Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

FARAR WUTA BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by FARAR WUTA BOOK 1


FARAR WUTA BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 89873



FARAR WUTA BOOK 1

Reading Time: 7 Hours

Added On: 20, Jan 2025

Author: Aysha Shafi'ee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08067794315

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 466.68 kb

File Type: txt

Views: 229+

Download: 266+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: SHIMFIDA.
A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...!
Me zai faru a lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai? A lokacin da ka shiga shiga cikin wata duniya da zaka ji baka son barinta? ka bi ahalin cikinta kuna nutsewa cikin ramin da baku san dashi ba? ka shagala da kallon FARAR WUTAR da ta juye tunaninsu, ta wanke kwakwalwar su har kowa a duniyarsu ya manta cewar wuta, WUTA ce! Duk kuwa irin FARINTA.
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.

BABI NA ƊAYA.
~~~~~
Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen ɗin da aka zagaye da langa-langa daga ɗan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani ɗaurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi.
Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa.
Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai.
Ƴar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai ɗaukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an ɗiga wani abu a cikinsu.
"Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a ɗora don yanzu zaki ji su sun dawo."
Amina ta buɗa labule ɗakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace.
"Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi."
"Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki."
Da murmushi tace.
"Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta."
Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin.
"Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah."
Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba.
Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daɗe da soke Jami'a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da ɗan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴan sa zasu huta da duk wani gata na duniya.
Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha faɗa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai.
Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa.
Mu'amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko ɗaga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai.
"Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa."
Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin.
"Ta nawa?" Ta tambaya.
"Ta naira Ashirin."
Sai ta ajiye farantin waken ta miƙe ta karbi kudin, watanni hudu kenan da fara sana'arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke ɗebe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu bukatunta da kanta har ma ta taimakawa ƙannenta da ɗan kuɗin kashewa, saɓanin a watannin baya da bata komai.
Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka... Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin abubuwan da suka dace da rayuwar mutum.
Ta ɗebowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo.
"Amma ina wuni."
Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukunyar data dauka.
"Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?"
Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum.
"A'a bata fita ba, girki take yi tukunna."
"To bari in gani nima idan na gama nawa ko zan iya bin ta, tun jiya nake waƙar ya kamata in koma wallahi."
"Ai jikin nata ma da sauki."
Cewar Fatiman tana nufar hanyar ɗakin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiya ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa.
"Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo."
Tana bude labulen ɗakin Fatiman ta fada, da fara'arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ƙarasa gefen katifarta inda Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi ɗaya sai kayan kwalliya.
"Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake."
Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da take alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne sosai.
"Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum."
"Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkhairi... Kai wannan tafi kyau wallahi." Ta fada tana daga wata.
"Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake."
Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace.
"Sallah fa da nisa, ki ɗinka abarki kawai. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo."
"To shikenan." Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace.
"Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?"
Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace.
"Shi da yake dan makaranta ta yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani."
Fatima ta tabe baki.
"Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ƙyale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don naga alama yanzu idanunki basa ganin kowa."
Sai a lokacin Amina ta kalle ta.
"Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu'amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma bana takura masa."
"Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?"
Ta daga kanta.
"Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.'
"Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai mutum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya ɗaukar ɗawainiyar wasu ma."
Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji a zuciyarta bane, sai da ta kai ƙarshe sannan ta shiga haɗa kayan tanafaɗin.
"To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin.
Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din.
"Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin..."
Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin ta shiga ɗaka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya.
Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download FARAR WUTA BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album