Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muna ta faman jinyarta."
Ya fada yana nuna wata tsohuwa dake kwance cikin tarkacen kaya, daga nesa ƙaryane ka banbance ta ma da tarin kayan dake wajen.
Ya amsa masa bayanin yayin da ya dawo da kallonsa daga kan matar zuwa tarin ƴaƴan da suka zube a gabansa, kusan su tara wanda da kammaninsu kaɗai ya san duka ƴaƴan Mr. Okaforn ne, yaji a ransa yana ƙudirta cewa ya riga ya gama samun bayanin da yake nema don romon da yake shirin kwaɗaitawa Mr.Okaforn wani abu ne da ko mahaukaci ba zai ƙi tayin ba.
Sai dai ɗan adam baya taɓa hango tazarar faruwar wasu al'amuran, don a lokacin da ya buɗe baki zai yi magana ne, a lokacin babbar ƴar Mr. Okaforn ta fito daga wani ɗaki ɗaya tal dake manne da falon, hannunta ɗauke da Hamidan da ta saba a kafadarta a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin cusa wasu kaya cikin jakar data ratayo tace.
"Papa, make I run go drop their pikin that woman go eat me alive if she returned." ( Baba zanje na kai musu ƴarsu, wannan matar zata iya cinye ji idan ta dawo.)
"Mary!" Mr. Okforn ya daka mata tsawar da lokaci guda ta dago da idanunta kuma lokacin gudan itama ta durƙushe kamar ƴanuwanta tana faɗin.
"Welcome sir."
Ya tuna yadda ta dinga rantsuwa jikinta na rawa tana gaya masa cewa kula da yarinyar take a wajen aikinta ce ta taho da ita saboda an kira ta cewar jikin mahaifiyar tasu ya tashi, idanunsa a rufe ya cigaba da hango ta sanda ta biyo shi har bakin motarsa tana fadin yayi mata rai ya bata yarinyar, kuma ya san cewa sanin da tayi cewa shi shugaban mahaifinta ne, shine kadai abinda yasa bata yi masa ihu ba.
A hankali ya taso, ya dawo daga gefen Hamidan dake baccinta har yanzu, tun a gidan ya fahimci cewa baccin da take yi yayi nauyi, don har yazo ya sanya ta a mota, sau ɗaya ta buɗe idanunta ta koma bata sake farkawa ba, jikinsa ya bashi cewar tabbas hakan da matsala don haka kai tsaye ya wuce da ita wani asibiti mai zaman kansa inda aka karɓeta da gaggawa kafin likitoci su tabbatar cewar maganin bacci aka bata wanda da alamu ma ta daɗe tana yinsa don jikinta babu kwari sam, a take aka bata gado aka shiga ɗura mata drip mai haɗe da ruwan magani.
Kuma sai bayan da ya sami kansa ne sannan ya iya kiran Mami ya gaya mata dukkan abinda ya faru, bai san me ya faru lokacin da suna waya ba, amma sai a wayar Samira ta kira shi daga baya ta shaida masa cewa gata nan zuwa ta cikin hayaniyar da yake jiyowa a gidan.
Ya sake gyara zamansa a hankali yana kallon fuskar yarinyar, wani irin abu yake ji yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar yana sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A hankali ya lumshe idanunsa yana tuno kalaman Rukayya wanda su suka yi sanadin raba shi da ita.
"...bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zabi dawowarka."
Kuma ya yarda da maganarta ne a wancan lokacin ba don komai ba sai don nauyin laifin da ya san nasa ne.
Don ranar da ya shaƙe Ruƙayya bayan ya karɓe yarinyar daga hannunta yayi wulli da ita, a wannan ranar ne kanta ya bugu da kujera, har buguwar ta haddasa wani ciwo a ƙwaƙwalwar ta wanda da duk da karancin shekarunta aka fahimci cewa bata iya gane mutane a lokacin, kuma sai likitoci suka bada shawarar cewar a ƙaiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ƙwaƙwalwar tata har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su karɓe ta daga hannun Ruƙayyan ba sai tayi wayon da za'a tabbatar ciwon yayi sauƙi tukunna.
Kuma bayan hakan sai Ruƙayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace.
"Ka taimaka kayi nesa damu Ma'aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko kaɗan ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ƙoƙarina wajen gyara maka rayuwar amma ka ƙi barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda baƙuwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zaɓi dawowarka."
Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tura mata isassun kuɗin da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ruƙayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da Shukra da kuma wata ƙanwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo.
Yaji kansa yana ɗaurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci... tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ƴanuwansa raɓarta akan dalilin da har iyayensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ƙorafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai san adadinsu ba.
A lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za'a siya kafin farkawarta kamar yadda likitan ta shar'anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta wajen fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta riƙe da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci.
"Innalillahi wainna ilaihir raji'un, me ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?"
Muryar Mamin ta faɗa, sai da ya taso ya miƙe sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ƙoƙarin riƙe hannun Hamidan da ya saki.
Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan lokacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke ɗamfare a fuskarta game dashi.
"Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma'aruf, daɗin abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a sannu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfaɗowa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya."
Roƙon da take ya san har da wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shiru kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan.
A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta miƙo masa, kuma ganin ƙoƙarin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don ya so ba, don haka ya karɓa a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon fuskar yarinyar.
A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta karɓi wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho ɗin a yanzu ba'a san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ƴanuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa.
Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages ɗin dake shigowa bi da bi suna nunawa akan screen ɗin, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin.
Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kuma ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal.
Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaɗin cewa gidan zai dawo ɓangaren da Baba Alhaji ya taɓa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar.
Ya cije leɓɓensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faɗa masa kwanakin baya.
"Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu kuɗin da har layi zasu yi idan kace zaka zaɓa."
Ya faɗi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin ɗaurin auren ga kowa a Office ɗin kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk ɗin yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waɗannan gidajen, misali aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci ɗaurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne.
Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuɗin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taɓa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan.
"Ina kika baro masu yin cin-cin ɗin ne da kika biyo ni?"
Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita ɗin ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace.
"Zanje in dawo."
Sai ta girgiza kanta..
"A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta ɗebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min."
Ya cije leɓɓensa kaɗan yana bin maganganun nata kafin ya gyaɗa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da ɗaukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe.
Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya ɗaukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta.
Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙaunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata.
A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin ɗakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa?
Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda ɗan ƙaramin ƙirjinta ke ɗagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a ɗaya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi ɗauke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara.
Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai alƙawari ne cewar ba zata taɓa iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaɗai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haɗa aurensa da yarinyar data san ba zata taɓa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam.
Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suɓuce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf ɗin ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaɓar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida...
Gaɓar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taɓa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin ɗakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suɓuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buɗe don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki.
Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don ɗakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taɓa farinta.
Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buɗe ta....
***
A cikin ɗakin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye.
"Wallahi Maamah Hanan ƙawata ce ta haɗa ni da ita, tace ta taɓa yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na ɗauke ta a lokacin, kuma itama ta taɓa fada min inda take amma na manta."
Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa.
"Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?"
Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu.
Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na ɓatan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba.
Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address ɗin gidansu ta karɓo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba.
Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haɗin kan ƴar tata, ita kaɗai ce mace kuma babba a cikin maza huɗu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita.
Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta ɗauki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma'aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan manya ake samun masu kwaikwayon ta.
Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, ɗaya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma'aruf ɗin, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa.
Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙuri da bai bawa Rukayyan zaɓin komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito.
Ƴarta Hamida bata taɓa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karɓe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin.
Har ta buɗe baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga.
"Wai Maamah ki dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo."
Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka.
"Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu.
Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa.
"Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita."
"What? Ta yaya? Tun yaushe?"
"Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna."
Ransa a ɓace yace.
"Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai ita zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?"
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
"Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?"
Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana faɗin.
"Is it true yarinyar nan ta ɓata? Umar just called me now wai ya ganki a waje ɗazu kuna tambayar Hamida."
Hajiya Nafisa ta gyaɗa kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar.
"Ƴansanda ɗin dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba."
"Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?"
Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka.
Ahmad yace.
"Akwai wani abokin Ashraf da ya taɓa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban ɗauko wayata daga ɗaki ba, Ibrahim kira shi."
Ya kalle shi.
"Wa zan kira?"
"Ashraf ɗin zaka kira kace ya baka number B-man."
Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta ɗauki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ƴan sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn.
Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir ɗan autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri.
Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shine zaɓin Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karɓi wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya.
***
"Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..."
Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da ɗimbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin ɗaurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu.
"Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan ɗaurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne?
Amina tana tuna

Please Login or Register in order to submit comment