Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN


HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 62699



HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN

Reading Time: 5 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Yusuf Abdullahi A Jibaga ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 332.89 kb

File Type: txt

Views: 804+

Download: 314+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

(1) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN

A wani dadadden zamanin da ya shude, an yi wani Sarki wanda ake kira Shahruzzaman.
Wannnan Sarki ya tara rundunonin [ http://
fb.com/waziriaku ] yaki masu karfi da yawa. Ya
yi mulkinsa ne a wasu tsibirai da ke iyaka da
kasar Farisa, ana kiran wadannan tsibirai da suna
Tsibiran Kalidan. Har lokacin da Sarki
Shaharuzzaman ya fara tsufa, a cikin matansa babu wadda ta taba yin ko bari balle ya [ http://fb.com/waziriaku ] sami haihuwa.

Ga shi kuwa yana da mata hudu, dukkansu'ya'yan sarakuna, sa'annan yana da kuyangi guda
sittin wadanda ya mayar sadaka. Kowane dare [
http://fb.com/ waziriaku ] sai ya kwana da mace daya daga cikinsu, amma duk da haka Allah bai
nufi ko daya daga cikin matan nan nasa da daukar ciki ba. Wannan abu kullum yana damun
Sarki a cikin ransa har ya kasa jurewa ya fada
wa Waziransa.

Ya ce, "Ni ina jin tsoron sarautata da daulata sugushe idan na mutu ba tare da na sami magaji
ba." Wazirinsa ya ce, "Ya shugabana, mai da
kukanka ga [ http://fb.com/waziriaku ] Allah
Madaukakin Sarki, ka yawaita addu'a da kuma
rokonsa, domin shi ne mai jin rokon bayinsa."
Aka ci gaba da fadanci. Bayan an tashi daga
fada, Sarki na shiga gida sai ya yi alwala, ya yi
salla raka'a biyu, yana mai kaskantar [ http://
fb.com/waziriaku ] da kansa ga Ubangiji.
Da ya gama salla, ya daga hannuwansa sama, ya
kai kukansa ga Ubangiji ya roke shi da samun
haihuwa.
A cikin wannan dare ya shiga wurin matarsa
daya. Allah ma ji rokon bayinsa, a wannan dare
matar tasa ta dauki ciki. [ http:// fb.com/
waziriaku ] Yayin da ciki ya isa haihuwa, matar
Sarki Shahruzzaman ta haifi da namiji, wanda ya
kasance kamar wata ranar daren goma sha hudu,
saboda [ http://fb.com/waziriaku ] kyawunsa.

Sarki ya ambace shi da suna Kamaruzzaman. Ya
yi murna wadda bai taba yin irinta ba.
Ya sa aka kawata birni da kwalliya domin
shagalin bikin wannan haihuwa. Aka gayyato
manyan sarakuna da masu mulki, aka gayyato
mawaka daga kowane bangare na duniya. Da
ranar suna ta zagayo aka barke da shagali. Aka
kwana [ http://fb.com/waziriaku ] bakwai ana
biki, sa'annan kowa ya kama gabansa.
Sarki ya nemo mai shayarwa, da kuma masu
reno, ya kebe musu wuri na musamman a cikin
gidansa. Suka ci gaba da kulawa da
Kamaruzzaman.
Da ya fara wayo, aka [ http://fb.com/waziriaku ]
danka shi ga hannun manyan malamai suka ci
gaba da koyar da shi. Yaro ya tashi cikin
tsananin gata da kulawa har ya kai dan shekara
goma sha biyar. Siffofinsa na kyau suka fara [
http://fb.com/waziriaku ] bayyana, ya zama babu
tamkarsa ga kyau duk fadin kasar.
Uban kuma ya dauki soyayyar duniyar nan ya
makala masa, ya kasance dare da rana yana tare
da shi, ba ya son ko kuda ya taba shi. [ http://
fb.com/waziriaku ] Wata rana ana fadanci, sai
Sarki Shahruzzaman ya ce wa Wazirinsa, "Ni na
yi niyyar in yi wa dana aure, domin ina jin tsoron
zamani, domin zamani mai shudewa ne. Ina so in
ga aurensa tun ina raye kafin zamani ya yi
halinsa a kaina." Waziri ya ce, "Wannan gaskiya
ne, ya shugabana. Aure abu ne mai amfani da
kuma [ http://fb.com/waziriaku ] daukaka darajar
mutum.
Ya kamata a fara yi masa aure tun kafin ya hau
karagar mulki." Sarki ya sa aka kira masa
Kamaruzzaman. Yayin da ya taho gaban ubansa
sai [ http:// fb.com/waziriaku ] ya durkusa ya
gaishe shi da ladabi.
Uban ya dube shi ya ce, "Ya dana, ka sani cewa
na kira ka nan ne domin in sanar da kai cewa,
ina so in ga aurenka tun ina raye." Da jin haka
sai Kamaruzzaman [ http://fb.com/waziriaku ] ya
kada baki ya ce, faufau shi ba ya aure har duniya
ta nade.
Ya ci gaba da cewa, "Ya mahaifina, ni na karanta
a cikin littattafai makircin mata da sharrinsu
kala-kala, wanda ya sa na tsane su har na ji ba
zan iya aurensu ba har abada.
Ya mahaifina, [ http://fb.com/waziriaku ] ko ba
ka ji yadda wani mawaki yake cewa ba: "Idan ka
tambaye ni game da mata, ni masani ne game da
halayensu.
Idan suka ga kan mutum da furfura, ko kuma
suka ga dukiyarsa [ http://fb.com/waziriaku ] ta
karanta, shi ba ya da rabo daga cikin zuciyarsu.
Saurayi ba ya rabanta idan ya sakar wa mata
ragamarsa.
Sukan fitine shi, su hana shi sukuni [ http://
fb.com/ waziriaku ] a cikin rayuwarsa. Ko da
mutum ya shekara dubu, ba zai iya karance
dukkan makircinsu ba." Saboda haka ba zan taba
yin aure ba ko da za a shayar da ni kaskon
mutuwa." Yayin da Sarki ya ji haka sai ya kume,
ransa ya baci, duniya ta yi masa baki a kan
wadannan [ http://fb.com/waziriaku ] kalamai na
dansa. Amma da yake an ce so hana ganin laifi,
sai ya yi murmushin karfin hali, ya nuna kamar
abin bai dame shi ba.
Ya sallami Kamaruzzaman, ya tashi ya tafi.
Kamaruzzaman ya ci gaba da girma, kullum
kyawunsa da [ http://fb.com/waziriaku ] haibarsa
sai kara fitowa suke yi a fili.

Mutane sai mamaki suke yi da irin wannan
kyawo nasa. Duk lokacin da iska ta kada, ta kan
kwashi kamshin jikinsa ta tafi da shi [ http://
fb.com/waziriaku ] wuri mai nisa. Yana da wani
irin farin jini mai jan hankalin masoya kamar
mai karfe da karfe.

Ya kasance tamkar lambun farin ciki ga masoya
masu bege. Yana da zazzagar murya, da [ http://
fb.com/waziriaku ] tattausan lafazi. Hasken
fuskarsa kuwa yana kunyatar da hasken wata a
daren cikarsa.

Kumatunsa jajaye ne masu sheki, kamar furen
wardi. Jikinsa kuwa madaidaici ne, ba ya da kiba,
kuma ba siriri ba, kamar icen turare.
Kamaruzzaman ya kasance [ http://fb.com/
waziriaku ] kamar yadda aka ambata a wannan
waka: "Suka ce alheri ya tabbata ga Allah
wannan da ya halicce shi, ya daidaita shi. Shi ne
wanda yawunsa ya kasance tamkar sakar zuma
farar saka abar tacewa. Akan tsinci lu'ulu'u a
cikin wushirya tasa. Shi ne wanda ya shafe kowa
da kyawo a [ http://fb.com/ waziriaku ] cikin
zamaninsa.

Dukkan talikai suna dimauta domin kyawonsa.
Hakika an rubuta kyawo bisa fuska tasa. Mun
shaida babu mai dadin hali face shi." Bayan
shekara uku da yi wa Kamaruzzaman maganar [
http://fb.com/waziriaku ] aure, sai Sarki
Shahruzzaman ya kara kiransa, ya ce masa, "Ya
dana, za ka yi biyayya ga umurnina?"
Kamaruzzaman ya durkusa a gaban mahaifinsa
ya ce, "Me zai hana in yi maka biyayya [ http://
fb.com/waziriaku ] ya mahaifina?
Allah madaukakin Sarki ya umurce mu da yi wa
uwaye biyayya, muddin dai umurninsu bai saba
wa umurninsa ba." Sarki ya ce, "Ka sani cewa,
ya dana, babban burina yanzu a duniya bai [
http://fb.com/ waziriaku ] wuce a ce na ga
aurenka ba tun ina raye. Daga nan kuma sai in yi
murabus ka hau matsayina." ***
Wannan tsakure ne daga sabon littafinmu na
sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA..

IDAN WANNAN HIKAYA TASAMU KARBUWA
TAWAJEN YAWAN CÒMMENT TO ZAMU CIGABA
GOBE IN SHA ALLAHU IDAN BAI KABUBA KUMA
TO SAI WANI LOKACI ZAMU CIGABA —(2) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN.

Bayan shekara uku [ http://fb.com/ waziriaku ]
da yi wa Kamaruzzaman maganar aure, sai Sarki Shahruzzaman ya kara kiransa, ya ce masa, "Ya
dana, za ka yi biyayya ga umurnina?"
Kamaruzzaman ya durkusa a gaban mahaifinsa
ya ce, "Me zai hana in yi [ http://fb.com/
waziriaku ] maka biyayya ya mahaifina? Allah
madaukakin Sarki ya umurce mu da yi wa uwaye
biyayya, muddin dai umurninsu bai saba wa
umurninsa ba." Sarki ya ce, "Ka sani cewa, ya
dana, [ http://fb.com/waziriaku ] babban burina
yanzu a duniya bai wuce a ce na ga aurenka ba tun ina raye.

Daga nan kuma sai in yi murabus ka hau
matsayina." Da Kamaruzzaman ya ji wannan
zance, sai ya sunkuyar da kansa kasa, ya yi shiru
na wani dan lokaci. Sa'annan ya ta [ http://
fb.com/ waziriaku ] da kansa ya ce, "Ya
mahaifina, Na sani Allah ya umurce ni da in yi
maka biyayya, to amma ina rokonka, kada ka
matsa mini a kan wannan batu. Na riga na fada
maka cewa ba zan yi aure ba har abada, ko da
kuwa za a shayar da ni kaskon mutuwa.
Domin kuwa ni na karanta a cikin littattafai
hikayoyin mutanen da suka gabata, da hikayoyin
mutanen wannan zamani, na ji irin masifu da
bala'o'in da suka afka [ http:// fb.com/
waziriaku ] musu sakamakon makirce-makircen
mata.

Har wani mawaki yana cewa: "Wanda mace
mazambaciya ta kusace shi, ba ya samun kubuta
ko da ya gina katanga dubu ababen shafewa da
darma, ba su kare shi daga zambarta.
Mata masu ha'inci ne ga dukkan makusanci da
manesanci daga gare su. Su [ http://fb.com/
waziriaku ] ne masu tattausan hannu, masu
manyan cinyoyi, masu tozali ga kuben idanu. Me
ya fi kyawo daga wannan fada?
Idan suka kira ka ka tsaya, sukan harbe ka da
abin harbinsu da ba ya kuskure. Idan ka yi
zancen asiri da ita a cikin dare, gobe tana shayar
da shi ga waninka." Yayin da Sarki
Shaharuzzaman ya ji zancen dansa, sai ya yi
shiru bai ce masa kome ba.
Ya hadiye [ http://fb.com/waziriaku ] fushinsa
saboda kaunarsa da yake yi. Ya sallame shi ya
tafi, ya kara masa ni'imomi da kulawa da shi.
Daga nan Sarki ya kira Wazirinsa gefe guda
domin su yi shawara, ya ce masa, "Ni dai na yi
iyakar kokarina a kan in janyo hankalin yaron nan
ya yarda da [ http://fb.com/waziriaku ] maganar
aure, amma ya buga kansa ga kasa ya bijire
mini. Da, na so ya fara yin auren nan, sa'annan
in yi murabus in bar masa sarautata.
To, amma yanzu mecece shawararka?" Waziri ya
ce, "Abin da za a yi shi ne, ka bari sai ranar bikin
salla, lokacin da sarakunanka da hakimanka da
alkalai, da duk sauran masu mulki na kasar nan
suka taru a fadarka gaba daya, [ http://fb.com/
waziriaku ] domin gaisuwar salla.
Ka sa a kira shi, ka maimata masa wannan
maganar a gabansu. Na tabbata yawansu da
kuma jin kunyarsu zai sa ya amsa wannan
bukata taka." Sarki ya ce, haka kuwa za a yi
Waziri. Ya gode masa a kan wannan shawara da
ya ba shi. [ http:// fb.com/waziriaku ] Bayan
shekara biyu da wannan magana, Kamaruzzaman
ya cika shekara ashirin ke nan da haihuwa.
Kyawunsa ya kara bayyana, hakika Allah ya hore
masa kyau, ya nada shi shugaban kyawawa na
wancan zamani nasa. Idanunsa tamkar idanun
Haruta da Maruta domin jan [ http://fb.com/
waziriaku ] hankali. Girar idonsa kuwa ta fi takobi
kaifi. Hasken goshinsa kamar na farin wata.
Gashin kansa kuwa baki wuluk kamar duhun
dare.
Murmushinsa yakan narkar da zuciya, ko da
kuwa zuciyar karfe ce. Kamar yadda aka ambata
a cikin wannan waka: " [ http://fb.com/
waziriaku ] Abin rantsuwa na ga fuska tasa. Abin
sha'awa na ga wushirya tasa. Abin mamaki na ga
tafiya tasa. Domin taushin jikinsa, da saukin
ganinsa, da farin fuska tasa, da bakin gashi nasa.
Domin matsarin da ya tsare barci daga ido nasa,
da zuciyar da ta tsare shi da hani ga mugunta, ta
yi [ http://fb.com/waziriaku ] masa umurni da
alheri. Domin kunamin da kyawunsa ke aikawa a
cikin zukatan masu bege, da hasken goshinsa, da
asalin sajensa, da ma fi farin murmushinsa, da
lu'ulu'un wushirya tasa, da kamshin jikinsa da ke
tashi ba da turare ba, da tausasan duga-dugansa,
da gajeriyar magana tasa, da daddadan furucinsa,
da kawaicinsa, [ http://fb.com/ waziriaku ] da
gaskiyar harshensa, da daukakar daraja tasa.
Menene almiski face daga iska tasa?" Ranar salla
bayan an sauko daga Idi, dukkan masu mulki
karkashin Sarki Shaharuzzaman sun taho fadarsa
domin gaisuwar salla.

Ya sa aka kira masa Kamaruzzaman. [ http://
fb.com/waziriaku ] Da ya zo sai ya fadi ya yi
gaisuwa a gaban mahaifinsa, ya koma gefe ya
sunkuyar da kansa kasa, yana jira ya ji dalilin da
ya sa aka kira shi.
Daga nan sai Sarki Shaharuzzaman ya ce masa,
"Na kira ka nan ne a gaban dukkan masu mulkin
kasar nan, domin in jaddada maka bukatata zuwa
gare ka ta son ka yi aure tun ina raye. Me ka ce
[ http://fb.com/waziriaku ] game da wannan
bukata tawa?
Jin haka sai ran Kamaruzzaman ya baci,
idanunsa suka rufe saboda fushi, zuciya ta debe
shi ya ce da mahaifinsa, "Me ya sa kake so ka
tursasa mini in yi abin da ba ni da ra'ayinsa? Ga
ka ka manyanta kamar mai fahimtar al'amurra,
na sha fada maka illar mata amma har yanzu ka
kasa fahimtata.

Na fada maka, ba sau daya ba, cewa ni ba zan
taba yin aure ba har abada, [ http://fb.com/
waziriaku ] ko da kuwa za a shayar da ni kaskon
mutuwa."
Yana gama fadar haka sai ya buge rigarsa, ya
tashi ya fita daga fadar fuu, cikin fushi yana
guna-guni. Ran Sarki ya yi matukar baci, yaro ya
kunyata shi a cikin jama'a. Ba amsar da ya ba
shi ce ta fi [ http://fb.com/waziriaku ] ba shi
haushi ba, irin yadda yaron ya nuna rashin ladabi
gare shi, da rashin ganin girmansa a cikin
mutane. Nan take zuciya ta turnike shi, ya daka
wa dogarawa tsawa ya ba su umurni [ http://
fb.com/waziriaku ] su kawo masa shi a gabansa
yana daure. Nan take suka je suka cafe
Kamaruzzaman, suka mayar da hannuwansa baya
suka daure shi tamau da igiya. Suka kawo shi a
gaban mahaifinsa, cikin tsananin tsoro, domin
kuwa ko da wasa mahaifin nasa bai taba ko
zungurar sa ba, ga shi yau ya sa an daure [
http://fb.com/waziriaku ] shi.
*** *** ***

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, . Za mu ci gaba
ranar ALHAMIS daidai wannan lokaci (karfe 9:00..

whataspp only pls
08032767547(3) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHARUZZAMAN

.
Ran Sarki ya yi matukar baci, yaro ya kunyata
shi a [ http://fb.com/ waziriaku ]cikin jama'a. Ba
amsar da ya ba shi ce ta fi ba shi haushi ba, irin
yadda yaron ya nuna rashin ladabi gare shi, da
rashin ganin girmansa a cikin mutane.
Nan take zuciya ta turnike shi, ya daka wa
dogarawa tsawa ya ba su [ http://fb.com/
waziriaku ] umurni su kawo masa shi a gabansa
yana daure. Nan take suka je suka cafe
Kamaruzzaman, suka mayar da hannuwansa baya
suka daure shi tamau da igiya. Suka kawo shi a
gaban mahaifinsa, cikin tsananin tsoro, domin
kuwa ko da wasa mahaifin nasa bai taba ko
zungurar sa ba, ga shi yau [ http://fb.com/
waziriaku ] ya sa an daure shi.
Da suka zo da shi, Sarki ya yi masa fada mai
yawa, sa'annan ya ba su umurni su kwance shi,
su kai shi [ http://fb.com/waziriaku ] can wani
gidan gonarsa, wanda yake babu kowa a cikinsa.
Suka tafi da Kamarruzzaman zuwa wannan gidan
gona, aka share gidan gaba dayansa, saboda an
dade ba a yi amfani da shi ba. Aka gyara wani
daki a cikin gidan inda Kamaruzzaman zai rika
kwana. Aka sa mai gadi a bakin kofa, ya dai
zama kamar dan gidan yari. Bayan sun rufe shi
sun tafi, sai [ http://fb.com/waziriaku ]
Kamaruzzaman ya kwanta bisa shimfida yana
mai matukar nadama a kan kunyata mahaifinsa
da ya yi a cikin mutane.

Ya roki Allah gafara, sa'annan ya ce a cikin
ransa, "Allah ya la'ani mata! Ba dominsu ba da
ban shiga cikin wannan kurkuku ba, da a ce na
amince da bukatar [ http://fb.com/waziriaku ]
mahaifina ta yin aure, da na zauna lafiya da shi."
A fada kuwa, bayan jama'a sun watse, sai Sarki
Shaharuzzaman ya kira Wazirinsa ya ce, "Ka ga
sakamakon da shawararka ta janyo ko? Ka sa
dana ya kunyata ni a cikin taro, wanda har ya sa
na yi fushi. Na aikata masa [ http://fb.com/
waziriaku ] hukuncin da ban taba zaton zan iya yi
masa ba, saboda sonsa da nake yi. To, yanzu
kuma wace shawara za ka ba ni?

Me ya kamata in yi masa?" Waziri ya dukar da
kai ya ce, "Allah ya ba ka nasara, a bar shi a
cikin wancan gida zuwa kwana goma sha biyar,
watakila ya ji tsoro, ko [ http://fb.com/
waziriaku ] kuma idan zaman kadaici ya ishe shi,
ya amsa bukatarka." Sarki kuwa ya aminta da
wannan shawara ta Waziri. Da dare ya yi Sarki
ya shiga dakinsa ya kwanta domin yin barci
amma ya kasa, domin kuwa [ http://fb.com/
waziriaku ] zuciyarsa tana cike da tunanin
Kamaruzzaman, da kuma halin da yake ciki. Ya yi
ta juyi bisa shimfida, kamar wanda yake kwance
bisa garwashin wuta, barci ya ki daukarsa.
[ http://fb.com/waziriaku ] Maimakon ya yi barci
sai idanunsa ne suka cika da...


Read / Download HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

6 months ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album