Join Our WhatsApp Group

TSAUTSAYIN TAUNA Complete Hausa Novel Document by TSAUTSAYIN TAUNA


TSAUTSAYIN TAUNA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24105



TSAUTSAYIN TAUNA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 09, Aug 2023

Author: Zainab Habib Mom Islam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : _✨GAWURTATTU BIYAR✨_

Author Phone : 08141799224

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 135.31 kb

File Type: txt

Views: 567+

Download: 205+

Last download: 5 days ago

Description/Story: *🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

_✨GAWURTATTU BIYAR✨_

*Zainab Babib(Mom Islam*

Kuyi following d'ina a arewabook
https://arewabooks.com/u/momislam22

Ina mik'a sak'on gaisuwa mai yawa, a gareku masoyana, musamman wanda suka nunamin zallar soyayya gurin siyan littafina *GUNTUN GORO* yauma gani tafe muku da sabo wanda nake ganin zakuyi farinciki, labarin yazo da sark'ak'iya, da zallar soyayya, karku manta da sunan fitaccen littafin wato *TSAUTSAYIN TAUNA* dagajin sunansa kunsan akwai cakwakiya over kudai muje zuwa.

Page 1-2
KADUNA STATE
Anguwar Dosa.

Wani irin tsawa ya daka mata tare da cewa ”meyasa kikeson sakani a hanyar da bata dace ba?, sokike inje inyi sata in kawo miki ko Yaya?",
Matar da zatayi 35yrs bak'a bamai jiki sosai ba, dakaga yanayin jikinta zakasan suna fama da matsanancin talauci,
Ta rik'e k'ugu tana girgiza ta matso gabansa kana tace "inhar bakaje kayi sata ka kawomin ba wallahi baka cika namiji ba"
Rik'e da baki malam Haladu ke kallonta, bai jira me zata sake cewa ba ya fice.
Yana fita ta kalli Aisha yarinya y'ar kimanin shekaru goma sha biyu  duniya, sai bala'in rawar kai, Aisha fara ce sbda Wanda baisan iyayenta bama ya ganta zai rantse y'ar masu kud'i ce, Allah ya azurtata da yalwataccen gashi, ga idanuwannan masu d'aukar hankali y'an madai-daita, gashin girarta kuwa luf-luf yake, sai d'an k'aramin bakinta na tsiwa pink kamar ansa masa janbaki,
"Mama wai baba bazai nemi aikin yi bane? Wallahi yanason zuciyarsa ta mutu ne irin na mijin Hansatu mai waina"
Aisha ta fad'a tana ta6e baki,
"Yo ni ina zan sani, muddin yace zai takuramin wallahi bazan zauna ba ai bashine autan maza ba, gashi tunda talauci ya aureshi muka shiga uku,sudai abin kamar a jini yake kaf danginsu matalauta ne"
"Mama ki fara yimin k'osai in mun sami ribar sai mu dinga adanawa kinga ma kya sami jarin siyarda gawayin ko?"
"Amma Aisha baki da hankali, kina ganin ana fama da cefanen gida ki kawomin yin aikin mangyad'a, yanzu komai da yayi tsada sokike ciwon zuciya ya kamani na murk'ushe kud'in da y'an uwana suka  aikomin dashi?"
Dajin haka Aisha ta cuno baki kana ta mik'e tare da ficewa waje tana gunguni.
Tunda malam Haladu ya fita, yake neman aiki koda kwa6ar k'asa ne ta masu gini amma Allah besa ya samu ba, zama yayi kusa da shagon wata mata mai abincin siyarwa, wata dank'areriyar mata ce ta fito bak'a, kanan yaji gashin doki kai kace ba musulma ba, cikin d'aga murya take cewa "wai yau ina almajiranne duk kunyi shiru, gashi babu masu wanke-wanken?"
Da sauri malam Haladu ya taso jiki na rawa yace "gani ni zanyi”
Cikin yamutsa fuska tace "sai ka shiga ka d'ibo plets d'in da akaci abinci ga ruwan wanke-wanken nan ga omo can" ta nuna masa inda aka ajiye.
"To"  yace jiki na rawa ya nemi leda ya kwashe ragowar abincin da mutane sukaci suka rage ya tara a bak'ar leda, kana ya fara wanke-wanken, yana gamawa cikin d'aga murya yace "hajiya an gama"
D'ari da hamsin ta mik'a masa sai abinci data zuba masa d'an kad'an
Jikin Baba Haladu a sanyaye ya kamo hanyar gida, koda yaushe in zai shigo gida gabansa fad'uwa yake saboda masifar maman Aisha,
Kasancewar akwai abinci a hannunsa hakan yasa ya sami k'warin guwaiwar shiga gidan,
Yana shiga ya sami maman Aisha a  d'aki tana sallahar azhar, mamaki ne ya kamashi a zuciyarsa kuwa cewa yake "wai har anyi sallah ni ban saniba?"
"Haladu me aka samo mana ne? kasan idan mukaga bak'ar leda da bayani"
Malam Haladu ya k'arasa d'akin ya nemi guri ya zauna sannan ya kunce bakin leda kana yace "d'auko kwanon a juye"
Jikin maman Aisha na rawa taje ta d'auko kwano ya juye shinkafar, ya had'a da wacce aka bashi, sai gashi shinkafa ta cika kwano,
Cikin fara'a maman Aisha tace "megida a ina aka samo mana beta?"
Malam Haladu yayi jimm kafin yace "zubar da mutunci na nayi,
Ta dafe k'irji kana tace "ban gane ba?"
Malam Haladu yace "wallahi zaman nayi a shagon mai siyarda abinci shine nayi mata wanke-wanken ta bani".
"Mtsw nama d'auka wani abun ashan kayi, ai wannan ba komai bane naga kamar da nama a ciki ko?" Kallonta kawai yakeyi Amma a zahiri zuciyarsa nayi masa zafi.
Tsince naman cikin abincin tayi kana ta ajiyesu a roba daban tace "in zuba maka ne ko kaci acan?"
Tsabar takaici kasa ce mata komai yayi.
Sai da taci tayi hani'an sannan ta ajiyewa Aisha tunda shikam yak'i kulata,
Cikin takaici ya fice a gidan ya nufi masallaci, Aisha kuma sai dare ta shigo,
Tana zuwa ta fad'a jikin mamanta a shagwa6e tace "mama baban kowa yana siyawa yaransa kayan dad'i niko baba ko biskit baya siyamin"
Maman Aisha tayi murmishin da zata iya kiransa dana takaici kafin tace "bak'in talauci ke dukansa ki rabu da matsiyacin ubanki kawai, yau dai ya kawo mana abinci harda nama"
Da murna Aisha ta mik'e tsaye tana rawa, Dan rabonsu da nama tun watan babbar sallah.
Abinci mai albarka itama Aishar sai da taci ta k'oshi sannan ta tashi, harzata kuma fita Maman tace "jekiyi alwalah rabonki da sallah tun ta asubha"
Cuno baki tayi kana tace "ke ina lissafa miki naki ne? Kin mance lokacin da kikayi sati guda ba sallah ba azumi?"
Waro ido maman Aisha tayi ta bita da gudu tana cewa "yau naji fitsara zuwa gaba Aisha zata zageni"
Sai da ta tabbatar da mamanta ta shiga d'aki sannan ta fito taje tayo alwalah tazo parlo ta kabbara sallah, kasancewar gidan nasu madai-daci ne mai d'auke da d'akuna uku na maman ciki da parlo sai makewayi sai kicin, shikenan tsakar gidan nasu ma ba wani mai fad'i bane, infact ma gidan haya ne duk shekara malam Haladu yake biyan dubu goma sha biyar kud'in wutar lantarki d'ari biyar.
Koda ta shimfid'a sallahya ba sallahar take ba, kana daga gefe kanajin mis-mis-mis d'inta, mamanta na daga d'aki tace "halin naki dai bazaki fasa ba ko?"
Aisha tayi ruku'u tace "duk nai 6atawa mutun sallah wuta zai shiga ni babu ruwana,taci gaba da sallaharta.
Zuwa dare basu wani samu abincin da zasu sake ci ba, haka sukasha ruwan d'umi suka kwanta, Aisha ce ta fara bacci sai mamanta itama kafin malam Haladu ya  shigo, yaji dad'i sosai dan baccinsu shine kwanciyar hankalinsa, yahau gadon tare da d'ago Aisha ya mayar gefe ya kwanta kusa da mama,
Can cikin dare mama taji ya fara lalubarta, bige hannun nasa tayi taci gaba da baccinta, malam Haladu dai ya kasa hak'uri ya kuma matsowa murya k'asa-k'asa yace "haba maman Aisha kiyi hak'uri ki bani hakkina wallahi nayi hak'uri har tsawon wata biyu sai kace dutse?"
Cike da masifa ta tashi zaune kana tace "mazan k'warai sune ake yiwa lale marhabun kaikuwa mai matacciyar zuciya mene ne abin faranta maka anan ko ance maka ni ina sha'awarka ne?"
Ta d'auko pilo ta koma Palo, kan wata doguwar kujera da ita kad'ai ce a palon sai kwanukan wanke-wanke da randar ruwa, kwanciyar tayi tana jan tsaki lokaci-lokaci har bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari asubar fari, Aisha ta riga kowa farkawa, waigawa tayi taga babu mama, ta fara dukan baba tana cewa "ina maman? sarai ya jita, dan haramar alwalah yake shirinyi ta tashi,
A hankali Aishan ta sakko ta taho parlo tana ganin maman tace "to kekuma meya kawoki nan?"
Jin shiru bata ansa ba, da alamun baccin har yanzu dad'insa takeji,
Aisha ta d'ibo ruwan randar k'asa ta juyewa mamanta a jiki, da sauri maman ta tashi zaune tana goge fuskarta da gefen zani tace "dan ubanki me yasa baki kwarawa ubanki ba saini da kika Raina?"
Shima ina nan zuwa gurinsa ai, naga kuma taimakonki nayi tunda kinaji ana Kiran sallah kikak'i tashi"
Maman na mik'ewa ta wanka mata mari tare da cewa "gaba ki k'ara"
Tsalle ta dingayi tana 6arin kwanuka had'i da wurgi da tukwane, a ranar dai anyiwa Aisha duka tun kafin gari ya waye.
Malam Haladu na kwance yana jinsu ko uffan bai ceba, har Saida ta gama dukan ya fito,bai kulataba ya wuce gurin alwalah.
Tunda yayi alwalah ya wuce masallaci.
Gari na wayewa ya dawo gida, zama yayi a tsakar gida kan kujera y'ar tsugunno ya zabga tagumi, fitowa mama tayi tana cika tana batsewa, tazo gaban malam Halatu ta tsaya kana tace "mene ne nufinka? mun kwana bamu k'oshi ba yanzu ma sokake ka horamu?" ta k'arashe maganar tana yatsina fuska.
"Uhm maman Aisha bazanso mu zauna da yunewa ba, amman idan bani dashi fa?" wata wawuyar cafka takai masa kana ta shak'e kwalar  rigarsa tana cewa "banda mutuwar zuciya irin taka da kanada iyali kana wani cewa baka da kud'i mazan k'warai na zuwa neman aiki kaiko kana gida idan y'an uwana sun bani muci idan basu bani ba mu zauna haka, to wallahi na gaji".
Malam Haladu dai baima waigo ba bare ya kalli fuskarta,
Zuwa rana wajen 11:34am malam Haladu ya fice daga maman Aisha sai ita Aishar, suna zaune tun safe babu abinda sukaci, sai kame-kame wanda aka sabayi, gurin tukunyar Aisha tayi kana ta bud'e tukunyar tana cewa "mama tsakin ya tsotse"
"Sauke"
Mama tace tana daga zaune, bayan ta sauke ta zuba musu a kwanuka biyu, daga ganinsa ma a iya su biyun koda sunci ba lallai bane ya ishesu, sunfara ci kenan Baaaba Indo ta shigo hannunta rik'e da dubu d'aya, bayan tayi sallama tace "Maman Aisha ko kinada canjin dubu guda?"
Maman Aisha ta rik'e baki kana tace "wuuuu dubu guda fa kikace, d'in mik'o min it'a insa albarka dan rabona da ganinta nakai wata"
"Wallahi ke kikaga dama ga mata nan masu maza wanda suka fiki hali  suna bara amma ke kin zauna, aiko zakiga zama, shi mijin da kike tak'ama dashi gayican a k'ofar gida yana zaune gurin y'an kashe wando"
Maman Aisha ta dafe k'irji kana tace "Aiko banga ta zama ba, tunda abinda ya za6a kenan ni na zamo mijin shi ya zamo matar inhar zamuci musha mu tsira da mutuncinmu"
Baaaba Indo tace "wane irin tsira da mutunci a harkar bara nasiyi akuya nasiyi fili ke har zannuwa na samu, ga wani alhji shahararren mai kud'i kullum yazo saiya fillo mana y'an dubu-dubu"
Maman Aisha ta zabura kana tace "aiko zan biki amma bari ya shigo"
Baaaba Indo ta tafi tana mitar cewa "shi mutuwar zuciya kema haka kikeso ki zamo kenan?nikam bazan dinga jira ba" tayi gaba.
Tana fita Aisha tace "wallahi mama Baaaba Indo ta kawo shawara sai ki mak'ale idonki d'aya ki dinga bara ni zanyi miki jagora inmuka tara kud'i mudingacin abin dad'i"
Suna cikin magana malam Haladu ya shigo hannunsa rik'e da bak'ar leda, da gudu Aisha  taje ta anso tana cewa "oyoyo baba"
Fuskarsa d'auke da murmishi yace "yauwa y'ar baba d'aukomin kujera in zauna"
Bayan ta kawo masa, mamanta tayi masa sannu ciki-ciki, ba yabo babu fallasa ya amsa yana fito da shinkafa da wake da manja da magi had'i da attaruhu da albasa,yace "ayi maza a d'ora mana abinci Allah ya kawo"
Jikin Aisha na rawa tace "mama yau zamuci shinkafa "maman ta bige bakinta kana tace "dan ubanki tunda kin wuni da yunwa dole kiyi magana, Allahn daya haliccemu yabamu munci munsha, ace tun safiya har 12:pm mutum bai k'arya ba Sai kace d'an boko, gara ma y'an bokon sunacin mai maik'o mukuwa wataran ma abincin babu magi"
"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, malam Haladu ya furta tare da dakatar da ita yace "ya isheni haka!! bakisan wannan gorin da kikeyi min yana konamin raiba bakisan tafarfasar da zuciyata takeyi ba, sam wad'annan kalaman basu kamaceki ba"
Malam Haladu na yin shiru tace "abinda kayi ake fad'a, akwai k'arya a ciki ne?" Ko kanada zuciyar nema? acikin abokanka akwai wad'an da suka yi gida da mota wasu har k'asar waje sunje, kaiko baka ma da muhallin kanka bare asa ran zaka taimaki wasu"
Dafe kai malam Haladu yayi zuciyarsa babu dad'i, yakawo masifa bai kawo bama masifa,
Suna cikin haka Aisha ta fice da gudu, zuwa anjima sai gashi an tasota a gaba wai ta fasawa wani d'a goshi, baba yace "Dan Allah kuyi hak'uri kasoshi a barbad'a masa garin ganyen kurna"
Mama ta mik'e tsaye cike da masifa tace "tsoransu kakeji da zaka wani magiyar basu hak'uri?"
"Idan d'anka ne da laifi dole kai zaka bada hak'uri dan haka ki dakatamin"
Aisha kuwa tanata tsalle inda kasan batasan komai ba,
Yaran na tsaye har malam Haladu ya gama basu hak'uri suka fice.
Aikin Aisha kenan kullum sai an kawo k'ararta gida, duk ranar da ba'a kawo ba kuwa bata da lafiya.
"Zaki d'auki kayan cefanen ki girka ko kuma kina ganin in koma dasu"
Malam Haladu ya fad'a a hassale,
"Yo aiba yau ka fara komawa dasu ba"
Ta fad'a tare da shigewa d'aki.
Gurin had'a wuta yaje ya had'a kana ya kira Aisha yaja mata kunne akan neman magana, sannan yace ta tayashi d'ora girki, babu abinda ta iya sai jajjaga kayan miya, iya shid'in tayi ta fice,
Sai daya gama had'a sanwa sannan ya fice yabar gidan.
Maman na ganin ya  fice ta fito tana cewa "ni wallahi sakina nakeso kayi inkuma kak'iji bazakak'i gani ba"
Ta nemi guri ta zauna, da ruwan ya tafasa ta wanke ta zuba ko tsincewa batayi ba,
Sai dare akaci abincin dan hatta Aishar ma sai dai in a yawonta taci dan bata, bata ba.
A wani kwano kamar na bola aka sanyawa malam Haladu abinci itakuma ta cika kwano ta koma d'aki.
Washe gari basuda abincin d'umame, iya kacin ragowar wanda ko Aisha taji ba k'oshi zatayi ba..!

# Love
# Romantic
# Funny
Zazzafan labari wanda yazo da sabon salo, wanda yazo da gwagwarmayar soyayya mai sanyi, mai sanyaya zuciyar masoya, saboda wannan karon mun ta6o lovers.

Domin magana da marubuciyar 08141799224



_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171



*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku  ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...

Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki...


Read / Download TSAUTSAYIN TAUNA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album