Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amarin auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waɗanda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ƴarsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba.
Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faɗi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake ɗauke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar ba, bata ce komai ba.
Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya ɗorar da saɓanin cewa faɗa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninta da mijinta.
"Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buɗe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaɓar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..."
Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne.
Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan ɗumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji.
Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata ɗaurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran jama'ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika danƙam don har ƴan unguwa sun shishigo.
Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta ɗebo nata itama tana kwara mata tare da nata addu'oin dake ƙara karya zuciyarta suna saka kukanta ƙaruwa. A lokacin ne kuma fuskar Ma'aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa, ranar da ta taɓa ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ƙarfi ya sake suɓucewa a bakinta.
A haka sai da duk wani babba na danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin saƙin, aka lulluɓeta dashi har ƙasa sannan kuma sauran ƴanuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana guɗa. Al'ada ce sabuwa ga duk wanda ya halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ƴan unguwa don haka abin ya birge kuma ya ƙayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi.
"Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza su zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba'a gaiyace su ba kenan."
Fatima ta faɗa da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai.
"To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa karyane duk su ƙarata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne."
Ummi ta faɗa tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin ɗinkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu.
Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ƙawayen su Ummin da kuma ƙawayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta faɗa ne da yawansu da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ƙarya ne basu yarda ba.
Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take riƙe da ƙaramar ƴar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanci daga ƴanuwan Amma, ƴaƴan Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ƴaƴan su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ƙaraso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa'anninsu bane, su hudu ne duk sunyi aure a can Abujan ɗaya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe ɗaurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ƴa sa'ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu.
Amina ta sani cewar ƴanuwan mahaifinta suna da arziƙin da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi ɗin ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dogaro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya miƙo masa ba.
Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ƙara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma'aruf suka shiga dawowa kunnenta.
"Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi ɗawainiyar konai damu har tsawon shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji ɗaya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ƙafafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ƴan fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ƙauye.
Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki.
Sanda Maryam bata da lafiya kuma karayar arziƙi ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai roƙo yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake buƙata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al'umma zasu amfana suyi alfahari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa'idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da yasa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba.
Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a idon duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan."
Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ƙara ƙalubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al'amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai ɗinki.
"Gobe zanje in karbo ɗinkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sarƙar nan mu ƙara yi musu tuni."
Fatiman ta faɗa tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace.
"Ɗazu Maryam take gaya min, wai ta samo me zuwa ta mana ƙunshi ma."
"Ƙunshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, kuɗi zaki karɓo zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za'a sake yiwa bayanin cewa ke amarya ce."
Ummi ta faɗa, kuma tana ƙarashewa wata ƙawarsu ma ta ɗauka da faɗin.
"Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa."
"To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fara naki."
Momi ta faɗa suna ƙyalƙyalewa da dariya, Amina kuwa ta haɗiye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline ɗin da take shafawa kullum shine dai, robar ko ƙarewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, abinda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne.
Don Allah ya sani idanunsa kaɗai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ƙwarin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi da kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba... Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara ɗaukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere.
Tsoro take ji da gaske,
Tana ji kamar tana faɗowa ne daga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta.
Abinda bata sani ba shine har yanzu a gaɓa take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar!
***
Wasa farin girki!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
Bari nayi sauri na wuce, a yafe min.🙏🙏🙏

BABI NA TAKWAS.
~~~~~
Ɗimbin jama'ar dake yin tururuwa suna ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas ɗin da aka ɗaura kowanne kan sadaki mabanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa suna daɗa adadinsu. Jama'a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne ango da ƙungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana ɗaukar hoto.
Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ƙaraso inda tasu tawagar ƴanuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa.
"Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba."
"Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ƙarfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan."
Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ƴanuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kawai ya juyo da kansa yace.
"Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba."
"Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu kuma na tabbata shi ɗin yana da hannun ɗaukarta."
Kawu Ibrahim ya girgiza kansa.
"Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi."
"Hankalin da bai kamata ace an ƙuntata rayuwarta tun daga yanzu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai taɓa faruwa ba."
Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ƙoƙarin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yana daga tsakiyar mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa ɗauke da ɗimbin fara'ar da ya kasa auna nauyinta dana kuɗin sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu ɗari cif!
A cikin ƙwaƙwalwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau goma baya jin zai taɓa iya bada ƴarsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ƙwaƙwalwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ƙin halartar wajen ɗaurin aurensa?
***
Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin da ya buɗe gate ɗin juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ƙofar mazaunin direba ta buɗe.
Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ƙofar sannan ya tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ƙasa. Security ɗin daya bude masa ƙofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin.
"Yallaɓai sannu da zuwa."
Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tambaye shi.
"Ma'aruf yana ciki ko?"
"Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai"
Jin haka yasa Ishaq ɗin yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi'at ta shiga gaishe shi tana murmushin da ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya ɗaga mata hannu yana zarcewa zuwa saman.
A hawa na farko can ƙarashe ofishin Ma'aruf ɗin yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa cewa ya canja office, ya isa ƙofar daidai lokacin da sakatariyar Ma'aruf ɗin mai suna Martha ke fitowa riƙe da wasu files a hannunsa.
"Sannu da zuwa yallabai, yana tare da wasu baki ne a ciki, ko zaka jira su kammala."
Martha ta fada da murmushin dake nuna masa da gaske take, kuma ya san lallai baƙin masu muhimmanci ne don babu ta yadda za'ayi ta tsaida shi idan ha haka ba.
Gyada kansa kawai yayi alamar ya fahimta sannan ya ƙarasa kofar ya buɗe ta, idonsa ya gane masa wasu inyamurai biyu da kuma wani ɗan china, dukkansu suna zaune a kujerun dake tsallaken teburin Ma'aruf ɗin, kuma budewar kofar tasa dukkaninsu suka juyo suka kalle shi, Ma'aruf na sanye da wani bakin yadi mai sealed ɗinkin da ya fito da tsarin jikinsa, hular kansa ma baka ce data dace da shigar da ita kadai ya kamata ta tabbatarwa da Ishaq cewar abinda yake tunani tabbas haka ne, dama baiyi niyyar zuwa wajen daurin auren ba.
"Bismillah, ka shigo mana."
Ma'aruf ɗin ya faɗa yana kallonsa, sannan a lokaci guda ya maida kansa kan takardar dake gabansa yana ƙarasa rubutun da yake yi, ya kuwa karaso cikin daidai lokacin da ya rufe takardun ya miƙowa mutanen tare da murumushin daya dace da fuskarsa.
Ɗaya daga cikin inyamuran ne ya karba tare da yin godiya kafin dukkanninsu suka mike a lokaci guda, Ma'aruf ɗin ma ya mike yana miƙa musu hannu, ɗaya bayan ɗaya suka gaisa kowanne da murmushi yayin da yake sake yi musu alkawarin cewar kar suji komai, suyi aikin da zasu yi kawai babu abinda zai gifta a tsarinsu.
Kuma watakila yanayin fuskar Ishaq ɗin suka kalla don babu wanda yayi masa magana a cikinsu suka yi hanyar kofar suka fita.
"Wanne za'a kawo? Tea ko Coffee"
Muryar Ma'aruf ɗin tasa hankalinsa dawowa daga rakiyar da yayiwa mutanen nan, ya juyo ya kalle shi.
"Kaima ka san ba abinda ya kawo ni ba kenan."
"Na sani..." Ma'aruf ya faɗa yana komawa kan kujerarsa.
"Shi yasa na tambaye ka hakan ai, don idan ka fara muryarka zata fi fitowa idan da abu mai zafi a kusa."
Sai kawai ya girgiza kansa, yace.
"Wane irin rashin mutunci ne wannan B? Ya za'ayi ranar da za'a ɗaura maka aure guda ka taho Office? Ka san tarin mutanen da suka neme ka a wajen nan?"
"Really? Ai da ka sani kawai su biyo bayanka ku same ni anan sai su ganni."
Wani irin abu ya sake tasowa Ishaq, sai kawai ya karaso gaban teburin nasa ya zube wayoyinsa sannan ya kalle shi sosai yace.
"Abinda kake yi ba daidai bane Ma'aruf, me yasa ko sau ɗaya a rayuwarka ba zaka yi abu irin na mutane ba? Ka nuna baka son auren nan da farko, daga baya kazo ka nuna ka yarda saboda Baffa, to idan haka ne me yasa zaka kunyata shi a yau? Me yasa baka je wajen ba alhali ka san rashin zuwan naka zai iya haifar da wani abu?"
"Me zai haifar?" Ya tambaya alamun hankalinsa a kwance, kafin ya cigaba.
"Zai haifar da rashin faruwar auren ne? Kana tunanin akwai abinda zai saka Baffa ya canja maganarsa? Na gaya maka na yarda da auren ne saboda naga ba zan iya karewa ba, naga babu abinda zanyi wanda zai canja ra'ayinsa, yanzu ka gaya min da ban je ba ya fasa ɗaurawa?"
Ishaq yayi shiru kawai yana kallonsa, sautin numfashinsa na fita da yawan da ya zarce daidai, don akan fuskar Ma'aruf din yake gane cewa abinda ya fada ba haka bane, dole akwai wani dalili daban da yake dashi game da auren nan, saboda abinda ya faɗa da farko gaskiya ne.
Su biyun sun sani cewar wannan auren ba ƙaramin haɗari bane, abu ne da bai kamata ya faru ba, don haka ba saboda Baffa ya ture hakan ba ya sani, shi yasa babban tsoronsa shine abinda zai iya yi, don shi shaida ne akan tarin abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da basa furtawa har yanzu balle na ukunsu ya sani, abubuwan da ba wai sunyi shawarar ɓoyewa bane kawai akwai su ne amma kamar babu su ɗin.
Ya haɗiye wani abu a ƙirjinsa yana jin yadda shakka da kuma tsoron abinda Ma'aruf din zai iya ke bin koina a jikinsa, bai san yarinyar nan ba, bai taɓa ganinta ba amma yana tausayinta tun yanzu, don ya san wani rauninta a rayuwa aka kalla aka haɗa wannan auren, tunda a bayyane yake ga kowa cewar ba kowanne uba ne zai iya ɗaukan ƴarsa ya bawa mutum irin Ma'aruf ba, kamar babu banbanci ne da ka tura ƴar taka cikin dokar dajin da babu ranar fitowa.
Sai kawai ya zaro wallet ɗinsa daga aljihu, kuma har a lokacin Ma'aruf ɗin na kallonsa da nasa idanun dake danne tarin abubuwan da yake dannewa, a cikin wallet din Ishaq ya zaro ID Card ɗinsa ya nuno masa shi, kuma da ganin haka Ma'aruf ya san me yake nufi, ya san cewa da gaske ransa ya ɓaci, don rana ta ƙarshe da ya fito da ID card ɗinsa yana tuna masa cewa shi lawyer ne zai iya ɗora aikinsa sama da alaƙarsu shine ranar da aka kai Baffa asibiti saboda ciwon zuciyarsa da ya tashi ta dalilinsa.
"Ban san me kake shiryawa ba Ma'aruf, amma na yarda cewa ba ka yarda da auren nan saboda Baffa ba, akwai wani abu da kake ɓoye min..."
"Jamal ya san yarinyar."
A lokaci guda muryar Ma'aruf ɗin ta katse shi yana kallonsa.
"Me kace?" Ya tambaya idanunsa na shaida rashin ganewar.
Ma'aruf ya gyara zamansa, ya ƙifta idanunsa yana kallon Ishaq ɗin sannan ya sake maimaitawa.
"Jamal ya san yarinyar Ishaq, so nake na san yadda akayi Jamal ya san yarinyar, wataƙila hakan zai iya bani damar da zan iya gano mutanen da suka sa na kashe shi!"
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Faruk ya shigo Office ɗin yasha adon wasu fararen kaya har da babar rigar, bakinsa a buɗe yace.
"Wai da gaske baka je ɗaurin auren ba?"
****
Kayan jikin Amina wani farin Lace ne wanda aka ɗinka daga cikin kayan lefen, ta yafa farin mayafin da shima a cikin kayan yake, hannayenta sun sha ƙunshin da suka je har zoo road tare dasu Ummi suka yini ana yi, ɗaurin ɗankwalin da Momi tayi mata yayi baya da yawa ta yadda hakan ya fito da gashinta ta gaba, akwai fararen awarwaro a hannyenta har da wani zobe mai kyalli ma.
Babu ko kwalli a idanunta amma ita kanta ta sani cewa kamanninta ba ɗaya suke da sauran ranaku ba, watakila suna da kuma matsayin aure yana zuwa ne da tasirin dake banbanta kowacce amarya da sauran fuskoki, don ita kanta ta sani cewar fuskarta tayi wani irin fresh da kuma kyan da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har maiƙo take saboda yadda take tas babu ko ɗigon ƙananun ƙurajen da ta saba fama dasu.
"Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!"
Wata Shukra ɗaya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar tsakar gida kira, a cikin ɗakin nasu ƴanmata me fal da suka haɗa da kusan duka ƙawayen su na islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ƙoƙarin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ƙawayen, don haka ɗakin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba ɗaya.
Don ko'ina a cike yake taf da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za'ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan waɗannan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba'a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su ɗin da kusan duk wanda suka mu'amalanta yana jin daɗin zama dasu.
A lokacin Maryam ta shigo ɗakin riƙe da wani faranti da aka cika da ƙullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace.
"Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira a kawo."
"Taɓ! Wallahi na wannan ƙawaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa."
"Au ba zaki bamu ba?"
"Waashi can fa ana ta ɗiba a ɗakin Amma, kuje ku ɗebo naku kafin ya ƙare don wallahi har yaje rabi."
Ummi ta miƙe da sauri tace.
"Mu nawa ne a dakin?"
"Ai kawai je ki ɗebo ashirin, in ma da saura ma kara." Cewar wata a cikin ƙawayen Aminan suna ƙyalƙyalewa da dariya gabaɗayansu.
Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na banɗashen gurasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba.
"Wallahi kowa ya ɗauke hannunsa kafin in ajiye." Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa.
"Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?" Cewar Shukra.
"Wallahi sai kowa ya ɗauke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa."
Ta faɗa tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ƙaru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ƙyalƙyala dariya, kuma yanayin fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har haƙoranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu.
Kuma dariyar taji tana tafiya har ciki ƙirjinta, tana taɓo wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta.
A cikin hayaniyar da ɗakin ya ƙara ruɗewa dashi Aunty Ma'u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, aka shiga ɗaukar hoton kowa da ƙungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an ɗauka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt ɗin kayan daya buɗe ta ƙasa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya ɗinki ba'a banza suke ta yabonsa

Please Login or Register in order to submit comment