Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa da yashin."
Ya zayyano dukkan wannan bayanin daga tsaye kasancewar shi yaje ya zaƙulo ta tsakiyar masu wasan yashin. Da jin haka kuwa Hafsa tayi narai-narai da muryarta ta shiga rantsuwa tana faɗin da gaske ture ta akayi ta faɗa kan yashin, wanda kowa ya san ƙarya ne wasanta tayi daga yadda baƙin gashin kan nata ya burɗine tsaf da ƙasa.
"Ko baki ɓata kanki ba meye amfanin zuwa wajen yashi da magriba Hafsa?"
Amina ta faɗa a hankali tana kama wata jelar, don ita ko kaɗan ba ta fadan nasu take yi ba, jikinta ne kawai zaune a gidan amma hankalinta ruhinta zarya kawai suke a hanyar gidan Kawu mallam kamar tururuwa, shi yasa ko girkin daren ma tace Maryam tayi.
Allah ya sani abu na ƙarshe da zata so a yanzu shine wata matsala ta sake gifta musu, rayuwarsu ta haska da kaloli mabanbanta a shekarun baya, sun fuskanci abubuwan da ko a labari basa son tunawa, kuma har yanzu ƙoƙarin tashi suke, ƙoƙari Baba yake don ganin rayuwarsu ta daidaita ko da ba kamar a baya ba, don haka ta yaya zasu taɓa son ace sai sun sako daga farko idan wani abu ya sake gifta musu ya a yanzu...
Har sai da ta gama wankewa Hafsa gashin nata da karkashi sannan Amma ta dawo, Baba kuma bai shigo ba sai bayan sallar isha, wanda kafin ayi hakan har Aminu ya riga su dawowa, a tsakar gidan ya tarar dasu tana sake yiwa Hafsa wata kalbar bayan ta wanke matta kan, yayi wanka yazo ya zauna a cikinsu shima yana ta mita da tsokana akan girkin da Maryam ɗin tayi, jollof din shinkafa da taliya ce da ko a ido tayi kyau, amma tunda ya zauna yake sukar abincin yana kuma kai loma.
"Wallahi akayi miki aure kika je kina irin wannan abincin sati daya zaki yi ya koro ki, ace jollof amma ba mai sa faman kora ruwa nake kamar dambu nake ci."
An kawo wuta a lokacin don haka tsakar gidan yayi tar da wasu sababbin ƙwan fitilar da ya haɗa da kansa ya saka musu. Maryam da a lokacin take wanke uniform dinta daga can bakin famfo tace.
"A haka babu man kake ƙoƙarin tayar da plate din ai."
"To idan ina jin yunwa ya zanyi? rufa miki asiri kawai nake ma wallahi, don yanzu ina tafiya wajen Isah (mai shayin layinsu) kowa sai ya gane cewar a gidanmu ba'a iya girki ba kenan, kinga masu kokarin zuwa nan gaba ma sai su fasa. Kuma Amina ita ta riga ta samu kece a ruwa."
Maryam ta juya bayanta amma yana ganin adadin yadda gefen fuskarta ke juyawa wajen murguɗa baki tana faɗar wasu abubuwa da ba jin su yake ba. Yayi murmushi yana sake faɗin.
"Hotonki zan nemo a wayata in maida shi fari da baki in rubuta ga matar da akan girkinta aka ƙirƙiri sunan abincin 'Ci kar ka mutu, 1987.'"
Bai saurari abinda take cewa ba ya juya ya kalli Amina da bata sanya baki a hirarsu har yanzu ba, ganin damuwar dake kan fuskarta har a lokacin ya dawo da hankalinsa kanta sosai.
"Wai har yanzu damuwa kike? Nace miki fa ki kwantar da hankalinki tun dazu. Ni alamar ma da na gani kamar wasu maƙudan kuɗi Baba ya samo shine aka tafi gidan Kawu mallam ɗin ake ta faman lissafi."
Ba shiri dole Amina tayi murmushi tana kallonsa.
"Aminu Allah ya shirye ka, komai sai ka maida shi wasa wallahi."
"To me yasa zaki yi ta damun kanki akan abinda bai ƙaraso ba tukunna."
Ya faɗi hakan sanda ya juyo, idonsa ya kai kan hannun Maryam dake ta cuɗa kayan wankinta.
"Ke, idan kinyi ƙunshin nan ma haka zaki cigaba da irin wannan wankin? Kwana biyu ya goge? Kuɗina zaki taso ki dauko min Allah indai haka ne."
"Kudin ka ai sun riga sun shigo kenan wallahi baza su dawo ba, sai dai idan nayi ƙunshin ka kankare shi."
Amina ta kalli yadda yake murmushi yana kallon Maryam din, ta san shima ya damu, watakila damuwar ma har tafi tata, amma haka Aminu yake a kodayaushe, shi mutum ne da zai sa kaji kamar baka da wata matsala koda kuwa kana nutsewa a cikinta ne tsamo-tsamo. Lokacin da Baba ya shiga tashin hankalin karayar arziƙinsa, Amma tace Aminu shi ya ɗauki kaso mai yawa bayan addu'a wajen dawo dashi daidai.
A daidai lokacin Amman tayi sallama ta shigo, kuma kallonta kawai Amina tayi taji gabanta ya faɗi duk duk da cewar yanayin damuwar fuskar tata ya ragu akan da safe.
"Haba Amma kun barmu sai kace marayu a gidan nan, ko shirin yaƙin duniya kuka tafi yi yaci ace kun gama."
Duk da yanayin Amman sai da tayi wani guntun murmushi tana girgiza kai sanda suka shiga yi mata sannu da zuwa, don ta saba a irin lokutan wasansa, Aminu ya riga ya mayar da ita kamar kakarsa.
A lokaci guda sai komai ya dawo daidai a gidan, da duk yawansu ji suke kamar a cikin wani fanko suke, Adam ya dawo daga siyan wainar fulawar da Maryam ta aika shi, Aminu ya kafa ya tsare cewar sai yaci rabi don wai ya san da kudinsa ta siyo, duk dauriyar Maryam sai da ta rufe idaninta ta fito da duk masifar dake cikinta wanda dama abinda yake jira kenan don haka shi da Adam suka dinga kyalkyala mata dariya.
Sannan a ƙarshe bayan sun shiga falo, wani film din indiyan da ake yi a tashar Bollywood ya ɗan daukewa Amina hankali daga wannan damuwar ganin cewar Amman ma har ta sake tana kokarin sakawa Hafsa maballi a wuyan rigar makarantar ta, tana yi tana mitar yadda Hafsan ke yawan yar da maɓallan rigar.
Falon ya ɗauka da sautin wakar film ɗin da ake yi lokacin da take ke kallon fuskar kowa tana murmushi, yadda Hafsa ta zuba manyan idanunta tana saurarar kashedin da Ammar keyi mata akan maballin, da yadda Aminu da Adam ke cigaba da dariya tsokanar Maryam da bata ganewa ta daina biye musu, har ma da idanun Maryam ɗin da suka cika da haushi fal! Haka take so... Haka take so rayuwa ta kasance musu a kodayaushe.
Sai dai rayuwar bata taɓa biyewa muradan zuciya, ita da zuciyar ma sunyi hannun riga, ƙaddara take kallo a kodayaushe tana bin takunta, don a lokacin da Baba ya dawo bayan sallar isha a lokacin komai ya ruguje, zuciyar Amina ta sake ruftawa cikin ramin da yafi wanda ta fito daga cikinsa zurfi. Su Hafsa suna makarantar dare a lokacin, Aminu kuma ya fita wajen abokansa sannan Maryam da wata ƙawarta sun tafi bakin titi wajen mai yin zayyanar allo kasancewar suna dab da yin sauka a islamiyya, gidan ya rage sai ita kaɗai, kamar dama ƙaddarar ta zaɓi wannan lokacin ne don ita kadai ɗin.
Amma ta kira ta zuwa ɗakin Baba lokacin da take kokarin haɗa kan kitchen ɗinsu, kiran daya tabbatar mata da cewar abinda take jira ne zai kasance kuma a hanyar zuwan tunanin ta ya ɗan ɗaure don a zaton ta ita da Aminu ya kamata su zayyane wa komai.
Ta shiga ciki lokacin da Baba ya rufe flask din nasa abincin da ya gama ci, ta zauna a daidai saitin Amma da har a lokacin ta kasa tantance yanayin fuskarta.
"Amina jiya da naje gidan Hajiya Kilishi aurenki na bayar ga ɗansu."
Maganar ta fito daga bakin Baban kai tsaye ba wane shamaki balle kewaye kewaye, kuma ta tafi kai tsayen har zuwa cikin ƙwaƙwalwar ta, sai dai bata nutse ba, zagaye kawai ta dinga yi a zaman kan nata kamar mai jiran a buɗe mata ƙofar shiga.
Shiru ya ratsa ɗaukacin dakin, shirun da a cikinsa Amina ta kasa ko zuƙar numfashi, kuma bata damu da tsayinsa ba don har a lokacin bata gane maganar da Baban ya faɗa ba, shiru kawai tayi kamar bata ji shi da farko ba a yanzu take jira yace wani abu, sai da shi da kansa yaga bata da alamar magana sannan ya sake kiran sunanta.
"Amina.."
Ta kuwa ɗago ta kalle shi, da idanunta dake haskawa a cikin hasken fitilar ɗakin, sai ya cigaba shima kamar bai fadi maganar farko ba.
"Jiya da naje gidan Hajiya Kilishi da mijinta nayi magana ba da ita ba, kiran nasa ne ba nata ba, don da na isa gidan mota kawai tasa aka ɗauke ni aka kaini har ofishin mijin nata.
Acan na tarar dashi tare da ƙaninsa, mutane ne manya-manya Amina masu mutunci da kuma kwarjini, kuma kai tsaye suka shaida min cewar aurenki suke nemawa ɗansu, yace min Hajiya Kilishin ita da kanta ta roƙe shi alfarmar hakan saboda yarda da hankali da kuma tarbiyar da muka baki. Al'amarin ya girgiza ni kamar yadda kika ji shi a yanzu kema, amma wallahi a wannan lokacin ba zan iya kallon idanun wadannan mutanen ince musu 'A'a' ba don bani da wata hujja ko dalilin da zai sa in faɗi hakan..."
Ba fahimtar abinda yake faɗa Amina take ba har a lokacin, kallonsa kawai take tana jin yadda muryarsa ke karyewa da kowacce kalma daya fada, mahaifinta mutum ne da ta sani jajirtacce, ko a lokacin da yake cikin tashin hankalin karayar arziƙinsa, baya taba fasa binsu da alkawuran cewa zai inganta rayuwarsu don kar su karaya da komai. Amma a yau kiri-ƙiri take jin duk wata amon karaya a muryar tasa, amon da take ji yana bin jijiyoyin ta yana tayar da tsigar jikinta bi da bi ta kowanne ɓangare.
"Na san karatu ne a ranki Amina, kuma na san ba sau daya ba sau biyu ba na sha yi miki alƙawarin cika miki wannan burin amma a kullum abinda muke tsarawa daban, wadda ƙaddara ta tanadar mana daban, kuma na san ba sai nayi miki bayanin wannan ba don a ƙananun shekarunki kin gan kalolin ƙaddarar mabanbanta, shi yasa nake son ki kalli wannan ɓangaren ƙaddarar ma, ki kalle ta idanun rahma Amina, Allah ya sani a zuciyata na yarda cewa ban miƙa ki inda zaki wahala ba, don komai halin da zan shiga a duniya ba zan yarda da duk abinda zai cutar daku ya matso kusa ba balle har in kai ku da hannu na.
Kin san Hajiya Kilishi kin san kirkinta, kin san yanayin gidanta, ina ga kinje kusan sau biyu ke da mahaifiyarki, saboda haka Amina wallahi zuciyata bata bani cewa zaki wahala a wannan wajen, damuwata kawai shine yunƙurin rushe miki burin ki da nayi da kuma cewar na yanke hukunci a lokaci guda."
Yayi shiru a lokacin, Amina ta haɗiye wani abu a makogwaron ta da bata san sunansa ba, maganganun Baba a gefe suke daga cikin kanta, har a yanzu damuwar dake cikin muryarsa itace a gabanta, ita take lissafawa tana son kirga adadinta. A hankali ta juyar da idanunta kan Amman dake zaune a saitinta, kuma a hankalin idanunta suka fahimci abinda ta kasa ganewa a fuskar tata ɗazu, damuwa ce fal ke yawo a cikin nata idanun!
Wani abu da ya ƙara rikita tunaninta a lokaci guda... Don bata taba tunanin cewa irin wannan maganar ce zata saka Amma cikin damuwa itama ba, idan har zata iya tunawa tun farko dama ita tafi son zancen aurenta akan karatun da take naci, kawai ganin cewar daga ita har Baban akan son karatun suka tsaya yasa ta sallama itama, amma duk da haka tasha gaya mata cewar ba ba lallai sai ta gama karatun zata yi aure ba, to me yasa wannan maganar zata dame ta?
Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta gyara zamanta a hankali, tana jin nauyin idanun iyayen nata biyu dake kallonta, so take tace musu in har wannan ne abinda ya tashi hankulansu a gidan tun jiya to su kwantar dashi, don a cikin aure da zancen rashin karatun tana jin ba wanda na zata iya daurewa ba don farin cikinsu.
"Baka ƙarasa zancen naka ba ai Mallam, baka gaya mata abinda yafi komai muhimmanci ba."
Kamar saukar ruwan sama a lokaci guda muryar Amman ta faɗa, kuma a lokaci gudan Amina taji gabanta ya faɗi, abu muhimmanci tace, kenan wani abu ne daban, wani abu da yafi girman abinda ya faɗa, wani abu da wataƙila shine dalilin damuwar dake kan fuskar Amman da ma zuwansu gidan Kawu mallam a yau.
Taji Baba ya sake gyara zamansa sannan ya kira sunanta.
"Amina..."
Ya kira kamar tayi nesa dashi, kuma ta san me hakan ke nufi saboda haka da sauri ta ɗago idanunta daga kan ƴan yatsunta ta kalle shi, ƙaguwar ya furta abinda zai faɗa na haskawa tar a cikin idanunta.
"Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin!
***
A wannan daren....
Wajen ƙarfe tara saura a lokacin da wata mota ƙirar kamfanin 'Elantra' ta shigo cikin layin, ƴan yara maza dake wasa akan hanya suka dinga darewa da gudu cikin wasansu suna bawa motar hanya kasancewar faɗin layin ba zai yiwu ta wuce kuma suna wajen ba. Ko'ina yayi tar da wutar nepar da aka kawo don gaka ƙyallin sabubtar motar haskawa kawai yake yi a idanun mutane kamar an shafe ta da maiƙo.
A cikin motar saurayin dake zaune a kujerar gefe mai suna Jamilu ya nuna ƙofar wani guda inda hasken jan kwai ke ci a samansa.
"Wancan ne gidan yallaɓai, in dai gidan Alhaji Sulaiman ɗin daka kwatanta min ne to shine gidan."
Ma'aruf dake rike da sitiyarin motar a gefen sa ya gyada kai a hankali yana kallon ƙofar gidan shima.
"Nagode sosai kaji."
Saurayin ya washe baki.
"Ah haba yallabai ai ba wani abu wallahi. A sauka lafiya."
Ya faɗi hakan da tsantsar murna yana ƙara rike sababbin kudin da Ma'aruf ɗin ya danka masa tun lokacin da ya shigo motar, a can farkon layin ya dauko shi, cikin dandazon wasu samari a inda ake sayar da rake. Kuma duk yadda ya kai ga kwatanta musu gidan Alhaji Sulaiman ɗin da yake nema, saurayin ne kaɗai ya gane don haka ya roƙe shi yazo ya ƙarasa dashi.
Saurayin ya rufe ƙofar motar daidai lokacin da kira ya sake shigowa a wayarsa, tun dauko shi dama ake kiran wayar kuma daga nambobi biyu kawai Ishaq da Mami, yana kallon yadda saurayin ma ke ta kallon wayar tun da ya shigo idanunsa na haskawa da mamakin cewa me yasa ba zai ɗauki kiran ba.
Ya ƙyale wayar yayi gaba a hankali zuwa daidai kofar gidan da yake kallo ya tsayar da motar daga gefe sannan ya janyo ta.
"Ma'aruf kana ina? Ina ka tafi?" Muryar ishaq ta fito a lokaci guda da ya amsa, sai ya koma da baya ya jingina kansa da kujerar motar sannan yayi murmushi.
"Kana magana kamar kana neman wani yaro ɗan karami, sau dubu nawa a rayuwata na ɗauki mota na fita da daddare Ishaq?"
Yaji yadda Ishaq din ya fitar da numfashi cike da takaici.
"Wai ka haukace ne gabadaya Ma'aruf? Yanzun nan fa muka dawo ƙasar nan, minti biyar kawai kayi a gida kayi wanka ka fito! Yanzu ƙarfe nawa? Tara fa ta wuce, ta yaya zaka ɗauki mota ka fita a halin da kake ciki?"
Ya sanya ɗaya hannunsa ya cusa yatsuntsa cikin gashinsa yana tuno abinda ya faru bayan barinsu Office ɗin Daddyn, tsaf ya zayyanewa Ishaq abinda Daddyn ya shaida masa tun a hanya kafin su ƙarasa gida, kuma zai iya rantsewa kamar yadda maganar ta tsorata shi haka ta daki Ishaq ɗin shima, amma duk da haka ya boye ta hanyar gaya masa cewa ya kwantar da hankalinsa kawai insha Allah zasu daidaita komai a hankali, wasu maganganu da jinsu kawai yayi a lokacin da yake furtawar.
Don suna shiga gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wasu riga da wando duka kalar baki sannan ya dauki wata rigar mai hula (hood) da dogon hannu ita kalar ruwan toka ya dora akai, ya rufe kansa da hular amma duk da haka ana ganin sumar kansa data taru itama baƙa wuluk da ita kamar kayan.
Lokacin da ya fito falo Ishaq ya shiga wanka shima, don haka wayarsa kawai ya dauka da muƙullin motar Ishaq ɗin yayi waje, don shi tasa motar tana can gida ba'a dawo da ita ba tun ranar da al'amarin ya faru (lokacin da ya ɗauko mutumin da yayi wa duka daga Office ya kaishi wajen Daddyn.)
Ya tabbata Ishaq yaji lokacin da maigadi ya buɗe masa gate ya fita, don bai ko bar kan layinsu ba kiransa na farko ya shigo, amma bai dauka ba, sai da ya katse sannan ya lalubo nambar Sameera a cikin wayarsa ya kira. Sameera itace kusan komai na gidan nasu don itake kula da kusan harkar komai a gidan, shi yasa duk wanda zaiyi wani abu sai ya neme ta, saboda haka ya sani duk wani information in dai ya taɓa ratsawa da gidan ba lallai ne taƙi samunsa ba.
Daddy ya gaya masa cewa mahaifin yarinyar da suke zancen zata shigo rayuwarsa ɗan'uwan Mami ne kuma sunansa Alhaji Sulaiman.
Don haka kai tsaye bayan Sameeran ta gama murnar dawowarsa da kuma shaida masa cewar ai direban Hajiya Madinan da yayi clear dashi kafin ya fito titi zai kawo musu abinci yanzu, sai ya tambaye ta.
"Waye Alhaji Sulaiman a ƴanuwan Mami?"
Shirunta ya nuna alamun tambayar ta bata mamaki amma duk da haka mamakin nata baiyi tsawo ba tace.
"Ko wanda yazo jiya? Ɗan'uwansu Hajiyar Mami ne, yana ɗan zuwa dai ba sosai ba."
Ya cije gefen lebbensa kafin ya sake tambayarta.
"Da yazo jiyan me yayi?"
"Bai wani daɗe ba Yaya, Mallam Sani ma aka saka ya tafi dashi office ɗin Daddy wai zasu yi magana."
Da jin haka ya tabbata shine wanda yake nema don haka kai tsaye ya sake tambayarta.
"Kin san gidansa?"
"A'a, amma Mami tace a Gadon ƙaya yake wai wajen layin transformer."
Ya gyada kansa.
"Kin san sunan ƴaƴan sa?"
"Eh, Babbar dai kawai na sani sunanta Amina."
Ya riga ya gama samun abinda yake so don haka ya gyada kansa kawai yana gode mata sannan ya kashe wayar, kwatancen daya kawo shi har kofar gidan kenan a yanzu.
"Ina Gadon ƙaya."
Ya bawa Ishaq amsa ta cikin wayar.
"Gadon ƙaya? Wajen wa? Me zaka yi?"
"Ni da kai mun sani cewa abinda Daddy ke shirin ba ƙaramin hadari bane Ishaq, don haka zuwa nayi na warware komai tun kafin lokaci yaja da abinda ba zai taba faruwa ba."
"What?" Ƙarara mamaki da kuma fargaba suka fito daga muryar Ishaq ɗin, kuma Ma'aruf zai rantse ya shiga girgiza kansa lokacin da yake faɗin.
"Kar kayi haka Ma'aruf dan Allah, ka juyo ka dawo. Zuwa wajen mutumin nan ba shine zai kwance komai ba..."
"Ba wajensa nazo ba don dashi da Daddy duk abu ɗaya ne. Ita nazo gani Ishaq, saboda a yanzu maganar ta koma ni da ita kawai."
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un... Ma'aruf me zaka yi?"
Salatin ya saka shi sake yin murmushi yana cije lebbensa.
"Nuna mata zanyi irin ramin da ake shirin jefa ta, nuna mata zanyi da gaske bani da hankali."
"B, tsaya kaji..."
Dib. Ya katse kiran ya ma kashe wayar gabaɗaya. Idonsa ya sake kallon ƙofar gidan yayin da zuciyarsa ke zana masa dukkan hotunan abinda zai faru kafin ya kashe motar ya fito.
Ya sake janyo hular rigar yana ƙara rufe fuskarsa daidai lokacin da wasu yara biyu mace da namiji suka zo shiga gidan idanunsu akan shi da kuma motarsa. Da sauri ya yafito namijin alamun yazo.
Ya kuwa taho yayin da macen ta tsaya tana kallon su hannunta rike da wani abu da take ta lasa.
"Bigboy ya sunanka?" Amon muryarsa mai zurfi da taushi ya tambaya sanda yaron ya ƙaraso.
"Adam."
Ya gyada kansa yana murmushi lokacin da ya zaro wata sabuwar ɗari biyar daga aljihunsa yana miƙo nasa.
"Idan ka shiga gidan nan Adam kace wai Amina tazo."
"Toh."
Ya amsa da nasa murmushin shima sannan ya juya, idanunsa ko kaɗan bama su ga kuɗin da yake bashi ba.
Da murmushin da bai san dalilinsa ba Ma'aruf ya maida kudinsa cikin aljihu yana kallon tafiyarsu zuwa ciki, ƴar yarinyar har sai da sake juyowa ta kalle shi lokacin da Adam ɗin yaja hannunta zuwa ciki.
A hankali ya dawo da fuskarsa kan katangar gidan, idanunsa na hasko masa dukkan abinda zai faru nan da mintunan dake shirin tahowa!
***
Me zai faru??
Me zai faru??
.
.
.
Me Ma'aruf zaiyi??
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA HUDU.
~~~~~
"Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! Kuma bayan walƙiyar ta ɗauke a idanun Amina, Baba ya cigaba da maganarsa.
"Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau..."
Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sake ɗago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ƙaraminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da 'Baban kurna' sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo karshen skirt dinta da ƙarfi.
"Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da ɗayanku zai ce kunji kanmu ni da ita game da wani al'amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba zan siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al'amarin.
Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al'amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki wanda su basa gani. Don haka na san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk ɓangaren da kika zaɓa shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki ga cewar na amsa musu acan, ki faɗi ra'ayinki Amina babu wanda zai taɓa ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai.
Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har ɓangaren mahaifiyarki kika ɗauka, ina so ne muje mu sami mutanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga ɓangarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina."
Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne.
Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gabaɗaya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a maƙogwaron ta.
"Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki..."
Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta
"... Ƴancinki nake nemar miki Amina, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai kuɗi a zaune yake cewar baya taba son mu'amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Kilishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai haɗa shi da kowa.
Da ke muka je auren wani ɗansu a shekarun baya da suka wuce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa 'ƙwarya tabu ƙwarya ba... Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho

Please Login or Register in order to submit comment