Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KISSAR UZAIRU Complete Hausa Novel Document by KISSAR UZAIRU


KISSAR UZAIRU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 2193



KISSAR UZAIRU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 02, Apr 2025

Author: Bashir Halilu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 12.93 kb

File Type: txt

Views: 31+

Download: 2+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: ƘISSAR UZAIRU

Mutumin da ya mutu tsawon shekara ɗari sannan su ka sake tashi, shi da jakinsa.

Daga shafin Bashir Halilu.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya faɗa a Alƙur'ani cewa:

أَوْ كَالَّذِي مَرَّ عَلَى قَرْيَةٍ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَى عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّى يُحْيِ هَذِهِ اللَّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا فَأَمَاتَهُ اللَّهُ مِائَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ قَالَ لَبِثْتُ يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ قَالَ بَل لَبِثْتَ مِائَةَ عَامٍ فَانظُرْ إِلَى طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّةٌ وَأَنظُرْ إِلَى حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ ءَايَةً لِلنَّاسِ وَأَنظُرْ إِلَى الْعِظَامِ كَيْفَ نُنشِرُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْمًا فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ •

Ma'ana:
"Ko kuma kamar mutumin da ya wuce ta wata alkarya alhalin ta zama kango, sai ya ce: "Ta yaya Allah zai raya wannan bayan mutuwarta?"

Sai Allah Ya karbi rayuwarsa tsawon shekara ɗari, sannan Ya tashe shi, Ya ce: "Mene ne tsawon lokacin da ka zauna?" Sai ya ce: "Ai na zauna yini daya ne ko ma wani sashi na yinin."

Sai Ya ce: "Ai ka zauna tsawon shekara dari ne, don haka dubi abincinka da abin shanka bai canja ba, kuma ka dubi jakinka mana ka gani, don Mu sanya ka ka zamanto aya ga mutane, kuma ka dubi kasusuwan ka gani yadda za Mu hada su, sannan Mu lullube su da nama."To lokacin da komai ya bayyana a gare shi, sai ya ce: "Na sani lalle Allah Mai iko ne a kan komai."

GA CIKAKKIYAR ƘISSAR

Is'haq bin Bishr ya ce: Sa’id bin Bashir ya ba mu labari daga Qatadah, daga Ka’ab, haka nan Sa’id bin Abi ‘Arubah daga Qatadah, daga al-Hasan, haka nan kuma Muqatil da Juwaybir daga al-Dahhak, daga Ibn Abbas. Haka nan Abdullah bin Isma'il al-Suddi daga mahaifinsa, daga Mujahid, daga Ibn Abbas, da kuma Idris daga kakansa, Wahb bin Munabbih. Is'haq bin Bishr ya ce: “Dukkansu sun ba ni labari game da lamarin Uzair, kuma wasu sun ƙara bayani akan na wasu.”

Suka ce da isnadinsu:
Uzair bawan Allah ne salihi kuma mai hikima. Wata rana ya fita zuwa gonarsa don duba halin da ta ke ciki. Da yake dawowa, sai ya tsaya a wani wuri da ya ruguje. Wani babbar birni ne wanda aka samu wani azzalumin Sarki yakai musu hari, ya ruguza gari, ya kashe dukkan mutanen cikinsa. A daidai lokacin da Uzairu ya sauka wajen rana ta yi tsananin zafi. Ya shiga cikin wannan wuri yana kan jakinsa. Ya sauka daga jakin tare da wasu kwanduna biyu, ɗaya da ‘ya’yan itacen ɓaure ɗaya da inabi. Ya zauna a cikin inuwar wannan wuri, ya ɗauko tasa, ya matse ‘ya’yan inabin da yake tare da shi a ciki. Sannan ya fitar da wata busasshiyar gurasa da yake tare da ita, ya jefa ta a cikin ruwan inabin domin ya jiƙa, ya kasance mai sauƙin ci.
Bayan haka, ya kwanta a bayansa tare da jingina ƙafafunsa ga bango.

Ya dubi rufin waɗancan gidaje, ya ga sun tsaya, amma mutanensu sun hallaka. Ya kuma ga ƙasusuwan da suka zama tsofaffi su ka ruɓe. Sai ya ce: "Ta yaya Allah zai raya waɗannan bayan mutuwarsu?"

Ba shakka ya san cewa Allah na iya yin haka, amma ya faɗa ne cikin mamaki da tunani. Sai Allah ya aiko Mala’ikan Mutuwa ya karɓi ransa, kuma ya mutu har tsawon shekaru ɗari.

Bayan waɗannan shekaru ɗari, an samu abubuwa da dama a cikin al’ummar Banu Isra’ila. Allah ya aika wani mala’ika zuwa ga Uzair, ya fara sake halitta zuciyarsa don ya fahimci abubuwa, sannan idonsa don ya iya gani, domin ya ga yadda Allah ke raya matattu. Daga nan, mala’ikan ya gina jikinsa sannu a hankali yana kallo, sai aka rufe ƙasusuwansa da nama, da gashi, da fata. Sai mala’ikan ya hura masa rai, kuma duk wannan yana faruwa shi Uzairu yana gani da fahimta.

Bayan ya farfaɗo, mala’ikan ya ce masa: "Kwana nawa ka yi a kwance?" Sai Uzair ya ce: "Na kwana rana guda ko rabin rana." Saboda ya farka lokacin yamma, kuma rana ba ta faɗi ba, sai ya ɗauka bai cika kwana ba. Mala’ikan ya ce: "A’a! Ka kwana shekaru ɗari!"

Sai ya ce masa: "Ka duba abincinka da abin shanka." Ya duba, ya ga busasshen burodinsa da ruwan inabin a daidai yadda suka kasance, ba su canza ba. Allah ya kiyaye su daga lalacewa, kamar yadda ya ce: "Ba su canza ba."

Sai mala’ikan ya tambaye shi: "Shin ka yi shakka?" Sai ya ce: "A’a, amma abin mamaki ne." Sai mala’ikan ya ce: "To, duba jakinka." Ya duba, ya ga ƙasusuwan jakinsa sun ruɓe sun zama ƙura. Sai mala’ikan ya kira waɗancan ƙasusuwan, suka tattaru suka haɗu, yana kallo. Sai ya sa musu jijiyoyi da tsokoki, ya rufe su da fata da gashi, sannan ya hura masa rai. Nan da nan jakin ya tashi yana haki yana duba sama, yana zaton tashin kiyama ne.

Bayan haka, Uzair ya ce: "Na tabbatar Allah na iya yin komai!"

Ya hau jakinsa ya koma garinsu. Amma sai ya taras mutanen garin ba su gane shi ba, shi ma bai gane su ba. Har ya isa gidansa, sai ya taras da wata tsohuwa makauniya, mai nakasa da shekarunta suka kai 120. Ita ce ‘yar aikinsu tun yana da shekaru 20. Sai ya ce mata:

"Ke kuwa, wannan gidan Uzair ne?"

Sai ta ce: "Eh, wannan gidan Uzair ne." Sai ta yi kuka ta ce: "Tun shekaru da yawa ba wanda ya ambaci Uzair, har an manta da shi."

Sai ya ce: "Ni ne Uzair! Allah ya kashe ni na tsawon shekaru ɗari, sannan ya raya ni."

Sai ta ce: "Subhanallah! Uzair yana daga cikin waɗanda Allah Ya ke amsa musu addu’a. Idan har kai ne Uzair, to ka roƙi Allah ya dawo min da idona don in gan ka, idan har kai ne zan gane ka."

Sai ya yi addu’a, ya shafa hannunsa a idonta, nan da nan suka warke. Ya kama hannunta, ya ce: "Tashi da izinin Allah!" Sai Allah ya warkar da kafafunta, ta miƙe kamar wadda aka daure aka saki.

Da ta ga shi, sai ta ce: "Na rantse, kai ne Uzair!"

Sai ta fita ta sanar da mutanen Banu Isra’ila. A cikin su akwai ɗansa, wanda shekarunsa 118, da jikokinsa da suka girma. Sai mutanen suka zo suna kallonsa. Sai ɗansa ya ce: "Idan har kai ne babana, to yana da wata alama a bayansa."

Sai suka duba bayansa, suka ga wannan alama, sai suka tabbatar da cewa shi ne Uzair. Sai Banu Isra’ila suka ce: "A baya, babu wanda ya haddace Attaura sai Uzair. Kuma Buktunassar ya ƙone Attaura, ba wanda ya haddace ta sai ‘yan kaɗan. To, sake rubuta mana ita!"

Sai Uzair ya jagorance su zuwa inda mahaifinsa ya binne Attaura a zamanin Buktunassar. Suka tono ta, amma takardun sun ruɓe, rubutun ya ɓace. Sai Uzair ya zauna a ƙarƙashin wata itaciya, sannan Allah ya aika wasu haske guda biyu daga sama, suka shiga cikinsa. A nan ne ya tuna dukkan Attaura, ya sake rubuta ta ga Banu Isra’ila.

Saboda haka, Yahudawa suka ce: "Uzair ɗan Allah ne!" - (Sub'hanAllah!). Sun faɗi haka ne saboda wannan mu'ujiza ta sake dawo da Attaura da kuma irin matsayinsa a cikin su.

Wannan labari yana cikin abin da Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: "Muna so mu sanya ka a matsayin wata aya ga mutane." Uzair yana zaune tare da ‘ya’yansa masu tsufa, amma shi kansa matashi ne, domin an mayar da shi kamar lokacin da ya mutu yana da shekaru 40.

Abu Hatim al-Sijistani ya rera wata waka don bayyana mamakin wannan lamarin:

"Shugaban da ya tsufa, amma dansa da jikansa sun fi shi shekaru,
Yana ganin jikansa mai tafiya da sanda, amma shi kansa matashi ne.
Jikansa mai shekaru 90 yana tafiya cikin rauni,
Amma shi matashi ne mai ƙarfin jiki!"

Wannan ita ce mu’ujizar Annabi Uzair, wadda ta tabbatar da ikon Allah na raya matattu!

Alhamdu lillahi.

Daga shafin Bashir Halilu
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KISSAR UZAIRU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album