Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

SHIMFIDA.
A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...!
Me zai faru a lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai? A lokacin da ka shiga shiga cikin wata duniya da zaka ji baka son barinta? ka bi ahalin cikinta kuna nutsewa cikin ramin da baku san dashi ba? ka shagala da kallon FARAR WUTAR da ta juye tunaninsu, ta wanke kwakwalwar su har kowa a duniyarsu ya manta cewar wuta, WUTA ce! Duk kuwa irin FARINTA.
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.

BABI NA ƊAYA.
~~~~~
Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen ɗin da aka zagaye da langa-langa daga ɗan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani ɗaurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi.
Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa.
Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai.
Ƴar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai ɗaukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an ɗiga wani abu a cikinsu.
"Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a ɗora don yanzu zaki ji su sun dawo."
Amina ta buɗa labule ɗakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace.
"Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi."
"Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki."
Da murmushi tace.
"Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta."
Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin.
"Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah."
Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba.
Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daɗe da soke Jami'a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da ɗan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴan sa zasu huta da duk wani gata na duniya.
Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha faɗa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai.
Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa.
Mu'amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko ɗaga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai.
"Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa."
Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin.
"Ta nawa?" Ta tambaya.
"Ta naira Ashirin."
Sai ta ajiye farantin waken ta miƙe ta karbi kudin, watanni hudu kenan da fara sana'arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke ɗebe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu bukatunta da kanta har ma ta taimakawa ƙannenta da ɗan kuɗin kashewa, saɓanin a watannin baya da bata komai.
Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka... Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin abubuwan da suka dace da rayuwar mutum.
Ta ɗebowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo.
"Amma ina wuni."
Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukunyar data dauka.
"Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?"
Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum.
"A'a bata fita ba, girki take yi tukunna."
"To bari in gani nima idan na gama nawa ko zan iya bin ta, tun jiya nake waƙar ya kamata in koma wallahi."
"Ai jikin nata ma da sauki."
Cewar Fatiman tana nufar hanyar ɗakin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiya ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa.
"Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo."
Tana bude labulen ɗakin Fatiman ta fada, da fara'arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ƙarasa gefen katifarta inda Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi ɗaya sai kayan kwalliya.
"Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake."
Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da take alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne sosai.
"Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum."
"Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkhairi... Kai wannan tafi kyau wallahi." Ta fada tana daga wata.
"Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake."
Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace.
"Sallah fa da nisa, ki ɗinka abarki kawai. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo."
"To shikenan." Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace.
"Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?"
Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace.
"Shi da yake dan makaranta ta yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani."
Fatima ta tabe baki.
"Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ƙyale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don naga alama yanzu idanunki basa ganin kowa."
Sai a lokacin Amina ta kalle ta.
"Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu'amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma bana takura masa."
"Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?"
Ta daga kanta.
"Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.'
"Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai mutum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya ɗaukar ɗawainiyar wasu ma."
Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji a zuciyarta bane, sai da ta kai ƙarshe sannan ta shiga haɗa kayan tanafaɗin.
"To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin.
Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din.
"Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin..."
Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin ta shiga ɗaka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya.
Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman dattijon mutum ne mai sana'ar harkar aikin katako, ya samu wadata a da, don gidan da yake zaune da iyalansa na kansa ne, amma a yanzu abubuwa sun tsaya masa ta yadda ya ɗauki hakan ya sanya a ransa har ya zama shine damuwarsa a kodayaushe. Ƴaƴan sa biyar tare da matarsa Halimatus- Sadiya bafulatanar Niger da iyayenta suka dawo Nigeria da zama.
Amina ce ta farko, sai Aminu, Maryam, Adam da kuma autarsu Hafsa. Maryam, Aminu, da Adam suna matakin secondary ne a karatu yayin da Hafsa kadai take Primary, amma da yake makarantar da suke zuwa wata community school ce dake waje ɗaya, tare suke tafiya dukkaninsu tare suke dawowa.
Babban damuwar Alhaji Sulaiman a yanzu shine ganin ƴaƴan sa na ƙara tasawa kuma harkar samun sa na ƙara yin baya, karayar arziƙin da ya samu ta taimaka ƙwarai wajen karya zuciyarsa akan komai, kullum cikin lissafi yake da kuma damuwar da ƙarara kowa ke gane ta duk da irin nuni da kuma nasihar da matarsa ke yi masa a kullum.
***
Ƙarfe Biyu da rabi.
"Yaya dan girman Allah zaki bani naira dari? Ƙunshi zanyi."
Maryam ta fada lokacin da take ƙoƙarin cire uniform ɗin ta bayan sun dawo daga makaranta. Amina na zaune tana ninke kayan wankinta tace.
"Ƙunshin me zaki yi?"
"Bikin yayarsu Na'imah fa, kin manta jiya nazo da katin."
Jin tayi shiru yasa ta sake tambaya.
"Zan baki Maryam, Allah ya kaimu gobe."
"Me za'a bayar? Idan ana ƙaunar Allah nima a taimaka mun."
Aminu ya fada yana shigowa cikin ɗakin.
"Kaima ƙunshin zaka yi?"
"Me kyau ma kuwa, don kin san sai yafi fitowa a hannu na ma akan bakar fatarta."
Ya fadi hakan sanin cewar shi fari ne, don ƴan mazan biyu su suka yiwo mahaifinsu sak a kammani da kuma hasken fatan, matan kuma Suka yo mahaifiyarsu, har gwara Maryam ma ana cewa idonta irin na babansu ne, amma Amina da Hafsa babu abinda suka bari a kammanin Amman.
"Wallahi ni ba baƙa bace kaima ka sani, irin wannan kalar fatar sai ka zagaye garin nan kaf baka samu irinta ba."
"To idan ma an samu me za'ayi da ita? Da dai irin ta Amina kika ce sai in yarda, amma ke duk gidan nan ma akwai mummuna kamar ki."
Maryam ta kara haɗe ranta tana saka hijabin data ɗauko. Amina ta jefo masa wata riga dake hannunta tana murmushi.
"Haɗa mu kayi kawai kake zagi Aminu, dani da ita ɗin me ya banbanta damu, ka takurawa Maryam wallahi."
"Haba ya zaki hada kalar ki data wannan fingilar? itama ta hakura ta karɓi kanta yadda take ne taƙi, sai faman iyayi fal ciki."
Da ƙunƙuni Maryam ta faɗi wani abun kafin ta tayar da sallarta. Hakan yasa shi dariya don shi kansa ya sani girman dake tsakaninsu ne kawai yasa take raga masa a azababbiyar magana da kuma rashin kunyar dake cikinta.
"Sai yaushe zaka fita yau?"
Amina ta tambaya sanin cewar da ya dawo baya dadewa a gidan yake tafiya can inda yake koyon gyaran mota a can hanyar gidan zoo, har ma ya fara kwarewa don kusan shekara biyu kenan da Baba ya kai shi wajen.
"Sai na ƙarbowa Baba, kayansa daga wajen guga..." Ya shafo kansa.
"... Tun dazu ma fa ya kamata in je, sun ce sun gama."
Kafin Amina tayi magana, Hafsa ƙaramar ƙanwarsu ta shigo gidan hannunta riƙe da ƙullin farar ledar atturuhun data siyo na girkin dare da kuma takardar yashin madina tana zubawa a ɗaya hannunta tana lashewa. Amina ta ɗaga murya ta kirata ganin bata da alamun shigowa.
"Ki shigo ki cire kayan nan ki saka na islamiyya, ga uku nan har ta kusa, Adam har ya tafi kina nan."
Tana jin hakan Idanunta irin na Amina suka kaɗa a take sannan muryarta ta koma ta kuka, ta shigo ɗakin da sauri tana faɗin.
"Dan Allah kice Ya Maryam ta raka ni, wallahi zane ni za'ayi..."
Kafin Aminan ta amsa, Aminu yace.
"Saka kayan muje in raja ki daga nan sai in wuce.
Ai kuwa da murnarta ta ruga da gudu zuwa dakin Amma inda kayanta suke, ta sani ba wanda ya isa ya dake ta makarantar tunda Aminu ne zai raka ta.
Aminu ya ciro Naira dari biyu daga aljihunsa ya cilla kan sallayar da Maryam ke sallah yana faɗin.
"Gashi nan kije a zana miki abinda ba ganinsa za'ayi ba."
Amina tayi murmushi tana godewa Allah a zuciyarta, tana son yadda suke tallafar junansu akan irin ƙananun buƙatun nan.
Hafsa bata dawo ba suka tsinci sallamar mahaifinsu, dukkaninsu suka kalli juna a lokaci guda sanin cewa lokacin ba lokacin dawowarsa bane, ƙa'ida ne sai bayan sallar magriba kullum yake dawowa don har Aminu yana yawan riga shi isowa ma.
"Allah yasa kar ya tambayi kayan nan..."
Aminu ya faɗa yana dafa kansa.
Ta tsakanin raga-raga labulen Amina ta hango yadda mahaifin nasu ya dafa kan Hafsa da ta taho ta rungume shi, sannan kai tsaye ya nufi hanyar ɗakinsa.
Taga Amma ta fito daga falo sanye da hijabi alamun salla tayi ta bin bayansa tana fadin sannu da dawowa.
"Ke maza ki dauko takalminki mu fita."
Cewar Aminun, sannan ya juyo ya kalli Amina.
"Kice masa tun dazu na tafi karɓi kayan."
Ai kuwa yana sanya kafarsa waje suka ji Baban yace.
"Fita ce ta kama ni Halima, ina kayan da nace a karbo min?"
Basu ji amsar da Amman ta bayar ba sai muryarsa da ta sake dagawo wajen kiran Aminu.
"Aminu! Yana gidan nan?"
"Na shiga uku.."
Cewar Aminun, kuma Amina na kallon sanda Maryam ta murmusa a sallarta don daɗi.
"Baba sannu da zuwa, wani abu ne ya faru ka dawo yanzu?"
Ta tsinci muryarsa da yayi sauri ya tsugunna yana shafa kai ganin ya fito.
"Ni da gidana don na dawo sai ka tambaye ni me nazo yi? Ina kayan da nace ka karbo min?"
"To, to, bari aje a karbo."
Ya fada kamar sai a lokacin yace 'je ka karbo din,' kuma bai jira ya sake cewa komai ba ya kama hannun Hafsa da ta gama shiryawa suka yi waje.
Alhaji Sulaiman ya girgiza kansa kawai saboda takaici sannan ya kalli Amma dake tsaye a gefensa.
"Hajiya Kilishi ce yanzun nan ta kira ni tace tana son ganina."
Daga cikin ɗakin Amina zata rantse daga ita har Amman a lokaci guda suka yi murmushi.
Hajiya Kilishi ƴaruwar Baba ce, mace ce mai kirki da son kyautatawa, ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu ta kowanne fanni, tun kafin Mahaifinsu ya rasa arziƙinsa har bayan komai ya cakuɗe musu, don hatta kuɗin rubuta jarabawarta ta fita daga secondary ita ta tallafa aka biya, babban taimakon da tayi musu na kwanan nan shine lokacin da Maryam ta kamu da rashin lafiyar ciwon ciki, wanda daga ita har su kowa ya wahala kafin a gano cewar wani ƙari ne ke fito mata a gefen cikin kuma yayi girman da har sai an cire shi.
A wannan lokacin komai nasu ya riga ya ƙare wajen jinya, don hatta abinci sai daga gidan wan Baban ake kawo musu kullum ko tukunya basa dorawa, ɗan abinda Baba ya samu da kuma na wajen Amman daga ƴan sana'o'in da take yi duk a asibitin suke karewa.
Don haka a dole Baban ya shiga neman bashi ƙofa-ƙofa, ƴanuwansa suka hada masa iya abinda zasu iya amma ko kwata ba'a shafe na lissafin ba, Hajiya Kilishi ita taji labari a danginsu, ta kira Baban har gida ta bashi tallafin naira dubu ɗari uku, kuɗin aikin har da ɗoriya akai, tun daga wannan lokacin zuciyoyinsu suka kara girman darajarta a wajensu.
Mijin ta wani babban mai kuɗi ne kuma sanannen mutum ne, itace matarsa ta biyu kuma ƴaƴan ta biyar dukkaninsu mata, amma ance saboda zaman amanar da suke yi da uwargidanta babban ɗanta ma a wajen Hajiya Kilishin ya tashi tun yana yaro ta yadda ba kowa ne ya san cewa ba itace ta haife shi ba, Baba yasha gaya musu cewar ko gidan yaje baya iya banbance ƴaƴan ta dana uwargidan.
"Shinkafa da wake kuka yi? A zubo min dan Allah kafin yaron nan ya dawo."
Muryan Baban ta katse tunanin Amina daidai lokacin da Maryam a gefenta ta idar daga sallah, ta sake kallonsa ta cikin labulen sanda da yake cewa.
"Allah yasa Amina ta daka yajin nan nata mai daɗi."
A lokaci guda murmushi ya suɓuce a fuskarta, sai kawai ta mike tana faɗin.
"Akwai Baba, Bari in kawo maka."
***
Royal Brompton Hospital.
Sydney St, London SW3 6NP, United Kingdom.
...So I took your hand, back through lamp-lit streets,
I knew,
Everything led back to you
So can you see the stars over Amsterdam?
You're the song my heart is beating to...
Waƙar a hankali take fitowa daga cikin labtop ɗin dake ajiye a wani ɗan ƙaramin tebur da kujerarsa dake can jikin dogon windon ɗakin, ɗakin asibiti ne da banda gadon mara lafiyar da kuma tarin computers ɗin gefe dake auna lafiyar wanda ke kwance, babu komai sai wata drawer daga can gefe wadda aka yi mata ado har da wasu ƴan fulawoyi, ɗakin a gyare yake tas yana kuma ƙamshi mai daɗi, ga room heater dake fitar da wani ɗumi mai daɗi sakamokon sanyin ƙanƙarar snow ɗin dake zuba daga waje.
A hankali idanun mara lafiyar dake kwance akan gadon suka buɗe, kuma duk da lumshewar su girman su ya fito a lokaci guda, matashi ne mai siririyar fuska, yana da yalwar gashin kai da kuma na gira kamar yadda na idanunsa suke dogwaye ta yadda idan ka kalle shi zaka ga kamar baya iya buɗe idanun nasa ne sosai.
Ya ɗago da hannunsa dake maƙale da allurar ruwan drip ɗin gefe, ya kalli hannun tsawon wasu sakanni kafin yasa ɗaya hannun nasa ya murza goshinsa alamun takaici, sannan a lokaci guda ya fizge drip ɗin daga jikinsa ya mike zaune, jini ya shiga fitowa daga inda allurar ta fita amma bai ko bi ta kai ba ya kalli rigar dake jikinsa, rigar asibitin ce wadda ake bawa kowanne mara lafiya.
Ya shiga ƙarewa ɗakin kallo a hankali har zuwa kan drawer dake can gefe, a lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da jakar da Ishaq ya ajiye a ciki jiya don haka ya mike tsaye, jiri ya so ɗaukarsa amma ya dage ya tsaya akan ƙafafunsa sannan ya isa ga drawer.
Ya buɗe ciki ya fito da wata baƙar jaka ya shiga fito da kayan ciki, ƙamshin turarensa na 'Dior Sauvage' shi ya tabbatar masa da cewar kayansa ne tun kafin ma ya gane su, kala biyu ne sai kuma wata ƙatuwar rigar sanyi wadda ke zuwa har gwiwa, bai yi tunanin komai ba ya shiga canjawa zuwa kayan, sai da yazo ɓalle maɓallan rigar saman sannan ya kula da jinin dake fita daga hannunsa.
Don haka ya saka rigar asibitin da ya cire ya goge sannan ya ɗora daya rigar, ya kuma jawo rigar sanyin ya dora akai, bai ko ɗauke rigar asibitin dake kasa ba ya saita facing Cap ɗin da ya ɗauko a ciki daidai fuskarsa sannan ya nufi hanyar kofar ɗakin, ya san duka wayoyinsa basa nan kuma Ishaq bai bar tasa a gefen labtop ɗin ba don haka ya nufi ƙofar ya buɗe, dogon korido ne a wajen mai dauke da kofofin ɗakuna da kuma mutane dake ta wucewa ta cikinsa, ya tabbata babu ma'aikatan da suka san shi a cikin waɗanda ke wucewa don haka kansa tsaye ya bi ta cikin mutanen dake tafiya ya saje, yana mai nufar hanyar waje.
Iskar dake kaɗawa a wajen mai tsananin sanyi ta ratsa fuskarsa sanda ya fito daga asibitin gabaɗaya, dare ne lokacin, ga fitulu a koina, na kan titi dana motoci, ga mutane birjik musamman na ƙafa sai faman wucewa suke.
Haka ƙofar asibitin take a kullum, tun daga shekarun da ya fara zuwansa har yau. Sanyi ya shiga ratsa kunnuwan sa dake buɗe sannan a lokaci guda yaji wata irin yunwa ta mamaye shi, sai kawai ya saka tafin hannayensa duka biyu ya gefen fuskarsa lokacin da idonsa ya sauka akan sunan wani kanti daga can tsallake, kantin da yake yawan yin siyayya duk lokacin da yazo kasar.
"24 dollors." (Dubu goma.)
Baturen dake kan kantar ya faɗa a lokacin da ya gama lissafa abubuwan daya ɗebo.
Ya kai hannunsa bayan aljihu kamar zai fito da wallet sai kuma ya dawo dashi, ya matso daidai jikin kantar yana kallon mutumin yace.
"You know me right?" (Ka san ni ko?)
Kallon da mutumin yake masa yasa ya cigaba da cewa.
"I used to come around, from that hospital...(Ina yawan zuwa, daga wancan asibitin..)"
Ya juya ya nuna asibitin sannan ya dawo ga fuskar mutumin da bata canja ba, sai kawai ya daga hannayen sa sama alamun sallamawa sannan yace.
"What I mean is my brother is coming to pick me from here... So do you mind If I just wait for him while I eat these? Because honestly I dont have anything with me right now but I assure you he's going to pay when he arrive...."
(Abinda nake nufi shine ɗan uwana zai zo yanzu ya dauke

Please Login or Register in order to submit comment