Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

IDAN RANA TA FITO BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by IDAN RANA TA FITO BOOK 1


IDAN RANA TA FITO BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13067IDAN RANA TA FITO BOOK 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Oct 2023

Author: Halima K Mashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 64.45 kb

File Type: txt

Views: 1156+

Download: 415+

Last download: 4 days ago

Description/Story: IDAN RANA TA FITO

NA
Halima m/mashi
PAGE 1.....! Na karama motar idanu kai bani ba ma duk mutanan da ke kauyan kallon motar suke domin ni dai a sanina wannan shi ne karo na uku daga na mota kuma duk gidan hakimi take zuwa wato gidan maigari dai su ne suke da yan uwa a birni,na bi motar don in ga gidan da zata na ma manta da batun aike na a kayi kaikuwa kofar gidan maigari ta tsaya,na kuma ci gaba don ina matukar so in ga cikin motar ina son sanin ko kamar daki take? Zare idanu na yi lokacin da naga wanda ya fito daga cikin motar wani saurayi ne dan birni me kyau yana sanye da wasu irin kaya,ga kuma wani kamshi yana tashi.Sam ban san na saki baki ina kallonshi ba,ya nufi cikin gidan maigari ashe nima na bishi ban sani ba sai kurum na ji ni cikin kwata,lokacinne fa hankalina ya dawo na gane me nake yi,na kuma tuna zan je siyan kanwar miye ne.Lallai yau zan ci duka gurin Baba Gaje,babu rana ta banza da ba za a dake ni sau uku ko sau hudu ba na sani wani lokacin da laifina domin bana ganin abin kallo na wuce kuma abin mamaki ba ya wuya a gurina.Lokacin da na....! Lokacin da na dawo siyan kanwa sai da na kuma yin zagaye ta gidan maigari ko zan sake katarin ganin motar tare da wannan dan gayun dan birnin.Abinda na gani yanzu shine ya fi bani mamaki tare da daure min kai.Wata yar karamar a ba ce na gani a hannunshi ya kara ta a kunnanshi yana ta magana shi kadai ba ni ba har samarin kauyan kalloshi suke ringa yi.Ya shiga motar ya tashe ta,na so in matsa kusa da motar in taba ta ko dan in karasa amma in tsoro,haka ya tasheta ya tafi ban nufi gida ba sai da motar ta kule.Ina isa na hau rabe-rabe saboda hangowar da nayi Baba Gaje tana kwashe tuwonta,miyar kuma tana aje gefen murhu,da alama an sauke ta tuni.Ta banko min harara "sai yanzu ki ka ga damar dawowa? Yar iska shegiya matsiyaciya babu,abinda zai hana ni kirbarki yau yar asara". Na soma kuka ina cewa "Don Allah Baba kiyi hakuri". Lanto ta dube ni ke ina ki ka tsaya ne?cikin kuka na ce um....um kofar gidan maigari ne a ke kallon mota shi ne fa na dan tsaya..." Ta katse ni kallo koh? Na yi shiru,ta ci gaba da shararta.Jummala da ke can gefe ta ce "ai kallon Haka matan gidanmu suka yi ta surutu.Baba Gaje tana ci gaba da sine min, dama haka fadan gidanmu yake musamman a kaina babu wanda ke bada hakuri domin kowa yasan masifar Baba Gaje kuma tsoronta suke yi, domin ta fi su samun kudi sana'o'i babu wanda Baba Gaje bata yi, kuli, goro, man gyada, shinkafa da wake ga kuma koko, sannan duk kauyen mu ita ce uwar adashe. Ina labe bayan rumbu ina ji Babana na nemana, na fito in shashsheka,

2...Ina la6e bayan rumbu ina ji
Babana na nemana, na fito ina
shashsheka, ya ce "Jidda wai me
yasa kullum sai kin nemi laifin da za
a ta6a lafiyarki ne?" Cikin
shashshekar kuka na ce,"Baba siyan kanwa aka aike ni." Ya kama
hannuna shine ki ja samu kallanki
na tsiya ki ka dade ko? Na ce mota
ce kofar gidan Maigari shi ne na dan
tsaya ya ce, na ce ki daina tsayawa
kalle-kalle kin. Gaje dai dukanki zata yi, eh dakunta zan yi Muka ji muryar Baba Gaje dama kun saba
ku dunga la6ewa kuna zagina duk
wahalar da nake da ita ba a ganoma
ba zan yarda ba, ehe." Baba ya ce,
Saurara Gaje ni ba na hana ki dake ta ba ne ina dai yimata nasiha ne ta daina tsayawa kalle-kalle, amma
yanzun ki mata hakuri in yaso nan
gaba in ta kara sai ki dake ta. "Ai
wlh sai na dake ta, kuma ba za ta ci
tuwon gidannan ba. In aike ta don ita 'yar tsinanniya ce sai ta je ta yi zamanta, tasan zata fita da goro ta
dan zaga don mugunta ta ki
dawowa. "Na ce kiyi hkr
don......"Kafin na karasa na ji saukar mari. Baba yasa kai ya fita
don na sani ba zaya iya ganin halin
da zan shiga ba ne dama nata tsarin
in tana dukana duk wanda ya ce
tayi hkr to zata ce yana goyon
bayana ne. Daga nan sun kulla gaba ita dashi, in kuma tana gaba da ke to doke ne duk matan gidan su
daina shiga harkarki, in kuwa wata
ta kula ki to itama ta shiga. Bisa ga
wannan dalilin sai dai su sa idanu, in
ma za su yi magana sai dai su ce maganina kenan duka, haka ta jibge
ni son ranta ta sake ni tare da
shurina da kafa tayi tafiyarta, na ci
kukana na gaji na koma gefe na
ra6e. Su Indo da Shafa suka biyo
mana gada Hinde ta fiti 'yar gabn gishin Baba Gaje kenan, ta kira Salame da Laminde suka fita, na
tashi zan bi su duk da na san Hinde
zata iya koro ni sai Baba Gaje ta ce,
"Ke Kuluwa zo nan yau in ake ba
zuwa dandali sai dai kai goron nan na dawo nta nuna min tiren gashi can kin san kudinshi saura kallon ki
na tsiya ya ja ki bar goron yau ki
sha wuya, ni dai na fita." Muryar
Baba na ji ya ce,"Jidda ya ki nan." Na
je na tsugunna "Gani Baba. "Ya ce,"Ungo, nasan ba ki ci abnci ba
ko?" Na ce, "Eh." Bakar leda ya bani
ban san ko me ciki ba, ya ce," kici
kin ji? Tashi ki tafi. Ina za ki ne da
tire?" Na ce "Dandali zan kai goro."
Ya jinjina kai "kada ki damu ki zama mai hkr, Allah yaba tare da masu hakuei, tashi kije ki kula da kanku
da kuma sana'arki kin ji ko?" Na ce
"To Baba....
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: Idan rana tafito

3... Sai da na tafi na duba naga rogo
ne da kuli, a fiki na ce Allah Sarki
Baba, Ina tafe ina ci sam ban ankara
ba sai ji na yi na ci karo da mu2m,
tuni tiren goron ya yi baya ya fadu
na fara kallon da wa na ci karo gabana ya fadi ganin Ado. Yana
tsaye yana kallona. na duka na
soma tsince goron ina fadin nashiga
3 na yau zan sha jibga in ban gansu
duka ba... Ado ya tsugunna tare da
hasko cocila 'yar karama duk da cewa akwai hasken farin wata
musamman yau watan yana 14 ya
ce duba a hankali na kalli cocilar 'yar
mai kyau ba kalar ta Babana ba da
ya ta6a sautu birni a ka siyo mishi,
sai na ji muryarshi yaba cewa ki duba mana me ki ke kallo haka? Ban
ce komai ba na ci gaba da
duddubawa banga wani ba ya ce
kirga ki gani ki ya cika, na ce ban
san ko na nawa ta zuba ba, ita ce ta
kirga da kanta, ya ciro naira 10 nawa nawa ne goron? Na ce"Da na ficika ne da na kwandala." Ya mika
min 10n "To rike wannan ki cika." Ya
yi tafiyarshi na bishi da kallo, ko
cikin mafarki bn ta6a zaton Ado
zaya iya yi min magana ba, saboda Ado Saurayi ne mai girman kai
game da jan aji, in ji 'yanmatan
kauyenmu sannan shi kadai ne ya yi
boki duk wata wasika in za a rubuta
ko za a karanta sai annemi Ado, duk
cikin kauyan shi ne babban yaron Maigari kuma duk kauyan babu
wanda ya kai Magari dukiya,
dabbobi da gonaki sannan su kadai
ne ke zuwa birni. Jin an dauke tiren
goron daga kaina sai na dawo cikin
hayyacina yare da yin firgigit don ganin ko waye.......Bint o ce kanwar Ado, ta ce Kuluwa garin kallo wata rana sai an sace ki, nayi
'yar dariya na ce "Binto ina za ki?"
Ta ce, "Dandali can za ki kai goron?
Na ce, "Eh." Ta ce "hu'um, ke dai
gaskiya ba kya hutawa gashi kin daina zuwa Mkrnt, na ce kema Binto
kin sani in ban ke ba duka zan ci
Mkrnt kuwa saboda kudin Laraba, ta
ce in daina zuwa da Baba ya bani
kuma ta kwace ta ce bani ba Mkrnta.
Binto ta ce, shi yasa na daina zuwa gidanku ce min take yi in daina kula ki kai ke kula Maza ne da ke su
Hinde sune dai-dai ni ni ko kin san
ko a dandali rana daidai ce ba ma
kwasar ta da su akanki....ko kin zo
ko ba ki ba, a haka muka isa dandali na zauna kusa da mai gyada don ta kunna aci balbal, wato fitlar
gwangwani
Mar 6, 2015
Aisha Ummu Shureim Sa'eed
4..Binto ma gurina ta zauna muna ta
hira ina bata labarin karon damu ka
yi da Yayanta, lokacin da muka
dawo gida ba wanda ya sai
goron,don haka sai na mika mata
naira goman a zuwan cinikin da nayi, ta zauna ta kirga goronta
sannan ta dube ni "Siyan goron aka
yi?" Na ce "Wani ne ya zubar min
bai sani ba shi...


Read / Download IDAN RANA TA FITO BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album