Join Our WhatsApp Group

ALAKAKAI Complete Hausa Novel Document by ALAKAKAI


ALAKAKAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22528



ALAKAKAI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 125.29 kb

File Type: txt

Views: 1133+

Download: 240+

Last download: 8 days ago

Description/Story: ALAKAKAI
Nazir Adam Salih
Made by Shuraih Usman
Daga http://fb.com/hausaebooks

ALAKAKAI-01
.
DAYA 1
Wata ranar lahadi aka tashi da gagarumin hadari wanda
yakan firgita birrai. Kodayake a safiyar ranar ba'a tashi da
alamun hadarin ba. Sararin samaniyar tarwai yake babu
alamar gajimare ko kankani wannan shi ya baiwa rana
lasisin ci gaba da dumama rufin gidaje da kayuwan bani
adama tun daga karfe goma na safiyar har zuwa karfe
daya na ranar. Abin bai zowa mutane a bazata ba
musamman ma wadanda suka sha miya da yawa domin
sun dade da yin amannar cewa duk sa'ar da zafi ya

tsananta alokacin damuna to hadari ne ke son haduwa.
Haka kuwa akayi babu zato ba tsammani sai hadarin ya
fara haduwa sahu sahu sannu ahankali har ya dakushe
hasken ranar ba'a dade ba sai iska gamida feshin
tsattsafar ruwa nan da nan jama'a suka fara tserere akan
tituna domin su sami gurin fakewa acikinsu harda Ni
wanda rabona da ofishina tun karfe tara na safe da wani
mutum yazo karbar bashinsa na gudu.
.
Wannan bashine karo na farko ba dana fara tserewa
masu bina bashi kusan watanni tara kenan da harkar fim
ta juya min baya tun fitowar fim dina na DAREN
MUTUWA shikenan sai mutane suka dau karan tsana suka
dora min.
Iskar hadarin ta fara tsananta dan haka sai nayi sallama
da mai shagon dinkin da nake boye aciki tun safe nace
dashi.
ISYAKU zan koma ofishina. Isyaku tela ya dubeni cikin
damuwa daman yasan irin matsanancin halin danake ciki
Gara ka tafi gida Hilal domin komawarka ofis ayanzu
ganganci ne... Na dubeshi gamida murmushin yake
kada ka damu isyaku leka waje ka gani hadari ne bakikirin
ga iska.. Nasan dai mutum yanzu in ba maye bane dole
ne ai yabar ofishin..... Kuma bugu da karawa ma dole ne
na koma ofishin domin na sallami sakatariyata LAURIYYA
dan nasan ko kudin mota bata dashi...... Abincin rana ma
bansan yadda zatayi ba.. Isyaku ya dubeni cikin mamaki.
Kana nufin haryanzu Lauriyya tana tare dakai? Na gyada
masa kai kwarai kuwa ai tattaraba ce uwar alkawari ita
kadai ta rage a yarana duk sun barni sai ita kadai... Isyaku
ya dan yi murmushi yana dubana.
Itama akwai dalili.. Na dube shi cikin mamaki
dalili... Kamar yaya ban fahimce ka ba isyaku yayi
atishawa sannan yace
Haba Hilal har sau nawa kake so in maimaita ma cewa
Lauriyya sonka take.
Nayi saurin girgiza kai
A'a bari bari isyaku kada kayi min mummunan fahimta
na yarda ni dan fim ne amma zakayi mamaki idan nace
dakai tunda nake ban taba soyayya ba da wata yar fim.
.
Kakkarfar iskar hadarin dake ta hankoron dauke rufin
dakunan masu rangwamen gata ta bugo kofar shagon
telan da karfin gaske
Isyaku yasa kafa ya tokareta.
Baka fahimce ni ba Hilal ko kuma ince kasan gaskiya ka ke
takewa ai ko makaho ya laluba yasan lauriyya tana
mutuwar sonka.
.
******* ********* ************
.
Lokacin dana baro shagon telolin saina tsallaka titi na nufi

ofishina cikin sauri da kyar nake ganin gabana saboda
kakkafar iskar ma'abociyar kara dake ta bulbule min
idanu.
Kura ta turnuke ko ina haka nan garin yayi jajur duhu ya
lullube ko ina kai kace karfe shida da rabi na yamma tayi
duk kuwa da cewa karfe daya ne na rana.
Cikin sauri na nufi ofishin inata waige waige domin
haryanzu jikina na bani cewa akwai sauran masu bina
bashi cikin ofishin suna jirana.
Tun kafin na karasa ofishin na fara hange hange da rabe
rabe sannu ahankali har na isa kofar ofishin wacce ke
rufe tana duban bakin titi.
Nayi tsaye a kofar ofishin kusan minti guda nayi kasake
kamar barawo ina saurare ko zan ji surutai ko hayaniya
shiru banji komai ba na dan dada matsawa kadan na kara
kunnuwana ajikin katuwar kofar nayi ajiyar zuciya
sannan sainayi shahada na daga hannuna zan tura kofar
kenan sai kawai naga an bude daga ciki.
Sannu da zuwa hilal yi maka ka shigo daga ciki yanzu
yanzun nan EMEKA yatafi tun sha daya yaketa jiranka
nace dashi katafi kaduna... Amma yaki yadda
Kirjina na dakan uku uku cikin sauri na shige ofishin.
Lauriyya ta mayar da kofar ofishin cikin gaggawa ta rufe
sannan saita jingina bayanta ajikin kofar ta kura min
idanu bata ko kiftawa.
Na nufi cikin ofishin ahankali hannayena cikin aljihunan
wandona zuciyata na kuna nayi kokarin nazarin ofishin
amma saboda duhun hadarin bana iya ganin komai cikin
ofishin.
Lauriyya ta fahimci haka cikin sauri ta nufi makunnar
lantarki ta kunna nan da nan dakin ya gauraye da haske.
Lauriyya tayi tsaye jikin makunnar lantarkin tana kallona
ina kallonta.
Akwai alamar tausayi karara a fuskarta banda wannan
kuma naso na hangi kwalla acikin kwayar idanunta. Cikin
sauri na dauke kaina gefe guda sannan nafara nazarin
ofishin..... Da a da dan wani lokaci can daya shude babu
wani ofishin darakta na fim daya kai koda rabinsa a
tsaruwa amma koda na tsaya ayanzu ina nazarin ofishin
sainaji kamar na fashe masa da kuka lallai ruwa ya daki
babban zakara.
Saidai hakuri Hilal haka duniya take rawar yan mata
lauriyya ce ke magana abayana cikin wata rarraunar
murya. Naji abinda ta fada to saidai kuma ban iya juyowa
na kalleta ba ballantana ma na tanka mata.
.
Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan
shudaddan zamani.... Sa'ar danake tauraron jarumai na
wasan fina finan hausa.
Na rufe fuskata da tafukan hannuna sannan nafara
tunanin sa'ar dana shigo harkar fim da kafar dama cikin
watanni ukun farko da shigata harkar na fito cikin fina

finai sama da shirin wadanda duk nine jarumi acikinsu
sannu ahankali sai sunana yayi tambari duk inda ka
zagaya babu sunan wanda ake fade sai HILAL.
Duk inda na zagaya yara da manya basa barina na huta
sun yita bina kenan abaya kungiya-kungiya kamar uban
garke idan naje sayayya kasuwa ba'a karbar kudina haka
nan da zarar an kyalla ido na ganni saikaga anata rububin
ganina kowa na gayyata dana zo nayi siyayya ta a
rumfarsa duk kuwa da cewa ba kudina zasu karba ba.
Na mallaki abubuwa da dama a shekarata ta farko da
shiga harkar fim wanda adacan wani lokaci ban taba
mafarkin mallakarsa ba akwana kusa motoci uku na
hawa kayan sawa na kwalisa sama da kala dari uku da
goma sha takwas agogunan sarka ashirin na fata goma
takalma sittin safa kuwa da singileti duk wacce nasa sau
uku bana kara amfani da ita sai wata sabuwar.
Sannu ahankali samari suka fara kwaikwayon yadda nake
direshin duk abinda nayi koda sakarci ne sai ya burgesu
saikaga sun zamo masu kwaikwayona.
.
Ashekarar ne na bude katon ofishina wanda aka kawata
shi da kyale kyale gami da manya manyan kujeru masu
numfashi da taushi kamar ada da sau da yawa idan muka
sauki baki indai har zasu shafe mintuna goma suna zaune
sai an sami wanda ya bingire da barci saboda dadi.
Duniya ta dawo min sabuwa ina da yara dake aiki
akarkashina sama da mutum ashirin suna kuma jin
maganata fiye data iyayen da suka haifesu wasu suna
bina sau da kafa ne wai don kawai suna so na sa su
kokuma nayi musu hanya su shiga shirin fim yayinda
wasu kuma suke yi min biyayya don kawai kaunata da
sukeyi. Nazama kamar sarki acikin fadawa duk abinda
nake so shi za'ayi batareda bata lokaci ba. Da ace yarana
awannan lokacin suna da iko da fitsari da numfashi ma
su zasuyi min.
Muna nan ahaka har shekaru biyu suka shude
Kwatsam ran nan sai duniyar data dagani sama ina
shanawa tafara yin kasa kasa dani sannu ahankali ta
damfara ni da kasa.
Abin yafara ne a yammacin wata ranar lahadi sa'ar
danake karbar kudaden sabon fim dina RAGAS daya fito.
Shagon farko danaje sai akace dani wai fim din baya
tafiya nayi mamaki domin tunda kamfanina yake fim ba'a
taba samun wanda bai shiga ba.
Me ya faru da fim din? Na tambayai wani dillalin kasa
kasan fim din.
Eh to kasan dai mutane yadda suke ba'a iya musu inajin
dai gajiya sukayi dakai.... Kuma sunata korafi akan cewa
wa fina finanka na kwanan babu labari mai kyau.
Tun daga ranar ne al'amura suka dagule min abin kamar
sa hannu komai na taba sai ya lalace gashi dai nagama
kashewa fim din Ragas kudi... Na ranto kudin jama'a duk

na lafta saboda a tunanina zaiyi bala'in karbuwa saigashi
cikin ikon Ubangiji saidata kawo ko kashi daya bisa goma
na kudin fim din basu komo ba.
Rayuwata tsananta kaina ya dauki zafi rikici goma da
ashirin ga tarin bashi fal akaina gashi kuma ya
furodusoshin ma da suke daukana na fito musu a
matsayin jarumi duk sun gujeni ba'a dade ba duk yarana
suka watse suka barni daga ni sai yar amana LAURIYYA.
.
Koda na daga fuskata sa'ar danake tunanin na dubeta
saina tuno da kalamanta saa'ar da gari yayi mana zafi
bazan taba mantawa da ranar ba. Ranar wata laraba da
yamma bayan sama da mutane goma sun zo tambayata
bashin su.
Hilal.. Ina da shawara in zaka yarda. Lauriyya tace dani na
dago kai na dubeta.
Fadi shawararki lauriyya...indai mai amsuwace ai na
dauka.. Tunda dai ko banza dai ke kadai kika rafe atare
dani.. Wallahi lauriyya ayanzu kin wuce sakatariya
agurina saidai ko in Yar Uwa.
Lauriyya ta dan matso daf dani duk da yake duk ranmu
abace yake to amma na lura da alamun jin dadin abinda
nace karara a fuskarta na sani ba tun lokacin ba har zuwa
yanzu Lauriyya sona takeyi to amma ta rasa yadda zata
fito ta fada min.
Hilal... Ni ina ganin a shawara da ace kullum mutane
suyita binka suna tambayarka bashi... Suna muzanta ka
kamar barawo gara in kana ganin babu damuwa ka daga
dan kadarorin daka mallaka kasa su akasuwa in yaso
saika biya mutane bashin su... Ko banza dai ina ganin ai
tsira da mutunci yafi tsira da kudi. Hakan data fada saina
fahimci tabbas ta fadi gaskiya ba'afi sati daya da bada
shawarar ba na sayar da motocina guda uku gidana kai
da duk wani abu danake ganin zai iya kawo min wasu
dunkulallun kudi saida na sayar dasu.
Acikin makonne na biya jama'a da dama basussukansu ni
kuma nakoma gidan yayana inda daman tun farko acan
nake kafin na samu abin duniya
UNGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA
.
To saidai kuma abin bakin ciki duk da kadarorina dana
sayar basu isa biyan bashin da ake bina ba.
Gashi kuma haryanzu babu wani labari daga gurin masu
shirya fina finai wadanda ada suke ta bina agindi agindi
suna rokona danazo na fito musu a fim yanzu da sun
hangoni sai su fara buya domin duk labari ya ishesu
acikin kankanin lokaci kamar wutar daji cewa wai
kasuwar fim ta daina yi dani......... Wannan duk wani
Abune daya shude Abaya.
.
ALAKAKAI 02

.
Wannan duk wani abune daya shude abaya
.
Hilal aka kira sunana abaya na juya firgigit Lauriyya ce
har yanzu tsaye ajikin makunnar lantarkin tana kallona
idanunta sunyi rau-rau kamar zata fashe da kuka.
Tunanin me kakeyi Hilal? Ta tambayeni bakinta na rawa
na juyo ahankali hannayenta harde da juna makale
abayanta.
Kikace Emaka yazo nemana? Lauriyya ta gyada min kai
bata yadda ta bude bakinta ba ina tsammanin da tayi
magana alokacin fashewa zatayi da kuka.
Sauran cikon kudin kwalin kaset din daya buga mana
yazo karba nace da ita batareda na iya hada ido da ita ba.
Ban da shima su shafi'i sunzo wai karbar kudin kayan
kwastum... Haladu da sabo da ma duk sunzo maganar
cikon kudinsu...
Tsahon lokaci babu wanda ya sake cewa kala nida ita can
bayan wasu yan dakiku sai lauriyya ta matso daf da inda
nake tsaye inata faman karatun wasikar jaki
ta dafa kafadata tace dani.
Juyo ka dubeni hilal... Ina da shawarar da nake
tsammanin me yiwuwa ta zama mafita agareka. Adaidai
lokacin aka saki wata katuwar aradu data girgiza ofishin
sannan wata walkiya mai tsananin haske ta harko cikin
ofishin duk kuwa da kwan lantar dake ci.
.
***** ******* ****** ****** ***
.
Na zurawa lauriyya idanu ina kallonta sannan kamar wani
sahorami domin bansan me zance da ita ba ganin bance
da ita komai ba sai ta dafa kafada na sannan ta sunkuyo
da kanta tace dani.
Ka gafarce ni hilal ba wani abu ne yasa nake tare dakai ba
haryanzu sai don...... Ta kasa karasawa tausayinta
yakamani haryanzu iska ake ta ketawa awaje saikuma
sautin yan kananan kwayoyin ruwan da iska ke ta alakoro
dasu akan rufin gidaje kafin isashshen ruwan ya karaso.
Cigaba lauriyya.... Ke nake sauraro nace da ita a sanyaye
lauriyya tayi dan jim na yan dakiku kana saitace cikin
karyayyyiyar murya.
Kau.....narka ce ta rike ni har zuwa wannan lokaci ina tare
dakai.... Duk abinda ya same ka kamar ni ya shafa ne
domin lokacin danazo garin nan kai ka karbeni ka
mutuntani ka maida ni mutum.
Banida cewa akan abinda tace dan haka sai nayi shiru ina
sauraron abinda zataci gaba da cewa.
Hilal.....abinda nake kokarin baka shawara akai shine me
zai hana muje kamfanin fina finan su ALHAJIJI me
yiwuwa...... Bata karasa ba sakamakon sauyin yanayin
data gani karara a fuskarta.
Haba lauriyya wace irin magana kikeyi ina ni ina wani

Alhajiji kuma? Lauriyya ta dada matsowa gareni kamar
zata kankameni.
Hilal ka saurari abinda nake son fada ma dan Allah nsan
dole bazakaji dadi ba domin zan saka yin abinda baka so
ba. Ta dan saurara.
Duk acikin yan shirin fim shi kadai ne nasan baya bakin
ciki dakai.... Shiyasa tun jiya nake tunanin me zai hana
muje mu gani ko zai samo ma wani fim din ajefaka aciki
koda a mataimakin jarumi ne saikaga kadan samu wani
abu ka rage bashin dake kanka. Tayi shiru tana dubana.
Nayi dim na yan dakiku ina jujjuya kalamanta acikin
zuciyata.
Lauriyya abinda nake so ki lura dashi shine mutumin nan
fa babu irin nacin da baiyi min ba sa'ar da nake kan
ganiyar tashe na akan nazo nayi masa jarumi a
finafinansa amma naki... Ke din nan da kanki sau nawa
yana bugo waya ina cewa kice dashi bana nan....?
Duk da haka dai hilal..... Haka nan zaka daure muje ai
durkusawa wada ba gajiyawa bane ni nasan ba zai
wulakanta ka ba tunda dai koda ada din ma ai ba fitowa
kayi kiri kiri kace dashi bazakayi masa fim din ba. Na
girgiza kai sa'ar danaji tayi shiru.
Lauriyya ban ki shawarar ki ba amma abinda kamar wuya
wai gurguwa da auren nesa ina ta faman nuna miki
Annabi kina runtse idanu abinda nake so ki gane shine
tuni labari ya watsu aduk fadin duniyar fina finan hausa
cewa kamfaninmu ya fadi bama wani tasiri akasuwar fim
shiyasa kikaga fa kowa ya gujeni an daina rububin sa ni a
fim domin ana ganin nazama asara.
To in dai kuwa hakane wacce irin hauka ce ta hau kan
alhajiji da kike tsammanin zai sani cikin fim dinsa in
janyo masa asara sa'ar danayi shiru saina lura tuni
hawaye ya fara sartu akan kumatun lauriyya.
.
Daina cewa zaka janyo masa asara Hilal....abin da nake so
ka gane shine ba kaine ka daina tashe ba kamfaninmu ne
ya karye ya daina tashe amma ni nasan ita duk duniyar
nan basu yarda ba ni nayi imani da cewa kana nan akan
HILAL dinka jarumin jarumai.
Kukanta yafara bayyana a fili.
Nayi sauri na rike hannayenta nace da ita a sanyaye.
Daina kuka lauriyya shikenan na yarda zamuje to amma
kuma wani hanzari ba gudu ba.
Lauriyya ta dago kai tana share hawaye cikin rashin
fahimta.
Yanzu idan mukaje bamu dace ba kinsan fa labari zai
watsu aduniyar fina finan hausa cewa tsohon jarumin
jarumai yafara tallan kansa..... Wacce illa kike tsammanin
hakan zata janyowa durkusashshen kamfaninmu?
Lauriyya ta bata fuska tace.
Hilal so dai kakeyi saika bata min rai ko? Da dai bana son
na fada amma yanzu ka takura ni saina fada? Na dubeta

cikin mamaki me zaki fada? Lauriyya ta harareni gamida
murmushin yake tace.
Alhajiji yana mutuwar kaunata nice dai ban bashi hadin
kai ba. Ni nasan ko yana so ko baya so dolene idan nayi
masa magana yasaka acikin sabon fim din zaiyi.
Tana gama fadin hakan saita kama hannuna ta fara jana
kamar wani karamin yaro.
Zo mu tafi dan Allah kada afara ruwa. Nabita abaya sumi
sumi kamar tunkiya muka shiga cikin iskar damina.
Jarumin jarumai Na kira kaina da kaina sannan sai na saki
daddadan murmushi. Lauriyya ta lura
Murmushin me kake? Na girgiza kaina nace babu
komai.... Kece kawai kika burgeni,
.
****** ********* *************
.
Sa'ar da muka isa kamfanin fina finai na alhajiji sainaga
toge abaya abjikin wani kantin kayan karau nace da
lauriyya
Jeki kuyi magana dashi ni...


Read / Download ALAKAKAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album