Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RUWAN DUFANA Complete Hausa Novel Document by RUWAN DUFANA


RUWAN DUFANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 2915



RUWAN DUFANA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 02, Apr 2025

Author: Bashir Halilu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 17.88 kb

File Type: txt

Views: 48+

Download: 7+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: RUWAN ƊUFANA

ƘISSAR ANNABI NUHU ALAIHIS SALAM

Daga shafin Bashir Halilu.

Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمْسِينَ عَامًا فَأَخَذَهُمُ الطُّوفَانُ وَهُمْ ظَالِمُونَ فَأَنجَيْنَهُ وَأَصْحَابَ السَّفِينَةِ وَجَعَلْنَهَا ءَايَةً لِلْعَالَمِينَ .

【Ma'ana】

14. Kuma haƙiƙa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin (950), sai (ruwan) Ɗufana ya ci su, alhalin suna azzalumai.

15. Sai Mu ka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Mu ka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai.

Annabi Nuhu (AS) yana daga cikin manyan Annabawan da Allah Ya aiko domin shiryar da mutane zuwa ga tauhidi. Ya kasance cikin jerin Annabawan da ake kira "Ulul Azmi", wato manyan Annabawa guda biyar mafiya daraja a gurin Allah.

Ibn Kathir ya kawo a cikin littafinsa Al-Bidāya wan-Nihāya cewa, Annabi Nuhu (AS) shi ne Nuhu ɗan Lamik ɗan Matushalakh ɗan Annabi Idris (AS) ɗan Yarid ɗan Mahla'il ɗan Qainan ɗan Anush ɗan Shith (AS) ɗan Annabi Adam (AS). Wato, Annabi Nuhu (AS) yana cikin zuriyar Annabi Idris (AS) kuma yana da nisa da Annabi Adam (AS) da kakanni tara kawai.
Annabi Nuhu (AS) ya rayu a wani yanki da ake kira "Al-Kūfa" a kasar Iraƙi, kusa da kogin Furat, ko kuma a wasu ruwayoyi, ana cewa yana kusa da yankin Armeniya da ƙauyukan da ke kusa da Dutsen Judi.

Ibn Kathir ya ambata cewa Annabi Nuhu (AS) yana da ‘ya’ya uku, waɗanda daga su ne aka samu rarrabuwar jinsin ƴan Adam da ƙabilu daban-daban. Daga cikin ƴaƴan na sa da akwai Samu, wanda shi ne Kakan Larabawa, Yahudawa, da Nasara. Sai Hamu, shi kuma shi ne Kakan mutane baƙar fata, musamman yankin Afrika. Sai na ukunsu Yafisu, shi kuma shi ne ya haifi Turkawa, mutanen Mongoliya, da sauran ƙabilun Asiya. Sannan yana da wani ɗa mai suna Kan'ana da kuma matarsa mai suna Waliya amma su ba su yi imani ba, don haka aka hallakar da su a ruwan Ɗufana.
Annabi Nuhu (AS) ya tashi cikin mutanensa lokacin an yi wasu mutane masu ƙima a idon al'umar zananin, kamar wasu shugabanni da malamai da sauran mutanen da ake girmamawa. Irin waɗannan mutane sun haɗa da wanda ake kira Wudda da Suwa'a da Yagusa da Ya'uwƙa da kuma Nasra. Mutanen zamanin sun kasance idan wani babban mutum ya mutu a cikinsu sai su sassaƙa gunki mai kama da shi su ajjiye don tunawa da wannan mutum da kuma koyawa ƴan baya halayensa na kirki da sanar da su tarihin manyan cikinsu. To lokacinda waɗannan mutane biyar su ka mutu su ma sai aka sassaƙa gumakansu aka ajjiye don tunawa da su. Bayan shuɗewar shekaru masu yawa sai shaiɗan ya dinga raya musu cewa ya kamata su dinga bautawa irin waɗannan mutane masu daraja, sai su ka koma bautawa waɗan nan gumaka a maimakon bautar Allah, sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya aiko Annabi Nuhu (AS) don ya kira su izuwa kaɗaita Allah da bauta da kuma barin bautar gumaka.

Sai su ka fara yi masa izigili, su na yi masa dariya, suna ce masa ya samu matsala ne, har ya fara tatsuniya yana cewa wahayi ake masa. Suna cewa ai ba zai yiwu Allah Ya aiko mutum ba saidai Mala'ika. Da su ga ka Annabi Nuhu (AS) lallai da gaske ya ke yi sai su ka fara yi masa barazana da kisa da azabtarwa kuma su ka hana mutane sauraronsa.

Annabi Nuhu (AS) ya dinga zuwa duk inda ya san mutane suna taruwa kamar kasuwanni da sauran gurare, yana yi musu wa'azi. Yana wa'azi a kowane lokaci, dare da rana, har ta kai Annabi Nuhu (AS) yana zuwa har gida yai sallama da mutum yai masa wa'azi. Duk inda ya ga taron mutane ko masu yawa ko kaɗan yana tsayawa ya isar musu da saƙon Allah amma mutanen sai ƙara kangarewa suke yi. Ta kai idan Annabi Nuhu (AS) yana magana sai mutanen su dinga saka hannu suna toshe kunnuwansu ko su rufe fuskarsu don kar ma su ganshi. Hatta cikin gidan Annabi Nuhu (AS) da akwai ɗansa wanda bai imani ba da kuma matarsa wacce itama ba ta imani da shi ba kuma ta yi yunkurin kashe shi a lokuta da dama amma ba ta samu nasara ba. Ita ce Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi alƙarin sai ya ƙonata ranar Alƙiyama, cikin suratut tahriym, ayah ta goma, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce

ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا لِلَّذِينَ كَفَرُوا امْرَأَتَ نُوحٍ وَامْرَأَتَ لُوطٍ كَانَتَا تَحْتَ عَبْدَيْنِ مِنْ عِبَادِنَا صَلِحَيْنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمْ يُغْنِيَا عَنْهُمَا مِنَ اللَّهِ شَيْئًا وَقِيلَ ادْخُلَا النَّارَ مَعَ الدَّاخِلِينَ.

Ma'ana:

10. Allah Ya ba da wani misali ga wadanda suka kafirta da matar Nuhu da matar Luɗu; sun kasance karkashin (igiyar auren) wasu bayi su biyu salihai daga bayinmu, sai suka ha'ince su, saboda haka ba su wadatar musu komai ba (daga azabar) Allah, (ranar alƙiyama) kuma aka ce (da waɗannan mata guda biyu): "Ku shiga wuta tare da masu shiga."

Allah Maɗaukakin Sarki Ya bayyana cewa kasancewarta matar Annabi Nuhu ba zai hana Allah Ya ƙonata a wuta ba, za a kaisu wuta ita da matar Annabi Luɗu (AS) saboda sun kasance suna ha'intar mazajensu.

Cutarwar mutane ga Annabi Nuhu (AS) kuwa sai ƙara tsananta ta ke yi, ga shi tsawon shekaru masu yawa amma sun ƙi yin imani. Sai da Annabi Nuhu (AS) yai shekara ɗari tara da hamsin yana wa'azi alhali an aiko shi yana ɗan shekara ɗari biyu da hamsin. Kenan sai da ya cika shekara dubu ɗaya da ɗari biyu a duniya amma kullum sai arna sun yi masa duka, wani sa'in ma suna zato sun kashe shi, sai daga baya kuma Allah Ya dawo masa da ransa, ya koma ya cigaba da wa'azi.

Sai bayan cikar waɗannan shekaru ne sai Allah Maɗaukakin Sarki ya yi wa Annabi Nuhu wahayi cewa "Babu wanda zai kuma yin imani daga cikin mutanenka, saidai wanda dama tini ya yi imani, don haka kada ka damu da abinda suke aikatawa".

Jin haka sai Annabi Nuhu (AS) ya yi addu'a kamar yadda ya zo a cikin Alƙur'ani. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

قَالَ نُوحٌ رَّبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِي وَاتَّبَعُوا مَن لَّمْ يَزِدْهُ مَالُهُ وَوَلَدُهُ إِلَّا خَسَارًا * وَمَكَرُوا مَكْرًا كُبَّارًا * وَقَالُوا لَا تَذَرُنَّ وَالِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا * وَقَدْ أَضَلُّوا كَثِيرًا وَلَا تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلَّا ضَلَالًا مِمَّا خَطِيئَتِهِمْ أُغْرِقُوا فَأُدْخِلُوا نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا لَهُم مِّن دُونِ اللَّهِ أَنصَارًا * وَقَالَ نُوحٌ رَّبِّ لَا تَذَرْ عَلَى الْأَرْضِ مِنَ الْكَافِرِينَ دَيَّارًا ) إِنَّكَ إِن تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوا إِلَّا فَاجِرًا كَفَّارًا ) رَّبِّ اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيْتِيَ مُؤْمِنًا وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَلَا تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلَّا تَبَارًا )

Ma'ana:

21. Nuhu ya ce, "Ya Ubangijina, lalle su sun saɓa mini, sun kuma bi duk wanda dukiyarsa da 'ya'yansa ba su kara masa komai ba sai asara.

22. "Suka kuma shirya makirci babba.

23. "Suka kuma ce: 'Kada ku bar abubuwan bautarku, kuma lalle kada ku bar Waddu da Suwa'u da Yagusu da Ya'uƙu da Nasaru."

24. "Hakika kuwa sun batar da adadi mai yawa; kar kuma Ka kari kafirai da komai sai bata."

25. Saboda saɓonsu ne aka nutsar da su, sai aka shigar da su wuta, don haka, ba su sami wasu mataimaka ba Allah ba.

26. Nuhu ya ce: "Ya Ubangijina, kada Ka bar wani mutum daya daga kafirai a bayan kasa.

27. "Lalle idan har Ka bar su, to za su batar da bayinka, kuma ba za su haifi kowa ba sai fajiri mai tsananin kafirci.

28. "Ya Ubangijina, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma wadanda suka shiga gidana suna muminai, da kuma (sauran) muminai maza da mata, kada kuma Ka kari kafirai da komai sai hallaka."

To bayan da Allah Ya amsawa Annabi Nuhu (AS) roƙonsa na cewa zai halakar da waɗanda ba su yi imani ba, sai Ya umarce shi da ya fara ginin jirgin ruwa. Ibn Kathir ya ce Allah Ya umurce shi da yanke wasu itatuwa, ya haɗa su da tarin laka ko taɓo sannan ya gina jirgin ruwa mai girma. Lokacin da Annabi Nuhu (AS) ya fara aikin gina jirgin ruwan sai Mutanen gari su ka fara yi masa dariya suna tambayarsa, “Kana gina jirgi a cikin hamada, cikin rairayin sahara? Ina ruwan da jirgin zai hau?” Amma shi bai kula su ba, domin ya san cewa umarnin Allah ne.

A duk sanda su ka zo wucewa sai sun masa izgili da rashin kunya, an ce har
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RUWAN DUFANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album