Join Our WhatsApp Group

SANADIN KADDARATA Complete Hausa Novel Document by SANADIN KADDARATA


SANADIN KADDARATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 47137



SANADIN KADDARATA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 07, Feb 2024

Author: Mhiz Innocent ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08124818273

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 262.42 kb

File Type: txt

Views: 388+

Download: 209+

Last download: 1 day ago

Description/Story: *♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to DON ADNAN'S destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV

Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi ta timmus salihat 🥺🥰 Allah ka qarawa Annabi daraja 🤲


Bismillahir rahmanir raheem


Free page_1

..........Garin a lumshe yake kasancewar lokacin damuna ne kuma ga yanayin safiya, iska ce me dadi take kada duk mutumin dake a waje harma da wanda yake a daki dan sosae ake iska, safiya ce sosae bayan asuba kenan wanda se a lokacin garin ya fara haske, mutane jefi_jefi na wucewa, wasu daga masallaci suke, wasu kuma harkar gabansu ce ta fito dasu.
Tafiya takeyi babu tsagaetawa dauke da goyo a bayanta wanda ke daure da wani kyakykyawan farin towel, sedae na kaasa fahimtar a yanayin da take ciki, dan kuwa ita ba sauri takeyi ba kuma ba'a hankali take tafiya ba, wani lokacin idan ta wuce ta wani wajen wasu mutanen kan juya su kalleta su cigaba da harkar gabansu, a hankali nakae kallo na zuwa qafarta da iska ta kada zaninta har hakan ya bashi damar dagawa, jini ne busashshe a qafarta ta, komawar zanin inda yake ya bata damar cigaba da tafiya ba tare data kalli ko mutum 1 daga cikin masu kallanta ba, bata tsaya ko'ina ba seda taje wajen wani tudun yashi dake ajje waje guda sannan ta fara qoqarin kwance towel din dake bayanta, hakan ne ya sake bani damar ganin jinin dake kwance akan fararen qafafunta, sedae ita da alama bata damu da hakan ba dan kuwa cigaba tayi da kwanto abinda ke bayanta...dai_dai lokacin wasu mutane su 2 mace da namiji suka fito dattijae, dattijon na bayan matar saying

" Ae dae kya yi da jiki mu isa da wuri.. Kinsan dae.." Be kae ga 'karasawa ba ya hangi wata matashiya na kwanto abu daga bayanta, quri yayi cikin hasken farin watan daya gama washe garin yana kallanta bakinsa na rawa ya furta

"Jirani anan, yau nake ganin wani ikon Allah " ya fada yana yin gaba, kamar wanda aka tsikara se kuma ya juyo ya kalli matar yace

" Aff! Kar nayi wani abun ya zama laefi, ki kula da matar nan don Allah, bari naje na sanarwa me gari tukun na " be jira tace komae ba yayi gaba, tsohuwar ta kalli garin babu kowa se ita se matar, seta maeda hankalinta kan matar wadda ta gama kwanto abinda ke bayanta, wata cute baby ce a cikin towel din wadda ke bacci calmly babu abinda ke damunta, bata kalli fuskar babyn ba bayan ta sakko da ita kawae ta ajjiyeta a wajen sannan ta miqe, tsohuwar tayi wani yunquri tayi baya tana kiran sunan Allah hango jinin da tayi a qafar matar kuma gashi ta ajje jinjinniya a wajen and not minding ga wata halitta na kallanta, binta da kallo tsohuwar tayi harta wuce ta gabanta tayi bakin titi sannan ta maedo da hankalinta kan yashin tana sakin wata gauruwar ajjiyar zuciya, yayinda matar ta cigaba da tafiya abinta harta kawo titi, tana qoqarin tsallaka titi, dae_dae lokacin da wata mota qirar taxi tazo wucewa and matar kuma na qoqarin wucewa ta tsakiyar titin, me motar yayi iya bakin qoqarinsa wajen ganin ya riqe steering motar tasa, sedae ina Allah ya riga ya qadarta, seda yayi gaba da matar wadda a lokacin ta fadi qasa warwass alamar babu rae a jikinta.........


.....Cikin sauri wannan tsohon mutumin suke tafe tare da yaron me gari zuwa wajen da abin ya faru, tsohon na gaba yayinda yaron me garin yake biye dashi har suka qaraso wajen, basu tsaya ko ina ba se wajen yashin nan, ganin alamar matar bata nan ya sanya Malam Inuwa (tsohon) ya kalli matarsa Gaje yace cikin rashin fahimta

" ina matar take ?

Gaje da tun dazu tayi mutuwar tsaye, ga zafin ciwo kuma ga tsoratar da tayi se a lokacin ta iya dagowa ta kalli malam Inuwa sannan ta tattaro wasu kalamae daga bakinta tace cikin in'ina

"Ta..tayi nan" ta fada tana nuna musu hanyar data bi ba tare data kalli inda take nuna musu ba, yaron me gari yayi gaba yana kallan inda gaje ta nuna wato hanyar titi, yayi iya duban da zeyi a titin shi dae bega kowa ba, se mutane tsilla tsillah da suke wucewa suma kuma maza ne, ta6e baki yayi yana juyowa ya qaraso ya kalli gaje da malam Inuwa yace

"Fisabillahi malam Inuwa da girmanku kuna irin wannan abun, yanzu ni gashi an tashe ni daga baccin da nake qoqarin komawa ba tare........" Maganar tasa ta katse sanda wani sautin kukan jariri ya karade ilahirin wajen da suke, Seya zabura yana juyawa ya kalli inda yake da tabbacin daga nan ne kukan yake fitowa, gaaje ta hadiyi yawu da qyar tana fadin

"Wlh matar ce ta ajjiyeta, duk yadda akayi aljana ce, malam karkaje !! Ta fada tana kallan malam Inuwa dake qarasawa saman yashin, Bismillah malam Inuwa yayi, yaron me gari dae na biye dashi a baya yana kallan ikon Allah, malam Inuwa yakae hannunsa inda yaga towel din ya sakeyin bismillah sannan ya dauko ta

"Innalillahi! Innalillahi" yaron me gari ya fada yana yin baya ganin da gaske jinjirin ne a hannun malam Inuwa se tsandara kuka yake, Malam inuwa ya kalli jinjirar dake cikin towel wadda a sanadiyar budewar da towel din yayi yasa ya fahimci ko kaya babu a jikinta, Seya dauke kae ya kalli gaje yace

"Kizo mu wuce wajen me gari"

Ita dae gaje bata iya sake cewa komae ba, ta bari seda su malam sukayi gaba sannan ta bisu a baya, binsu kawae take kamar wata doluwa bata cewa komae, motsi kadan seta dan leqa ta kalli jinjirar da malam ke riqe da ita seta cigaba da tafiya, shima dae yaron me gari yana daga gefen malam tambayoyi fall a ransa, a haka har suka qarasa gidan me gari. Yaron me gari yayi sallama a gidan, uwar gidansa da bata koma bacci ba kasancewar gari yayi haske sosae tana tsakar gida tana hada wuta taji sallamar yaron me garin, seta amsa sallamar tasa tana dorawa da fadin

"Abdullahi lafiya dae koh? Seda yayi shiru kadan sannan yace

"Ehh toh, idan dae babu damuwa don Allah a taso mana me gari" Mamaki ya qara kasheta amma seta barshi kawae tace

"Toh bari in masa magana, Allah dae yasa lafiya" daga haka ta wuce dakin me garin....

Suna nan tsaye a qofar gidan me garin wanda wajen ya kasance rufaffe ne samansa, gaaje na gefe har lokacin qirjinta bebar bugawa ba kawae dae qarfin hali take, yayinda malam Inuwa shima har lokacin yake riqe da jinjirar, Mintuna wajen 5 sega me gari ya fito daga cikin gidan nasa yana kallansu su duka, Abdullahi ya zube a wajen yana fadin

"Barka da safiya yalla6ai"

"Barka ka dae abdullahi" me gari ya fada yana kallan malam Inuwa fuskarsa fall cike da alamomin tambaya, malam Inuwa ya matsa suka gaesa cike da ladabi sannan yace

"Wato ranka ya dade wata magana ce me muhimmanci ta kawo mu, kaaga wannan 'yar ? Ya fada yana sakko da ita daga kafadarsa sannan ya Dora da

"Yanzun nan mun fito zamuje asibiti, saboda muna so muyi sammako..."

"Kae abdullahi, shiga ciki ka samo mana tabarma" me gari ya fada yana kallan abdullahi, Abdullahi ya miqe ya shige gidan, can se gashi ya fito da tabarmar ya shimfida ta anan qofar gidan kasancewar ke6antaccen waje ne, Malam Inuwa ya nemi waje ya zauna bayan me gari ya zauna, ita kuma gaaje dama tana gefe tun dazu, Bayan me gari ya zauna ya kalli malam Inuwa yace

"Ina jinka" Jin haka ya sanya malam Inuwa dorawa da fadin

"Ranka ya dade lokacin da muka fito se naga wata matashiyar yarinya da goyo a bayanta ta hau kan yashin dake qofar gida na, toh ranka ya dade kasan sha'anin garin nan, abinda yasa kenan nacewa me daki na ta jira a wajen ni kuma zanzo in kiraka ko wani wakilinka, toh da nazo shine na tafi da abdullahi kasancewar ance mana shigowarka gidan kenan, sedae kafin komawarmu har ita yarinyar ta gudu tabar jaririyar, ga me dakina can ita zata qarasa bayanin" Me gari dae kallan malam Inuwa kawae yake cike da mamakin zancen nasa, se kuma ya kalli gaaje yace

"Bismillah" ya fada yana nuna mata kan tabarmar, a hankali ta qaraso ta zauna kan tabarmar kanta a qasa ta fara magana

"Yalla6ae bayan tafiyar malam, ina tsaye ina kallan matar yadda nasan zata iya gani na, dan nasan idan ta ganni zataji tsoro ta fasa aekata abinda tayi niyya, sedae ga mamakina ko gezau batayi ba sanda ta ganni, ta ajiye jaririyar tayi tafiyarta, ranka ya dad'e abinda ya bani tsoro kenan yasa na kasa tsayar da ita dan nayi tunanin ko aljana ce" me gari yaja numfashi kafin yace

"Yah salaam, Allah yasa dae ba rabota akayi da iyayenta akazo aka yarda ita ba"

"Wa ?? Wallahi ranka ya dade wannan data yarda ita itace ta haefeta, zan iya dafa qur'ani akan abinda na gani wallahi, dan kuwa dukda na tsorata hakan be hanani ganin jinin dake qafarta ba, ba sau 1 ba ba sau 2 ba, kuma indae ba qarya nayi ba jinin haehuwa ne, dan da alama sabuwar haehuwa ce, yalla6ae duk yadda akayi irin masu haefar shegun nan ne suje su jefar dasu kafin kowa ya ankara da hakan shiyasa......"

"Ya isa haka" me gari ya dakatar da gaaje daga bayanin da take sannan yakae hannu ya kar6i jinjirar dake cikin towel tayi shiru abinta tana bacci hankali kwance, kyakykyawa da ita fara sol, dukda sabuwar haehuwa ce hakan be hana dogon hancinta bayyana ba da dan qaramin bakinta wanda ta kama qasan lips din nata a cikin bakinta, me gari ya kalleta cike da tausayawa yana kallan yadda ko kaya ba'a saka mata ba haka zalika ga bushashshen jini jini a jikinta wanda hakan ze alamta maka da ba'a dade da haefarta ba, haka kurum yaji tausayin yarinyar ya kamashi, yarinyar da bataji ba bata gani ba, an haefeta da dattin zina, tunda yasan dae duk d'anda aka haefa na sunnah babu yadda za'ae uwar data haefeshi ta yadda shi, sedae waladiz zina din tunda ba sau 1 ba ba sau 2 ba ya saba kar6ar irin case din kuma daga baya idan akayi bincike se a gano cewa yaron shege ne, seya kawar da wadannan tunane tunanen ya juyo ya kallesu su duka yace

"Kuma ba kiga inda matar tayi ba" gaaje ta girgiza kae

"Wlh ranka ya dade, rudewa tasa banga inda tayi ba amma dae tabbas titi tayi" Me gari ya gyada kae yana jinjina al'amarin sannan yace

"Shikenan zaku iya tafiya, zan saka a bincika min, idan ba'a samu 'kwa'kw'kwaran abinda zamu ri'ka ba to shikenan semu kaeta wajen 'yan sandan cikin gari, duk suka amsa da "Toh Allah ya qara girma" sannan suka miqe suka wuce.
Me gari ya shiga gidansa da sallama, har lokacin uwar gidansa na tsakar gida tana sarrafa musu karin safiya, cike da mamaki ta miqe daga gaban murhun tana kallan me gari sedae ta kaasa cewa komae, ganin yanayinta ya tabbatawa me gari tana buqatar qarin bayani ne dan haka cike da kulawa yace

"Ajjiye abinda kikeyi kizo kiji" Ae bata koma ko'ina ba tabi bayan me gari daya shige dakinsa ya nemi waje ya zauna, itama ta zauna, kafin tace komae me gari yayi mata bayanin duk abinda gaaje ta fada masa, Uwar gidan nasa ta girgiza da jin abinda ya fada din, idanunta har sun ciko da 'kwalla ta qarasa ta kar6i babyn tana kallanta cike da tausayi tace

"Kayya!Allah sarki baewar Allah babu ruwanta anja mata, Allah ya kiyaye ta daga gorin asali, yanzu meye mafita malam ? Me gari ya ajje numfashi sannan yace

"Yanzu dae zan saka ayi min wasu bincike, idan hakan be yiwu ba toh semu miqata police station na cikin gari" Gyada kae tayi kafin tace

"Toh Allah yasa hakane mafi alkhaeri"

.....'Bangaren gaaje kuwa asibitin da ba taje ba kenan, ba irin maganar da malam Inuwa beyi mata ba akan zuwa asibitin amma ina firr taqi tace ita ta warke, ta zari jiki da sanyin safiyar nan zuwa gidan qawarta ta labarta mata abinda ya faru, toh kunsan tsofaffi akwae daukaka abu shikenan zance ya fara yaduwa cikin garin, kasancewar qaramin gari ne dad'in dad'awa kuma 'kauye yasa kafin azahar maganar ta baza lungu da saqo na cikinsa "Wata mata tayi cikin shege, a ranar data haefe shegen taje tayar dashi, yanzu haka abinda ta haefe din na gidan me gari" Kafin kace menene wannan maganar ta zama kamar wani topic of discussion, ko ina ka zaga zancen akeyi.WANNAN SHINE MAFARI....


........"Malam lafiya dae koh ? Naaga ka shigo gida kamar a firgice" Wata mata da ba zata wuce 30years ba ta fada tana kallan mijinta, Malam habu ya janyo kujerar dake kusa da ita 'yar tsuguno ya zauna sannan yace

"Wallahi wani zance ne ya dauremin kae habi, kinji zancen dake ta yawo a gari kuwa" Seta saki wani miskilin murmushi tace

"Aff ! Ae nan da kake gani na jiranka nake ka shigo in fada maka abinda na yanke akan maganar"

"Aww, kinji ma kenan ? Ya tambaya yana kallanta, Seta wani yatsine fuska

" Toh banda abinka baban ilyasu wannan maganar inane bata zaga ba a cikin garin nan, kasan dae halin 'yan garin nan dae, ya aka 'kare ma mutum beyi abu ba ballanta yayi ? Ta 'karasa maganar cikin sigar tambaya, Seya gyada kae yace

"Ehh kuma hakane, yanzu dae fadamin meya faru ? Gyara zama tayi akan kujerar da take tana kallansa tace

"Wani hukunci na yanke kuma nasan kaema zeyi maka dadi" bata jira ya bata amsa ba ta cigaba da fadin

"So nake mu kar6o yarinyar da aka tsinta a gidan me gari mu ri'keta" Malam Habu ya wani zabura kamar wanda aka tsikara yace

"Kina nufin mu reni shegiya ?

"Toh ina ruwanmu mu, Allah yasa tsinanniya ce ba shegiya ba mu dae in har burimmu ze cika ba shikenan ba ? Ta fada tana watsa masa wani kallo, kallan da kana ganinsa kasan babu mutunci daga wajen wanda yakeyi din zuwa wanda ake aekawa

"Toh fadi inji menene"

"Yawwah, bafa wae mu dauketa mu riqe tane haka kawae ba, a'ah ina nufin musan yadda zamuyi mu tausashi me gari ya bamu ita mu raeneta yanzu, idan ta girma mu zamu more ta, dan kuwa zata zame mana JARI ne"


Sanadin Kaddarata na kudi ne akan kudi N300kcal, Amma yanzu zan baku the whole Sanadin Kaddarata (the beginning) Free ne, da zarar mun gama Free pages zamu cigaba da tafiya ne da wad'anda sukayi payment kawae, Zaku iya fara payment naku tun yanzu in case muna gama Sanadin Kaddarata (the beginning) mu dora tafiyar cikin Sanadin Kaddarata (the conclusion).

Ki tura kudin ta cikin...


Read / Download SANADIN KADDARATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album