Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farko ya rungume ta, hannunsa ɗaya ya zagayo wajen ƙugunta yayin da kanta ya samu mazauninsa a kusa da wuyanta.
"Kar ki maida shi zai cutar dake... Just let it out."
Muryarsa ta faɗa a cikin kunnenta da wani sauti daya shiga dagargaza dukkan wata jijiya ta dauriya a jikinta.
Kuma a karo na farko Amina ta manta komai akan Ma'aruf ta sunkuyar da kanta a jikinsa don babban abinda take buƙata kenan, kukan da sautinsa kaɗan ne ya suɓuce daga bakinta yayin da jikinta ke girgizawa a cikin hannunsa.
***
Bayan kwana biyu.
"Kin shirya?"
Ma'aruf ya tambaya yana kallon Amina data fito riƙe da wata ƴar ƙaramar jaka a hannunta da kuma wani madaidaicin basket, doguwar riga ce a jikinta ta baƙar abaya, ta yafa baƙin mayafin kawai akanta ba tare da ta saka ɗankwali ba, tana tsaye daga hanyar koridon dakunan tana cakuɗa yatsunta cikin junansu, har yanzu ta kasa yarda da abinda yazo dadaddare ya gaya mata jiya cewa ta shirya zasu je jigawa a yau.
Jiya da safe a wayar tasa suka yi waya da Amma ta shaida mata lokacin tafiyarsu wanda bayan hakan tayi ta binsa da kallo tana so taji yace wani abu amma bai faɗa ɗin ba har ya fita, ya barta a zagayen halin da take ciki, kuma Allah kaɗai ya san yawan abubuwan data saka ta kwance a cikin kanta a jiyan wanda duk iya tunanin nata yana ƙarewa ne a gaɓar da bata san yadda zata yi ba.
Haka ta yini har a jiyan tana share hawaye duk lokacin da ta tuno cewa duk irin halin ciwon da Aminu ke ciki saboda ita ne, saboda itan da bata san yadda zata budi baki ta gayawa wani ba, ko da Ma'aruf ɗin ne kuwa tunda shi kansa babu alamun yana da wata masaniya irin wadda ita ta sani yanzu akan Mamin, duk da cewa bata gama sanin ainihin abinda take nufi game dashi ba ko kuma shi nasa ra'ayin akanta.
Sai da daddare bayan ya dawo ne kawai yace ta sako mayafinta zasu shiga cikin gida, wajen Mami suka fara zuwa kamar yadda suka zata, kuma gaishe ta kawai suka yi kafin ya furta abinda yasa kowannensu mamski daga ita har Hajiya Kilishin.
"Gobe zamu wuce Jigawa Mami, na san kin samu labari, brothern ta ne ya gamu da hatsari zan kaita ta dubo shi."
Har yanzu tana jin nauyin yadda idanun Hajiya kilishi suka dinga kallon fuskarta, tana jin tafiyarsu a ko'ina na fuskar tata, yadda ta dinga kallonta da wani irin yanayi da yake nuna mata cewa itama a lokacin taji zancen, da kuma yadda tata zuciyar ta dinga bugawa har sai da taji kamar ta tsugunna ƙasa ta ɗauko ta lokacin da suka miƙe tsaye, don tsabar tsoro ƙirjinta fayau ta dinga jinsa kamar yadda jikinta ya zama kamar fallen takarda har lokacin da suka tafi ɓangaren Hajiya Maimuna, idan acan ma suka sha addu'ar Allah ya kiyaye hanya kamar yadda Mamin tayi tata.
Jiya haka ta kwana tana juyi akan gado, da asuba kuma tunda tayi sallah bata koma ba, don yace mata ƙarfe takwas zasu tafi a yau ɗin zasu je su dawo kamar yadda ya tsara.
Abincin breakfast ɗin da tayi ma bai ci ba don yace mata azumi yake yi kasancewar ranar Alhamis ce. A yanzu ya shigo daga wajen maigadi ne da ya gama wanke masa motarsa, yana tsaye daga bakin ƙofar falon yayin da karar yadda maigadin ke share ruwan wankin motar daga waje ya cika falon.
"Kin shirya a haka?"
Ya ƙara tambaya yana kallonta, sai ta sunkuya ta kalli kayan jikinta sannan ta dago ta kalle shi tace.
"Eh na shirya."
Shi nasa kayan dogwaye ne kalar sararin samaniya, ya saka hula wadda ta dace dasu, da ace zuciyarta a nutse take ta sani tsaf zata tsaya yabawa yadda kayan suka karɓe shi amma a yanzu ba abinda ke gabanta kenan ba, tashin hankalin dake kwance a ƙasan zuciyarta ya isa ya binne ta da ranta. Sai kawai ya taho gabanta riƙe da mukullin motarsa a hannu, kuma bata matsa ba, don watakila a yanzu ta saba dashi a kusa da ita, kar a lissafa da shekaranjiya lokacin da ya rungume ta, wannan don ba'a cikin hayyacinta take ba kowannensu ya sani.
Hannunsa taji ya sauka akan gashinta da ya fito ta gaba kafin yace.
"Shi wannan ba'a rufe shi?"
Zuciyarta ta buga yayin da wani abu ya tsarga tun daga saman kan nata har zuwa tafin ƙafafunta amma ta haɗiye shi, sai ya matsa baya kadan sannan yaba cigaba da kallonta yace.
"Bana son wani yaga gashinki."
Bata ɗago ta kalle shi ba amma kalaman sun daki zuciyarta ta yadda duk tarin hargitsin dake ciki sai da suka girgiza. girgizawar da bata yi tunanin zuciyar tata zata yi ba a yanzu tare da abinda ya faru game da ita.
A hankali ta juya ta koma ɗaki, wani pink dankwali ta ɗauko ta daura, ai kuwa ya hau sosai da kayan ya ƙara haska fuskarta, wanda bata ko gani ba ta sake ɗaukan ƴar ƙaramar jakarta da kuma wannan basket din ta fito, sai da ta tabbata ta kashe fitulu da switches ɗin ko'ina, na fridge kawai ta bari sannan ta fito.
Yana tsaye daga bakin barandar falon yana jiranta, wani guntun murmushi da yayi mata yasa gumi fitowa a tsakanin yatsunta kafin ta bashi waje ya kulle ƙofar gidan, kuma juyowar da yayi yasa shi tsayawa dab da ita, wanda kafin tayi tunanin yin gaba idonta ya hango mata wasu manyan ledoji akan booth ɗin motarsa.
"Mami ce ta aiko a kawo miki, yanzu muka yi waya tace ki kai musu." Muryarsa ta faɗa dab da bayanta.
Zuciyarta ta buga a ƙirjinta, hannayenta suka fara rawa riƙe da kayan nan, ta sani bana tasirin muryarsa ne kaɗai bane har da na sunan Hajiyan Kilishin daya furta. Numfashinta ya shiga kakkatsewa a kirjinta ta yadda tayi tunanin zai iya jinta amma sai taji lokacin da yayi baya ya ɗauki waya yana cewa.
"Zuwa 10 zasu iso Faruk, idan kana ƙaunar Allah ka tabbata kana nan..."
Sai kawai tayi ƙarfin halin motsa kafafunta ta tafi wajen motar, ta isa wajen daidai lokacin da idonta ya nuna mata sauran kayan daga gefen motar, buhun shinkafa guda biyu da jarkokin mai suma guda biyu.
Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta kafin ta ajiye kayan hannunta, ta buɗe ledar farko inda kayan tea manya-manya gwangwanayen su Madara ya shiga idonta, a ɗaya ledar kuna wani ƙaton food flask ne shi kadai mai faɗi, taji har a lokacin hannunta na girgizawa a hankali sanda ta buɗe shi, kuma tun kafin ta gani ƙamshin wani farfesun naman kaza ya cika hancinta, shine fal ya kusan cika flask din har baki.
Ba shiri ta rufe idanunta tana jin koina a jikinta na girgizawa. Fata take da dukkan imaninta cewa Allah ya kawo mata mafita akan matar nan.
"Ya ubangiji kaine tanadin kowanne bawa idan ya fada masifa, Ya Allah na miƙo maka hannaye na ka taimake ni akan wannan al'amarin da yafi ƙarfina, ba zan iya ba ya rabbi! Bani da wata mafita da wata dabara wadda ta wuce taka ya Allah."
Wani lokacin bawa yana yin addu'a ne akan gaɓa, wani lokacin ubangiji yana amsa addu'a ne a take! Kuma komai yana da tushe yana da asali, kamar yadda tafiyarsu Jigawa ke shirin zama tushen faruwar abubuwa masu yawa.
Kuma rashin sani yana ɗaya daga cikin raunin ɗan Adam!
***
Waye yake cikin wannan rashin sanin ne?
A cikin dukkan wannan hargitsin, me yake jiran mu a jigawa ne?😉
Wace mafita Amina zata samu game da Hajiya Kilishi kafin zagayowar sati guda?
A yau kun fara jin tarihin Hajiya Kilishi!😰
Ku shiryawa abinda ke faruwa daga ɓangaren Ruƙayya.
Har da Jawad ma.😅
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA HUDU.
~~~~~~
I fall in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul.
- Unknown.
***
Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta.
" ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..."
Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan ɗin kafin kai tsaye ta katse ta.
"Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?"
"Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?"
Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan ɗin wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace.
"Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf."
Ta fada ba tare da ta ɗauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta.
Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta daɗe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan ɗin ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba.
Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta.
"Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faɗa da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki ƴarki ki taho gida da ita.
Kwana ɗaya kawai a tsakani, zaki haɗa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za'a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haɗu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta.
Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za'a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya."
Ta ƙarashe zancen da wani faffaɗan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta.
"Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata."
"Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saɓani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai."
Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya.
Ta mike a hankali riƙe da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kurɓar shayin kafin ta ɗauki wayar ta kara ta a kunnenta.
"Barbie yau kika ce, 5pm."
Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sani cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi.
A hankali ta ajiye kofin hannunta akan windon, sannan tace.
"Ban manta ba J."
Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace.
"Then where did you decide?" (Ina kika zaba?)
Ta sake cije lebbenta na ƙasa
"Where we first met." (Wajen da muka fara haɗuwa.)
Kalaman suka daki zuciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata ɓangaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara haɗuwar anan ya kamata ta kawo ƙarshen alaƙarsu gabaɗaya, ko yaƙi, ko ya so.
Kuma ƙarfe biyar da ƴan mintunan tayi mata a kofar Joint ɗin 'Harish', ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani ɗinkin mai kyau daga kasa kuma tayi buɗewar umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, ƴan kaɗan ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da kuma ƙamshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta.
Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara haɗuwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hula dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska.
Kafafunta suka ƙarasa wajen a hankali sanda shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ƙara tuna mata da kammaninsa.
"Kina da cika alƙawari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki."
Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawai ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna.
"Wane flavour za'a kawo miki?" Ya tambaya yana tasowa daga kishingiɗen da yake.
Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece ɗin hannunta sannan ta kalle shi sosai.
"Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawad, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana."
Ya gyada kansa yana kallonta.
"Zanyi duk abinda kika ce Barbie."
Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba kai tsaye ta fara magana.
"Jawad abubuwa sun cakuɗe a rayuwata yanzu, I've got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke alaƙa ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole ne na ajiye ka a gefe.
Kuma nayi ƙoƙarin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki."
Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da dukkan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba.
"Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake tun a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na haɗu da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really did help 'cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai.
Yadda kayi treating ɗina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka zai iya sawa na canja ra'ayina akanka, but honestly ban ɗauke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka taɓa zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad.
Zuciyata ta mutum ɗaya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za'a tsaida tashin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let's just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad.
Erase all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gabaɗaya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, kuɗi, age, time... You have it all J. (Kana da komai) zaka samu ƴanmata guda dubu da kallo ɗaya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka."
Ta ƙarashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta yake shima, sai da ta kai ƙarshe ɗin sannan ya ƙifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito.
"Anything more Barbie?" (Akwai wani abu kuma Barbie?)
Ta haɗiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.
"Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni."
Sai ya gyada kansa haɗe da rufe idanunsa ya buɗe kafin yace.
"Thank you." ( Nagode.)
Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskarsa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai ɗin, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye.
"Nagode nima, sai wani lokacin."
Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayanta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke kaɗawa da tafiyar da take yi yayin da ƙwaƙwalwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro.
"Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi maka alƙawari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!"
Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan leɓɓen nasa lokacin da Ruƙayya tayi kwana ta fita daga wajen tana ɓacewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu kaɗan kuwa ya ɗaga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zuƙo hayaƙinta ya busa a iska sannan yace.
"Tayi biyu babu Haro, let the plan start!"
***
Jigawa,
11:05 Am.
"Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi ba? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?"
Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shiga jiya, tana zaune a gabansa tana ƙoƙarin zuba sukari a kofin tea ɗin data take hada masa.
Abinda ya faɗa yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace.
"Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce kaɗai ma zata iya kashe bakin ka."
"Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata ƴar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan."
Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska.
"Aminu wannan fa ba zancen wasa bane."
Ya ɗaga duka hannayensa sama.
"To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?"
Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta.
Kuma sai akayi sa'a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya ɗauka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan ƴan mintuna ake kiransa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ƙasa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman.
Kusan awar su guda kenan da sauka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma'aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa'ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ƙasa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa har yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfiɗar Aminun lokacin da zai fita.
"Guess what?" (Kin san me?)
Ta tuna yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su ɗauko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumuɗi tsaya bata ko tuna da ita ba ta buɗe kofar motar ta fita.
Yadda ya tsaya a kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko.
"Naga yadda zaki koma idan kin ƙara girma."
Hakan yasa tayi saurin ɗagowa ta kalle shi, ya harde hannayensa duka biyi a kirji riƙe da wayoyinsa, kuma a take sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa.
"Kamar ki ɗaya da Mamanki, na daɗe ban ga masu kama haka irinku ba."
Ruɗani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kanta kafin ta iya lalubo muryarta.
"Haka kowa yake cewa." Ta faɗa a hankali.
"Haka kowa yake gani that's why."
Bata ce komai ya sake cewa.
"Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki."
Bata san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake ɗagowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ƙara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba.
"Nagode sosai."
Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tamau ba.
A wannan lokacin Ma'aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta.
Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ƙankantar ta, don a lokacin da Mami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma yadda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya daɗe daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya.
Tare da Ruƙayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin expectation ɗinta akansa, ta daɗe tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake yi ba, hakan baya masa daɗi, amma ko fuskar Amina ya kalla, innocent kammaninta kaɗai yana sashi jin wani cikakken iko irin wanda kowanne namiji ke ji akan iyalinsa.
Don haka yadda take kallonsa a wannan lokacin, yasa shi ture abubuwa da yawa a cikin kansa ya tako ya karaso gabanta, ya tsaya dab da ita sosai lokacin da kallon cikin idanun nata ya koma kalar mamaki da kuma ruɗani, irin

Please Login or Register in order to submit comment