Join Our WhatsApp Group

MATAR DAMUSA Complete Hausa Novel Document by MATAR DAMUSA


MATAR DAMUSA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 93366



MATAR DAMUSA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 21, Oct 2023

Author: Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : NASARA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 09065443871

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 591.66 kb

File Type: txt

Views: 4454+

Download: 3962+

Last download: 1 day ago

Description/Story: ๐Ÿ… *MATAR DAMUSA*๐Ÿ…
(the wife of tiger)

Mallakin Asma'u Muhammad Auwal
โœ๏ธ *ASMEETAH*โœ๏ธ

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________


๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

Book one 1.

Pages 1 to 10

Wata tsohuwar Mata ce zaune a bakin bishiya, ta jingina bayanta a jikin bishiyar tana shafa sumar kan Yarinyar dake kwance saman cinyarta,
Yarinyar bazata wuce 20yrs ba, tana kwance kamar mai yin bacci taji uwar tana shesshekar kuka! A firgice ta tashi zaune tana fadin "Uma lafiya kuwa, meya faru dake?"
Cikin kuka Tsohuwar tace "Ayush inaso ki tayani neman gafarar ubangiji, na tafka babban kuskure a rayuwata, inaji ajiki na zan mutu, Ayush! Zan mutu ba tareda na nemi yafiyar Junaid ba"
Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai kashe zuciya
"Uma Dan Allah ki daina kukan nan banso, banso na rinka ganinki acikin wannan halin,
Shin wanene wannan JUNAID din? Sannan mai kika Aikata masa haka har kike fad'in munanan kalamai akanki saboda shi? Cikin zubda hawaye Ayush take fad'in "Uma idan baki furta mun abunda ke ranki ba taya Zan iya temaka miki da Addu'a bayan bansan laifin da kika Aikata ba"
Cikin takaici da cije la66e Umma take kallon Ayush wacce itama Ayush d'in kallon Umman take,
"Ayush! Na tsani kaina, kema idan kika ji labarina na tabbata zaki tsaneni ne, Zan gaya miki Amma kafin nan inaso ki yafe mun Dan Allah" tana kallon Ayush cikin tausayawa.
Da mamaki a fuskar Ayush cikin kasalalliyar murya tace "ni kuma Uma? Nasan bakiyi mun komai ba, duk abinda kikayi mun nasan aciki soyayya ne, bazaki iya cutar dani ba Mamana, saboda haka na yafe miki duniya da lahira". Murmushin takaici Umma tayi murya a sha'ke tace "Ayush a yanzu rayuwata batada amfani, a shirye nake dana mutu, sai dai Ina mai tausaya miki idan na mutu bansan halin da zaki shiga ba, Ayushh banida en uwa banida kowa, mutane gudu na suke saboda ban aikata abu mai kyau ba, hakan yasa laifi na ya shafeki kowa kyamar mu yake," kinga can๐Ÿ‘‰ ta nuna wani 'Dakin Kara sannan ta cigaba da cewa "nasan kinsan cewa nan ne 'Dakin mu na kwana, tin kina jaririya muke wannan dajin! Kinsha tambayata cewa Ina BABANKI, SU WAYE EN UWANKI amma na kasa baki amsarki saboda kada ki gujeni, amma yanzu a shirye nake dana fuskanci duk wani 'Kalubale"
Taja dogon numfashi murya Ciki-ciki tace "AYUSH"
Cikin Sanyin murya ta amsa "Na'am Uma Ina sauraronki" fuskar nan duk ya jagalgale da hawaye ga yayi jawur abunka da farar mace.
Ta cigaba da cewa "Ina so naga kinyi Aure kin haihu, Ayush kina da kyakykyawar zuciya, kinada tausayi, Sam bana fatan ki d'auko kalar halina koda da qwayar zarrah, sannan banaso ki d'auko halin mahaifinki shima, tirrr da halayen mu" ta sake fashewa da wani sabon kukan mai cin rai!
Ayush itama kukan take ta rungumi Uma tana shafa bayanta rarrashinta take cikin kulawa, cikin sassanyar murya tace "Uma kibar mun wannan labarin indai zai Saki kuka, banson abunda zai sakaki kuka Umma nah Ina matukar kaunarki"
Umma ta raba jikinta dana Ayush tana sharar hawaye sannan tace " a'a Ayush indai ban fitar da abunda ke raina ba, bazan samu nutsuwa ba,
Zan gaya miki ko ni wacece.

Da farko ni sunana *AGATHA* ni ba musulma bace, asalin er kasar Ghana ce ni, na rasa iyayena ta sanadiyar hatsarin motor, banida kowa bayan su saboda rashin zumuncin dake tsakaninsu da en uwansu hakan yasa basu ta6a gaya mun cewa inada en uwa ba, ni kuma ban damu da sanin hakan ba, ni dai nasan cewa mahaifina christal ne, mahaifiyata kuma musulma ce sai dai mahaifina ya rinjayeta zuwa chrital hakan yasa gava ta shiga tsakanin en uwan mahaifina da kuma mahaifiyata,
Sakamakon ba Wanda ya kula dani yasa na shiga harkar karuwanci ta hanyar nan nake ci da sha da kuma sutura a kaina,
Ina cikin wannan halin Allah ya had'ani da wani Attajirin Bawan Allah, ya fitar dani daga cikin wannan halin da nake ciki,
Ya taimake ni a rayuwa sannan ya kwad'aita mun musulunci, na musulunta ta sanadiyarsa, ya canza mun suna na koma *BARA'ATU* shi 'Dan nan Nigeria ne kasuwanci ya kaishi kasar Ghana,
Nayi kusan shekara guda ina tare da shi amma ba wani abu daya ta6a shiga tsakanina dashi, nabi duk wasu hanyoyin dazan bi domin ya nemeni da lalata amma Sam yaki, ni kuma ina da munguwar sha'awa Gashi na kamu da matsanancin son sa,
Duk wani nauyi na akansa ya rataya shi yake mun komai hatta kudin da zan kashe shi yake ban,
Wata rana yana zaune yanata Lissafe-lissafensa na kudurta a raina cewa zan sanar masa cewa ina sonsa kuma zan Aure shi,
Bayan na sanar masa bai nuna mun 6acin ransa ba amma sai dai yaki amincewa da Aurena,
Kinsan mai ya cemun??
Ta karasa maganar tareda tambayar Ayush.
Girgiza Kai Ayush tayi tareda 'kura Mata ido cikeda mamaki take kallon mahaifiyar tatan,
Ta cigaba da cewa "naji takaicin maganar daya gaya mun"
Hmmmm! Taja ajiyar zuciya sannan tace "cewa yayi yabar Matarsa a Nigeria tare da 'Dansa, baya bukatar 'Kara Aure saboda gudun matsala!
Sannan yace "zai tafi Dani gidansa a matsayin er Aikin matarsa,"
Ayush zaro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana kallon mahaifiyar ta, ta rasa abun cewa
Sai ji tayi Umma tace "a lokacin na kudurta a raina cewa saina rabashi da matarsa, saboda Ina matukar kishinsa, kuma sai nabi ta hanyar dazan bi na Aure shi,
Na bishi a hakan har muka komo Nigeria, ya gabatar dani a wajen matarsa Doctor Fateemah mutumiyar kirki, batada tashin hankali, sai 'Dansa mai suna Junaid karamin yaro ne lokacin baifi 10yrs ba,
Alhajin bai 6oyewa matarsa komai ba ta yanda muka hadu, sai dai bai sanar mata da cewa ina sonsa ba,
Na fara gabatar da Aikin gidan a matsayin er Aiki suna biyana salary duk wata"
Umma ta dakatar da labarin tayi shuru kamar mai tunanin wani abu sannan tasau murmushin takaici
Ta cigaba da cewa "a lokacin na nemi wani hatsabibin boka babban matsafin duniya, ta hanya wata shu'umar mata wacce muka hada kawance da ita,
Tafiya mai nisa mukayi domin zuwa gurin bokan ni da kawata,
Kuma mun sameshi amma guri ne mai hatsarin gaske ba kowa ne yake zuwa dajin ba sai mai karfin ikoh,
Na sameshi da maganar Alhajin nan, Bokan yayi wani irin matsanancin Dariya mai rikitarwa sannan ya sanar mun cewa
Zan mallaka masa Abu uku ne kafin ya biya mun bukatata,
Na farko zan bashi kudi 100Bs,
Na biyu zan mallaka masa jinin yaro namiji domin biyan bukatarsa na daban ,
Na uku zan bashi kaina, ma'ana yayi lalata Dani,
Duk na amince masa saboda nima inason bukatata ta biya,
Sai dai Abu na farkon daya fad'a shine zai ban wahalar samu wato 100Bs,
Bayan mun bar dajin hotel muka Kama saboda garin yayi nisa sosai,
Anan ne nayi shawara da kawartawan akan batun kudin
Ta sanar mun cewa wannan bazaiyi wahalar samu ba, nayi mamakin jin hakan saboda kudi ne mai yawan gaske,
Daga baya tace mun zata iya bani duk kudin kyauta amma saina bata Abu daya,
Na nuna Mata cewa komai ma zan iya bata indai zan samu kudin,
Ashe cikakkiyar er lesbian ce (madigo)
Ban nuna Mata komai ba sai cewa nayi na Amince "na mallakawa 'katon boka mah balle ke kawata"
Taji dadin wannan furucin nawa
Haka muka aikata madigo cikin jin dadin juna ba tareda fargaban komai ba, ta mallaka mun kudaden nan nakaiwa boka, shima na bashi abunda yake bukata ajikina sannan na bashi yaron Alhaji wato Junaid,
Sai dai kash abun bakin ciki anan shine Bokon nan yana son haihuwa amma manyan Aljanunsa sun hanashi har saiya mallaka musu jinin yaro namiji kafin su bashi haihuwar,
Ya nemi Mata da yawa amma ba haihuwar, yaran da suke kawo masa jininsu baiyi dai dai da kalar jinin da suke nema ba shiyasa ya hakura da neman matan,
Sai akaina kuma jinin Junaid yazo dai dai da jinin da suke bukata,
Boka yayi matukar farin ciki sosai, ya kamu da sona hakan yasa ya ruguje duk wani tsafin da yayi don na mallaki alhaji, yace "bazan Auri kowa ba, kuma bazai Aureni ba saboda su basa Aure,
Bansan hakan ba sai da ciki ya fara 6illowa daga tumbina, na tsorita sosai,
Har cikin ya girma! shi kuma bokan ya haskaka madubinsa gareni duk wani motsina yana gani ta madubi, kuma duk abunda nakeso zai bani saboda cikin dake jikina,
Har Allah yasa na haihu jaririyar mace ba kowa bace face ke *AYUSHMAT*
Ayush suman zaune tayi jin mahaifiyarta ta ambaci ita diyar boka ce
Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,
Abunda Ayush taketa furtawa kenam,
"Umma kin cuceni, kin 'kazantar mun da rayuwata, na shiga uku nah, wayyo Allah nah, Umma laifinki babba ne, kin gama da rayuwata, bayan ni er cikin shege ce hakan mah diyar babban boka iblis"
Cikin takaici ta zubawa mahaifiyarta ido, idanunta duk sunyi jaa tsabar zubar hawaye, ta lankwasa wuya ta zamo kalar tausayi, murya a sanyaye take fad'in "Umma ya rayuwarki a haka? Meyasa kika za6arwa kanki kalar 'kazamar rayuwar nan , Gashi nima ya shafeni, Allah sarki Junaid yaro bai san komai ba gashi an jefa rayuwarsa cikin hatsari"
Umma Bara'atu gaba daya ta susuce, ta fita hayyacin ta, idanuwanta duk sun 'kan'kance tsabar kuka, bakinta na rawa tace "Ayush kiyi hakuri, nasan na cutar da rayuwarki, naso ace kema kin zamo d'iya mai enci" kuka ne yazo mata mai cin rai.
Cikin tausayawa Ayush ta kamo hannun Uman tana rarrashinta "Umma ki daina kukan nan, ki sanar mun abunda ya faru bayan nan"
Umma ta d'ago da rinanan idanuwanta tana kallon Ayush wanda itama kukan take ta gagara rarrashin kanta domin abun da ciwo,
Cikin karayar murya Umma tace "Ayush! Bayan na haifeki na nuna cewa ke d'iyar Alhaji ce, wanda hakan ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da matarsa, nasa Alhaji kuka cirr da idanunsa yana rantsuwa akan shi bai ta6a kusantar zina ba, baisan ya akayi na samu cikinki ba, naji tausayinsa alokacin sai dai inaso ya amince da ke a matsayin d'iyarsa" bata karisa maganar ba taji Ayush ta katseta da cewa "tayaya Umma, taya zai yadda ni diyarsa ce bayan yasan ba alakar data shiga tsakanin ku, haba Umma"
Cikin kuka Umma tace "toh ki tsaya mana ki saurareni, ai a lokacin matarsa cewa tayi bazata cigaba da zama dashi ba, naji dadin hakan sosai saboda nasan ko bai Aureni ba zamuyi zaman dadiro ne da shi, Amma sai dai kash yana cikin bawa matarsa hakuri zuciyarsa ta buga lokaci guda Alhaji ya rasa rayuwarsa,
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un Allah sarki Alhaji ka gafarce ni" ta Kara fashewa da wani irin kuka,
Ta cigaba da cewa bayan rasuwar Alhaji an gano cewa karya nake Anyi mun korar kare a gidan nan, har hukuma sai da ta kulleni daga baya mahaifinki yazo ya yi baili na,
Mutane sun kyamaceni, wasu har tofa mun yawu suke da zaran nazo wuce wa, gaba daya zaman cikin garin ya gagareni hakan yasa mukazo nan dajin da zama,
Na kuma yanke alakata da mahaifinki babu ni babu shi amma duk da hakan bai daina bibiyata ba saboda ke, yanzu haka yana kallon mu ta cikin madubinsa kuma yana jin duk abunda nake fad'a,
Rauninsa kuma kece"
Wani irin juya ido Ayush tayi tana wani yamutsa fuska kamar mai jin kyama tace "ni kuma? Tayaya rauninsa zai zama daga gareni yake, can't believe"
Murmushi Umma tayi sannan tace "kwarai kuwa, duk wani abun cutarwar da zai sameki to shima haka, idan kika ji ciwo a jikinki toh shima zaiji zafin ciwon a jikinsa, shiyasa tin kina karama idan kikayi laifi bana dukanki saboda zai d'au fansa ne domin shi zaiji zafin dukan, idan kikayi zazza6i toh shima a ranar zai kwanta jinya, duk abunda ya faru da ke shima zai faru da shi, sai dai kuma shi ata 6angarensa duk abunda ya faru dashi babu abunda zakiji"
Ayush ido ta zaro waje still tayi tambaya atakaice "Umma duk meya jawo hakan?"
...


Read / Download MATAR DAMUSA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album