Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KASAITA 3 Complete Hausa Novel Document by KASAITA 3


KASAITA 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 29110



KASAITA 3

Reading Time: 2 Hours

Added On: 02, Mar 2025

Author: Maryam Kabir Mashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 145.78 kb

File Type: txt

Views: 69+

Download: 71+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 1


Lafiyayyar dardumar kafet muka dinga takawa har izuwa wajen su waziri, waɗanda su ne iyayen fada. Ya ɗan sunkuya ya gaishe su, nima sai na yi yanda na ga ya yi. Madadin na ga sun amsa cikin nuna isa,su manya ne, sai na ji sun yi masa ɗan ƙaramin kirarin yabo.

Yana ɗagowa kuwa, sai na ga sun bi layin gaisawa da shi, wato ya dinga bin su ɗaya bayan ɗaya yana gaisawa da su. Ni kuwa da mun iso sai in ɗaga masu hannu. Suna gamawa dogarawan nan na zubewa ƙasa, domin gaishe da mu. Mamaki kam ya dirar masu a lokacin da suka bayyana shi a fili, shi ne amsa musu da ya yi da.

"Mun same ku lafiya?" Har da ɗan jan sunayen biyu daga cikin su. Ba su ba,ko ni nayi mugun mamaki.

Shi kuwa wucewa ya yi abinsa bai tsaya neman ba'asin mamakinsu ba, balle da ya ce su tashi mana. Me ye na saurin zubewar su ƙasa. Da ya isa ga wasu masu kayan mu na gida kuwa, ma'ana ta da ganinsu ka san ba dogarawa ba ne, ba wanda ko ni nasan na kusa da shi ne, ban dai san ko su waye su ba,abokanansa,ko ƴaƴan manyan fada. Yana isa ya rungume ɗaya daga cikinsu, kowa kam ya yi mamakin haka, ya dinga binsu ɗaya bayan ɗaya yana yi masu masabahar runguma, irin gaisuwar larabawa,su ma kuwa sun kai su taƙwas. Bayan nan kuwa muka juya motar mu wadda aka buɗe ta tun kafin mu isa gare ta.

Limousine ce, amma na san ba wacce na san Yarima da ita ba ce ba, saboda waccan baƙa ce mai ƙofa uku, kuma gabanta irin na kowacce mota ne, amma wannan ruwan toka ce mai duhu ash colour, sannan gabanta tamkar End of Discussion. Sai da na shiga sannan na ga ya zagaya shi ma ya shiga.

Subhanallahi!. Ba don kada a ce na ruɗe ba, da sai in ce motar nan ta fi jirgi daɗi da ƙyau, duk da na je ƙasashe na gano kala-kalar motoci da jiragen sama kansu.

Lulluɓe muke ta ko'ina, ba mai ganinmu. Na ja jiki na isa na ƙwanta kafaɗar mijina. Ya ɗago goshina kaɗan ya sumbace ni.

"Thank you. Au! Ɗan ɗaga ina zuwa, kada na yi laifi biyu." Ya ɗan ware ƙafafunsa, sai na ga ya janyo wani abu kamar ƴar sabuwar alkyabba mai ruwan hoda, ya dinga zarowa har da ɗan mayafinta, shi ma mai ruwan hoda.

Ban da takalma da jaka masu ruwan ƙasa,jakar wata ƴar maƙalalliya ce,a silin hannu kawai ake maƙala ta.

"Cire ta jikinki ki saka wannan. Gidan Mai Martaba za mu wuce mu gaishe shi,mu gaishe da Mama." Ya janyo ni ya ja hancina.

"Har wajen Daddy za mu fa yau." Ina zaro idanuwana.

"Me ye?"

"Ni kunyar shi nake ji." Na faɗa cikin shagwaɓa.

"Me yasa ki ke jin kunyar shi?"

Na ɗan harare shi irin hararar da na san zata sa idanuwana su yi mishi ƙyau. Ya yi dariya.

"Kin san kullum ina ƙara son ki da ɗokin ki Yasmin,saboda yanda ki ka mayar da ni autan ki."

"Na daina,ni dai kada a je wajen Dad."

"Ba zai yiwu ba,watan mu nawa da aure har yau ba ki taɓa zuwa gida ba. Ko a da da kika ga naƙi kai ki, tsoro nake ji kada in na kaiki ki ce ba ƙya dawowa. Ki sani na koma uku saura ƙwata a garin nan. Yanzu kuwa ko kin ce ma na san yanzu ina da garanti ɗin bin ki duk inda ki ka nufa, yanda suka ba ki ɗaki, nima haka za su ba ni,in ba haka ba ƙwanan falo ya kama ni. Ke ni ko kicin ma na dinga ƙwana,ai dai ina ganin ki kullum."

Na ɗan ture shi kaɗan tare da ɗan narkewa alamar shagwaɓar da na san tana sa shi ya ji daɗi. A take ya yi ƴar ƙara kaɗan.

"Ina! Ashe da nayi sakaci a baya da ƘASAITA ta janyo mini haɗarin da yafi na mota wahala. Rasa ki Yasmin ai wani babban gurguntar rayuwa ne."

"Ni?"

"To ya isa, na daina."

"Na ɗora saman kayan jikina,dama kuwa wani material ne mai ƙyan gaske (yadi), shi ma naga ya cire ta jikinsa ya saka fara tas. Dama kayan jikinsa boyal ne baƙi,safari da wando irin ɗinkin sarauta, sai ya ɗora ruwan tokar alkyabba yanzu ya tuɓe ta ya ɗora fara.

Na zaro foda mai tafi da madubinta, na ƙara gyara fuskata na ƙara rangaɗa ƙwalli wanda dama ni kaina na san na yi kalar ja, tamkar jini zai fito daga jikina. Na ƙara gyara gashin idanuwana suka miƙe tsaye, ban da baƙi da suka ƙara, juyowar da zan yi sai na ga Yarima ya rabga tagumi ya ƙura min idanuwansa, tamkar mutum-mutumi, saboda ko ƙiftawa ba ya yi.

Sai da na kai ga taɓa shi, sannan na ga ya yi irin murmushin nan mai nuna alamar daɗi, ya yi masa yawa, ya ɗauko turare ya fara yi min fesar nan tasa. Duk fesawa ɗaya tare da sumbata ɗaya, wuya, baya saman ƙirjina, zuwa bayan kunne, wanda a ƙarshe ya kan ajiye turaran ya rungume ni da jikinsa,ko ma ya ɗauke ni cak ya tafi da ni, inda zuciyarsa ta fi so.

Amma yanzu na yi saurin ɗago shi daga ɗan ƙaramin fita daga hayyacinsa da ya yi, idanuwansa a lumshe, na sa yatsuna biyar na wara su saman fuskarsa na shafa zuwa ƙasa.

"Honey, we are in the car, wake up."

Ya buɗe idanuwansa da suke a lumshe ya yi murmushi, tare da lakatar hancina.

"Ba ƙya ji."

Na yi murmushi haɗe da ɗan fari da idanuwana, ya zame jikinsa ya ƙwanta a cinyata.

"Har na ji na gaji."

"Aikin me ka yi? Kai da Allah ya gama haɗa maka daɗin duniya, sauran ka fa lahira da addu'ar mata ta gari, ƴaƴa na gari."

"Mata ma na samu, ƴaƴan ma ina sa ran matata zata iya yi mini tarbiyyar su da irin tata tarbiyyar mai ƙyau."

Tsayawar mota ita tasa ya yi wani saurin tashi zaune cikin sakan ɗin da bai fi rabi ba, tare da gyarawa yana saka gilashin fuskarsa. Ana buɗe ƙofar nan da nan na ga har ya rikiɗe ya tafi cikin jinin sarautar sa. Kafin na ƙarasa kallon ikon Allah har an buɗe mini nawa ɓangaren take na tunano irin tawa ƘASAITAR a baya. Na yi saurin juyewa ni ma.

Ina kunno kai wajen motar nan na ga taron mutanen da sai ka ce wani biki ake,ko gagarumin taro. Yana tsaye har sai da na zagayo sannan muka jera da shi cikin kunya da naji. Muna isa cikin fada aka wuce kai tsaye,fadar ma ta waje, ba ta cikin gida ba.

Allah Sarki. Gaskiya Sarki yana son Yarima,son da na rasa cikin mu uku nawaye ya fi ƙarfi. Mama ko Mai Martaba ko ni? Wannan tunanin ya faɗo mini ne a daidai lokacin da muka shiga fada na ga Sarki ya yi saurin miƙewa tsaye yana fara'ar da ta bayyana a filin fuskarsa. So da so ya haɗe,a take Yarima ya yi saurin isa yana murna, ya tsugunna a gaban mahaifinsa, tsugunnon girmamawa, Mai Martaba ya sunkuya tare da dafa kansa.

Fadawa suka ɗauki roƙon kirarinsu, "Nan Sarki ya amsa."

Mai martaba ya ɗago shi, madadin ya sake shi, sai kawai na ga ya rungume shi. Fada ta ɗauki ihun murna har da tafi. Ni kuwa wani irin daɗi ya saukar mini a lokaci ɗaya, saboda Yarima na ɗagowa sai ya nunawa Sarki ni. Ganin haka yasa na isa na yi saurin tsugunnawa a gabansa. Ya dafa kaina nima. Gaba ɗaya fadawa suka ɗauki maganarsu.

"Sarki na amsawa, Gimbiyar mata wacce ta isa, gaba sarauta baya mulki,so da ƙauna dole a yi miki shi."

Ina tsugunne Sarki ya koma ya zauna, sannan duk faɗar aka zauna har da shi Yarima, ya tsugunna kusa da ni. A nutsuwa Sarki ya fara magana, wanda ƴan jarida da ƴan ɗaukar hoto da na talabijin sun zagaye fadar.

"Na godewa Allah da ya kawo ni wannan ranar ta farin ciki, shi ne ranar da Yarima mai ci gaba da mulkin mutanena ya dawo lafiya tare da iyalansa. Allah yasa masu albarka ga auren su. Ya yi tafiya ta hutu tare da iyalansa ta tsayin watanni uku. Allah ya dawo mana da shi lafiya, Allah ya bashi ikon riƙe iyalinsa lafiya da kuma al'ummar garina.

Na gode da irin karancin ƙaunar da ku ka nuna mana,ni da iyalina gaba ɗaya, Allah ya saka, ya kuma kawo mana canjin rayuwar jin daɗi a nan gaba. Kuma buƙatar da iyalinshi suka buƙata a takardar da ta iso min daga hannun jakadiyarsu,an gama ta tun wata biyu
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KASAITA 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album