Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KISSAR BILKISU MAI GADON ZINARE Complete Hausa Novel Document by KISSAR BILKISU MAI GADON ZINARE


KISSAR BILKISU MAI GADON ZINARE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 3496



KISSAR BILKISU MAI GADON ZINARE

Reading Time: 0 Hours

Added On: 02, Apr 2025

Author: Bashir Halilu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 19.5 kb

File Type: txt

Views: 24+

Download: 3+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: ƘISSAR BILƘISU MAI GADON ZINARE

Matar Annabi Sulaimanu Alaihis salam.

Daga shafin Bashir Halilu

Acikin Alkur'ani mai girma, Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa:

وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَالِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ الْغَابِبِينَ لَأُعَذِّبَنَّهُ عَذَابًا شَدِيدًا أَوْ لَأَأَذْبَحَنَّهُ أَوْ لَيَأْتِيَنِي بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيدٍ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِهِ، وَجِئْتُكَ مِن سَبَإٍ بِنَبَإٍ يَقِينٍ إِنِّي وَجَدتُّ امْرَأَةَ تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِن كُلِّ شَيْءٍ وَلَهَا عَرْشُ عَظِيمٌ * وَجَدتُهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِن دُونِ اللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ فَهُمْ لَا يَهْتَدُونَ *

20. Kuma (Annabi Sulaiman) ya bincika tsuntsaye, sai ya ce: "Me ya sa ba na ganin Alhudahuda, ko kuwa yana cikin waɗanda ba sa nan ne?

21. "Na rantse zan yi masa azaba mai tsanani, ko kuma tabbas zan yanka shi, ko kuma lalle ya zo min da hujja bayyananniya."

22. Sai ko ba da daɗewa ba ya dawo, sannan (bayan an tambaye shi) ya ce: "Ni fa na gano abin da ba ka sani ba, na kuma zo maka da tabbataccen labari daga birnin Saba'u.

23. "(Shine) lalle na sami wata mace tana mulkar su, an kuma ba ta daga kowane abu (na mulki), tana kuma da gadon sarauta mai girma.

24. "Na same ta ita da mutanenta suna sujjada ga rana ba Allah ba. Shaidan kuma ya kawata musu ayyukansu, sai ya kange su daga bin hanya ta gaskiya, don haka su ba sa kan shiriya.

GA CIKAKKIYAR ƘISSAR NANA BILƘISU MAI GADON ZINARE.

Ibnu Kathir ya kawo a cikin littafinsa Al-Bidāyah wan-Nihāyah cewa: "Ita ce Bilkisu ‘yar As-Sayrah, Mahaifinta yana daga cikin manyan sarakuna, kuma yana kin auren ‘yan asalin Yemen. Sai ya auri wata mace daga Aljanu mai suna Rayhana bintus Sakan, wadda ta haifa masa wata diya mai suna Talqamah, wadda kuma ake kira da Bilƙisu." بلقيس

An yi wa Bilƙisu laƙabi da wannan suna ne bayan ta hau karagar mulki, ma’anarsa kuma ita ce "Alƙiyās", wato kwaikwayon mahaifinta. Ta gaji sarauta daga mahaifinta, Al-Hadhad bin Sharhabil, wanda ya fito daga zuriyar Banu Ya’fur.

Bilkisu ta kasance ‘yar sarauta mai tsatson daraja, kuma sunanta yana nufin "damuwa da bakin ciki". Mahaifinta bai samu ‘ya’ya maza ba, shi ya sa ya damƙa mata ragamar mulki, domin yana da cikakkiyar amana a gare ta.

Bayan ta zama sarauniya a masarautar Saba’u, mutanenta sun nuna rashin yarda da ita, har ma su ka raina jagorancinta. Wannan ya sa labarin rashin amincewarsu ya bazu zuwa ƙetaren iyakokin masarautar, lamarin da ya jawo hankalin wasu sarakuna makwabta da ke da burin kwace mulkinta, daga cikinsu har da sarki Zul-Adh’ar (Amr bin Abrahah).

Bilƙisu ta kasance mace mai basira, dabara, da ƙwarin gwiwa. Da ta fahimci cewa Zul-Adh’ar yana shirin yaƙar ta, sai ta ɗauki dabarar ɓuya. Ta saka kaya kamar na wani Balarabe, ta bar masarautarta ita kaɗai ba tare da an gan ta ba, har ta isa ga sarkin. Ta yaudare shi da maganganun soyayya, ta ce za ta aure shi kuma za ta ba shi mulkinta. Ta rika zuba masa giya har sai da ya bugu ƙwarai, yana tunanin tana janye shi ne da ƙauna. Da ya bugu mankas sai ta zaro wuka ta kashe shi.

Daga nan sai ta koma masarautarta da nasara, ta ƙarfafa matsayinta a idon mutanenta. Wannan lamari ya zama darasi gare su cewa babu damar tada husuma, kuma mace ma tana da cikakken ƙwazo da iya tafiyar da masarauta.
Ibnu Kathir_ Albidayah wan nihayah.

Idan mu ka koma cikin Alkur'ani kuwa, A wadannan ayoyi na suratun Namli da mu ka kawo, Allah (Mai tsarki da daukaka) Ya bayyana cewa: wata rana Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fita zuwa wata tafiya, a tare da shi akwai jama'a da yawa, sai ya zo yana bibiyar rundunoninsa na aljannu da mutane da tsuntsaye, don ganin halin da suke ciki. Lokacin da ya zo kan tsuntsaye sai bai ga tsuntsun Alhudahuda a cikinsu ba. An ce kuwa Alhud'huda yana da amfani acikin tawagar, domin shi ne ya ke nemo musu inda ruwa yake, daga nan sai a tura Aljanu su ɗebo, ko kuma su tona rijiya a ɗiba. Sai Annabi Sulaiman (AS)ya tambaya cewa, me ya sa bai ga Alhudahuda ba? Watau shi ne bai gan shi ba yana cikin ribibi ko kuma dai ba ya wurin ne? Sai aka sanar da shi cewa ba ya nan. Sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi barazanar cewa lallai idan ya dawo sai ya yi masa azaba mai tsanani, ko ya yanka shi sakamakon rashin ganin sa da ya yi, ko kuma ya zo masa da wata bayyananniyar hujja karba66iya wadda za ta nuna uzurinsa a fili.

Ba a jima ba kuma sai ga Alhudahuda ya dawo, ya bayyana wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) uzurinsa na tafiya yaho, bai dawo da wuri ba, da cewa ya gano masa wani abu da shi bai san da shi ba, domin ya zo masa da wani sahihin labari wanda babu kokwanto a cikinsa daga birnin Saba'u na kasar Yaman. Watau ya samu mutanen wannan birnin wata mata ce take mulkinsu, kuma an ba ta duk wani abu da mulkinta yake bukata na karfin mayaka da tattalin arziki, sannan kuma tana da wani gadon sarauta mai girman gaske wanda takan hau shi don gudanar da sha'anin mulkinta. Alhudahuda ya ci gaba da bayyana wa Annabi Sulaimanu abin da ya gano a birnin Saba'u, da cewa ya sami wannan mata mai mulki da mutanenta suna bautar rana ne ba Allah ba, kuma Shaidan ne ya ƙawata musu ayyukan shirka da saɓon Allah da suke yi, ya kuma hana su bin hanyar gaskiya, don haka suka kasa shiryuwa su bauta Wa Allah shi kadai wanda yake fito musu da ruwan da yake ɓoye a sama, da tsirran da suke cikin kasa, kuma yake sane da ayyukansu da suke boyewa da wadanda suke bayyanawa. Shi ne Allah wanda babu abin bauta da gaskiya sai shi Ubangijin Al'arshi mai girma.

Lokacin da Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji duk bayanan Alhudahuda, sai ya bayyana masa cewa za su duba su yi bincike don tabbatar da gaskiyar labarinsa ko karyarsa, watau kafin su san irin matakin da za su dauka a kai.

Daga nan sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fara ɗaukar matakin bincike, ya rubuta takaitacciyar wasika ya ba Alhudahuda don ya isar da ita ga Sarauniyar Saba'u, ya umarce shi da ya je garin ya jefa musu wannan wasikar, sai ya dan ja da baya kadan ya tsaya inda zai ji abin da Sarauniya da fadawanta za su tattauna a kansa da kuma irin martanin da za su dawo da shi.
Malaman tarihi su ka ce, sai Alhudahuda ya ɗauki wasiƙar, ya je har ɗakin daBilƙisu ta ke kwance da sassafe, daidai lokacin hudowar rana, wato lokacin da ta ke tashi ta yi wa rana sujjada, ya buɗe tagar ɗakin na ta. Kawai sai ta ga ahsken rana ya dallare ma ta ido, sai Alhudahuda ya jefa ma ta takardar, ya koma gefe, ba ta san wa ya jefo ma ta ba.
Bayan Alhudahuda ya aikata abin da aka umarce shi da shi, wasika ta je hannun Sarauniyar Saba'u, ta kuma karanta ta ga abin da yake ciki, sai ta tara manyan gari a fadarta ta fada musu cewa an fa jefo mata wasika mai girma. Abin da wasiƙar ta ƙunsa kuwa shi ne, "Wannan wasika daga Sulaimanu take" kuma an bude ta da Bismilla, watau "Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin kai". Sannan wasikar ta ce: "Lalle kada ku yi min girman kai, ku zo min kuna masu mika wuya". Watau dai yana sanar da su cewa kada su bijire masa, su zo suna masu mika wuya ga abin da yake kiran su a kai na Kaɗaita Allah da barin shirkar da suke kai ta bautar rana. Ta kuma tabbatar musu da cewa ba za ta yanke komai ba a kan wannan al'amari har sai ta saurari shawarwarinsu da ra'ayinsu.

Sai su ka mayar mata da jawabi da cewa, su mutane ne karfafa kuma jaruman mayaka, saboda haka ko da ta bijire wa Annabi Sulaimanu ta ki yarda da shi, to su a shirye suke su fafata yaki a kan haka, amma dai sai suka mayar da magana gare ta domin sun yarda da cewa ita mace ce mai zurfin hankali, don haka
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KISSAR BILKISU MAI GADON ZINARE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album