanzu harna fara yarda,yaro shekara tara amma kamar me shekara sha biyar ko sama?”
”Ato agaskiya Luba kinemawa d’anki magani dan gaskiya ni ganinsama tsoro yake bani gaba d’aya gashi idan ya kalleni hantar cikinama kad’awa takeyi saboda tsoro”

”Habi Daman kinzo gidannan ne saboda ki qaran d’agan hankali?Dake zanji koda waccan Matsafiyar zanji?Niyau banyi farin cikin zuwankiba akan Haneef zan iya bada raina dan haka kificemin agida tinkafin raina ya b’aci”

Ta fad’a tare da nuna mata hanya alamar ta fice.....

Aikam ba musu sumsum tafice daga d’akin tana kallonta sama da qasa.

🤦🏻‍♀️Wayyo ni Luba meke shirin faruwa dani ne?
Nima lamarin yaronnan yana ban tsoro,kai gashi naga kullum abin gaba yakeyi dole na koma gurin QAURA naji kodai musanyamin yaro na yayine?
Tafad’a tana dafa kai tare da cizon le’be.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”KULU Wallahi tsoron shiga nakeji bakiji yadda gabana yake fad’uwaba”
”Haba HAFSA mene abin tsoro aciki nifa banajin tsoro kijima na fad’amiki ninan da kika ganni KAINUWA CE DASHEN RABBU dan haka ba wanda zai iya dani kinga ni ban wuri nahuce idan nafito nabaki labari”

KULU! KULU! KULU!!!......
Kira ya doki kunnenta,juyowar dazatai sukai ido hud’u da abba yana mata kallon tuhuma,waige-waige ta farayi nan ta lura ashe tini Hafsa ta gudu ta barta.
”Abba sannu da dawowa”
D’aga mata hannu yayi tare da fad’in,

”Kulu tinba yauba ina lura dake kaf mutanen gidannan ba wanda yatab’a zuwa wajannan saike,abaya na rabu dakene saboda wani tinani da nayi,amma yanzu na kura so kike ki tona min asiri to wallahi tallahi kinji na rantse miki koda wasa kika kuskura qafarki ta taka d’akinnan to dagaranar kitabbata na tsine mikj albarka na tsameki acikin ’ya’yana,kuma kisani ayanzuma idan wani yyaji wannan zancan to banyafe mikiba............✍️





Tsokaci kad’an daga cikin labarin 🏡A WANI GIDA🏡




’YAR GATAN MAMA✍️







More comments more typing🥰
🏡A WANI GIDA🏡

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

__________________________________________________
_________________________


🅿️2️⃣


Na sadaukar da wannan page din gaduk wanda ya karantashi😍😍





🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Kuma wannan maganar da mukayi dake yanzu idan kika bari wani yaji tom banya miki ba! nace banyafe miki ba, kulu inamai tabbatar miki zan iya yin komai dan naga na rufe wannan 6oyayyen sirrin nawa, Hauwa kulu kitina nifa mahaifinki ne idan baki rufamin asiriba wazaki rufawa? Dan girman Allah ’yata kibarwa cikin ki”
Abba ya qarasa fad’a yana mai had’a hannuwansa alamar roqo.
”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”abinda kulu taita maimaitawa kenan akan le66enta cike da tsoro, firgici, razani, fad’uwar gaba wanda suka ziyarceta lokaci guda, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ta sake fad’a tare da dafe qirjinta sanadin bugawar da taji yanayi, Menene Abba yake 6oyewa?
Abba zai tsinemin?
Ya salam..! ta fad’a dukda haka hannunta yanakan qirjinta jitake gaba d’aya kamar qafarta bazata iya d’aukan gangar jikinta ba, Menene Abba? menene? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tasake fad’a da qarfi akaro na ba adadi tare da d’ago da kanta sama, amma me? babu Abba babu dalilinsa ganin haka yasa tafara jan qafarta cike da rauni tafara takawa da niyyar tabar wajan.
Durqushewa qasa tayi da sauri sakamakon zugi, rad’ad’i da zafin da taji aqafarta, da sauri ta kalli qafar tare da riqewa bakin qofar wani d’aki dake kusa da ita taja jiki ta zauna inda idanunta ke zubar da ruwa kamar hawayenta zai qare, menene Abba yake iqirarin zai iya cireni acikin yaransa saboda shi?
Wannan wane irin sirri ne haka mai girma?
Ohhh!!! Ya rabbi ya rabb!!. abinda take nanatawa kenan ita ba zafin kwalbar data shigetane yake damunta ba A’a wannan sirrin na Abba shi ne yake damunta, wannan wane sirri ne da har Abba yake roqonta akansa?
Azaba ce ta isheta inda tasa hannu tare da rintse idanu tafara qoqarin cire kwalbar data shige cikin tafin qafarta, fad’in zafin da takeji yafi qarfin afad’eshi saboda yau jitake aduniya ba wanda yakaita jin zafi azuciyarta.
Bayan ta cirene taci gaba da tinanin sirrin da Abba yake 6oyewa dukda jinin dake zuba aqafarta bai d’aga mata hankali kamar yadda wannan sirri ya d’aga mata hankaliba.
~~~~~~~~~~
Hafsa ce taji shirun yayi yawa tintana jira ta fito harta fara tinanin kodai ba lafiyaba, hakanne yasa taji kozata mutu sai itama taje taga halin da ’yar uwarta take ciki.
Shigarta keda wuya ta iske halin da kulu ke ciki cikeda tsoro ta qarasa gabanta tare da dafa kafad’arta saboda taga yadda tayi nisa acikin tinani, d’an kwalin kanta ta cire inda tadage ta yaga tad’aure mata qafar dashi sannan tace ta dafata suka nufi d’akinsu.
Likitan gidan aka kira yazo ya duba qafar sannan yabata maganin dazata sha daga baya.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Mama ki taimaka mini wallahi da gaske nake maki mama ki taimakeni, ko bazaki temakeni ba? mama mutuwa zanyi ”

Hankali atashe Luba ta farka daga baccin da takeyi tare da kalle-kalle ko zataga Haneef amma me? Bayanan, tashi tayi da sauri ta nufi d’akinsa dan ta tabbatar lafiya lau ta bashshi, sauri-sauri take sakkowa daga benen tana daf da isowa falon qasa kenan fitilar gidan gaba d’aya ta d’auke, waige-waige ra shiga yi kozata ji makunnin fitilar, takai hannunta jikin makunnin kenan taji muryar muryar Haneef yana wani irin ihu me rikitarwa yana neman taimako muryarsa na shashshaqewa,cikeda firgici da tashin hankali mara misaltuwa ta nufi hanyar d’akinnasa dukda duhun dake d’akin wanda ko tafin hannunta bata iya gani, tana daf da shiga d’akin taji muryarsa asaman benenta yana qwala mata kira yana neman temakonta..........

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Nikuwa Nafi yaya zancen yarinyar nan?
Kinsankwa jiya ban iya bacci ba saboda yadda lamarin yarinyar nan ya tsayemin arai?
wallahi Nafi nashiga cikin tashin hankali”
Abba yafad’a yana kallon Hajiya Nafisa.
”Uhummm, Abba ai sedai haquri nima lamarin ya d’agamin hankali wallahi gaba d’aya gigicewa nayi ajiyannan”
”Haba.. Nafisa bafa nanata zance nace kiminba tambayarki abinda yafaru nakeyi”
Abba yasake fad’a da alama ya fara qosawa da zancen.
”Kasan mu mata ba kasafai muka fiye haquri da mazajenmu ba, itama haka taje taita wauta shi ne fa jiyan yace tazo gida zaizo to daga bayama saiya turo mata saqo yace wai tayi zamanta ya yanke alaqar auren dake tsakaninsu ”
Innalillahi Abba yaita ja kafin yace akira masa ita, Hajiya Nafisa da kanta ta tashi taje tayo kiranta .
”Ke...... Safiyya fad’amin menene ya had’aki da Mukhtar har ya sakeki? ko bakiji abinda nace bane? ”
Abba yafad’a cikin d’aga murya kamar zai rufeta da duka.
”Abba wallahi ba laifina bane ba shi ne da laifi ”
”bazaki fadaba kenan sai jikinki ya gayamiki ko”
Ya qara fad’i yana huci kamar wani zaki.
”Abba banso zan fad’a ba amma tinda kadage zan fad’ama, Abba tinda aka kaini gidan mukhtar kullum idan dare yayi akwai wani d’aki da tinda naje gidan baitab’a bari na shigaba, shi ne rannan nad’auki makullin d’akin bai saniba bayan yafita naje zan bud’e saigashi ya dawo yana ganina awajan shi ne fa yace wai na tawo gida zaizo gidan daganan kuma yace wai ya sakeni... ”
Ta qarasa fad’a tare da sakin kuka mecin zuciya.
”Tom naji Allah yasa hakan yazama alkairi ”Abba yafad’a yana ficewa yabarsu ad’akin, gani. haka yasa itama Safiyya tashi ta koma d’akinta na gidan.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Cikeda qololuwar tashin hankali Luba ta koma hanyar benen da niyyar tahau saikuma taga fitilara gidan tafara farfari atake wasu daga cikin qwayayen suka fara farfashewa fankokin d’akin suka d’auki wani irin qara kai sekace qarfe akasa ana bugunsu, toshe kunnuwanta tayi tare da sakin wata razananniyar qara tana mai rintse idanuwanta, idonta arufe tafara taka matattakalar da gudu-gudu saboda yanda takejin kukan Haneef ya qaruwa jitayi tana taka ruwa aqafarta mai danko bud’e idonta tayi domin taga menene awajan dukda tasan bazata gani ba sanadin duhun daya mamaye wajan gaba d’aya, amma me? ga mamakinta saita ga haske kamar duhu baitab’a zuwa wajan ba, wata razananniyar qara ta saki tare da toshe bakinta take qafarta ta fara rawa jikinta ya fara karkarwa inda ta sake ware idanunta dan ta tabbatar da abinda take gani............


’YAR GATAN MAMA✍️


More comments more typing🥰

*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

TUNATARWA!!!

LOKACI WANI ABUNE DA BABU ABINDA YAKAISHI GIRMA ACIKIN RAYUWAR DUNIYA BAKI D’AYA, DAN HAKA MU RIBACI LOKACINMU TIN KAFIN YA KUFCE MANA, ALLAH YASA MUDACE YARABAMU DA IYAYENMU LAFIYA👏.

🅿️3️⃣


Wata razananniyar qara ta saki tare da toshe kunnuwanta take qafarta ta fara rawa jikinta ya fara karkarwa inda ta sake ware idanuwanta danta tabbatar da abinda take gani... me zata gani?, Jini ne ke tawowa jikin matattakalar benen sai kace ana yanka raguna, duhu-duhu ta fara gani inda jiri ya fara d’ibarta kanta kuwa jitayi kamar and’ora mata dala da goron dutse tsabar nauyin da yayi mata, Jitai gaba d’aya d’akin yana juya mata kamar wadda tahau kumbo takasa koda motsi balle ta qarasa tahau saman tashin hankalinta ne ya qaru sanda ta lura jinin qara yawa yakeyi tamkar wanda ake zuboshi dafe kanta tayi tare da sakin qara mai qarfi ta fad’i awajan.
~~~~~~~~
”Hafsa!, nifa kamar qara nakeji abangarensu Haneef ”Kulu ta fad’a tana sauka daga kan gadon, ”A’a Hauwa kema kinsani sanin kankine bayau kika farajin iface-iface agidannan ba balle kitada hankalinki , kinga ni saida safe”Hafsa tafad’a tana gyara kwanciyarta.
”Haba Hafsa Mama Luba ce fa take qara kumama muryar ba tatabace itakad’ai, kai... wallahi nidai kozan mutu sainaje naga ko lafiya”tafad’a tana fita daga d’akin.
~~~~~~~~~
Gudu-gudu sauri-sauri ta sakko daga samansu ta fice daga bangarensu, Saurin da takeyi ne yai sanadin tsinkewar takalmin qafarta batai wata-wataba ta sunkuya zata d’auka amma me saita nemi takalmin ta rasa nan da nan ta kalli d’ayar qafartata amma saitaga warin aqafarta d’aya kuma babu, addu’a ta bud’e baki da niyyar tayi taji bakinta yayi mata nauyi, cikin qarfin hali da dakewar zuciya tad’ago domin taci gaba da tafiya kawai saitaga wasu mata sun giftata da sauri suna sanye da jajayen riguna ajinkinsu hannayensu na d’auke da wani abu wanda ta kasa tabbatar da menene, tom suwaye wad’annan?, menene ahannunsu?, ina kuma zasuje?, ta tambayi kanta tare da qara saurin tafiyarta da niyyar saita bisu taga ina zasuje kuma taga suwane ita sam tama manta da abinda yafito da ita da tsohon darennan.
Tafiya sukeyi tana binsu gashi sam sunqi su waigo koda sau d’ayane, Batare da tsoro ko tinanin wani abu zai iya samuntaba ta rinqa binsu, tafiya suke kamar wad’anda zasu bar gari batai auneba sai ganinsu tayi awani wawakeken daji mai matuqar duhu tare da manyan bishiyu bata iya ganin komai giftawarsu tsayawa tayi tana kalle-kalle lokacin data nemesu ta rasa sun 6ace mata 6at ko wulqawarsu bata gani tana cikin dube-dube idonta yakai kan wani wawakeken kogo me babbar qofa kuma tana hango haske jajir acikinsa, batare da wani tinaniba taji lallai saita shiga wannan kogon taga menene aciki, wata irin wutace keci gungu guda kamar wutar daza’a dafa mutane acikinta banda iface-iface babu abinda kunnuwanta keji , tsoro bai kamataba saida taga mutane suna wucewa d’aya bayan d’aya kuma da alamun dukkanninsu mata ne kowacce idanunta tamkar gwarwashi saboda ja baka iya gane fuskokinsu dan duk wadda ta wuce saidai kaga fuskarta baqiqqirin jan idanunta kad’ai kaje hangowa, hankalin kulu ne ya tashi amma hakan bai hanata qara zura jiki cikin kogonba bakinta d’auke da addu’a wadda sai ayanzu bakinta ya iya karantawa, tintana leqawa ahankali abu har ya kaita ga ta shige cikin kogon, wata macece mai matuqar qiba da tsayi ta tawo zata wuce daf da inda kulu ke tsaye tana saqe-saqe niyyarta idan matar zata wuceta tasa hannu tacizge baqin qallen dake fuskarta, batare dataga zuwan matar guntaba kawai saiji tayi taja hannunta ta qarfin tsiya tayi-tayi ta qwace amma matar tafi qarfinta janta take iya qarfinta suna tafiya batare data waigoba hai saida.....


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Lallaima Mukhtar ya d’auko ruwan dafa kansa harni zai sakarwa yarinya saboda tana qoqarin ganin wani banzan sirrinsa wanda bashi da ma’ana?, nikam indai na amsa sunana NAFISATU to wallahi ni da kaina saina binciko wannan sirrinnasa ”, hajiya Nafi ke fad’a bayan Safiyya ta tashi daga haka itama tashi tayi tad’au abinci...


Read / Download A WANI GIDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album