Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DAN SARKIN SAUBAN Complete Hausa Novel Document by DAN SARKIN SAUBAN


DAN SARKIN SAUBAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 88500



DAN SARKIN SAUBAN

Reading Time: 7 Hours

Added On: 27, Feb 2025

Author: Farida Bashir Ummu Safwan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 512.38 kb

File Type: txt

Views: 123+

Download: 337+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍




🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴




Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*Page 1*






*Barka da sallah da fatan kowa yayi sallah lafiya*???





****** Manyan motocine bak'ake guda biyar a jere da juna, suna tafiya a kan lafiyayyen titi wanda yaji kwalta sai jiyaniya kakeji Tana tashi " Wanda motar jami'an tsaroce Suka rako yarima sauban domin Kula da lafiyarsa."

A katafaren wani babban gida Mai girman gaske mai d'auke da kwalliyar sarauta a jikin gidan duk wanda yaga gidan yasan gidan sarauta ne dibo da yanayin gidan da kuma fadawan dake, gadin get din kofar gidan,
Idan ka diba KO wanne yana sanye da uniform dinsa blue tare da Dan sirkin ja a, jikinsu,
gidan adalin SARKI ne maiji da mulki da k'asaita."
Fadawa dake gadin get d'in k'ofar gidan zasu Kai kusan su ashirin ko wanne da abinda yake Kula dashi a wurin,
Suna jiyo jiniya da sauri ko wannensu ya mik'e tsaye jiki na rawa Suka bud'e get sai murmushin farin ciki sukeyi tare da d'agawa motocin hannu cike da farin ciki, sai da motocin Suka gama Shiga cikin gidan gaba, d'aya snn suka rufe get d'in, Suka runtuma su dukansu sukabi bayan motocin suna zubawa yarima Sauban kirari."

jiniya tare da kid'e kid'e da bushe bushe ya karad'e gidan sarautar ga baki d'aya Wanda duk, wani halitta dake rayuwa a cikin gidan yasan yarima sauban ya iso mahaifarsa."

Da gudu sarkin gida ya Isa fada ya durk'usa a gaban maimarba sarki Abdullah ya Kai gaisuwa gareshi cike da, girmamawa tare da yimasa Albishir na isowar yarima cikin k'oshin lafiya."

Murmushi sarki yakeyi Yana girgiza kai, Wanda duk Wanda ya kalli fuskar sarki kasan, yana cikin farin, ciki d'ansa Wanda yafi soyuwa a ransa ya, dawo, cikin k'oshin lafiya,

, fadawa suka shiga cewa sarkin gida, "sarki yaji dad'in wnn Albishir naka, sarkin yayi murna, sosai, tukuicin ka na musamman ne a wurin sarki Mai Adalci."

"Runsunawa sarkin gida ya Kuma Yi Yana "fad'in godiya nakeyi Allah ya k'ara Nisan kwana, da lafiya,
Snn ya tashi ya fita cikin sauri yanufi sashen fulanin sarki domin y Kai mata Albishir d'in dawowar sauban."

Cikin saurin masu Kula dashi suka fito daga motar da suke,
suka zagaye motar da yake ciki sai da aka d'auki kusan minti biyar suna zagaye da motarsa snn suka bud'e Masa ya fito, duk da dama hakan Al'adarsa take baya saurin fitowa a mota da zarar anyi parking sai ya d'auki kusan minti biyar a ciki snn yake fitowa." Saboda tsaro😎

Kyakkyawar K'afarsa yafara zurowa a waje Mai d'auke da rufafin talkaminsa masu tsananin kyau,
duk Wanda yaga yanda ya fito da k'afar sa a waje yasan mamanlakin k'afar ya Kai k'arshe wurin had'uwa da gayu,
cikin k'asaita ya Kuma ziro k'afarsa d'aya sai da a kuma d'aukar minti biyu snn,
Cikin isa da mulki yafito da gangar jikinsa daga motar,
subahanallah tsarki ya tabbata ga mamanlakin wnn halitta,
Dogone Mai matsakaicin tsawo fari ne fes, kakkaura Mai cikar halitta, fuskarsa Tana zagaye da saje Mai had'i da gashin Baki Wanda ya kwanta luf a fuskarsa ya k'ara yiwa fuskar k'awanya da adon kyau, hancinsa dogone har baka yana da manyan idanu, tare da d'an k'aramun bakinsa, fuskarsa Tana d'auke da murmushi Domin Yana cikin farin cikin ganinsa a cikin k'asarsa ta haihuwa wato Nigeria."

*SAUBAN KENAN D'AN SARKI ABDULLAH*

Busa Kakeji tak'ara tashi tare da kid'e kid'e Ana zuba Masa kirari tare da yimasa sannu da zuwa a Nan take harabar gidan sarautar ta cika da kuyangi da bayi tare da fadawa ko wanne sai kawo gaisuwa yakeyi cike da girmamawa
Murmushi kawai yake sakar masu tare d'aga masu hannu Alamar ya Amsa,
Kasancewar Sauban mutum ne Wanda baya wulak'anta nak'asa dashi, snn yana daraja d'an Adam musamman bayinsa da kuyanginsa da duk Wani Wanda yasan yana k'asa dashi,
Dan hakan suma suke matuk'ar son sa suke gurmamasa tamkar sarki dake mulki,
snn suka bi bayansa sukayi masa rakiya har zuwa sashensa."

Hakince take akan kujerarta ta sarauta wacce tazo da ita tin daga gidan mahaifinta,
da gudu d'aya daga cikin bayinta tashigo ta Kai durk'ushe a gabanta tana fad'in "ranki ya dad'e Allah ya taimakeki ya k'ara maki lafiya da Nisan kwana ya uwar gijiyata nazo maki da Albishir Mai dad'i, jarumin mijinki d'a d'aya tamkar da dubu kyakkyawan mijinki Mai cikar Kamala da haiba mai kyawawan halayya irin naki, a yanzun nan ya dawo daga k'asar England ranki ya dad'e na ganesa da idona yanzun nan ya nufi b'angarensa duk wannan k'id'e kid'e da bushe bushen da kikeji duk shi akeyiwa Ana tayashi murnar dawowarsa."

Tsawa matashiyar budurwar Wanda bazata wuce shekara 25 ba, ta daka mata cikin d'aga murya tace "yimun shuru rufemun bak'in bakinki mummuna kawai marar kyawon gani tabbas yau sai kin fuskanci hukunci Mai tsanani a gareni tinda har kike iya durk'usawa a gaban idona ki dinga zanyanomun suffar mijina tare da yabonsa,
Hakan ya nuna a duk lokacin da Kika gansa sai kinbishi da ido kina k'are masa kallo kina masa kallon k'urullah, kina kallemun shi tes tin daga k'asansa har samansa."
shin ko kin Manta ban had'a yarima da kowa ba?
Shin ko kin manta da Nasha fad'a maku da zarar kunga fitowarsa ko wacce daga cikinku ta rufe idonta kada ta kuskura ko sawon k'afarsa ta kalla bare a Kai ga kayan dake sanye a jikinsa."

Ta nuna mata wani fili dake can bayan sashenta nesa da ita sosai filine Wanda ba komai a cikinsa sai itacen mangwaro da gwaiba tare da iccen bedi Wanda ya rufe wurin ruf ko wacce irin halittar k'waro mai cutarwa zaka iya samunta a wurin kasan cewar ba kowa yake zuwa wurin ba,
Ta nuna mata wurin tace "a can Zaki dinga kwana har tsawon sati d'aya batare da anbaki abinci ko ruwan Sha ba, snn kada ki kuskura nazo wurin na tarar da kwarar ganye d'aya ya fad'o k'asa batare da kin d'aukeshiba."

Runsunawa tayi tana fad'in tuba nakeyi ranki ya dad'e godiya nakeyi Allah ya k'ara girma da d'aukaka, snn ta tashi tanufi wurin da aka umurceta tana tafiya tana sharar hawaye domin tasan dolene ta aikata abinda uwargijiyarta tasakata Wanda tasan da zarar tashiga wurin mutuwa kawai zatayi domin batasan iya abinda zata tarar a wurin ba "

Yana shiga harabar b'angarensa ya d'agawa fadawa hannu alamar su dakata cak suka tsaya tare da runsunawa cike da girmamawa snn yayi masu nuni akan suyi tafiyarsu,
Cikin sauri suka juya suna fad'in kahuta lafiya yarima mai jiran gado, suna zuba masa kirari suka bar wurin, Wanda ya dad'e da shigewarsa sashensa. "

K'ofar bithdrom d'insa ya tura yashiga komai yana nan a gyaransa tsaf tamkar yana rayuwa a cikin d'akin Wanda yasan aikin Amintattun bayinsa ne masu kula da b'angarensa tare da abincin sa. "

Ajiyar zuciya ya sauke ya kai kwance akan lafiyayyan gadonsa Wanda yaji zanen gado na Alfarma, yashiga furta Alhmdulillah tare da kai hannunsa a fuskarsa yashafi sajen dake kwance a kan kyakkyawar fuskarsa har, zuwa gemonsa ya lashe leb'onsa na k'asa tare da lumshe idonsa yashiga tunanin rayuwarsa ta, baya tare da, rayuwar da akeyi a cikin masarautar nan tare da dalilin tafiyarsa, England. "

Doguwar ajiyar zuciya ya sauke Tare da mik'ewa tsaye ya soma cire kayan jikinsa domin ya d'an watsa ruwa ya shirya ya tafi fada domin gaida maimartaba mahaifinsa
Bayan ya kammala yin wankan ne yafito d'aure da towel hannunsa yana d'auke da d'an k'aramun towel yana tsane ruwan jikinsa zuwa kansa,

Turo k'ofa akayi cikin isa da k'asaita ba tare da anyi sallama ba aka shigo,

K'amshin turarenta ya tabbatar masa da wacce tashigo, masa d'aki a dai dai wnn lokacin,
Ransa yab'aci matuk'a da rashin yin sallamarta, wato har yanzun saudat tana nan da halinta bata sauyawa ba,
shi har ga Allah ya manta da yana da wata mata a rayuwarsa." Saboda Sam ya tsani halin saudat da duk wani mai hali irin nata,
Ci gaba yayi da abinda yakeyi yayi kamar bai san tashigo d'akinba. "

Tsaye tayi wuri
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DAN SARKIN SAUBAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album