Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne da nauyin waɗannan kalaman ɓoyayyiyar yarjejeniyar da suka yi kamar yadda koda da rana guda shima bai taɓa manta su ba.
Ya isa gida bayan ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha'i, ya shiga da motarsa ciki sannan ya fito ya rufe gate din yana takaicin yadda sai wani satin zai samu maigadi kamar yadda kamfanin suka shaida masa.
Kuma bayan ya ɗauko wayoyinsa biyu daga cikin motar ya dade tsaye a wajen yana waya da Ishaq, a yanzu haɗuwarsu ta ɗanyi wuya, yana ta yawon zuwa Abuja ne akan wani workshop da suka fara a kotun tasu, don haka a cikin satin ma sau daya kawai suka haɗu.
Magana suke tayi akan gininsu, wasu filaye da suka siya a Lamiɗo Cresent ana musu gini iri ɗaya, bayani yake yiwa Ishaq ɗin cewa zasu canja masu gini don na yanzun an basu kudin kaya mai kyau amma sun siyo wani siminti da bashi da kyau har wani waje a cikin ginin Ishaq din ya rufta. Daga karshe suka tsaya akan Idan ya dawo zasu fara neman wasu ma'aikatan kafin suyi sallama da kalaman da Ishaq din ke gaya masa a mafi yawancin ƙarshen maganarsu.
"Dan Allah ka kula B."
Ya cije leɓɓensa yana kallon wayar, har yanzu Ishaq bai yarda dashi ba ya sani, gani yake a kowanne lokaci wani abu zai iya faruwa saboda yanayin ciwon nasa, amma shi baya jin hakan, akwai abubuwan da yawa a gabansa amma baya jin sunyi yawan da a cikinsu zai iya samun abinda zai canja yanayinsa, don haka yana amsa masa ne kawai don ko yayi bayanin ba zai yarda dashi ba.
Ya kashe wayar sannan ya debo kayansa na cikin motar ya shiga ciki da ƴar karamar sallamarsa, babu kowa a falon amma ƙamshin turaren wutar daya kula kwana biyu ana yinsa a gidan ya shiga hancinsa. Yayi sallamar da babu mai amsa masa sannan ya cire takalmansa daga gefe ya taka zuwa ciki, zuwa hanyar korodon nan, fitilar dakinta a kunne take kamar kowanne lokaci irin haka idan ya dawo, ya jiyo motsinta daga ciki har da ƙara ma kamar wani abu ya fadi kafin ya zarce zuwa dakinsa.
Wanka zaiyi ya fito ya shiga cikin gida, a can wajen Mami yake cin abincinsa kullum, kafin ya fita dai ya san watakila zai ganta su gaisa, amma zuwa lokacin da zai dawo ma ta riga ta kashe fitilar dakinta ta kwanta, ta kasan kofarta yake ganin hakan idan zai wuce. Ya isa ɗakin nasa lokacin da yake tuno maganganun Baffa sanda yake masa fadan rashin halartarsa wajen daurin auren nan, Baba Usman yana daga gefensa yake cewa.
"... Idan kana tunanin zaka wulakanta yarinyar nan saboda iyayenta ba masu arziki bane Muhammad, ina so ka kalli iyayenka biyu da suke cikin gidan nan, daga ita Kilishin har Maimunan da ta haife ka, ka gaya min waye ya fito daga gidan mai kuɗi, ko kuma ni kaina da nake mahaifinka, ka gaya min gidan iyayena na gado da yake Bakori yaya yake, Mahaifina har ya mutu ɗakin kwanansa na ƙasa ne bai ko kai girman ɗakin nan ba ka sani.
Saboda haka na daura aurenka da yarinyar nan ne saboda shaidar halayen kirki da aka yi mata ita da iyayenta, ba don abin duniya ba babu ruwana da abinda mutane ke faɗa wai kwarya tabi kwarya, zaman aure nutsuwa da kwanciyar hankali ake nema a cikinsa ba suna ba, game da aurenka na farko kaima shaida ne akan hakan, don haka ina rokonka kar ka bani kunya a karo na biyu Ma'aruf."
Ya rufe idanunsa lokacin da ya saki ruwan shower akansa, indai Baffa zai kira shi da sunansa na asali ya sani cewa babban al'amari ne.
***
Doguwar riga ce a jikin Amina ta atamfa kalar milk da sea green, ta daura dankwalin sannan ta yafa wani karamin mayafi shima kalar sea green ɗin da ya tsaya iya kafadunta, ba kwalliya tayi ba don babu ko hoda a fuskarta amma fatar ta da'a kwana biyu ta kara washewa sakamakon canjin ruwa tana haskawa tare da fararen idanunta, kuma kawai ta yafa mayafin ne don bata son fita haka, taji lokacin da Ma'aruf ya shigo, har wucewarsa ta gani ta kasan ƙofar dakin daidai lokacin da robar vaseline ɗin dake hannunta ta subuce ta fadi.
Sati guda kenan da fara rayuwarta tare dashi amma har a yanzu duk sanda ya fita ya dawo sai taga kamar shine ganinta dashi na farko, taji zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda duk da cewar wannan taraddain da take ji a farko ya fara tafiya, don bata san me yasa ba komai yazo ne sabanin tunsninta kuma lokaci yana saukaka mata abubuwa fiye da zatonta.
Ko kaɗan bata ga wani yunƙurin cutar da ita a tare dashi ba, hasalima harkokin gabansa yake, da sun gaisa shikenan ba zai kara bi ta kanta ba. Ita kanta ta fara sabawa da gidan a yanzu, ranar da su Fatima suka zo sun taya ta sake kimtsa komai nata, sauran kayan kwalliyar nan da jakunkuna da takalman dake cikin Ghana must go ɗin nan duk an samar musu wajen daya dace dasu, ta basu kayan kwalliyar ma da yawa da kuma wasu daga cikin undies din.
Sannan a kitchen ma sun jera komai a muhallinsa, store din ya zama babu komai sai iya abubuwan da ba lallai amfaninsu yazo a kusa ba, bata san adadin mamakin da tayi ba na yawan ganin kayan, don bayan wanda aka siya mata kusan duk wanda zai kawo wata gudunmawa kayan kitchen ɗin ne, don haka har wasu abubuwa ta ware a cikin ranta cewar zata ajiyewa Maryam idan lokacin nata auren yazo.
Sauran ɗakunan nan biyu ashe ɗaya carpet ne kawai da labulaye da kuma su tintin a jere, sai ɗayan ne aka tsara shi da wani irin nau'in furnitures masu tsananin kyau da ɗaukar ido, komai kalar grey, milk da kuma ash ne, wani silk bedsheet din da aka shimfide gadon dashi yana ta daukar ido a cikin hasken fitulum ɗakin, Aunty Safiyya bata sani bane da take cewa tayi zamanta a dakinta, dama ba'a tsara wannan don ita ba, shi suka yiwa abinsu, don har wasu fitulu aka saka a tsakiyar ceiling ɗin dogwaye masu haske, ga kalar fentin shima grey ne, labulayen kuma milk gabaɗayansu.
Kasa rufe bakinta tayi a lokacin da su Ummi ke cigaba da santin ɗakin daga inda suka tsaya a bakin kuma ƙaton akwatin dake ajiye akan gadon, shi ya hana kowannensu shiga don ba sai ta gaya musu ba sun riga sun gama sanin dakin na waye.
Ta fita ɗakin ta rufe kofar a hankali kamar mai tsoron kar a jita sannan ta nufi hanyar kitchen, daga tsakiya akan work table ɗin nan tray din dake dauke da flask din abincin da ta gama ne, a yau zata danne zuciyartaa tayi abinda ta kasa jiya, shekaranjiya ya aiko aka kawo kayan abinci kamar ya san dana ta matsu ta fara girki da kanta, don haka kai tsaye ta gayawa Samirah cewa ta huta tunda dama ita ke kawo mata abinci kullum, abincin da ita kadai take ci don ko yana sanin an kawo ɗin ma bai taɓa tambaya ba, ta fahimci idan ya dawo yayi wanka wajen Mami yake tafiya yaci abincinsa sannan ya dawo.
Don haka ko jiya da tayi girkin, har dashi tayi amma tana ɗaki tana biya abinda zata ce masa taji ya buɗe kofar falon ya fita, haka ta debi abincinta ta rufe a fridge, amma yau ta gama shirya cewar ba zata bari ya fita ba, ba don komai ba sai don tarin nasihohin nan da aka yi mata suna ta yawo a cikin kanta, gani take kamar laifi take idan zata yi girkin babu shi, don akwai nasa hakkokin akanta kamar yadda shi ya sauke nasa wajen kawo abincin.
Bayan haka ma, ta karanci kalolin kayautata zamantakewa fiye da adadi a wajen Ammarta, abinda ke cikin zuciyarta kenan fal kuma dashi tayi tunanin zata iya cin galabar komai dama, har yanzu bai nuna wata alama ta cutar da ita ba don haka don me yasa ita zata fara da abinda bai dace ba?
A cikin addu'o'in da Gwaggo Balkisa tayi mata tace '... Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa..'
To idan bata kyautata masa ba ta yaya zai ji tausayin nata, Me ƴan uwansa ma zasu yi tunani idan hakan ta cigaba? Idanunta suka hasko mata Hajiya Kilishin da yake zuwa wajenta yaci abincin, bata san me yasa ba ita har yanzu zuciyarta bata kwanta da ita ba, ranar da su Samirah suka fara kaita wajenta, hannayenta duka biyu ta kamo tace.
"Barkanki da zuwa cikinmu Amina, zuciyata cike take da murna idan na tuna cewa ƴa ta na kawo gidan nan ba kowa ba, ki saki jikinki ki saba da kowa, don a gidan nan bama taba banbanta kanmu, kowa ɗaya ne kuma kowa yana samun tallafawar ɗan uwansa saboda ƙaunar dake cikin zuciyoyin mu, kuma kema kin shigo kenan cikin wannan lissafin namu, rayuwarki zata canja da dukkan alkhairin da dake tare damu, kuma ina fatan kema zaki bamu damar amfana da irin naki alkhairin."
Haka kurum a lokacin sai taji maganganun basu tafi har cikin zuciyarta ba, sai taji kamar sun tsaru da yawa ace kai tsaye take faɗarsu daga zuciyarta a wannan lokacin, amma ko da ta daga ido ta kalli fuskarta, sai zuciyarta ta ture wannan kokwanton a gefe, tana tuna mata cewa itace wannan Hajiya Kilishin da ta tallafi rayuwarsu ta ɓangarori da yawa.
Hajiya Kilishin da kullum Baba yake ambato da kyawawan kalamai sannan kuma kamar yadda ta gani ta itace jagorar wannan gidan, don a yinin yau kawai ta fahimci abubuwa da yawa sai da izininta ake yi, don haka saboda tana ganin itace umul'abasin faruwar wannan auren bai kamata zuciyarta tayi wannan tunanin ba.
Amma Allah ya sani da suka shiga wajen Hajiya Maimunan wadda aka gaya mata itace asalin mahaifiyar Ma'aruf, zuciyarta kusan narkewa tayi tun kafin ta kai ga zama, mace ce har mace, irin manyan matan nan masu tsananin kamala da nutsuwa, fukarta fuska ce da za'a iya amfani da ita a koina a fadin duniya ta wakilci kalmar 'Uwa a rayuwar bahaushe' sai dai babu ƙafafu, tana zaune kan Wheelchair ɗinta da Hisnul Muslim a hannunta.
Kuma abinda ya bata mamaki shine itama da fara'arta da komai itama ta karɓeta, tana ta zuba tarin addu'oin fatan alkhairi da kuma fatan zaman lafiya a tsakaninta da Ma'aruf, wani abu data lissafa cewa yayi ƙaranci a kalaman Hajiya Kilishi.
Sai kawai ta ture wannan tunanin ta dauki tray din ta taho falon, sai da ta tsaya tana ta tunani inda zata ajiye kafin ta tsugunna a hankali daga gaban Three-sitter dake gabanta, kuma tsugunnawar tata tayi daidai da fitowar Ma'aruf daga falon, ta dago da kanta lokacin da kafafunsa suka tsaya cak yana kallonta daga hanyar kofar da ya nufa.
Yayi wankan, ya canja yansa zuwa wani bakin wando da dark navy blue riga data dace da kalar daren, kallonta yake yi da mamakin dake nunawa karara a fuskarsa, sai kawai tayi saurin ƙarasa ajiye tray din sannan ta mike tsaye itama. Kanta a sunkuye hannayenta cakude da juna tace.
"Barka da dare."
A cikin shirun dakin muryarta ta fito kamar wani fukafikin dake tahowa kasa a hankali, Ma'aruf ya gyada kansa yana kallonta har yanzu da mamakin a fuskarsa kafin ya amsa da.
"Kin yini lafiya?"
Haka yake tambayarta kullum, don haka ta gyada kanta ba tare da ta dago ko ta daina cakuɗa yatsunta cikin juna ba, kuma sai tayi shiru bata ƙara cewa komai ba. Amina ta san ya kamata tace wani abun game da abincin da yake kallo a gabanta amma bata san me zata fara cewa ba, kuma ga mamakinta sai kawai taji yace.
"Wannan abincin..."
"Naka ne..."
Ta ƙarasa da sauri tana ɗago da kanta, idanunsu suka haɗu waje guda sai tayi saurin sake maida kanta kasa ta cigaba da murza yatsunta, amma zata iya karanta mamakin daya karu cikin muryarsa sanda yace.
"Masha Allah, kamar kin sani dama yunwa nake ji."
Wani abu a cikin zuciyarta yayi tsalle da jin hakan, yayi kokarin subucewa daga zuciyarta zuwa kan fuskarta amma ta tare shi da karfi tana cigaba da motsa hannunta, ƙarar takunsa taji yana tahowa don haka tayi saurin tsugunnawa ta ɗauki plate din tana bude murfin flask ɗin farko.
Ƙamshin abincin ya shiga hancin Ma'aruf sanda ya karaso kan carpet din, idanunsa na kallonta tana zubawa yayin da ƙaramin mayafin data yafa kalar kayanta ya zame yana reto a gefen fuskarsta, wani abu yake ji na daban yana shiga zuciyarsa bayan mamaki, sai kawai ya zube wayoyin hannunsa akan kujerar sannan ya ƙarasa kan kapet ɗin gaban abincin ya zauna, ƙamshint turarenta mai sanyi ya shiga hancinsa tare da na abincin don a yadda ya zauna tray ɗin shi kaɗai ya raba tsakaninsu.
Kuma bai ce mata komai ba, yana kallonta ta zuba iya adadin da take so na komai sannan ta ture tray din gefe a hankali ya tafi cikin laushin carpet din kafin ta ajiye plate din a gabansa. Shinkafa ce fara da vegetables a ciki sai kuma miyar dake tashin ƙamshin daya baɗe falon a lokaci guda, akwai wani abu a dan bowl data zuba na cabbage da kuma Irish potato mai hade da nama duk da wanda yake cikin miyar.
Wani abu ya motsa a cikin zuciyarsa cike da yabawa kokarinta dama abincin tun kafin ya kai bakinsa, yana tuna masa da wani al'amari daya shuɗe a labarin aurensa na farko, ba kai tsaye ya samu irin wannan gatan ba.
"Thank you so much."
Muryarsa ta furta a hankali da wani sauti da yasa numfashin Amina katsewa a kirjinta, ba shiri ta gyada kanta sannan ta mike da sauri.
"Ina zaki je?" Shima yayi tambayar kamar kai tsaye bai shirya mata ba.
"Zanje in kawo ruwa ne."
Muryarta ta fito tana fallasa bugun da zuciyarta ke yi, kuma kafafunta basu motsa ba sai da ya ɗaga mata kansa.
Ta isa kitchen din ta ɗauko robar ruwa guda ɗaya da ba'a fridge ba, don ta kula duk sanda zata ganshi da ruwa a hannunsa to ba mai sanyi bane, shi yasa lemon data haɗa ma ta kaishi can kasan fridge din baiyi sanyi sosai ba, Samirah ce ta koya mata hada lemon, kuma ta tabbatar tayi komai daidai, sai dai bata san dadinsa ko akasin sa ba tunda bata taba sha a wani waje ba.
Ta isa falon lokacin da idonta ya sauka akansa ta baya ya kai lomar da bata san ta nawa bace cikin bakinsa, zuciyarta ta kara nutsewa cikin kirjinta da tsarin nata ya tafi daidai, a hankali kafafunta suka ƙarasa kan carpet din, tana jin yadda kafar tata ke shigewa cikinsa saboda laushin sabunta. Wannan karon nesa kaɗan dashi ta zauna sannan ta fara ƙoƙarin zuba lemon a kofi.
Ma'aruf ya dago ya kalle ta, har yanzu mamakinta bai bar kan fuskarsa ba, kuma a lokaci guda yaji kalaman da Mamin ta taɓa gaya masa suna dawowa cikin kansa.
... Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata.
Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa ta fara hakan ne don an saka ta, don bin umarnin da ya tabbatar shi tayi har auren nasu ya kasance, yaji zuciyarsa ta matse da wannan tunanin amma kuma sai ya samu sauƙi da hasashen cewa haka ba zai iya zama gaskiya ba.
Ta gama zuba lemon a wannan lokacin, ƙarar awarwaron dake hannunta ya janyo hankalinsa sanda take ajiyewa a gabansa daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga kan kujerar nan, don haka tayi amfani da damar don miƙewa ta bashi waje amma sai muryarta ta tsaida ta.
"Ki zauna."
Fuskarsa fayau yana kallonta kafin ya juya ya dauki wayar. Ta haɗiye wani abu a makogwaronta a hankali sannan ta dawo da baya ta zauna ɗin, nesa kaɗan dashi kamar ɗazu.
Ya ɗauki wayar yana magana ta ciki, ta fahimci da wani yake magana kuma akan harkar aikinsu ne bayan hakan bata gane komai ba, amma kuma yanayin yadda yake maganar ya saka taji zuciyarta na sakewa da amon muryar tasa. Ya gama wayar ya ajiye ta a gefensa sannan ga mamakinta taji yace.
"Faruq ne, abokina ne a wajen aiki."
Sai ta daga kanta lokacin da ya sake kai wata lomar bakinsa sannan yace.
"Abincin nan yayi daɗi sosai Amina. Kinyi kokari."
Wani abu ya matse a zuciyarta daga yadda muryarsa ta ambaci sunanta, kamar zata yi magana amma kuma sai ta sake gyada kanta kawai tana wasa da karshen mayafinta. Kuma Yanayinta yasa Ma'aruf yaji a lokaci guda yana son suyi hira, aƙalla yau maganar tasu ta tsallake babin gaisuwa saboda haka yana kallonta yace.
"Munaya ta gaya min kina son karatu, tace ta samu wasu novels a wajenki. kina da litattafai da yawa."
Sai da sakanni biyu suka wuce sannan Amina ta yarda da maganar da ya furta saboda ɗan mamakin da ya kamata, ranar da take kokarin samawa litattafanta waje ne Munayan ta shigo ta ganta, a ciki har da wasu English novels dama na Hausa wanda take tarawa tun tana makaranta, shikenan sai suka shafe kusan rabin yinin suna hirar labarai kala-kala har ta ara mata wasu ma ta tafi dasu, don haka ta tabbata a yanzun ma ganinta yayi tana karatun ɗaya daga cikin wanda ta ɗauka.
"Wanne da wanne kika karanta?"
Muryarsa tana fitowa ne kamar yadda take jinta a kullum idan yana waya ko kuma da wani, amma a yanzu da ta san cewa ita yake wa magana sai take ji ta daban, tana saka ta ƴar rikicewar da bata shirya ba. A hankali ta daurewa hakan muryarta ta shiga jero masa sunayen littattafan da ta san sunyi suna amma da yawansu yace bai san su ba saboda yawanci akan Romance ne shi kuma yace ma yafi karanta Non-fiction, yana yi yana cin abincin cike da wani abu da zata iya kira da nishadi.
"Akwai wani 'The Life we had' na san zaki san shi.'"
Ta ɗaga kanta da sauri don ji tayi kamar hakan na kaɗe tasirin da muryarsa ke yi a zuciyarta, kuma a lokaci guda bakinta ya ɓalle da wani murmushin da bata shirya masa ba tana tuno yadda akayi ta karanta littafin a wani shagon bakin titin unguwarsu inda ake sayar da shi, zuwanta shagon nan bakwai kafin ta kai karshen littafin saboda yayi mata tsadar da ba zata iya siya ba, kuma wata ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya da yawanci litattafan wajenta ma ita ta bata, itace ta dame ta zancensa, bayan sun bar makaranta ne a lokacin ita tana can Bauchi babu ta yadda zasu iya haɗuwa sai dai ta kira ta a waya tayi bata labarinsa. Tana tuna ranar da ta kai ƙarshen labarin da wani a cikin masu tsaron shagon ya gane ya tada ballin sai ta biya, da taimakon Aminu aka rufe case ɗin.
Bata sani ba ko shima murmushi yayi don kanta yana sunkuye amma taji muryarsa ta ɗan canja lokacin da yace.
"Ke ma kamar su Munaya ce ashe, ban san me marubucin littafin yayi da ya siye zuciyarku da yawa ba, babu wani abu da yake gaskiya a labarin nan."
Amina bata san sanda ta ɗago ta kalle shi ba tana girgiza kai, tace.
"Ai dama Fiction ya gaji ƙirƙire-ƙirƙire da yawa, shi yasa ya kirkiro komai ɗin don ya fito da ma'anar labarin sosai."
Ya girgiza kansa shima.
"Saboda kawai ya karya zuciyar mutane ne, shi yasa ma ya kashe su daga karshe, daga lokacin da na fahimci itama yarinyar mutuwa zata yi, na tsayar dashi ban ƙarasa kallo ba."
Sai ta sake ɗagowa ta kalle shi.
"Na zata novel ne."
Ta fada kamar tana tsoron labarin nasu zai banbanta, amma sai yayi saurin daga mata kai.
"Novel ne, amma lokacin da Munaya ta takura min da zancen labarin bani da time ɗin karatu, so sai kawai na siyo film din na kalla instead."
Ta gyada kanta sau daya sannan ta sake maida shi ƙasa ba tare da tace komai, yaji wani abu na shiga zuciyarsa yadda ta fara sakewa dashi a yanzu, don haka kai tsaye ya sake tambayarta.
"Baki kalli film din ba?" ya tambaya yana nazarin abinda bata faɗa ba akan furkar ta, kuma sai ta bashi amsar da ya riga ya sani ɗin ta hanyar daga kanta.
"Insha Allah zan kawo miki ki gani."
Sai ta ɗago ta kalle shi, yayin da hannunta ya tsaya da wasa da mayafin nata.
"Allah ya yarda."
Ta furta a hankali tana kallonsa, kuma a cikin idanun nata Ma'aruf yaga daren ya tsaya cak kafin ta sake sunkuyar da kanta a hankali, yaji wani abu yaji kamar tausayinta na bi ta kan zuciyarsa.
Tana da rayuwarta ya sani, watakila har ma da mafarkai na abubuwan da take son cimma, amma yanayin yadda auren yazo ya sani cewa yabi ta kan abubuwa da yawa a rayuwar tata, wanda da shine baya taɓa jin zai jurewa hakan, amma ita gata a zaune har tana kokarin yi masa hidima, yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaron sa a lokaci guda, a baya yana jin zai iya bin kowacce hanya don sanin meye haɗinta da Jamal amma tun a yanzu ya fara jin cewa ba zai iya yin abinda zata yi dana sanin haɗuwa dashi a rayuwarta ba.
***
Washegari da safe Hajiya Kilishi ta buɗe kofar ɓangarenta, fuskarta ta faɗaɗa da wannan murmushin nata mai armashi a duk lokacin da ta ganshi duk kuwa da cewar a jiya tayi ta kallon agogo cikin lissafin zuwansa amma bata ganshi din ba, dalilin da yasa a yau ta tashi da sassafe kenan don ta san yana da karbar magani a yau, don haka ta buɗe kofar zuciyarta na fatan ya kasance Ma'aruf ɗin ne, kuma fatan nata ya karɓu don yana tsaye a gabanta yana murmushin da take jinsa kamar ashanar dake ƙyasta zuciyarta wajen kamawa da wuta.
"Tun jiya muke kallon hanya Ma'aruf..."
Ta fada tana kallon idanunsa da kullum suke gaya mata shi daban ne a lissafinta ba sai ta rantse ba, zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da ta ganshi a gabanta irin haka.
"Mami I'm sorry, jiya aiki ne yayi min yawa kuma a gida naci abinci shi yasa baki ganni ba."
Maganar ta taho kamar wani gingimeman dutsen da ya faɗo daga kolulowar sama ya dira a tsakiyar kanta, a lokaci guda murmushin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka tsaya akansa cak a sanda ya kara wayar hannunsa a kunne ya shiga yiwa wani Benjamin magana cewa yayi wa Legal Department ɗinsu bayani su ƙarasa shiryawa kafin ya ƙaraso.
Ya katse wayar ya juyo ya kalle ta a lokaci guda da yanayin nata ya baje, fuskarta ta cakuɗe da murmushin da yasa shi gyaɗa mata kai kafin ya wuce zuwa ciki, Abinda bai sani ba shine wannan karon murmushin ba nasa bane, na halittar da take hangowa a cikin idanunta ce... Amina!
A yau an ƙaraso gaɓar da take jira, a yau tsarinta zai fara ba sai gobe ba, bata wasa da lokaci balle har tayi sake da koda ƴar mitsitsiyar dama ce... A yau Amina zata shigo cikin ukunta!
A yau duk wani mahalukin da yake da kusanci da Amina zai shigo cikin lissafinta!
**
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA SHA DAYA.
~~~~~~~
I've never fallen from quite this high
Fallin' into your ocean eyes
Those ocean eyes.
-Billie Ellish
A wannan ranar Amina na kwance daga kan gadon ɗakin tana sauraren wani shiri mai taken 'Allah ɗaya gari banban' da baya taɓa wuce ta daga cikin rediyon wayarta.
Idanunta kusan a rufe suke yayin da take sauraren maganganun mutanen dake gabatar da shirin, yau hira ake akan daya daga cikin garuruwan da take son zuwa a rayuwarta, Paris... Don haka sosai take jin daɗin duk wani bayani da baƙin da aka gaiyato suke yi na yadda garin yake da kuma tsare-tsaren su.
Sai dai duk yadda hankalinta ke kan shirin zuciyarta kuma nata zarya a can falon gidan inda ta kammala komai na abincin Ma'aruf ta ajiye

Please Login or Register in order to submit comment