Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, taga ya sauke ya koma sake ɗauko wani... Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al'amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya ɗauke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu.
Hawayen ya cigaba da bin fuskarta yayin da zuciyarta ke rawa a kirjinta, tunanin ta ɗaya ne a lokacin, idan har mahaifinta zai iya sadaukar da girmansa yayi wannan aikin don kawai ya fita kunyarsu meye su baza suyi don fita tasa kunyar a duniya da kuma lahira ba?
Ta share hawayenta lokacin da wani mai wulbaro ke miko mata ledar garin da Allah yaso bata fashe ba. Kuma bata fadawa Maryam abinda ta gani ba, bata fadawa Amma ba, bata fadawa kowa ba, don ta san hakan wani abu ne da Baban ba zai taɓa so waninsu ya sani ba.
Kuma a wannan daren sai gashi ya dawo da ledar kaza har guda biyu ta miyar sallah, su Hafsa suka yi ta tsallen murna yana binsu da nasa murmushin shima.
Wajen karfe biyun dare bayan kowa ya kwanta, ta hango shi ta ƙofar ɗakinsu a wajen banɗaki yana miƙe bayansa, kukan da tayi a cikin filonta a wannan daren Allah kaɗai ya san yawansa, abu ɗaya kawai ta sani shine tayi wa kanta alƙawari a wannan ranar cewa ko abinda yafi rayuwarta ne zata sadaukar a duniya don farantawa mahaifinta.
*
"Wallahi gani nake yi kamar zaki ƙyalƙyale da dariya ki gaya min wasa kike yi."
Fatima ta faɗa tana kallon Amina data idar da sallah a gabanta.
"Ke ma kin san ai ban taɓa miki irin wannan wasan ba, da gaske nake Fatee, don yanzu haka ma Baba ya tafi gidan Kawu Mallam ya faɗa masa."
"Ya fada masa cewa kin yarda zaki auri wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa Amina...? inalillahi wa'inna ilaihir raji'un Amina kin san Allah ko da nake cewa ki rabu da Abdallah ki samu wanda yafi shi ba irin haka nake nufi ba, ya za'ayi kiyi irin auren da ake bada labarin ire-iren sa a sigogi mara sa daɗi?"
Fatiman ta ƙarashe muryarta na karyewa. Amina ta cire hijabin sallar tana kallonta,
"Ban gane me kike nufi ba?" Ta tambaya tana kallonta. Fatima ta girgiza kai kafin ta gyara zamanta.
"Amina duk wanda yaji batun auren wallahi shaidar da zaiyi miki daban, kowa cewa zaiyi auren kuɗi zaki yi, musamman ƴan unguwar nan da kin san daman ƙiris suke jira akanki."
Amina ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, abinda Fatiman ta faɗa gaskiya ne ta sani, kuma maganar iri ɗaya ce da maganganun Amma na jiya, duka su biyun ƴancinta suke nemar mata, amma a wajenta darajar mahaifinta itace a gaba da ita kanta don haka ta riga ta gama yankewa kanta hukunci, ta gayawa zuciyarta cewa zata tsaya tare da mahaifinta koda zata mutu sau biyu idan ana yi.
"Fatee na tabbata ba fa ba wai matsala ce sosai ba, kawai sun faɗa ne saboda kinga a aure ba'a ɓoye komai, kuma ma Baba yace baza'a bari maganar ta fita ba, kema kin san ba zan iya ɓoye miki bane."
Ta faɗi hakan yayin da idanunta ke hango takardar data cusa cikin kayanta a jiya, babu wanda ya san da ita, babu wanda ta gayawa hatta Amma kuwa duk yadda kowanne abu mai hankali a cikin kanta ya tsorata da maganar dake rubuce, amma ta sani cewar in har iyayenta suka ji hakan dole zai iya sake zama wani ƙalubale musamman ma a wajen Amma don haka ta yanke hukuncin ɓoyewa tunda ba zata taba fatan abinda zai hadassa mahaifinta yaji kunya ta dalilinta ba.
Kuma kafin Fatiman ta sake cewa wani abu suka tsinci sallamar Ummi daga tsakar gida, ƴar Kawu mallam wadda suke kusan sa'anni da Aminan.
"Ina amaryar take?" Muryarta ta fito da fara'a bayan ta gaisa da Amma da kuma Maryam wadanda suke kitchen, ta karaso ya ɗage labulen ɗakin tana kallon Amina bakinta a washe.
"Yarinyar nan da tsinannen wayo, sai dai muji kawai wai zaki yi aure?"
Sai dai Amina tayi wani guntun murmushi kafin tayi mata sannu da zuwa.
"Ni ba zan amsa ba wallahi, tunda sai da muka ga meeting ɗin su Kawu yayi tsawo sannan da kyar muka san me ake ciki, da ake ɓoye mana naga wanda zai raka ki siyayyar kayan bikin ai."
A cikin maganar ta Amina ta tsinci wani abu, cewa da gaske Baba yake a ɗazu daya shaida mata cewar kowa zai ji maganar auren ne ta fuskar alkhairi, babu wanda zai san me ake ciki, gashi kuwa ko iyalan Kawu Mallam ɗin da ake taruwa a gidansa basu san komai ba, zurfin maganar ya tsaya a iyakar Baba da yayyensa ne sai kuma Amma, Fatima, Maryam da Aminu da suka sani a yau. Ance zancen duniya baya ɓuya, amma har cikin ranta tana fatan zancen ya tsaya a iya wadannan mutanen kawai.
"Ai ni ban yi zaton har ɗan bokon naki ya gama makaranta ya shirya ba, shi yasa wallahi abun ya bamu mamaki sosai, har su Umma ma cewa suka yi koda wasa Amma bata yi musu zancen a kurkusa ba."
Amina ta girgiza kanta.
"Ai ba shi bane Ummi, wani ne daban."
Sai da Ummin tayi shewa kafin tace.
"Gaskiya ne yarinyar nan, kice da karfinki kika taso, Fatima bani labari don na san zanfi ji a wajenki, wane ne sabon kamun?"
Fatima tana take tace.
"Wallahi kin san al'amarin Allah ai, kawai komai a lokaci guda yazo."
"Eh, amma dai da maiƙon sa ko? Yadda komai ya taso a lokaci gudan ai na san a shirye yazo ko?"
Kawu malam mutum ne malami mai sauƙin sha'ani, amman sai Allah ya bashi matansu duka ukun masu azabar son kuɗi, kuma suka taso da ƴaƴansu ma gabaɗaya akan hakan, gashi mata sunfi yawa a ciki don haka a zaune yake cewa basa auren kowa sai mai abin hannunsa ire-iren ƴan kasuwa, gasu da surutu da kuma kauɗi, hakan yasa duk kusancinsu dasu Amina basu fiye shiga cikinsu sosai ba don halayensu sun banbanta duk kuwa da cewa suna da mutukar kirki.
"Ai kuwa dai yana da kuɗi gidansu ma haka."
Fatima ta bawa Ummin amsa har a lokacin tana murmushin yaƙe.
"Kice dole ne mu raƙashe a bikin nan, wallahi azo a saka mana rana ma nan kusa Momi tazo mu fara shirye-shirye, zaki yi anko?"
Amina taji wani abu ya tokare mata a maƙoshi, don ita har ta yanke hukunci bai taɓa zuwa kanta cewar ma biki za'ayi ba, gani take kamar jana'iza kawai za'ayi akaita, kuma sai Allah ya taimake ta kiran Amma yazo a daidai lokacin don bata san amsar da zata bawa Ummin ba.
Amma ta kalle ta bayan ta isa kitchen din, fuskarta fayau tace.
"Kizo ki zuba muku abinci gashi nan an sauke."
Ta haɗiye yawu a hankali tana ƙarasawa ciki, lokacin da flask ɗin ruwan zafin nan ya faɗi daga hannun Amma, sai ya zama kar ya fashe da dukkan irin hukuncin da take tunanin Amman zata dauka akan ƙin bin maganarta da tayi, don a lokacin bata ce komai ba, juyawa tayi kawai ta bar wajen yayin da Baba ke saka mata albarka, kuma bayan taje ta same ta a ɗaki, abu daya kawai tace.
"Rayuwarki ce dama Amina, na nuna miki kuskuren dake ciki ne kamar yadda yake alhaki na a matsayin uwa, kuma tunda har kinga zaki iya dauka, ga fili ga maidoki nan, zuciyata ba zata riƙe ki da komai ba, Allah ya baki sa'a."
Daga haka bata ƙara cewa komai ba, kuma bata yi fushin da Amina tayi zato ba, harkokinta ta cigaba da yi a gidan kamar dama maganar bata taso ba, kamar dai shekaranjiya da Baba bai ko ziyarci gidan Hajiya Kilishi ba, balle su san da komai.
Ta zuba abincin ta kai musu, suna ci Ummi na daɗa bada bayanin yadda abubuwa zasu kasance wanda daga ita har Fatiman yaƙe kawai suke suna amsa mata, wajen la'asar ta tafi, lokacin ma Fatima ta daɗe da tafiya asibiti inda tace yau za'a sallamo kakarta.
Wajen ƙarfe biyar, Aminu ya shigo gidan riƙe da wani flask lokacin da take wanke-wanke ita kaɗai a gidan, don Amma ma ta shirya ta tafi gidan wata ƴaruwarta a Goron dutse ta shaida mata al'amarin.
"Ina yarinyar nan take?"
Ta san Maryam yake nema don haka tace.
"Ta tafi makaranta tun ɗazu."
Sai ya ajiye flask ɗin a ƙofar kitchen sannan ya ƙaraso ya tsugunna a kusa da ita, muryarsa ɗauke da nutsuwar da zaka shafe rabin rayuwarka kafin kaji ta a wajen Aminu yace.
"Hukuncin da kika yanke yayi daidai Amina, ba don Amma ba daidai ta faɗa ba, sai don kare mutuncin Baba da kika yi, kuma na tabbata Allah zai duba hakan ya kyautata rayuwarki."
Kwalla ta taru a idonta lokaci guda, don haka ta gyada kai kawai ba tare da tace komai ba. Wucewar wasu ƴan sakanni shima yana tsugunee kamar yana sake biya abinda ya fada a zuciyarsa, sai kuma yayi gyaran murya sannan ya koma Aminun da yake.
"Kin gayawa Malam ne?"
Ta san Abdallah yake nufi don dama haka yake kiransa, saboda haka ya girgiza kanta tace.
"Na san dai zai zo anjima."
"Kice yau Malam zai danɗani baƙin cikin latecomer kenan."
Bata san lokacin da ta watso masa ruwan wanke-wanken ba tana jin wani abu a zuciyarta na fadawa, ya kauce shima yana dariya sannan yayi hanyar fita yana faɗin.
"Idan wannan ƙwalamammiyar ta dawo kice mata ga wainar masar da take ƙalata nan na samo mata."
Bayan ta gama wake-wanken ta koma ɗakinsu har a lokacin ƴan islamiyar basu dawo ba balle kuma Amma, a ƙasan kayanta ta sake ɗauko wannan takardar tana karantawa, idanta suka tsaya akan sunan yayin da a yanzu bayan tsoron ma'anar rubutu wani sabon tsoro daban ke shigarta.
Ma'aruf B.
Ta karanta sunan tana jin yadda tsoron harafan kadai ke zanuwa a zuciyarta, ba wai don ta sanshi ta gane waye ba sai don zuciyarta bata cika manta fuskokin mutane ba koda kuwa sau ɗaya ta taba arba dasu, kamar dai shi rana guda ta taɓa ganinsa a rayuwarta kuma bata ƙara ba daga sannan.
Ranar ɗaurin aurensa, ranar da Baba yasa suka tafi tunda sassafe ita da Amma don wai suyi yinin bikin da gaske kamar yadda aka rubuta, a lokacin da ya shigo gidan shi da abokansa da ƴanuwansa bayan ɗaurin auren, ita da Amman suna rakuɓe daga can jikin wata kujerar a falon Hajiya Kilishin, kuma duk da tarin ƴan bikin mata da suka yanyame shi da tsokanar 'ango kasha ƙamshi...' sai da idanunta suka iya hango mata shi yasha farar shaddar dake ƙyalli kamar murmushinsa, yana tsaye daga tsakiyar mutane yayin da masu hoto ke ta yi musu kala-kala.
A wannan lokacin gani take kamar bambancin su ita da Amma da mutanen gidan ya zarta na mutum-mutum, don bayan Hajiya Kilishin da ta amsa gaisuwar su cike da fara'a ta kuma sa aka kawo musu abinci babu wanda ya ƙara lura dasu a gidan, sai wata mace guda ɗaya da tace Amma ta ara mata hijabinta lokacin sallar azahar, itama da alama irinsu ce don ta ɗebo tarin ƴaƴan da ta cika musu faranti taf da abinci suna ta ci. Daga baya ma dole suka bar cikin falon suka zagaya baya can wajen ɗakunan masu aiki, inda anan ne suka ɗan sake har Amma ma taga wata ƴar ajinsu ta sakandire a ƴaƴan dattijan da sune manya-manyan masu aikin gidan.
Don haka kwatanta tsoron cewar a wannan karon ita zata maye gurbin wannan kyakkyawar amaryar da aka shigo da ita gidan wajen yamma abu ne da ta tabbata babu wanda zai iya kwatanta shi a duniyar nan.
Tsaya ma tukunna... Ina matar tasa take??
*****
"Baffa ya gaya maka komai ko?"
Hajiya Kilishi ta tambaya tana kallon Ma'aruf ɗin dake zaune a gabanta, a cikin falon ɓangarenta suke su biyu sai Surayya dake can wajen dining tana danne-danne a wayarta, yana zaune a kujerar dake kallon Tv yana kokarin canja channel daga ta india zuwa wata channel da ya san a lokacin ana wani Tv show na likitoci mai suna 'Code Black'.
Sai da ya kai tashar ya karo volume sannan hankalinsa a kwance ba kamar yadda ta zata ba ya juyo ya kalle ta.
"Ya gaya min, and I was surprised har dake Mami."
Tayi murmushi tana kallonsa daɗi na cika kowanne lungu da saƙo na zuciyarta na ganinsa a gabanta, zata rantse da alƙur'ani ko ya'yan da suka fito daga cikinta basa ƙarasawa inda Ma'aruf ke kaiwa a zuciyarta, matsalar ɗaya ce kawai... duk wani ado da zai ƙawata kusancinsu dole ana kaiwa gabar da za'a yaye cewar shi ba mallakinta bane, kuma tana jin cewa da zata iya samun mai gyara mata hakan babu makawa zata bada komai na duniyarta don kawai a wayi gari duniya ta shaida cewa shi nata ne.
"Baffa ya riga ya gama yanke hukuncinsa shi da Alhaji Baba, daga ƙarshe kawai suka tuntubeni Mai gaskiya kuma ka san ba zan iya cewa Baffa A'a ba, shi yasa sai na bada tawa gudunmawar ta hanyar zaɓo maka yarinyar da na san zata dace da yanayinka. Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata."
Wani murmushi yayi kaɗan sannan yace.
"Na dade ina gaya miki kulawarki kaɗai ta ishe ni in rayu Mami, tunda har Rukayya ta kasa bana tunanin akwai wadda zata iya jurewa mess ɗina a duniyar nan kuma."
Maganganun suka taɓo wani abu a can ƙasan zuciyar Hajiya Kilishi, wani abu da sai da ta ji shi har a ƙarƙashin tafin ƙafarta musamman yadda muryarsa ta fito da wannan amon mai zurfi da kuma sanyi. Kuma sai da ta maida wata ƙaramar ƙwalla a idanunta sannan tace.
"Yanzu dai ka san baza'a fasa ba ko? Don haka zamu fara shirye-shirye, za'a kai musu lefe dole sannan idan kana so ma zaka iya zuwa ka ganta."
Maimakon ya bata amsa, sai kawai ya juyo ya kalle ta, lumsassun idanunsa suka tsaya a nata.
"Wai zaman me Ishaq yake yi ne ma? Me yasa Baffa baice a haɗa dashi ba?"
"Sai gida ya koshi ake kallon na waje Ma'aruf, kaine damuwar mu a yanzu ba shi ba."
Kamar bai ji dadin maganar ba, don juyawa yayi yana cigaba da kallonsa ba tare da yace komai ba. Hakan yasa tayi saurin gyara zancen ta.
"Kar ka damu amma, da an gama zancen nan ni da kaina zan saka shi a gaba sai ya motsa."
Murmushin da ya sake yi ya sata jin wani ɗaci a zuciyarta, ba sau daya ba sau biyu ba tasha tunanin kawar da Ishaq daga hanyarta kamar yadda ta kawar da abubuwa da yawa a rayuwar Ma'aruf, don duk wani abu da zai jawo ya raba zuciyarsa da kowa bayan ita, bata ƙaunarsa sam! Amma matsalar shine Ishaq ba ƙaramin amfani yake mata ba, amfanin da shi ta lissafa har ta bada shawarar dawo dashi wajensu bayan ya rasa iyayensa ba don kyautatawar da duniya ke kallonta dashi ba.
"Akwati nawa kake so a haɗawa yarinyar?"
Kamar bai damu ba, hankalinsa kwance yace.
"Duk yadda kika yi Mami daidai ne, ni yanzu abinda ke gabana daban harkar Office ce da zanje in gyara, Baffa yace anyi asara da yawa a wannan watan."
Ba shiri maganar ta doka wata tsawa a cikin kan Hajiya Kilishi tana janyo ta daga ramin da zuciyarta ke shirin kai ta, taji kamar ta miƙe tsaye tana karkaɗe raunin daya baibayeta tun bayan data ɗora idanunta akan Ma'aruf ɗin.
"Shikenan, Allah ya taimaka. Ka taho min da magungunan naka?"
Wata ƴar ƙaramar jakar daya shigo da ita a gefensa ya ɗauko ya miƙa mata ba tare da ya janye idonsa daga Tvn ba, kuma da Ma'aruf ya saurara da kyau, zai ji lokacin da ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta buɗe jakar tana nazarin kayan ciki.
A lokacin Samirah ta shigo ɗauke da lemo mai sanyi da kuma cake a faranti, yarinya ce ita mai tsananin kula da son kyautatawa kowa, shi yasa kusan komai na gidan yanzu sai da izininta ake yi, hatta abincin Baffa ta daɗe da karɓar ragamarsa sai dai ko in tana makaranta sai wani a cikin yayyenta yayi, don su Hajiya Kilishi basa girki a gidan. Kuma ko a ɓangaren Hajiya Maimuna akayi baƙi Sameerah ita zata fara tarbarsu da waje da kuma kayan cima kafin kowa, ƙarya ne wani ya shiga gidan nan yace ya fito da yunwa in har tana nan.
"Dan Allah Yaya ka bani kwangilar sati ɗaya in cicciko maka da waɗannan kasusuwan, wallahi baka ga yadda ka rame ba."
Ta faɗa tana ajiye masa farantin a gabansa. Ma'aruf ya ɗago ya kalle ta yana murmushi lokacin da Hajiya Kilishi ta mike riƙe da jakar magungunan tayi hanyar ɗaki. Kusa dashi ya nuna mata a kujerar yace.
"Zo ki zauna muyi ciniki Please, how much do you need? ( Nawa kike so) coz ƙarfi nake nema nima yanzu."
Ta kuwa ƙyalƙyale da dariya daidai lokacin da Shukra (ƙanwarsa dake bi masa a wajen Hajiya Maimuna) ta shigo daga hanyar wajensu, kuma ganin Ma'aruf ɗin yasa tayi murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau tana fadin 'Alhmdlilah" sannan ta juya da sauri don ɗebo takardun research ɗin da ta tara zai duba mata.
Don haka Ma'aruf bai samu shiga wajen Hajiya Maimuna ba sai da yamma tayi sosai. Kuma a falo ya same ta itama, tana zaune daga kan Wheelchair ɗinta tana karatun azkar ɗin yamma, yayin da Zahra da kuma Sahla ke zaune suna kallon video ɗin wani tutorial daga labtop ɗin Munaya da suka aro.
Ya durƙusa har kasa a gabanta ya gaishe ta cike da girmamawa, girmamawar da bayan ita baya taɓa kallonta da wani abu.
"Yaya jikin naka?" Muryarta mai taushi ta tambaye shi bayan sun gama gaisuwa.
"Lafiya ƙalau Hajiya, naji sauki ai."
"Allah ya ƙara sauki. Kaje wajen Inna ne?"
Ya girgiza kansa.
"Yanzu zan shiga idan na fita."
Tayi shiru yayin da idanunta ke nazarinsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa sanye da dogwayen kaya na farin yadin da ko a ido mai laushi ne don ya kwanta a jikinsa sosai ta yadda ya fito da ƙirar jikinsa mai tsari, wani abu dake ɗaya daga cikin abinda ke ƙara masa kwarjini a idon mutane.
A lokacin ne kuna maganar ƴar uwarta a kwanakin baya ta haska a cikin kanta.
'Ban ce ki tada hankalin gidan ki ba Maimuna, amma abin yayi yawa, kin rasa Jamal kuma Ma'aruf shine Babba a gidan yanzu, ko yaya ne ya kamata ya dinga tunawa cewa ke kika haife shi ba ita ba...'
Tayi saurin kawar da wannan tunanin tana haɗiye wani abu da batasan sunan sa ba, a lokainda ƙwaƙwalwar ta ke tuno mata damagaar da Baffa ya yanke taauresa jiya da daddare, sai dai har ta buɗe baki zata yi masa magana kawai taga ya miƙe tsaye yana yi mata sallama, sai ta mayar da maganarta a hankali sannan ta amsa, kuma murmushin da yayi wa su Zahra a matsayin amsa tasu sallamar ya sake ɗago wani abu a zuciyarta da ta daɗe tana danne shi tsawon shekaru. Idanunta suka bishi da kallon da har ya rufo mata ƙofar falon hankalinta bai koma kan karatun da take yi ba.
A falon Inna Danejo Ma'aruf ya tarad da ita tana sallah daga kan sallayar ta da anan take kwana ta yini in har ba tashi ne ya kamata ba, don haka ƙafafunsa suka tako cikin falon a hankali, yana jin kamar zai nutse a sabon carpet din da aka shimfide mata falon dashi, (wall to wall). Ya karaso ya sami waje daga gefenta ya jingina da wasu ƙullin kayanta da ya san na wanki ne sannan ya zaro wayoyinsa daga aljihu.
Tarin messages ɗin da har yanzu bai duba ba suka shiga tururuwa akan screen ɗinsa, sai ya zura hannunsa ɗaya cikin gashin kansa kawai sannan ya cillar da ita a gefe ya dauko ɗayar.
A ciki ya lalubo nambar Faruk, aboki ɗayan da yake dashi bayan Ishaq kuma mataimakinsa a wajen aiki.
"Ka gaya min ba maganar aiki bace dan Allah B, don wallahi as we are talking now ina Coldstone ni da yara, kowa yana son hutu a rayuwarsa Ma'aruf."
Faruk din ya faɗi hakan tun kafin yace komai, don shi kansa ya sani ba zai iya kirga adadin wayar da suka yi akan zancen Office ɗin ba tun bayan dawowarsa. Sai dai kalmar yaran da ya furta ta daki zuiyarsa da wani irin tasirin da baya taɓa sabawa dashi don haka ba shiri ya tafi kai tsaye ga abinda yake son tambayarsa.
"Account number Daniel zaka turo min."
"Me zaka yi da ita? Na gaya maka gayen yana can har yanzu da kumburarriyar fuska wallahi."
Ya cije leɓɓensa a hankali yana hango fuskar Daniel ɗin a idanunsa, sanda ya cakumo wuyansa yana kai masa naushin da baya ƙarewa, kuma duk da zafin dukan nan Daniel baya kare ba ko sau ɗaya, kallonsa kawai yake da idanunsa dake nuna tsantsar mamaki da kuma ruɗani har ya fita daga hayyacinsa.
Ya sake tuno yadda ya jawo shi ya fito dashi har waje ɗimbin jama'ar Office ɗin na kallonsa, da lokacin da ya saka shi a boot din motarsa ya rufe sannan yaja motar zuwa gida, yaje gidan kuma ya fito dashi dashi daga boot ɗin motar ya ja shi har falon Baffa a lokacin ma ya riga ya suma...
Sai kawai ya sake mai da kansa baya, yana motsa ytsunsa cikin gashin kansa a hankali, idonsa ya cigaba da hango masa yadda a lokacin duk da baya cikin hayyacinsa amma nauyin idanun Baffa suka sa ya durƙushe akan gwiwoyinsa sanda ya kai Daniel ɗin har gabansa, amma kuma duk da hakan bai fasa gayawa Baffan cewar wai ya kawo shi ne ne don ya kore shi daga aiki ba...
"Just send it Umar..." (Kawai ka turo min...)
Ya faɗa yana katse tunaninsa kuma bai ƙarasa abinda zai ce ba hayaniyar yaran nan ta shiga kunnensa daga cikin wayar, don haka ba shiri ya katse kiran yana ƙoƙarin ture abinda ke ƙoƙarin tasowa daga ƙasan zuciyarsa.
Ya cillar da ita gefen ɗayar itama sannan ya rufe idanunsa yana cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin nasa daidai lokacin da Inna Danejo ta idar daga sallarta.
"Wai rana kika koma bautawa ko me? Wannan wace irin sallah ce bayan la'asar?"
Inna Danejo ta kalle shi zuciyarta fara ƙal! da farin cikin ganinsa lafiya ƙalau, don a cikin addu'inta na tsukin kwanakin bata jin ko kanta ta ambata a cikin addointa banda fatan nema masa sauki, don haka da guntun murmushi a fuskarta ta kai laziminta na sallamar sallah sannan tace.
"Idan ranar na koma bautawa Muhammadu, iyayenku ai su zasu fara biyo ni kafin ku."
Murmushi yayi a hankali sannan ya buɗe idanunsa ya juyo ya kalle ta dasu a lumshe.
"Allah yasa da kika dama furar kin rage min, tun da na shigo nake jin ƙamshinta."
Maimakon ta bashi amsa sai tace.
"Yanzu Allah baza ka ji magana ta ka aske gashin nan ba ko? Ko iska ba ka so kaji tana ratsa ka Muhammadu?"
Ba shiri murmushinsa ya karu.
"Saboda me zan so iska ta ratsa ni? Wadda ke shiga hancina ma ta ishe ni Inna... Ki tashi ki ɗauko min furar dan Allah."
Ai kuwa kamar ya ziga ta ne akan irin mitar da tayi a duk lokutan da baya nan a gidan, ta faro ta tunda daga farko daki-daki har tana faɗin idan ma ba zaiyi askin ba wai ya tsaya ta wanke masa da sabulun salo ta tabbata ranar sai yayi bacci mai daɗi, murmushinsa kawai yake yi yana jinta tunda dama ya riga ya shiryawa hakan.
A haka har Ishaq ya shigo ya same su, shima aka zuba masa furar sannan ta tasa su a gaba su duka biyun kuma da zancen aure. A lokacin Ishaq ke gaya mata hukuncin da Baffa ya yanke game da Ma'aruf, don haka bayan ta gama hamdala da mitar cewa Baffan bai zo ya same ta ya gaya mata ba, sai faɗan kuma ya koma kan Ishaq shi kaɗai, tana yi tana zayyano masa jikokin ƴanuwanta na ƙauye, kowacce ta faɗo Ishaq sai ya gyada kai yace "Kuma da alamun tana da hankali."
Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa game da abubuwan dake gabansa, sai dai ko kaɗan babu batun auren nan a cikinsu, don tunaninsa ya gaya masa cewa ko iyayen yarinyar nan mahaukata

Please Login or Register in order to submit comment