Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa kaar jiya, a yau ta riga ta tsarawa kanta cewa ba zata fita ba don Allah ya sani bata so yaga kamar tana kokarin shige masa ne ko kaɗan, ƙundubalar da tayi wajen yi masa abincin ta wadatar tunda har yanzu bata san manufarsa akanta ba.
Ko a jiya umarnin da ya bata ne kawai yasa ta zauna ba wani abu ba, yadda muryarsa ta furta 'Ki zauna' da kuma yadda ya kalle ta da idanunsa bai bata damar zabi ba ko kadan. Duk da cewa kuwa taji dadin hirar, tsaya... Ba hirar tasu ce ta mata daɗi ba, zancen cewa wannan labarin yana da film ne, don Allah ya sani zata so ganin yadda dukkan tunaninta game da komai na labarin zai fito zahiri.
"... Wato ina gaya maka samun gida a garin nan shine babban abu mai wahala, gidaje ba karamin tsada ne dasu acan ba..."
Hirar rediyon ta cigaba da fitowa yayin da zuciyarta ta fara lissafin kamar yau ya daɗe da yawa, don ko da safe bata ganshi ba kuma yau ita kadai ta yini a gidan, su Sahla da Zahran da suka yi mata alkawarin zasu sake shigo mata yau sun manta da zuwansu makarantar Haddar da suke zuwa shi yasa bata gansu ba.
Tun da tazo gidan basu shigo mata ba sai jiyan, kuma sai a jiyan ta gane ashe su ma suna da magana kamar su Samirah, a cikin gidan idan ta gansu da littafinsu kawai gaishe ta suke yi su cigaba da harkokinsu, amma jiyan da suka shigo tasha labarai kala-kala wanda mafi yawanci ba komai ta gane ba.
Don a baiyane yake yanayin rayuwarsu da tata ba iri ɗaya bane, abubuwan da suka taso suka sansu ita har yanzu saninta bai ƙaraso nan ba, yanayin makarantar su dama ƴaƴan masu kuɗin da suke mu'amala dasu ba iri daya bane da abinda ita ta taso ta sani. Ta tuno wata magana da Aminu ya taɓa gayawa Maryam ranar da yake tsokanarta bayan ta gama kurin cewa ai ita babu inda zata je a raina ta.
"... Nan bayan layin nan idan aka ƙarasa ba sai anje da nisa ba za'ayi iya ɗebo sa'anninki biyar da in suna hira ba zaki taba iya magana ba wallahi sai dai kiyi ta binsu da kallo kina wage baki."
Itama dai kuwan ta wage jiya, don murmushi kawai tayi ta binsu dashi kamar yadda take yi a wajensu Samirah, don har gwara su Zahran ma, su idan suka fadi wani abu sai ta biya shi sau biyu akanta kafin ta fahimta musamman Surayya da ta fahimci tafi su iyayi gabaɗaya. Suna da daɗin mu'amala sosai, da gaske suke sun karbe ta a cikinsu ba tare da tunanin komai ba,
Ta tuna sanda Samirah ke mata bayanin dalilin da yasa basu je gidansu da biki ba.
"Mu fa bamu san da bikin ku da Yaya ba sai ana saura two weeks da aka haɗa lefe sannan Mami ke gaya mana, kuma ko ranar dinner ma munso mu kai muku cards din. Yaya Shukra ce ma ta bani ranar luncheon na saka a jakar Khadija (wata kawarta) ita kuma sai tazo da wata jakar kuma ta manta bata ɗebo ba. A ranar ni kuma I was so busy kamar me, shikenan ban samu time munje mu ɗauko ba. Da na kira Yaya kuma na gaya masa cewa yayi kar mu damu kawai."
Amma duk da yadda ta fara sakewa a cikin nasu, tana kewar gida kamar ba gobe, abubuwa da yawa akwai su anan na duk wata buƙatar rayuwa, ga komai sabo koina ƙal-ƙal, gashi babu wanda ya taɓa ko haɗe mata rai har yanzu, idan ta shiga cikin gidan kowa haba-haba yake da ita, hatta su Salma amaren da akayi bikinsu tare dukksnsu sun gaisa a wayar Samirah, da Salman ma ba sau biyu suna gaisawa.
Ga Hajiya Kilishi da take nan-nan da ita kullum fuskarta dauke da fara'a tana fadin ita ƴarta ce, Ranar da taje ta gaishe da Baffa ranar ta fahimci dalilin da yasa Baba ya bada aurenta a gabansa ba tare da wani tunani ba, dattijo ne kamili mai nutsuwar da a fuska kadai kowa zaiyi masa shaidar hali na gari, don haka babu wata matsala da ta guskanta a gurinsa shima.
Sannan shi kansa uban gaiyar har yau ko haɗe rai bai taba yi mata ba, amma duk da haka, tafi son rayuwar cikin ƴanuwanta akan wannan, tunda har yanzu zuciyarta bata gama kwantawa da komai ba, tunaninta iri ɗaya ne da Amma dama kuma Fatima, dukkaninsu sun yarda cewa akwai wani abu dake tahowa wanda bai karaso ba, don ba'a ɗora turbar auren da cewar komai ya tafi daidai ba, sun sani cewa ba sun kawo ta cikinsu ne don su nuna mata kirkinsu ba dashi da ƴan gidan nasu, dole akwai wani abu da yake a ɓoye wanda har yanzu basu kai ga saninsa ba.
Su Aminu da Baba ne kawai hankalinsu a kwance don duk sanda suka yi waya da Baban, zai yi ta zubo mata tarin addu'o'in da suke karya zuciyarta, shi har yanzu zuciyarsa guda ɗaya ce game da auren, ya riga ya aminta da Baffa da ma Hajiya Kilishi ta yadda baya taɓa iya hango komai.
Ta lumshe idanunta a hankali tana jin yadda bacci ke shirin ɗaukarta a lokacin, ta shiga ƙokarin kore shi don aƙalla tana son jin lokacin da Ma'aruf zai dawo amma baccin mai nauyi ya ƙara karfinsa, don haka wata zuciyar ta gaya mata cewa zata iya ɗan runtsawa tunda tayi sallar isha kuma bata wani samu baccin safe ba sosai, da wannan lasisin da zuciyarta ta bata taji maganganun cikin rediyon nan suka zuƙe daga kanta a hankali, taji su suna yin nisa da kunnenta kafin a lokaci guda taga Aminu a tsaye daga bayan idonta.
"Me yasa kika kasa Amina?"
Kai tsaye ya tambaye ta yayin da idanunsa ke kallonta, kuma kalaman suka isa kanta amma suka kasa bada ma'ana saboda dukkan tunaninta ya tsaya cak tana kallonsa da dimbin mamaki, Yaushe yazo? Yaushe yazo ko kuma ita yaushe ta bar cikin gidan, don daga nesa tana hango duhuwar wasu dogwayen bishiyu, hakan yasa gabanta fadi da dukkan tsoron da zuciyarta zata iya dauka.
Tayi ƙokarin ta kalli kanta amma sai ta fahimci bata iya ganin jikinta kwata-kwata, kamar idanunta ne kawai a wajen suke ganin komai amma babu gangar jikinta, ta ɗago ta sake kallon Aminun da har yanzu ke tsaye a gabanta.
A lokacin ta kula cewa idanunsa sun canja, kalolinsu ba iri ɗaya ne daga yadda ta sansu ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata taɓa gani a fuskar Aminun ba, Aminun mai raha da fara'a, Aminun data sani mai ɓoye damuwarsa a kodayaushe.
"Me yasa kika kasa Amina?"
Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama.
Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta ɗago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa.
Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata taɓa hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba.
Kuma kwatsam sai ta nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su ɗin balle kuma alamun wutar, kuma babu wani ɓata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai haɗe da salati, sai ta jiyo ta Hafsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba.
Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran sunayen su Maryam ɗin har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota'ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye tana kallonta, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya.
"Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina?"
Tayi tambayar a lokaci guda da itama ta neme ta ta rasa, wajen ya koma babu komai sai tashin ihun ƴanuwanta da kuma hargowarsu yayin da warin ƙonewar nan ya cigaba da cika wajen. Ta kasa gane komai ko kuma abinda yake shirin faruwa, abinda kawai zata ita tunawa kafin ta farka shine daga cikin muryoyin dake ihu, ta jiyo wata murya da ta kasa gane wacece ko kuma inda ta santa, muryar tana ƙyalƙyala wata irin dariyar da bata taɓa jin irinta ba!
Dariyar ta shiga amsa kuwwa a kowanne ɓangsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi.... A lokacin ne kuma ta farka a firgice, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a cikin ɗakinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya ɗauke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ƙarar shuuuu kawai take fitarwa.
Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe rediyon tana neman lokaci, karfe ɗaya da rabi na dare, wani salatin ya sake suɓucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka, sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya zame akan filon data kwanta tayi saurin ɗaure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ƙara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta taɓa irin wannan mafarkin a rayuwarta.
Taji maƙogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan
ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa.
Makogwaronta ya ƙara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ƙasa ba ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga ɗakin.
Kitchen zata je ta ɗauko ruwa, wataƙila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ƙishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka'a biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai.
Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen ɗin, ta buɗe ƙofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable ɗin tsakiya na kitchen din, fitilar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask ɗin abincin data dafa ne.
Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da faɗin kafaɗunsa ta kowanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ƙofar.
"Me ya faru? Me ya same ki?"
Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren tana gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta ɗaga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake haɗiye abinda ke bakinta kafin tace.
"Ba komai, ruwa zan ɗauka."
Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma'aruf ya bita da kallo zuwa wajen fridge ɗin, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen ɓoye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida.
Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba idan har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci.
Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case ɗin dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda aƙalla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai.
Don haka dole a yanzu da ya ɗebo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya ɗauko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nutsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse.
Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye.
"Wani abu ne ya same ki?"
Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin buɗe fridge ɗin, kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne... wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san me yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda ɗankwalin kanta yayi kala ɗaya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya.
"Mafarki kika yi?"
Amina bata san lokacin da ta ɗaga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan baƙar singlet din nan, three-quarter din wando ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da taji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi.
Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya riƙo nata ɗaya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna.
"Kinyi addu'a?"
Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ƙokarin yin ƙaryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tunani mai kyau ba slhali har yanzu yana riƙe da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ƙasan rigar nan, bama za'a lissafa da kayan jikinsa ba...
"Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku..."
Muryarsa mai zurfi ta sake faɗa yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa.
"Ayatul Kursiyu..."
Ta kai ƙarshe lokacin da taji kamar almara, ƴar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi riƙe da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun zama wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta.
"Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah."
Sai kawai ta gyada kanta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi.
Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani lokacin mafarki na juyewa tamkar mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa!
***
Ƙarfe bakwai na safe.
Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma'ruf ta baya, shine ƙaunarsa da football (ƙwallon kafa) shi kaɗai ne abu guda ɗaya bayan sunansa da kuma kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma'aruf ɗin da yake a baya ba, Ma'aruf ɗin da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace.
Son football ɗin ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi yasa yawanci duk weekend da safe yana stadium ɗin Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana ɗaya daga cikin members ɗin dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke badawa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma'aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen.
Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yayi da motarsa taƙi tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball ɗin sa daga booth ɗin motar ya shiga training ɗin da ya saba a compound ɗin gidan.
Kusan ƙarfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ƙara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya ɗauka, Martha ce.
"Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a Kano, don haka meeting din zai zama karfe huɗu na yamma."
Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta ne don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije leɓɓensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members ɗin nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya ya manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office.
"Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka buƙace su kafin a shiga meeting ɗin."
Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin kansa.
"Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za'ayi ba gashi motata taƙi tashi, amma bari na kira Ishaq sai a ɗauko min tasa."
"Okay sir." Ta amsa muryarta a ƙasa.
Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq ɗin da har yanzu bai dawo ba, bugu ɗaya biyu kuwa ya ɗaga.
"A ina ka ajiye muƙullin motarka?"
"Me za'ayi?" Ishaq ɗin ya amsa daga cikin wayar.
"Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima."
"Ka kira Jamilun?" (Makanikensu.)
"Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunna saboda gabaɗaya na manta da meeting ɗin ne."
Dariya Ishaq ɗin yayi daga ciki yace.
"Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don't know ma ya take take yanzu."
Ya girgiza kansa kafin yace.
"Baka da amfani."
Da haka ya kashe wayarsa, ya kira Malam Sani.
"Yallaɓai Barka da safiya."
"Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?"
"Ai kuwa Babu ranka ya daɗe, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro za'a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a ƴankaba."
Sai kawai ya gyaɗa kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun.
Da haka ya mayar da ball ɗin cikin booth ɗin motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ƙamshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanyar dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma waɗannan siraran ƙafafun nata.
***
Ƙarar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san ba Ma'aruf bane, don a yanzu ƙwaƙwalwarta ta haddace yanayin nasa bugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba.
Ta kashe gas ɗin da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda ya faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma ɗaki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya ɗauke ta, baccin da baiyi nisa ba ƙarar wani abu ta tashe ta.
Kuma ba'a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar ɗinta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma'aruf ta cikin sliding windows ɗin dake wajen sink yana ball, ta fahimci ƙarar data tashe ta kenan. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ƙirar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin ball yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci.
Ta daɗe tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata taɓa tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ƙara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma har yanzu ba'a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya ya zama gaskiya ba.
Komai zuwa yake saɓanin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma akan idan shi ya rubuto mata wannan saƙon, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi.
Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta faɗa ganin kwanukan abincinta a gefensa... Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya riƙe hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ƙonewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gabaɗaya.
Da wannan tunanin ta kammala haɗa abincin breakfast ɗin lokacin da ta tsinci bugun ƙofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma

Please Login or Register in order to submit comment