Join Our WhatsApp Group

RAYUWAR CIKIN AURE Complete Hausa Novel Document by RAYUWAR CIKIN AURE


RAYUWAR CIKIN AURE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 45971



RAYUWAR CIKIN AURE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 19, Sep 2023

Author: Nafisat Isma'il Lawal ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PERFECT WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 232.07 kb

File Type: txt

Views: 781+

Download: 344+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: [28/08, 12:57 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

   *RAYUWAR CIKIN AURE*
               _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
       _Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*











      *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwarsa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






        *PAGE: 1*

______Tana gaban murhu tana iza itace, sai da ta gama gyara wa kafin ta ɗago kanta tana fyace majina; ta dubi Hauwa dake gaban ɗakin ta

Inda ita kuma take dakan daddawan da zata zuba a miyan ta

Tace da ita, "Wai kin san me Atine tayi min ɗazu da naje amsar adashi na?"

Hauwa ɗago kai tayi itama tana kallon ta bayan ta tsayar da dakan tace, "A'a sai kin faɗa?"

"Hmm matsiyaciya; ai wlh duk wanda yaci tuwo dani, to, miya ya sha.. duk wani rashin mutuncin mutum dai-dai nake da ƙugun ɗan banza, wabillahil lazi idan har bata biya Ni kuɗi na a goben da tace ba, wlh sai mun kwashi ƴan kallo dani da ita. Kin san tun wancan satin nake bilayin zuwa gidanta ta biya Ni amma ta ƙi, yau kuma da naje take faɗa min zancen banza in dawo gobe".

Murmushi Hauwa tayi kafin tace, "ban da abin ki Sauda; tun yaushe nake faɗa miki ki dena wannan zubin na Atine? Wlh matsalar ta yawa ne da ita, kin san tana taƙama da Mijin ta ɗan sanda ne".

"Yo ɗan sandan uban ta. Ɗan sandan da shi ne me gadi uban waye ya isa yayi wa jan ido? Ina ce kuɗi na ne? Wlh dama duk abinda ake faɗa a kan ta don bata yi min bane, amma yanzu ta taɓo Ni kuma zata san ta taɓo Saudatu".

"To ki dai yi haƙuri don Allah tunda ta ce zata ba ki goben".

Sauda tace, "ai ba wai faɗan bane cikawan ne, Ni kuwa idan bata bani ba banga uban da ya isa na ɗaga mata ƙafa ba, duk anguwar nan sai an ji mu".

"To Allah ya kyauta". Cewar Hauwan tana ci gaba da dakan ta

Sauda tace, "Amin". Tana yin gaba ta ɗauki buta a ƙofar ɗakin ta tashige Toilet.





      Lokacin ne yaran ta biyu suka shigo gidan sun dawo daga makaranta, babban ɗan shekara shida Sulaiman, sai ƙanin sa Haidar me shekara huɗu. Da gudu suka shigo gidan suna murna

Hauwa ta tare su da faɗin, "ah ah ƴan makaranta an dawo?"

"Eh Aunty. Kawo in miki dakan". Cewar Suleman yana son ƙwace taɓaryan

Yayinda shima Haidar ya saka hannu zai amsa yana cewa, "Ni ne zan miki Aunty, ai Ni na fi iyawa ko?"

Tana dariya tace, "a'a ku bar min kaya na, daga dawowar ku baku huta ba? Ku dai je ku cire kayan ku kun ji?"

Ba sa jin ta ma illa gardama da suke faman yi kowa na son amsar taɓaryan

A haka Sauda ta fito daga Toilet, ta kalle su bayan ta ajiye butan tace, "kai Sulaiman ka ga Baban ku a waje?"

"Eh Mama, yana nan a majalisan ƙofar gidan su Samir".

"To maza ka kira min shi, ko kuma kace mishi ya bani kuɗin Sabulu da nace ya bani ɗazu be ban ba ya fita, maza ka wuce mana ina magana".

Da gudu ya saki taɓaryan yayi waje da jakan buhun sa a rataye a wuya

Inda shi kuma Haidar ya sami damar ci gaba da dakan

Ita kuma Hauwa girgiza kanta kawai tayi tana bin Sauda da kallo, Sauda ko kaɗan baza ta taɓa sauya halin ta ba, yanzu wai aikan yaro tayi cikin jama'a da wannan saƙon wurin mijinta? In ba tijara ba ta bari a kira mata shi ɗin mana tayi masa maganar a gida.





       "Kai Haidar zo ka wuce ka cire kayan nan, ka ɗauki koko yana nan a ɗaki a saman Fridge na ajiye maka, yanzu insha Allahu zan gama abincin nan ma sai in Yi Muku wanki". Sauda take maganar lokacin da ta zauna bakin murhu tana ci gaba da iza wutan

Shi kuma Haidar ɗin tuni ya saki taɓaryan ya wuce ɗakin su da gudun sa

Hauwa tace, "dama ina so in sanar miki ranan sati na sama bikin Muhseen".

"Wani Muhseen kuma? Ba dai abokin Mijin ki ba?" Sauda ta tambaya tana kallon ta

Ita kuma Hauwa ta bata tabbaci da cewa, "shi fa, kin san abu da an sa mishi lokaci shikenan kuma".

"Cab ɗijam... Wai har yaushe ya sami aikin da zai yi aure? ina ce watannin baya kika ce min ya sami aiki ko?"

Hauwa tace, "a'a fa wajen watanni uku ne yanzu, kuma ai nan na sanar miki an saka mishi ranan aure, har kike cewa idan bikin yazo in sanar miki kema za ki je, kuma don ya sami aiki nan kusa ai ba shi ne zai hana shi aure ba, bare kuma da rufin asirin shi".

Kama baki Sauda tayi tace, "kai Hauwa ban da sharri fa? Yaushe kika faɗa min an yi baikon shi?"

Hararan ta Hauwa tayi tana miƙe wa tace, "Ni ba na son irin haka wlh Sauda, ke kenan idan an yi magana dake sai ki zo kina ƙaryata Mutum, idan baza ki je ba ai babu dole".

"Haba wlh wasa nake miki zan je mana, amma wlh da gaske na manta mun yi maganar, to Ni me zai hana Ni zuwa ai duk inda biki yake ƙafan mu na wurin".

Taɓe baki kawai Hauwa tayi tana saka hannu cikin turmin ta kwashe daddawan ciki, sannan ta juya ta isa gaban murhun ta ta buɗe murfin miyan ta zuba tana kakkaɓe hannu

Sai ga Bilal ya taso Sulaiman a gaba sun shigo gidan

Tunda taji ya soma kumfar baki Hauwa ta shigewar ta ɗakin ta

Shi kuma sababi ya hau ma Sauda yana mata faɗan aiko mishi yaro da tayi cikin jama'a wai ya bayar da kuɗin Sabulu

Dama Sauda ba kanwar lasa bace, ba ta raga wa kowa ko da shi mijin nata ne, nan kuwa ta tashi tsaye itama ta hau shi da masifa. "To na hana ka ka bada kuɗin ne da zaka fita? Ina ce tun kafin ka fita na sanar maka ina buƙatar sabulu domin in Yiwa yaran nan wanki? Dan Allah fisabilillahi ka duba ka ga yanda yaran nan suka je makaranta da kayan su, har sai Ni nace ka bayar da kuɗin Sabulu sannan zaka bayar? Kuma nace ɗin ma amma ka fice kayi uwar kunnen shegu dani, to wlh ko a ina kake bazan ji kunyar aika maka ba tunda kai ka ja".

"To yanzu ke Saude idan ba rashin imani irin naki ba ai kin san bani da kuɗi, kuma tunda kika ga na fita ban ba ki ba bani dashi ɗin ne, meyasa baza ki siya da kuɗin ki ba idan na dawo sai in biya ki tunda kin san ba hana ki zan yi ba?"

Tsaki taja tana cewa, "kaima ka san baza ayi wannan gangancin da Ni ba, sau nawa nake baka kuɗin amma sai ka ƙi biya na? Wlh Bilal ka sha Ni na warke Ni da in ƙara ara maka kuɗi har abada".

Girgiza kansa kawai yayi ya juya zai fice

Tace, "ina kuma zaka je baka bani kuɗin ba?"

"To bani dashi Saude, don Allah ki ɗauke Ni kiyi wankin dani kinji ko?" Yafaɗa a fusace bayan ya juyo yana kallon ta

Hararan sa tayi tana gyara zanin ta tace, "kaima ka san da zaka zama sabulun tun tuni da na ɗauke ka nayi wankin da kai, har sai ma ka saka Ni?"

Tsaban ɓacin rai be tanka ta ba ya juya ya fice da sauri.




    Su kuwa su Sulaiman suna zaune a wuri ɗaya suna kallon su, ko wannen su ya kafa kai a kofin koko, idan suka kalli uwar sai su kalli uban

 Ita kuma zama tayi taci gaba da duba shinkafar da take dafa wa, har yanzu bata yi shiru ba sai masifa take yi tana faɗin, "ai kuwa sai dai su shekara babu wanki wlh, idan malaman su suka gaji da ganin su da datti sai su koro su tunda haka kake so, Ni kuwa bazan zauna kullum ina maimaita kaya ɗaya da dattin dauɗa ba, zan wanke nawa in bar maka na ƴaƴan ka, idan ka zo yin naka sai ka haɗa ka wanke".

"Wai don Allah me ne kike yi haka Sauda? Wai meyasa ba ki san ya kamata bane?" Cewar Hauwa da ta fito daga ɗaki masifar Sauda ya ishe ta. Ta ci gaba da faɗin, "idan ba ki taimaka wa mijin ki ba wa za ki taimaka ma wa? Kuɗin nan ba rasa shi kika yi ba kullum kina sana'ar ki, amma ke babu ruwan ki da taimakon miji, don Allah Sauda ki sauya hali wlh ba na jin daɗin zama dake a wannan halin".

"Hauwa idan ba kya jin daɗin zama dani don Allah ki ce Mijin ki ya sauya muku gidan haya, ina ce itama Maman A'isha gajiya tayi da hali na tabar gidan? Ke idan za ki iya taimakon mijin ki to Ni bazan iya ba, wlh tallahi ina faɗa miki duk namijin da yaga kina tausayin shi wlh sai ya mayar dake rana, shiyasa nake tausaya miki Hauwa duk ranan da aka ce Anwar ya juya miki baya ko yaci amanar ki, Ni dai ki fita harka na in dai irin wannan wa'azin ne na san su tunda Ni ba jahila bace, bazan zauna ina ma miji bauta ba koyaushe, hakan be isa ba sai na haɗa da ɗan jarin nawa shima na mallaka mishi, gaba ɗaya sai in zauna a salwance in koma kamar tsumma babu cin yau bare na gobe, kullum ina bin gidaje ina yawon roƙo...".

Hauwa ta katse ta da faɗin, "Allah ya ba ki haƙuri ki mayar da wuƙan don Allah, ba Ni ce na kar zomon ba.. ratayan ma ba'a bani ba". Sai ta shige ɗaki abin ta don ta san halin Sauda idan ta kama faɗa ba ta jin bari, kullum ita a kan fitina take ba ta gajiya, sai dai idan ba'a motsota ba, duk mutuncin da kuke yi da ita babu ruwan ta ta wanke ka soso da sabulu ta nuna tamkar bata sanka ba.





      Kuma ilai bata dena jaraban nata ba har ta gama girkin ta, ta zuba wa yaran nata tace, "su zo su ɗauka". Sannan ta zuba wa Hauwa ta aiki Haidar dashi ya kai mata. Ita kuma a nan wajen ta zauna ta cinye nata cikin tukunya, sannan ta zuba wa Bilal nashi a ɗan wani ƙaramin kwano na miya tana faɗin, "da ita yake zancen zai zo ya sami dai-dai abinda ya ajiye, dama ita ta siya maggin ta zuba a abincin ba shi ne ya bayar da kuɗin ba".








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️




        "Ke Intisar.. Intisar.."

A firgice ta buɗe idanun ta tana zame iyafis ɗin dake kunnen ta, tayi saurin zamo wa ƙasa tana amsa wa a tsorace tana kallon sa

Tsaki yaja yace, "ke dai ba kya jin magana ko Intisar? Yanzu me kike yi a gida da ba ki je islamiyya ba?"

Sosa ƙeya ta soma yi cike da rawan baki tace, "uhm Dad.. bab.. babu.."

"Babu makarantan?" Yayi maganar yana tsare ta da ido

Saurin girgiza kanta tayi kafin tace, "a'a akwai. Mom CE tace in zauna in tare mata gida zata je anguwa".

"Anguwa kuma?" Ya maimaita a fili. Sai kuma yace, "yayi miki kyau to. Ina su Sumayya sun tafi dai ko?"

"Eh sun tafi tun ɗazu".

Be sake ce mata komi ba ya juya ya shiga ɗakin Fauziyya.



    Ajiyan zuciya Intisar ta sauke tana ɗaukan wayan ta da ya faɗi tun zamowar ta ƙasa, koma wa kan kujeran tayi ta sake mayar da iyafis ɗin tana ci gaba da shan waƙan ta.




             *******







      Jamal na shiga ya ganta zaune gaban mirror tana ta caɓa kwalliya, da kallo yake bin ta cike da mamaki, ganin ta ƙi mishi magana duk da ta ga shigowar sa sai yace mata, "wai ina kike son zuwa da yamman nan ne ba ki sanar min ba?"

Sai a lokacin ta ɗan juyo ta kalle shi, sai tace, "dama zan sanar maka ai ba wai tafiyan zan yi haka kawai ba, yanzu nake shirin kiran ka a waya. Zan je Gidan Aunty Salaha ce".

"To shi ne kuma baza ki bari sai gobe ba sai yanzu? Bata da lafiya ne ko me?"

"Lafiyan ta lau, yanzu dai naga damar zuwa shiyasa".

Kaɗa kansa yayi kafin ya juya yana zame hulan kan shi ya ajiye a saman kujeran dake ɗakin, be kalle ta ba ya soma cire bottles ɗin rigan shi yana cewa, "wai ba na ce miki ki dena hana yaran nan zuwa makaranta ba? Ba kya jin magana Fauziyya idan basu je sun nemi ilimi yanzu ba yaushe kike son su je?"

Tashi tayi daga gaban mirrorn hannun ta a kan ɗaurin ɗankwalin ta tana gyara mishi zama, inda take cewa, "na fi ka sanin haka Yallaɓoi.. kuma da kake cewa in dena hana ta idan da ace na fita yanzu ka dawo ka tarar da gidan a rufe ka dinga faɗa kenan ai".

"To kin sanar min ne?" Yayi maganar yana kallon ta

Bata ce masa komi ba ta gama yafa gyalen ta tana zira takalmi

Sai yace, "amma dai kin je kin duba Mama da nace miki ɗazu ba ta jin daɗi ko?"

"Ni ban je ba".

"Ba ki je ba Fauziyya? Kina nufin haka kika bar ta ko abincin ma ba ki aika mata da shi ba?"

"To wai ya kake son in Yi da raina ne? Inji da yara ko inji da kai ko kuma da girki? Ni fa yau ban dafa abinci me yawan da wasu zasu samu su ci ba, ka bari idan wancan me ƙwaƙulallun idon ta dawo sai ta riƙa dafa wa da ita". (Tana nufin me aikin su, kuma ɗiya ce wajen ƙanwar Jamal, da mahaifiyar Jamal da Kakar Hafsan uwa ɗaya uba ɗaya)

Cikin ɓacin rai Jamal yake kallon ta yace, "lallai Fauziyya wuyan ki ya isa yanka.. Maman nawa ce wata har baza ki iya dafa abinci ki kai mata ba? Meye amfanin ki a gidan? Ɗazu na ce miki ba ta jin daɗi memakon ki je ki duba ta ba ki je ba, kuma ba ki kai...


Read / Download RAYUWAR CIKIN AURE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album