Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai akayi sa'a mai dinkin ya zabi wani ɗinki mai kyau da ya dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa ɗankwalin V kawai ta yafa shi a haka.
Ta buɗe ƙofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, ta bazo gashin data ɗora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da saƙo na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ƙatuwar jaka irin ta aiki.
"Good Morning my name is Martha, I'm..." ( Barka da safiya, sunana Martha, nice...)
"She's my sectary." (Sakatariyata ce.)
A lokaci guda muryar Ma'aruf ta faɗa daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ƙamshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din yake kallo da wani dan guntun murmushi a leɓɓensa.
Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya kaɗan yana haɗa ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafaɗunsa.
"You're welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman."
Sai da numfashin Amina ya katse a ƙirjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta miƙo mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba.
"You came with everything right?" (Kinzo da komai ko?)
Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha ɗin wadda ta ɗaga kai.
"Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A." (Eh yallaɓai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi maka.)
Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ƙoƙarin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta.
"Kin tashi lafiya?"
Muryarsa ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ƙafafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace.
"Barka da safiya."
Ya shafo gashinsa ta baya.
"Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?"
Ta san me yake nufi don haka ta ɗaga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa.
"Wannan sakatariyata ce sunanta Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min."
Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen dake rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta ɗaga kanta a hankali alamun ta fahimta.
"Zamu ɗan yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?"
Da sauri ta sake girgiza kanta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne, light brown, suna ta kyalli a cikin hasken safiyar.
Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake ɗauka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta shaƙi wani numfashi mai nauyi a ƙirjinta sannan ta rufe ƙofar falon a hankali.
***
"Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin gidan da sassafen nan?"
Muryar Fatima ta faɗa cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kurɓa.
"Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke tayi wai meeting suke dashi anjima."
"Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai."
Saura kaɗan murmushin da take yi ya suɓuce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar 'Gidan aurenta' ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar.
"Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?"
Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuciya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya ɓoyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su haƙa su binne, ko Maryam da take ƴaruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don haka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata.
"Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jiya, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne."
"Ya salam! Allah ya kyauta, kinyi addu'a dai ko?"
Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya 'Kinyi addu'a?'
"Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa."
"Babu abinda yake nufi insha Allah, ki cigaba da addu'a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wataƙila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi."
"Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee..."
"Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna." Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta.
"Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan kullum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min."
Fatima ta girgiza kanta itama.
"A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake ɓallo wani abu daban."
Ta haɗiye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa.
"Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo."
Sai Fatiman tayi dariya tace.
"Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya miki kiyi azumi guda uku."
Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina ɗauke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan ɗan screen ɗinta kafin hasken ya ɗauke.
***
"Eh, yanzu zan fito... I will be there in 10 minutes insha Allah. "
Ma'aruf ya faɗa cikin wayar da yake yi a lokacin da ya fito daga ɗakinsa.
"Idan kana yiwa Allah Faruq kar ka tsaya a wani wajen, Let's not make them wait." (Kar mu barsu su jira.)
Abinda aka faɗa a cikin wayar yasa shi kallon lokacin a agogon hannunsa kafin ya kashe wayar, a yanzu ya shirya cikin wasu kayan daban ba na safe ba, ƙarfe uku daidai, Martha ta daɗe da tafiya kuma shima bai daɗe da tashi daga kan system ɗinsa ba.
Don bayan tafiyar Marthan anan Amina ta same shi da kayan breakfast ɗinta, ta durƙusa har ƙasa ta ajiye a gabansa, ya tuna yadda skirt din kayanta ya baje a kan carpet ɗin lokacin da ta durƙusa, a lokacin yaji yana don ganin yadda ƴan siraran ƙafafun nan nata suka lanƙwashe da durkusawar, kuma bata ce komai ba ta shiga zuba masa kawai, idonta a kasa, dogwayen gashin idon na sama ya haɗe dana kasa kamar ta rufe su ne gabaɗaya amma kuma tana cigaba da abinda take yi.
Bai san me yasa duk abinda tayi yake jin kamar wannan ne karon farko da yake fuskantar rayuwar aure ba, shekarar sa uku tare da Ruƙayya a matsayin matarsa, amma har yanzu ba'a zo wajen da yaga wani abu nata yayi kamanceceniya da irin rayuwar da yayi da Ruƙayya ba, gani yake kamar komai sabo yake faruwa.
Yaso sunyi magana a lokacin nan, amma yawan aikin dake gabansa bai barshi ba, ya raina meeting din daga farko sai a yanzu da yaga yawan abinda za'a tattauna ya san cewa da gaske mutanen suke kuma idan har suka yi nasara ba karamin alkhairi zasu samu tare dasu ba, saboda haka dole ya ture komai gefe ya maida hankalinsa kan nazarin bayanan nasu, kuma watakila itama ta lura da hakan don tunda ta shiga ɗaki bayan yaci abincin tazo ta kwashe kayan bata sake fitowa ba.
Jamilu yazo tun dazu yayi tabe-tabensa a motar komai ya dawo dai, dama ya sani gyaran ba lallai ya zama mai yawa ba tunda motar bata cika bashi matsala ba tunda ya siye ta, don haka bayan ya gama saka links din ya nufi hanyar kofa rike da wayoyinsa kawai, ya riga ya kai duk abinda yake bukatar tafiya dashi motar tun ɗazu, din ya kusan haddace komai, zuciyarsa dama idanunsa kawai biyo dukkan abinda ya san zaiyi magana akai suke.
Ya ɗora hannunsa akan ƙofar falon har ya buɗe lokacin da yaji muryarta.
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
Idanunsa suka juyo da sauri zuwa inda take tsaye, daga hanyar koridon nan ne alamun daga daki ta fito, hannunta na hagu na riƙe da wani baƙin bokiti data ciko jikakkun kaya dasu, yabi hannun nata da kallo da kuma gaban rigarta daya jiƙe yana tabbatar masa wanki tayi, ɗankwalin da take yafe dashi tun safe ta ɗaura shi a yanzu, yayi baya ma kamar zai zame gashinta na fitowa ta gaba, mai laushi ne da alama don duk ya tashi sama.
Bai san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskarsa ba kafin ya ɗaga mata kai.
"Ameen ya Allah, nagode sosai."
Kuma ga mamakinsa sai itama tayi nata guntun murmushin sannan muryarta ta ƙara fitowa.
"Insha Allah meeting ɗin zai tafi daidai."
Tana faɗin haka ta shige hanyar Kitchen ɗin dake gefenta bokitin na bin bayanta.
***
Dab da magariba ne lokacin, Aminu ya kammala komai na aikinsa na ranar a garejinsu, kuma har yayi sallama da kowa ya fito bakin titi lokacin da wayarsa tayi kara, yana tsaye da gefen titin ya dauko ta ya duba, Baba ne, don haka ya dauka da sauri ya kara a kunnensa yana gaishe shi.
"Lafiya kalau Aminu, kun tashi ne?"
"Eh Baba, yanzu ma na fito zan taho gida."
"To ka biyo ta nan, akwai kayan da zaka dauka sai mu tafi tare."
"Insha Allah Baba gani nan."
Da haka ya kashe wayar, ya sauke ta ɗaga kunnensa daidai lokacin da mai mashin ɗin ya taho da wani irin saurin da ba Aminun kaɗai ba hatta mutanen dake baya dashi basu ga wucewarsa ba sai dai ƙarar injin mashin ɗin da kuma sanda yabi ta kan Aminun dake tsaye a bakin titin ya take shi tun daga kan ƙafafuwan sa.
Salatin mutane har da ihun wasu ya gauraye iska a lokacin da mai mashin ɗin ya murde kan mashin ɗin ya miƙe titi ba tare da ta tsaya ba, kansa na dauke da hular kwano baka don haka babu wanda ya iya ganin fuskar sa.
Wasu daga cikin mutanen suka bishi da jifa amma babu wanda ya same shi, gudu kawai yake yi har lokacin da ya fita daga unguwar baki ɗaya, ta lunguna ya dinga gujewa danja ba tare da ya tsaya a koina ba har ya zuwa unguwar Sardauna Cresent ƙofar gate ɗin gidan da ya fito, inda tun kafin ya karasa mai gadin dake zaune a waje yana jira yayi saurin buɗe masa gate ɗin ya shige.
A gaban wata ƙatuwar bishiya dake harabar gidan ya tsayar da mashin ɗin sannan ta cire hular kwanon dake kansa, daidai lokacin da wayarsa ta shiga fitar da karar vibration daga aljihunsa. Ya ɗago ta ya danna wajen amsawar ba tare da ya damu ya duba sunan mai kiran ba.
"Awa ta biyu a waje kafin yaron ya fito." Ya faɗa yana ƙoƙarin balle maɓallin rigarsa na gaba.
Daga ɗaya ɓangaren wayar, Hajiya Kilishi tayi murmushinta mai armashi kafin tace.
"Kace min an gama kawai Awwalu."
"An gama Hajiya, kema kin san komai daidai yake tafiya."
Ta gyaɗa kanta a hankali, tabbas haka ne, komai daidai yake tafiya, me yasa ma zata damu da tambaya? Awwalu ya taɓa kasawa umarninta ne?ko kuwa ta manta sanda yayi babban aikin da yafi wannan a wajen hatsari ne ma? Aikin da shine ginshiƙi samun ƴancin da take kirgawa dashi a kowacce nasarar da take samu.
Bakinta ya sake tafiya da wani murmushin, abinda ya faru yanzu tsaraba ce ga Amina, don ba'a banza zata buɗe mata fuskarta ba, ba'a banza zata san wace ce ainihin Kilishi ba, dole ne ta tunkare ta da kakkarfar hujjar da kokwanton ikonta ba zai taɓa samun waje a zuciyarta ba.... Aminu shine farko a yanzu, kuma idan komai ya tafi daidai zai zama na karshe, amma da an samu wani akasi ƙofar ta buɗe kenan, duk wanda ya jiɓanci Amina ya shigo cikin lissafinta.
Zata ɗaure Amina ne da jijiyoyin jikinta, bata isa ta tsallakewa dukkan sharrinta ba a yanzu, ta riga ta shigo cikin jerin mutanen da take juyawa da yatsan hannunta.
"Ya batun Ma'aruf ɗin Hajiya? Na gaya miki yayi nisa a binciken da yake yi, idan har ya riga mu nemo inda Mr. Okafor yake wallahi abubuwa zasu canja daga kalar da muka san su, ya kamata ki tsayar dashi har sai mun riga shi nemo mutumin nan mun tura shi lahira tukunna."
Muryar Awwalun ta katse ta daga tunaninta, kuma a lokaci guda sai murmushin dake kan fuskarta ya ɗauke, yanayin fuskarta ya koma wani iri da babu abinda zaka tsinta a ciki, ta haɗiye wani abu a cikin maƙogwaronta tana kallon tarin magungunan Ma'aruf ɗin da ta baje daga kan gadonta, a hankali ta girgiza kanta sannan tace.
"Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL ɗin nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma kuɗaɗen sun shigo zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da kuɗin kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor ɗin... Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!"
***
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA BIYU.
Life is what happen to us when we are busy making other plans.
-Unknown.
**
Ranar lahadi ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwan da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya.
"Wallahi sai ayi baƙi kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili."
Cewar Samiran a lokacin da take daka tafarnuwa ƴar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta.
Munaya tana yanka carrots ta ɗago ta kalle ta tace.
"Ki kara faɗar abu guda ɗaya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba."
Amina tana murmushi daga inda take blinding abarba tace.
"Ki ƙyale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk ɗaya ne."
Samiran ta girgiza kanta.
"Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin wannan lokacin ba'a ganinta wallahi, idan ta shiga ɗaki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta faɗan taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba..."
Bata karasa ba kuwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana faɗin ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya.
Amina ta tsiyaye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya taɓa ciwon hannunta da bata daɗe da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru.
Munaya tana da saukin kai sosai, don tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da ɗan yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta ɗanyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gabaɗaya suka gaisa sau ɗaya ra kara shigowa ranar da suka yi zancen littafin nan.
Samirah ce dama kusan kullym zata leko ɗan bsyami ko saƙonta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata daɗe ba kuma sai ga Munayan itama ta shigo, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su.
"Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi."
Munayan ta faɗa yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta ɗauko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge ya ɗanyi sanyi kafin ta ƙarasa abinda zata yi tazo haɗa lemon.
Fridge ɗin yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen ɗin take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da Ƙofar kitchen din ta buɗe Ma'aruf ya shigo ciki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota'ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don tun safen yana ɗakinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting ɗin.
"Kinyi addu'a mai kyau kuma Allah ya amsa."
Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai daɗi suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan ɗaya kamfanin suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ƙara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma'aruf ɗin da ya bata wannan saƙon ba... Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba.
Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq ɗin da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin aƙalla ta tarbe shi da irin tarbar da ya kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ƙarya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa.
Ƙafarta ta ƙarasa wajen Fridge ɗin ne daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi.
"Me yake faruwa anan?"
Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta faɗaɗa da murmushi yayin sa Munaya ta kira shi cikin wani abu mai kama da waƙa.
"Yayaaaaa B...."
A ƴan kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun daɗe rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yanzu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wataƙila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya.
Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya faɗa a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke ɗauke da fara'a sun baibaye shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a ɗazu na wani competition ɗin kamfanin Maggi da aka zaɓe ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop ɗinsa take so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta...
Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar waɗannan mutanen?
Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba'a daɗe ba taji an ƙwankwasa kofar store ɗin dake buɗe a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta.
"Akwai ruwa anan?"
Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ƙofar store ɗin, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ƙare tun dazu kuma bata fito da wani ba, don haka da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere ta buɗe na saman ta ɗauko ɗaya, yana tsaye yana kallonta har ta ƙaraso ta miƙo masa, kuma ga mamakinta tana ƙarasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba ɗaya ya jawo ta zuwa gabansa, ƙafafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ƙirjinta lokacin da yasa ɗan yatsansa ɗaya ya taɓa daidai wajen data yanke ɗazu.
"Me ya faru?"
Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon.
Sai da ta haɗiye yawu tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin tace.
"Da wuƙa na yanke."
"Me kika saka a wajen toh?"
Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin ƙarar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen ɗin, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje tana waya.
Ta sake haɗiye wani yawun a makogwaronta.
"Ba komai na wanke ne kawai."
Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya buɗa ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cije lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace.
"I'm sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep." (kuma yayi zurfi.)
Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta ɗaga kai ba tare da tace komai ba, kuma bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta ɗago da idonta kalle shi da ɗan ƙaramin mamaki.
"Aikin me kuke yi haka?"
Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta.
"Abinci ne kawai."
"Kala-kala haka?"
Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ƙarfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka haƙiƙance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru.
"Kace abokin ka zai zo."
"Ishaq?" Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa.
"Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?"
Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq ɗin zai zo ya kamata ayi wani abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi baƙi Ruƙayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace.
"Thank you."
Ta ɗaga kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji ɗuminsu yana barin fatarta.
"Zan nemo abu in rufe miki ciwon anjima insha Allah."
Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa.
A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zuƙo shi, ssi kawai ta juya itama ta ɗauko wata robar ruwan ta balle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store ɗin.
Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunawa kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari

Please Login or Register in order to submit comment