Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anyi wasu hadaddun drawers a ciki da wani bakin katako da ya dace da kalar marbles din, ta ja numfashi a hankali sannan tayi addu'a ta taka kafarta ciki a hankali tana jin sanyinsa na ratsa ta.
A gaban katon mudubin ciki ta tsaya tana kallon yadda idanunta suka yi ja dama yadda fuskarta ta dan kumbura, sai kawai ta bude fanfon kasan sa tayi alwalarta, ta haɗa da wanke wuyanta dama rabin bayanta, kuma dadin ruwan yasa wata zuciyar tace mata taje ta ɗauko sabulu a akwatin cosmetics ɗin nan tayi wanka gabaɗaya amma ta girgiza kanta. Ba yau ba, ba yanzu ba.
A akwatin undies ɗin nan da Maryam tace ta dauko hijabinta guda daya, ta dawo kan carpet din dakin tayi sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta dago da hannayenta da niyyar addu'a amma sai ta rasa ma me zata roƙa, saboda haka sai kawai ta dunƙule jikinta waje ɗaya ta ɗora kanta daga gefen gadon tayi shiru.
Shirun da a cikinsa taji lokacin da aka buɗe kofar dakin.
**
Karfe sha ɗaya daidai ta iso da Ma'aruf ƙofar gidan, ginin ya tsaya a gabansa kamar wani tsauni, babu wanda zai ce ma a cikin gidansu aka fitar dashi, don gate dinsa yayi gefe da yawa ta daya bangaren. Ya lashe lebbensa na kasa daya bushe yana gayawa zuciyarsa cewa sun zo matakin da suke jira, sakon ya isa kuma maimakon ya dawo cike da kwarin gwiwa sai ya dawo da wani raunin da kalaman da Ishaq ya gaya masa a dazu suka yi sanadiyarsa.
"Ka sani cewa wannan ba labari bane Ma'aruf, ba labari ne da zaka rubuta a yadda kake so kuma har ka kai ƙarshe da son zuciyarka ba. Na fahimci dukkan abinda ka faɗa da kuma dalilin da yasa ka dawo ka yarda da auren, amma hakan baya yana nufin cewa ka tsallakewa abinda zai iya faruwa ne.
Kar ka manta a baya ciwonka ko matakin HypoMania bai kai ba abubuwan da suka faru suka faru, yanzu kana stage na karshe Ma'aruf, kai da kanka kana tsoron wannan matakin, ba sai ka gaya min ba, a idanunka kawai nake gane cewar kaima kana tsoron faruwar wani abu kamar yadda kayi tunani a farko, tunda ni da kai mun sani cewa ba lallai ne mu iya binne komai ba a wannan karon..."
Ya sake lashe leɓɓensa yana jin yadda har a yanzu tasirin kalaman ke yawo a cikin kansa, gargadi Ishaq ɗin yake yi masa ya sani, gargadin da shima ya riga yayi wa kansa duk da cewa bai tsara komai game da auren ba bayan cewar yana son samun bayanansa daga yarinyar, zai tafi da abinda lokaci ya bashi ne kawai yana kuma ƙoƙarin kiyayewa dukkan abinda gaban zata haifar, haka ya gayawa Ishaq, ya kara gaya masa cewar shi yanzu abubuwan dake gavansa ma Allah yayi yawa dasu, sai yaga komai ya lafa masa tukunna ma zai maida hankali kan yarinyar.
Ta cikin glass ɗin motar ya hango ƙofar gate ɗin shiga wajen su Mami dake can gefe, babu kowa a wajen alamun da gaske dare yayi don ya sani cewar an sha hidimar mutane tunda yau ne rana ta karshe a bikin.
Wayarsa ya jawo ya kira Mamin, bugu daya biyu, kuwa ta dauka tunda dama jiran isowar tasa take, har a hanya ta kira shi taji idan ya taho.
"Ma'aruf..." Muryarta dake shaida dimbin gajiya ta kira shi da sunansa.
"Mami na iso amma ba zan shigo ciki ba."
Sai da ta ɗanyi shiru kafin muryarta tace.
"Kai da mutane ne?"
Ya girgiza kansa.
"Ko Ishaq ma nace yayi zaman sa kawai. I'm alone."
"Tohm shikenan da safe na ganka, dama bana son kayi dare sosai baka iso bane, don tun wajen Isha'i suka ƙawo ta, anyi muku addu'o'i masu tarin yawa, hatta ƴan uwan Hajiya Maimuna da basu so abin da farko ba sun yaba sosai da ita da kuma ƴanuwanta Ma'aruf, Ina fatan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa a zaman da zaku yi, Allah ya baka ikon sauke sabon nauyin da ya hau kanka."
Bai san lokacin da ya haɗiye wani abu a makogwaron sa ba kafin ya amsa a hankali, don ji yayi kamar itama tana tuna masa da abinda Ishaq ya faɗa ne.
"Insha Allah Mami. Nagode."
Yaji kamar ta gyada kanta kafin ta sake cewa.
"Na san da wuya idan kaci wani abun, ga abinci nan ma nasa Samira ta tanadar maka tun dazu, a miƙo maka ne?"
Ya girgiza kansa tun kafin ma ta ƙarasa, don baya tunanin a yanzu ko ruwa zai iya sha, tarin abubuwan da ƙwaƙwalwar sa da kuma zuciyarsa ke rabawa basu da adadin da har zai sami nutsuwa ta cikinsu.
Saboda haka sai kawai ya canja zancen da cewar.
"Na zata ma kowa yayi bacci Mami."
"Baccin mai gaskiya? Yanzun nan fa suka dawo daga kai sauran amaren, ai gidan nan yana nan kamar rana don baka shigo daga ciki bane, kuma naku ɓangaren ai yasha dab-dalarsa, sai da kayi haƙuri da abinda zaka gani."
Wani guntun murmushi da bai san dalilin sa baya suɓuce a gefen fuskarsa, don shi a yanzu baya son ganin yarinyar baya jin akwai abinda ya dame shi na harkar auren, sai kawai ya zaro hannunsa daga cikin gashin nasa yana bude kofar motar dashi sannan yace.
"Shikenan Allah ya bamu alkhairi, Allah ya huta gajiya, ta amsa kafin ya kashe wayar. Ya tsaya daga wajen yana kallon ginin gidan kafin ya sake komawa kan wayarsa ya danna wata number, bugu ɗaya biyu matar dake ɗaya layin ta dauka, kuma bayan sun gaisa ta tabbatar masa da cewar Hamida tayi bacci sannan ya katse wayar.
Inda ya kira ɗin, wani Creche ne kamar asibiti inda ake bawa yara kulawa ta musamman, na wasu ƴan Turkey ne musulmai, amma akwai hausawa a cikin ma'aikatan nasu, asibitin da aka kwantar da Hamidan ne da farko suka bashi shawarar ya kawo ta wajen, kuma sai hakan yazo daidai da cewar bai shirya kaita gida a lokacin da ake hidimar bikin nan ba.
Ranar farko da suka je, tayi rigimar cewa ba zata zauna, amma cikin ƙwarewar aikinsu da kuma tarin abubuwan wajen dake kama zuciyar yaro, sai rigimar tata bata je ko'ina ba.
A iya kwanakin nan yana zuwa kullum ya ganta wanda hakan yasa yayi sabo da ita sosai don har ta fara sakewa dashi tana amsa duk ƴan ƙananan tambayoyin da yake mata, da farko ne duk maganar da zai yi mata sai dai ta kalle shi kawai, sai bayan barinsu asibitin ne da ya kawo ta nan sannan ta fara yi masa magana, kuma ya fahimci tana da maganar sosai, kawai bata gama sabawa dashi bane har yanzu, amma ya san aƙalla suna making progress din da za'a zo gabar da zata fahimci cewa shi mahaifinta ne.
Ya sake kallon gidan, babu maigadi don haka shi ya shiga da motar, sannan ya sake rufe gate din ya dawo, ƙafafunsa suka taka kan barandar gidan sannan ya tura ƙofar falon ya shiga a hankali.
Hasken fitulun ɗakin ya shiga idanunsa tare da hotunan kayan da suke ciki, daga kujeru labulaye dama carpet ɗin cikin komai kalar Army green ne da kuma brown, babu wajen dining don haka kofofin korido biyu ne kawai da ya san ɗaya ta kitchen ce ɗaya kuma ta hanyar ɗakuna, sai kawai ya juya a hankali ya rufe kofar falon.
Iskar da akeyi a waje mai zafi ce, yaji ta bayan ya fito daga Acn motarsa, amma a yanzu da ya shigo gidan yaga yadda labulayen falon ke dagawa sai yaji kamar ba irinsu ɗaya da ta wajen ba. A hankali ya zame takalmansa daga kafarsa sannan yayi gaba, ya kuwa ji ƙurar da Mamin ke fada amma bai damu ba, ya shiga hanyar koridon a lokacin da yake jin wani abu kamar bugun zuciyarsa na ƙoƙarin canjawa.
Ƙofofi uku ne a ciki, kuma bai buɗa kowacce ba don guda ɗayan dake gefe da kuma ta can karshe ta kasan kofofinsu ya kula duk fitulunsu a kashe suke, ta farko daga gefen daman sa ce kawai hasken cikinta ya saje da na cikin koridon.
Don haka kai tsaye ya ƙarasa gare ta ya ɗora hannunsa akan mariƙinta, sannan ya buɗe ta a hankali ba tare da tayi wata ƙara ba, kuma babu wani hijabi idanunsa suka sauka akan matar da kowa ke kira da tasa, ɗan karamin frame ɗin jikinta na naɗe a gefen gadon ɗakin, ta jingina kanta da gefen gadon idanunta a rufe, rabin fuskarta na shigewa cikin gadon yayin da hasken fitilar ɓangaren ɗakin ya haske ɗaya gefen fuskar tata.
Hijabin dake jikinta ne ya shaida masa cewa sallah tayi, kuma kafin ya iya sake wani tunanin ta buɗe idanuwanta duka biyun ta kalle shi.
Bai san me ya zata ba, bai san yadda yayi tunanin zai zo ya ganta ba, bai taɓa ma hasko ta a cikin kansa ba balle ya kintaci yanayinta, amma a lokaci guda yaji wani abu ya balle daga cikin zuciyarsa ganin ƙanƙantar ta, don duk a lissafinsa irin Ruƙayya zai gani, amma wannan ƙarama ce sosai, idanunta are so young haka ma jikinta ƙarami ne, yawun da ya sake haɗiyewa yana kallonta yasa wannan karon Adam's Apple dinsa motsawa sama da ƙasa. Kuma a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ƙafafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi.
*
Lokacin da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ƙirjinta, yayin da take jin ƙafafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ƙarshe yayin da take cigaba kallonsa.
Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai ɗan siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki bane, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ƙofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru.
Zuciyarta ta cigaba da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi ɗin ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama?
Taji kamar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da ta faɗawa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru.
"Assalamu alaikum." Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta daɗa hargitsa tunaninta, tasa numfashinta katsewa a maƙogwaronta.
Ma'aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira kawai take yi yayi wani abu ta ɓace daga dakin.
Ya fitar da numfashin daga ƙofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahimci cewa a yanzu ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba.
"Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke kaɗai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min..."
Kalaman suka daki zuciyar Amina ta yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta.
Ya fahimci ba zata yi magana ba don haka ta ga ya sake riƙe hannun kofar sannan ya furta mata.
"Sai da safe."
Ya rufe ƙofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa ɗaukarta gabaɗaya.
**
Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen yayi mata kyau a ido, yadda hasken ya haɗe da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar ɗakinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe da taje wani wajen ta kwana ba tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi.
Ta rufe idanunta ta buɗe tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ƙasa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al'amarin da ta kasa ganewa.
Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ƙarshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani zaɓi illa ta fara fahimtar manufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi.
Ta miƙe zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ƙwaƙwalwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ƴar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yadda akayi alarm ɗinta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ƙofar dakin ta tabbatar muƙullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki.
Bayan ta idar da sallar ta daɗe tana addu'ar neman gafara da kuma ƙwarin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahalar gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito.
Ta dawo cikin ɗakin dake ƙara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aayƙin da take ji daya ne kawai na cewar ƴan gidansu zasu zo, don haka da ƙyar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata ɗaura ɗankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta.
Ta kalli kanta a mudubin ɗakin tana ganin yadda idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman ɗankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gabaɗaya ta ajiye akan mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin.
Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta buɗe ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ƙofofin ɗakuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida haɗuwarsu tun daga nesan da take, komai yana haɗewa cikin kalar ɗanuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin.
Ta jinjina kai a hankali kafin ƙafarta ta tafi zuwa daya korido ɗin anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ƙurar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai ɗan girma data buɗa ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba'a buɗe ba.
Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta cigaba da duba kayan.
A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ƙarasowa hanyar kitchen ɗin, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store ɗin amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya tsaya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ƙofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta faɗo daga wata sama mai nisa.
Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wani yadi kalar sararin samaniya da irin ɗinkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa ta cikin wayar kafin yayi magana.
"Me kace?" Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din?
Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashin kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ƙamshin turarensa, wani abu kamar ƙamshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa.
"That issue aside Faruk, ba yanzu zamu neme shi ba, let's give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let's just focus akan waɗannan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar."
Murza ƴan yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana faɗin.
"Yaya baka ganta bane?"
Kuma kafin ƙwaƙwalwar ta ta gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen ɗin hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour.
"Bata nan kitchen ɗin?"
Ta sake tambaya tana ƙarasowa ciki fuskarta ɗauke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ƙannensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen ɗin ita yake nema. Taga yadda hannayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask ɗin can kusa da gas cooker.
Sai kawai tayi karfin halin ɗauko wani jug a gefe sannan ta buɗe ƙofar store ɗin ta fito, zuciyarta na gaya mata ai tunda a yanzu ƙirgen ya tashi daga su biyu ta tsira.
"Sannu da zuwa."
Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara'a sannan ta taho da sauri ta rungume ta.
"Ashe kina ciki, Barka da safiya."
Sai da zuciyarta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta.
"Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?"
Ta faɗa bayan ta janye daga jikinta, sai ta ɗaga kai da nata murmushin mai fadi ta amsa da.
"Lafiya kalau, nagode sosai."
A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya faɗi sakamakon haɗa idanun da suka yi, kallon da yake mata mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta.
Kuma a lokacin ne babban al'amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya buɗe su akanta, kamar ma ƙifta mata idanun yayi, abinda kafin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen ɗin.
A kusa da kafafunta taji cikinta ya faɗi gabaɗayansa har ƙasa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta tsugunna tana ƙoƙarin tattara jikinta waje ɗaya kafin ta iya fahimtar me take cewa.
"Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta... Na san kema kinyi taki ko?"
Bata gama daidaita tunaninta ba, don haka bata san sanda ta ɗaga mata kai ba tace.
"Ina tashi nima naga na manta chager wayata."
"Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system ɗinta gabadaya ta manta kuma project ɗin masters take yi..."
Ta gyada kai tana ƙoƙarin murmushi sanda wata ta ƙaraso cikin kitchen ɗin itama, watakila itace zasu yi sa'anni ɗaya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda ta fito da ɗan hasken fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi ɗaya da yayan nasu.
"Ashe kina nan matar Yaya..."
Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin.
"Oyoyo, we welcome you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba."
A yanzu ƙwaƙwalwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma'u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan da ƴanuwansa.
"Ƴan gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki..."
Haka Aunty Ma'un ta raɗa mata a kunne.
To me yasa ne komai yake faruwa saɓanin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane?
"Sunana Munaya.."
Ta kara faɗa tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama.
"Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce."
Samirah ta faɗa tana kallonta.
Sai kawai ta girgiza kanta.
"Yarinyar nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita."
"Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ƴanuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ƙwaƙwalwar su ɗaya da Yaya."
Munaya ta girgiza kanta tana murmushi.
"Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya."
Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su.
A falon wadda suka kira da Surayya na zaune kan kujera mai zaman mutum ɗaya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ƙasa kuma wasu ƴan mata biyu ne su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ƴan aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke.
Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa'anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayin gaisuwar tasu.
"Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?"
Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ƴan aikin nan tana gaya musu akwai wata baƙar keda da badu shigo da ita ba.
"Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai." Cewar Munaya tana neman waje kan daya daga cikin kujerun.
Amina ta daga kai tana murmushi.
"Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma."
"Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ganina a compound din

Please Login or Register in order to submit comment