Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA


HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 10085



HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Danladi Z Haruna ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 50.99 kb

File Type: txt

Views: 463+

Download: 118+

Last download: 3 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

1ARZIKI RIGAR ƘAYA (1)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Sarkin Bagadaza, kuma Sarkin Musulunci, Halifa Haruna Rashid na zaune kan karagar mulki ya harɗe, fadawa kuwa sun kewaye shi ana tsakiyar fadanci sai ga wani saurayin bawa ya shigo riƙe da wata hula da masu mulki ke sanyawa. Ita wannan hula ana kiran ta kambin sarauta. Wannan kambi da bawa ya shigo da shi an ƙera shi da jan zinari aka yi masa ado da lu'ulu'u da jauhari da dukkan duwatsu masu daraja, amma ba a rufe saman shi ba. Wannan kambi babu tamkarsa a wannan zamani, kambi ne da kuɗi ba zai iya saye ba.

Bawa ya faɗi gaban Sarki ya yi gaisuwa, sa'annan ya ce, "ya Sarkin Musulunci, Uwargida Zubaidatu ce ta aiko ni gare ka da wannan kambi da ta sa aka ƙera mata. Ga shi an kammala ƙera shi, ta nemi jauharin da za a liƙe saman shi, ta kasa samun wanda ya yi daidai a cikin taskarta, duk wanda aka gwada sai a ga ya yi ƙarami."

Sarki ya dubi barori ya ce a tafi a dubo irin jauharin da Zubaidatu ke buƙata. Barori suka zabura da hanzari suka tafi. Can jimawa sai ga su sun dawo. Suka ce wa Sarki, "Allah ya taimake ka, mun duba taskar Sarki duka, amma ba a samu jauharin da ya yi daidai da wannan hula ba."

Halifa ya fusata ya ce, "ta yaya Sarki kamata, wanda ya mallaki sarakunan duniya duka, ɗan ƙanƙanin abu kamar wannan ya gagare ni mallaka. Kaicon ku! Ku tafi cikin kasuwanni, ku binciki dillalai da tajirai da fatake, maza ku nemo wa uwargida abin buƙatarta."

Barori suka fantsama cikin kasuwannin Bagadaza suna cigiya, har Allah ya gajishe su ba su samu jauhari mai girman da suke buƙata ba. Suka dawo gaban Sarki suka ce, "ya Sarkin Musulunci, wannan abu ya wuyata ga tajiran wannan birni da fataken da ke shigowa. Amma an ba mu labari cewa, ba za a samu wannan jauhari gun kowa ba, sai wurin wani attajiri ɗaya da ke zaune a birnin Basara mai suna Abu Muhammad Kasala."

Yayin da Halifa ya ji wannan zance, sai ya umurci wazirinsa, mai suna Ja'afaru al-Barmaki, da ya rubuta takarda zuwa ga Hakimin Basara, Muhammad al-Zubaidi, ya faɗa masa cewa, maza-maza a zo masa da tajiri Abu Muhammad Kasala zuwa Bagadaza.

Nan take Waziri Ja'afaru ya ɗauki takarda da alƙalami ya rubuta saƙon Sarki zuwa ga Hakimin Basara. Ya buga hatimi kan takarda ya naɗe ta, ya danƙa wa Masrur as-Siyafi, babban haunin Sarki. Wanda shi kuma nan take ya yi shiri tare da 'yan rakiya, suka rankaya sai birnin Basara.

Hakimin Basara ya tarye su da murna, ya shirya musu gara, suka sharɓa. Bayan sun huta sai Masrur ya ce wa Hakimin Basara, "to, ba fa zama muka zo yi ba." Ya zaro takarda, ya karanta wa Hakimi saƙon Sarkin Musulmi. Hakimin Basara ya ce, "na ji, na karɓa." Nan take ya shirya wata tawaga ya haɗa su da Masrur suka nufi gidan tajiri Abu Muhammad.

Da isar su gidan sai suka ƙwanƙwasa ƙofa. Wani bawa ya buɗe ƙyaure ya leƙo. Masrur ya ce masa, "je ka wurin ubangidanka ka faɗa masa cewa, Shugaban Muminai na nemansa zuwa Bagadaza."

Bawa ya koma cikin gida. Jim kaɗan sai ga tajiri ya fito. Ko da ya ga Masrur tare da tawagar Hakimin Basara, sai ya faɗi ya yi gaisuwa, sannan ya ce, "na ji, na kuma karɓa kiran Sarkin Musulmi. Amma ba kwa shigo daga ciki ba, ko ɗan ruwa ku kurɓa kafin na kimtsa mu tafi?"

Masrur ya ce, "ai ba dama, sata lahira! Halifa na can na jiran mu. Don haka babu buƙatar ɓata lokaci. Maza shirya ka fito mu tafi, kafin ran Halifa ya ɓaci."

Tajiri ya ce, "to bari na shiya yanzu mu tafi, amma ku shigo daga ciki ku zauna, kun san an ce shirin zaune ya fi na tsaye. Idan na shirya kuma na samu ɗan guzurin da zan kai wa Halifa, domin zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri." Ya yi ta lallashin su dai, har suka yarda suka shiga cikin gidan.

Da kutsa kansu cikin turakar farko ta gidan, sai suka ga an daje duka bangayen nan da labulayyen alharini wanda aka yi wa cin baki da ɗanyen jan zinari, aka ƙawata su da duwatsu masu ƙyalƙali da daukar ido. Abu Muhammad ya umurci ɗaya daga cikin bayinsa da ya kai Masrur bayi, ya yi wanka, ya fitar da ƙurar tafiya daga jikinsa.

Bawa ya yi wa Masrur jagora har zuwa ɗakin wanka. Masrur ya ga ɗakin wankan da bai taɓa ganin irinsa ba. Bangayen ɗakin da daɓensa duka na duwatsu ne masu darajar gaske, waɗanda aka cakuɗa da zinariya da azurfa. Ruwan wankan kuma an gauraya su da ruwan wardi.

Bayi suka himmatu wajen yi wa Masrur da 'yan rakiyarsa hidima yayin da suke wanka. Da suka gama wanka, aka ba su tufafi na alfarma, waɗanda aka yi wa ado da kumfar zinari yayin saƙa su, suka sanya.

Bayan Masrur da 'yan rakiyarsa sun kimtsa sai suka nufi inda Abu Muhammad Kasala ke jiransu, suka tarar da shi zaune bisa wani dandamali da aka yi cikin turakarsa. A saman wannan dandamali aka girke wata ƙatuwar kujera mai kama da gado, wadda aka shinfiɗa wa katifu, aka lulluɓe katifun da zannuwan alharini. A saman wannan kujera maigidan yake zaune. Bangon da aka jingina kujerar kuma an lulluɓe shi da labulen hatsaya da alharini da aka saƙa su tare da zinariya, aka kuma lilliƙa masa duwatsun jauharai masu launi daban-daban.

Sa'adda Masrur ya shigo cikin turakar, sai Abu Muhammad ya sauko daga kan kujera, ya tarye shi da fara'a, ya sake yi masa maraba. Ya ja shi suka koma kan kujearar suka zauna wuri guda, sauran mutane kuma suka zauna kan kujerin da ke cikin turakar. Daga nan mai gida ya yi umurni da a fito da abinci da abin sha. Nan da nan bayi da kuyangi suka yi ta jido akussan abinci da gorunan abin sha suna girkewa a gaban baƙin nan.

Masrur ya saki baki yana tu'ajjibin kyawun akussan da aka kawo musu abinci a ciki, su dai ba daga itace aka sassaƙa su ba, ba kuma da dutse aka yi su ba, to ko da ƙashi aka yi su? Oho. Ya ce a ransa, 'na rantse da Allah ban taɓa ganin akussa masu kyau kamar waɗannan ba, waɗanda babu irinsu ko da a fadar Halifa.'

Kowane akushi da irin abincin da ke cikinsa, wani an zuba soyayyen nama, a wani kuma an zuba dafaffe. A wani akushin kuma an zuba farar shinkafa da zuma, wani kuma gurasa ce da miya. Aka dai girke musu abinci iri daban-daban. Suka fara ci suna taɗi, suna annushuwa, ba su farga ba har dare ya ƙwace musu. Da za su koma masauki, Abu Muhammad ya ba kowannensu dinari dubu biyar.

Washegari kuma ya ƙara yi musu kamar yadda ya yi musu jiya. Ya tufatar da su tufafi na alfarma, masu launin kore da ruwan zinari. Ya himmatu ga yi musu hidima. Da Masrur ya ga suna shirin shantakewa, sai ya ce wa Abu Muhammad, "ya kamata ka shirya mu tafi, kada Halifa ya ga mun daɗe, ransa ya ɓaci."

Abu Muhammad Kasala ya amsa masa da cewa, "ya shugabana, yi haƙuri dai ka jinkirta mini, zuwa gobe na gama duk shirin da nake yi, sai mu tafi." Don haka suka sake kwana ɗaya.

Da gari ya waye, Abu Muhammad ya sa bayi suka shirya masa wata alfadararsa da yake hawa. Sirdin da aka ɗaura wa alfadarar da sauran kayan da aka shirya ta da su duka an yi su ne daga zinariya da azurfa da lu'ulu'u, sai ɗaukar ido suke yi cikin rana. Masrur ya dubi alfadarar nan, ya ce cikin ransa, 'zan yi mamaki idan har Halifa bai tuhumi Abu Muhammad yadda ya yi wannan arziki, idan ya je masa da tarin dukiya haka.' Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
29/04/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (2)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci.

Suka wuce kai tsaye wurin Halifa. Bayan sun yi gaisuwa, Halifa ya umurci Abu Muhammad da ya zauna. Da ya zauna, sai ya sake gayar da Halifa da kyakkyawan lafazi, sa'annan ya ce, "Ya shugaban muminai, na zo maka da wata 'yar tsaraba, idan ka yarda na kawo ta gabanka yanzu."

Halifa ya ba shi dama. Daga nan sai Abu Muhammad ya ɗauko akwati ya buɗe shi, ya fara zaro tsarabar da ya kawo wa Halifa, tsarabar da babu tamkarta. Daga cikin tsarabar akwai wata bishiya da aka yi jikinta da zinariya, rassanta da yaƙutu, ganyayenta da zabarjadi, 'ya'yanta da lu'ulu'u, girman 'ya'yan kamar ƙwayayen tattabara. Halifa ya cika da mamakin ganin wannan itaciya, gayar mamaki.

Abu Muhammad ya kuma jawo wani akwati ya buɗe, ya zaro tanti irin wanda ake kafa wa sarakuna idan sun fita shan iska bayan gari, ko idan an tafi farauta ko yaƙi. Shi wannan tanti an yi rufinsa ne da dardumar da aka saƙa daga alharini da jauharai iri daban-daban, aka ƙawata ta da kwalliyar zinariya da yaƙutu da zabarjadi aka kuma yi zanen surorin tsuntsaye da dabbobi iri-iri, na gida da na daji. Sandunan da ake kafa tantin da su kuwa an yi su ne daga ɗanyen itacen turaren sandal ɗan asalin Hindu, waɗanda da zarar an fito da su waje, wuri zai gume da ƙamshi.

Halifa ya yi mamki matuƙar mamaki da waɗannan abubuwa da ya gani. Abu Muhammad ya duƙar da kai ya ce, "Ya Sarkin Musulunci, ban kawo maka wannan tsaraba don kwaɗayin wani matsayi da za ka naɗa ni ba, ban kuma kawo maka su ba a matsayin rashawa wai don wani laifi da ba aikata. Na kawo maka su ne domin kuwa babu wanda ya dace da waɗannan kaya sai kai. Ni ba kowa ba ne face talaka daga cikin talakawanka. Kuma idan Halifa ya yarda, zan nuna masa wata baiwa da Allah ya hore mini."

Halifa ya ce, "Aikata abin da kake so mu gani."

Abu Muhammad ya ce, "To, madalla."

Ya dubi wani gini da ke cikin fadar, ya motsa leɓɓansa kamar mai karanta wata addu'a, sai mutane suka ga ginin ya zo gabansa ya rusuna. Abu Muhammad ya sake yin wata ishara, sai ginin ya koma inda yake, ya kuma miƙe kamar yadda yake da fari. Daga nan kuma ya yi wata alama da idanunsa, sai aka ga dogayen akwatuna sun bayyana a cikin fadar. Ya yi musu magana, sai mutane suka ji kukan tsuntsaye na fitowa daga cikin akwatunan.

Waɗannan abubuwa sun ƙayatar da Halifa ainun. Ya ce wa Abu Muhammad, "Ya aka yi ka samu duka waɗannan abubuwa? Shin ba kai ne ake kira Kasala ba saboda ragwanci? An fa ce mini mahaifinka wanzami ne, mai yi wa mutane aski a gidan wanka. An kuma ce mini bai bar maka komai ba sa'adda ya mutu."

Abu Muhammad ya ce, "Ya Halifa, abin duk da mutane suka faɗa maka game da ni gaskiya ne, amma saurari labarina ka ji. Akwai abin al'ajabi a cikinsa, wanda da za a rubuta shi da tsinin allura bisa ga kusurwar ido da ya zama abin lura ga masu hankali.

Ka sani cewa, ya Shugaban Muminai, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana. Kamar yadda ka ji mutane sun ba ka labarin ƙuruciyata, to, haka ne. Ko da mahaifina ya mutu bai bar mini kome ba sai zabirar aski domin kuwa shi wanzami ne, kamar yadda ka faɗa.

Lokacin da nake yaro ana kirana da suna Abu Muhammad Kasala saboda tsabar ragwancina, ga kuma son jiki sai ka ce kyanwa. Saboda kasala idan na kwanta barci a cikin inuwa sai rana ta cim mini, ina ji ina gani, ban tashi ba, kome kuɗar da take yi mini ba ni tashi in shiga inuwa sai fa in wani ya zo ya riƙa ni na tashi. Haka na tashi a sangarce har na kai shekara goma sha biyar, lokacin ne kuma mahaifina ya karɓa kiran Ubangiji. Ya mutu bai bar mini kome ba na dukiya, sai zabirarsa ta aski.

Bayan rasuwar mahaifina, sai mahaifiyata ta shiga ɗawainiyar neman aikin da za ta riƙa samo mana abinci, har ta yi gamo da katar ta sami wurin aiki. Sai ya kasance kullum tana zuwa wurin aiki domin samo mana abin kalaci. Ni kuwa kullum ina kwance gida, sai ka ce ruwa, in mimmiƙe abina bisa shinfiɗa ina jiran dawowarta. Idan ma ta dawo ba na iya tashi sai ta kama ni ta zaunar, sai ka ce mara lafiya. Abincin ma sai ta ba ni ga baki sannan zan ci.

Ran nan ina kwance bisa shimfiɗa, sai ga mahaifiyata ta shigo inda nake, riƙe da dirhami biyar na azurfa. Ta ce mini, "Ya ɗana, na ji labarin cewa Dattijo Abu Muzaffar zai tafi fatauci Birnin Sin. Tashi mu tafi wurinsa mu ba shi waɗannan kuɗin, idan ya isa Birnin Sin ya sayo maka wata haja da su, wadda idan aka sayar da ita nan za a sami riba, idan zai koma kuma, mu ƙara ba shi wasu kuɗin tare da ribar ya ƙara sayo mana wata hajar. Wa ya sani ko Ubangiji ya yi mana arziki da waɗannan 'yan kuɗin, domin kuwa shi ne mai arzutta wanda ya so ta inda ba ya tsammani."

Ni kuwa a lokacin na ji daɗin kwanciyar da na yi, ba na son ko motsa ƙafata saboda ragwanci. Yayin da mahaifiyata ta ga haka sai ta yi fushi, ta ce, "Na rantse da Allah, idan ba ka tashi mun tafi wurinsa ba, ba na koma kawo maka abinci ko nama. Ko ruwa ba zan ƙara kawo maka ba, sai dai yunwa ta kashe ka."

Yayin da na ji haka, ya Shugaban Muminai, kuma na tabbata lalle za ta aikata abin da ta faɗa idan ban tashi ba, sai na turɓune fuska, na ce da ita, "To, riƙa ni in tashi."

Ta kama hannuna na miƙe zaune. Na yi miƙa tare da hamma, na ce ta ɗauko mini takalmina. Ta tafi ta ɗauko. Na ce ta saka mini su ga ƙafata, ta saka mini. Daga nan sai na ce, to, ta riƙa ni in miƙe tsaye. Ta riƙa ni na miƙe tsaye, har za ta sake ni, na ce ni sai na dogara ga jikinta zan iya tafiya, idan kuwa ba haka ba faɗuwa zan yi. Haka dai ta yarda na jingina ga jikinta, muka tafi ina jan ƙafafu, jallabiyar da na...


Read / Download HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album