Join Our WhatsApp Group

SARAUNIYAR KYAU Takun Farko Complete Hausa Novel Document by SARAUNIYAR KYAU Takun Farko


SARAUNIYAR KYAU Takun Farko

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 163789SARAUNIYAR KYAU Takun Farko

Reading Time: 13 Hours

Added On: 24, Apr 2024

Author: The Nainarh KD ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : LAFAZI WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 08081129487

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 926.66 kb

File Type: txt

Views: 280+

Download: 342+

Last download: 1 day ago

Description/Story: *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


💓*SARAUNIYAR KYAU*💓

👑_(The Glam Queen)_ 👑

```Takun Farko```

Story & Written By:

*_The Nainarh KD_*

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._


*_Special Thanks to:_*

- Official Muhammad Aufan Mahmoud
- Afeefarth Abubakar Mai Kyau
- Zaynerb Abubakar Mai Kyau
- Aasief Mai Waje
- Bardia Fazzan
- Jieddarth Juraej Komai Naga
Love you all 💞💖💘💗💝


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*Page 1&2*


Abuja, Nigeria

Mai Kyau District

Doguwa ce dirarra ƙyaƙyawa ajin farko wacce idan aka ce kyau to fa ana zuwa kanta an rufe ƙofar kyau. A shekaru ba za ta haura twenty years or twenty one years ba a duniya.

Akwai ta da diri wanda a Turance ake kira da Coca Cola Shape, tana da manya-manya kuma dara daran kyawawan fararen idanu masu shining, masu egg shape. Yanayin launin kwayar idon nata su ba blue color ba, haka ma ba green color ba sannan kuma ba ash color ba. Su dai ga su nan yanayinsu sky purple masu matuƙar shining da ɗaukar hankalin duk wani mahaluki.

Akwai ta da wasu kalar laɓɓa ƙanana sirara jajayen gaske da su, ga shape nasu gwanin ban sha'awa da burgewa. Daɗi da ƙari ga ɗaukar hankali.

Hancinta kuwa wani kalar dogon hanci ne wanda ya zauna daidai a kykkyawar fuskarta ga shi ɗan daidai. Tsayawa bayyana yanayin kyawunta ya zama kauyanci. Ta hada dukkan wasu suffofi da mace ke bukata don jan hankalin namiji.

Tana sanye cikin wasu dakakkiyar doguwar gown ƙirar Malaysia, wacce ta kama jikinta ɗas ta zauna. Gown ɗin mai gajeren hannu ce saboda haka sai ta ɗaura after dress sky purple mai adon stones masu bala'in sheƙi, ita kanta rigar da ke jikinta sky purple ce doguwa har ƙasa.

Dogon gashin kanta wanda yake asalin dark brown, ya sha gyara ta tufke shi da wasu shegun ribbon masu masifar kyau da tsada guda uku wanda hakan ya ba dogon gashin damar zubo mata har tsakiyar gadon bayanta.

Ga wani yalolon mayafi da ta yafa gefen kafaɗarta, fuskarta kuwa tasha light make-up, ta yi kyau sosai. Ga wani haɗaɗɗen Wrist-Watch da ke saƙale a hannunta. Yanayinta ta fi kama da mutane marasa hayaniya.

Tsaye take gaban dress mirror tana ƙoƙarin fesa wani perfect perfume mai masifar kyau da daɗin ƙamshi mai sanyaya ran bil-adam. Turo ƙofar katafaren haɗaɗɗen bedroom ɗin da take ciki aka yi. Ba tare da ta juya ba sanin da ta yi kowace ce ta shigo, ta ce cikin wata kalar murya mai masifar daɗin sauraro ga ta siririya yanayin sautin ta kamar ana busa sarewa.

"Oh my lovely dad mister mai kyau, ɗiyarka tana so ta fa takura mini. Yanzu zan iya cewa fa na fasa zuwa wajen birthday party ɗin nan kuma ta zauna, kin san da wannan tunda da ma can satar hanya za mu yi zuwa birthday ɗin saboda an ga daddy ba ya nan."

Ta yi maganar like a little girl kuma cike da tsabar shagwaɓa wacce ba ƙaramin kyau hakan ya ƙara mata ba, sannan kuma maganar duka da ta yi tana yi tana hutawa ne.

Dariya mai sauti wacce ta shigo bedroom ɗin tayi, sannan ta ce, "My Feefarh! Ba na son rashin mutunci fa, sai da aski ya zo gaban goshi za ki ce kin fasa haba ɗiyar mister mai kyau! Kar ki yi wa Zahra haka mana, ko dai kin manta wace ce ita gurinki?"

Mayar da perfect perfume da ke hannunta ta yi zuwa ma'ajinsa saman haɗaɗɗen dressing mirror ɗin sannan ta juyo gabaɗayanta tana fuskan tar budurwar da ta kammala yi mata magana.

Kawar da zancen zuwa birthday ɗin ta yi da faɗi, "To ya ya na yi kyau kuwa kamar SARAUNIYAR ƘYAU ta duniya?" Ta yi maganar cike da mafificin nishaɗi tana dariya.

Wannan karon ƙayataccen murmushi mai ɗauke da sauti mai cike farinciki da nishaɗi, budurwar ta kuma yi a karo na biyu tun da ta shigo sannan ta zauna gefen gado tana fuskantar ta....

A hankali ta fara magana ita ma cikin lallausar muryarta, "My Feefarh tawa ta kaina kin san ai shi mai kyau ba ya buƙatar tambaya a kan kyansa, da ganin shi kai ka san mai kyan ne shi, yanzu kamar ke dube ki. Kamar sananniyar jarumar India 'Anu Emanuel', dogon hanci mai kyau da tsari kamar Chinese actress 'Janine Chang'. Ga ɗan ƙaramin siririn baki naki kamar a gurin wannan ɓarumar Korea 'Kim Sohyun'. Gashinki tsayi da yawa ga shi asalin dark brown kamar na fittaciyar jarumar Korea ɗin nan mai suna 'Park Shin Hye'. Ga fatarki mai masifar sheƙi da ɗaukar hankali kamar na..."

Ai tun kafin ta ƙarasa faɗin abin da take niyyar faɗa budurwa ta yi saurin tarar numfashinta da fadin, "Auntie Leesarth, ina ga wannan yabo kamar wata SARAUNIYAR ƘYAU ta duniya ya yi yawa gare ni."

"E, sarauniyar kyau ce mana tunda dai all most one month ya rage daga nan za a ga sarauniyar ce ko kuwa dai..."

"Oh bari dai na yi shiru kawai tunda naga kamar Ba a so na yi maganar." Cewar wata ƙyaƙyawar matashiyar budurwa da ta shigo bedroom ɗin, ita ma tana rufe bakinta sannan ta canza maganar da cewa, "Ku yi ku fito mu tafi birthday party ɗin nan tun kafin daddy ya dawo fa."

Ta yi maganar ne tana zare manyan idanunta, wanda ba komai ya sa ta yi saurin sauya maganar da ta yi niyya ba, fa ce hararar da Haleesarth ta antaya mata, ba tare da ɗayar budurwar ta ankara ba.

Miƙewa Haleesarth ta yi tana faɗin, "Ai duk ga wacce duk ta bi ta ɓata mana Lokaci nan da kwalliyarta nan sai ka ce wacce za ta je wajen gasar BRITISH QUEEN."

Ta yi maganar ita ma tana antaya wa budurwar da still har yanzu tana nan tsaye gaban mirror wata uwar harara amma fa ta wasa.

Dariya ta yi sannan ta ce' "To mu je ba don halayenku ba, tunda dai na riga da na shirya." Ta faɗa tana yafa veil ɗinta da ta cire tare da ɗaukar haɗaɗɗiyar handbag ɗinta mai shige da kayan jikinta wato sky purple. Gabaɗaya waje suka yi, har sun fito ƙayataccen falon daya gaji da haɗuwa ta ko,ina fes-fes.

Wannan budurwar ta tsaya tana bin ko'ina na falon da kallo ko za ta hangi wacce take nema, sai dai har ta yi waige-waigenta ta ƙare ba ta ga wacce take da muradin gani ba a katafaren falon.

Juyowa suka yi suna kallon ta cike da ƙosawa Haleesarth ta ce, "To yanzu kuma mene ne ya faru kika tsaya kina ƙare wa falon kallo kamar baƙuwarsa?"

Ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ina anti Zainab take? Kash damn it oh my God!"

Da sauri ta juya gabanta na mugun bugu, ba ta tsaya jira ko saurarar amsar da za su ba ta ba, ta nufi wani ɗan madaidaicin korido bedrooms biyu ne gurin, hannu ta kai da niyyar knocking ɗaya ciki wanda yake ɓangaren dama abin mamaki a buɗe ƙofar take.

Shiga ciki ta yi da sallama ɗauke saman laɓɓanta, ba ta ga kowa ba a ciki, saboda haka sai ta nufi hanyar bed. Tsayawa ta yi cak tana ƙarewa bedroom ɗin kallo sama da ƙasa gabas da yamma kudu da arewa, gabaɗaya a mugun hargitse yake kamar ba mutum ke rayuwa ciki ba, sai ka ce ba ɗazun nan yake tsaf-tsaf ba.

Pillows a ƙasa shi kansa bedsheet ɗin a ƙasa shi ma yake da alama an sha bidiri cikin bedroom ɗin. Daga can ƙarshen bangon ɗakin kuwa wata ƙyaƙyawar budurwa ce baje saman tiles na ƙofar shiga toilet, ga kwalabe a gabanta sun kai kala uku duka na Whiskey.

Da sauri ta ƙarasa kusa da ita, "Zainab, Zainab, anti Zainab! Please tell me! What happening to you? Kwalba kuma me kike yi da waɗannan kwalaben haka?"

Gabaɗaya ta bi ta ruɗe ta fita hayyacinta sabodaa tashin hankali, sam ƙwaƙwalwarta ta gaza tuna mata cewa yau ɗin ranar da suke ranar Valentine's Day ce, ranar da ta kasance wacce Zainab ba za ta taɓa mantawa da ita ba har abada kuwa a rayuwarta.

Zainab ba ta amsa mata ba sai ma kokarin kafa kwalbar Whiskey da ke hannunta take a baki, da sauri ta kwace kwalbar cikin kunar rai.

Ta fara magana, "Wai anti Zainab sau nawa zan faɗa miki cewa Shannon giya na da matukar hadari ga lafiya? Amma ba kya ji. Ba ma wannan ba, shin ba kya tsoron fishin Allah ya sauka kanki?"

Cikin muryar mashaya Zainab ta ce, "Haba my kanwa Afeefarh, na faɗa miki ba yin kaina ba ne gabaɗaya jikina ji na nake kamar ba ni ba. Ni ma fa so nake na daina wannan mummunar halayyar ta dabbobi, amma hakan ya ci tura na kasa. Please Afeefarh ki rabu da ni wannan rayuwa ta ce kuma kaddarata ce."

Cike da tsabar tausayawa, matashiyar budurwar wacce Zainab ta yi mata kira da Afeefarh take kallon yayarta Zainab wacce kaddarar soyayya haɗe da son zuchiya ya jefa ta cikin wannan mummunan halin.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta miƙe tsaye tana bin ƴar uwar tata da kallon tausayi ta ce, "Anti Zainab ɗita! Bari na kira anti Sa'adah ta gyara miki bedroom ɗin amma please kafin ta zo ki taimaka ki tashi ki kwashe wadannan kwalaben kuma a kullum ina kara tuna miki cewar ki kasance mace mai yawan yarda ya kaddara a duk ta inda ta zo miki sannan ki kasance mai juriya kin ji my anti? Ni yanzu zan tafi saboda za mu ta fi Birthday Party na Zahra da navyi miki maganar tun last sai mun dawo."

Tana gama faɗin haka ba tare da jiran ta bakin Zainab ɗin ba ta fita daga bedroom ɗin.

Katafaren aljannar duniyar falon ta dawo sannan ta karisa gurin Haleesarth da ke tsaye tsakiyar falon, gabaɗaya ta gama tunzura da ɓata musu lokacin da Afeefarh ɗin take.

Ba tare da Afeefarh ta kula complain ɗin Haleesarth ɗin ke mata ba ta fita daga falon zuwa farfajiyar katafaren gidan ta karisa parking lot da ke shaƙare da manya-manyan motoci na alfarma a fake..

*SARAUNIYAR KYAU*♥


_(The Glam Queen)_👑
```Takun Farko```Story & Written By:


Khadeejarth Sabi`u Yahyah


*_The Nainarh KD_*
_In dedicated to my dear Classmates Science G.S.S.S BELE ROAD_*Page 3&4*


Sautin dariyar da ake ɓaɓɓakawa ne yasa ta tsaya cak da tafiyar da takeyi,a hankali ta juyo gefan damarta ta saitin da dariyar take fitowa,ɗan zaro kyawawan idanunta tayi waje baki a hangame da mamaki ganin wa`inda suke wannan dariya haka kamar babu gobe..

Su bakwai ne,dukansu sanye cikin kayan ma`aikata Launin black and white suit,daga inda kowannen su yake tsaye akwai rata da ɗan uwansa,domin suna tsaitsaye ne tsayuwa irinna ma`aikatan tsaro wato {ESCORT} wasu daga cikin su ma Jami`ai ne na ƴan sanda wa`inda aikin su shine tsaron gidan,Dariya kawai suke ɓaɓɓakawa kamar masu cutar hauka,domin wasu daga cikin su ma harda hawaye saboda tsaban dariya,saidai da ganin yadda suke dariyar zaka fahimci na dole ne..


Hii Afeefarh wai menene kike kallo haka ne,ma`aikatanne baki taɓa gani ba,ko kuwa dai akwai sabo ne cikinsu,da kika tsaya haka Like a Gunki kina kallon su?....

Da sauri afeefarh ta juyo tana kallon haleesarth da tayi maganar hankali kwance tana ƙoƙarin buɗe tsadaddiyar mota ƙirar Bugatti, launin sky purple ta shiga..


Zuwa yanzu ta fahimci komai ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "a`a bawai kallon su nake ba dan ban gane wani ba,ko naga sabo cikin su, kallon su nake ganin yadda suke wannan dariyar da alama ɗaya daga cikin ku kodai ke,ko kuma LAILAH wata ta aikita haramci."

Eh kina da gaskiya wannan dariyar da sukeyi da akwai dalilinta kuma lailah ce sila bawai ni ba.Haleesarth tayi maganar tana mai ya mata nuni da lailah data iso wajen tana baza ƙamshi cikin takun isa da gadara...

menene kuma naji ana Lailah ce sila gani nayi ba zasu taɓa bari mu fita cikin daɗin rai ba shiyasa kawai nayi abinda ya kamata dasu....

Abinda ya kamata fa kikace hakanne abinda ya kamata lailah are serious,mutane ne fa,waima tukunna menene abinda kika musu ne?. Afeefarh tayi maganar tana danne ɓacin rai dama cikin sa take tun lokacin da taga halin da zaynerb take ciki....

Haba afeefarh menene na ɓacin rai da fushi kuma?,naga ma`aikata ne kuma a ƙarƙashin uba suke samun na ci da sha, da kike maganar menene abinda nayi musu,naga kema likita ce kama ta saboda haka kinsan abinda nayi, kawai LAUGHING_GAS na fesa musu mintuna ƙalilan zasu ɗauka suna dariyar bazai cutar dasu ba nayi miki alƙawari...

Ɗan jim afeefarh tayi tana kallon lailah da tayi maganar hankalinta kwance tana ƙoƙarin shiga motar gidan gaba, daya ke itace zatayi driving nasu. ..


Allah ya shirya ki lailah muguwar gidan mu,afeefarh tayi maganar cikin ƙyaɓe fuska da ɗan hararar lailah ɗin domin kuwa batasan abinda zatace mata ba,tasan wannan kaɗan daga cikin halin lailah ne, wato mugunta..

Madam nace ina zaku tafi ba tare da kunyi min magana ba mu shirya motoci kinsan dai fitarku ku kaɗai babu guards akwai hatsari ko?..

Fasa shiga motar afeefarh tayi ta juya tana kallon mahalukin da yayi maganar,saida gabanta yaɗan faɗi ganin wanda ke tsaye cikin black suit yana kallonta,ba kowa bane fa ce SALSA ɗaya daga cikin manyan ma`aikatan gidan zama`a iya kiransa da shugaban gabaɗaya ma`aikatan gidan.SALSA dai wani jibgegyan qaton Arne ne ɗan asalin ƙasar Philippine qato ne mai qirar samudawa,wanda wannan ƙirar tashi ne tasa gaban afeefarh bugu, ai dole domin kuwa jinsa yake shida qirar sa kamar basamude...

Rasa abinda zatace mishi tayi tsawon minti ɗaya,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara magana kamar haka...

"Kaga mai ƙirar samudawa tun wuri ka bari mu tafi tun muna mu kaɗai,kafin raina ya ɓaci"tayi maganar cikin haɗe gira kuma da hausa dama da gangar tayi sanin da tayi bayajin hausa,domin maganar da yayi mata da farko ma da turanci yayi..

Kinga madam koma menene zakice saidai ki faɗa dole tare zamu tafi domin alhakin kula da lafiyarki Boss ya damƙa a hannun mu,saboda haka koma miye zakice saidai ki faɗa dan tare zamu.....

Tunda haka ne, na fasa tafiyar kuma kasa ido zakaga abinda zai biyo baya, badai ka hanani fita ba,daddy zan kira na faɗama kasani daga yau,kabar aiki a gidannan tunda dani zakayi compromise.....

Tayi maganar tana kashewa lailah ido ɗaya sannan ta fara yunƙurin saka hannu a handbag ɗinta tana ƙoƙarin ciro wayarta...

Murmushi lailah tayi sannan cikin ɗan zaro ido da ɗaga...


Read / Download SARAUNIYAR KYAU Takun Farko

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album