Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruɗanin da ya kula dashi tun ranar da ya dawo ya same ta tana kuka, zuciyarsa ta gaya masa cewa so yake ya rungume ta har sai kayanta sun koma ƙamshin turarensa gabaɗaya, amma yayi kokarin ture zuciyar dake gaya masa hakan yace.
"Kin manta baki ɗauko basket ɗinki ba."
Ta kuwa juya ta kalli basket din dake ajiye akan kujera kamar bata san dashi ba sannan ta dawo da fuskarta wanda hakan yasa ta ƙara matsowa dab da jikinsa amma sai tayi saurin yin taku baya kaɗan kafin tace.
"Abinci ne a ciki, ban sani ba ko zamu yi magariba a hanya, kace kana azumi."
Bayan ta faɗi hakan, bata san me yake tunani ba don sai da wasu sakanni suka wuce kafin yayi magana.
"Ban san ta yaya zance miki nagode ba, amma I'm really grateful, Allah ya saka miki da alkhairi dear."
Dear, dear, dear....
Sunan da ya kasa barin zuciyarta kenan har yanzu, yake rikita zuciyarta duk sanda ta tuno duk kuwa da irin zagayen tashin hankalin da take ciki ba cewar shi kansa a yanzu bai kamata ta yarda dashi ba duk kuwa da yadda komai nasa ke nuna mata akasin haka.
"Amina..."
Muryar Amma ta dawo da ita zahiri, ta ɗago da sauri ta kalle ta, har Aminu ya gama wayar yana shan tea din data hada masa.
"Ko zaki karɓo mana maganin da za'a saka masa yau a cikin gidan, kina shiga ɗaki na farko ne wajen Malam Ibrahim ɗin."
Malam Ibrahim Mijinyawa shine ɗanuwansu Fatima mai dorin, kuma gidan nasa ba'a cikin garin Jigawan yake ba, a wani ƙauye ne dake gaba kadan mai suna Kuɗai, gida ne kato da iyalansa, amma kusan rabin dakunan gidan yana saukar marasa lafiya ne wanda ciwonsu yayi tsamari ya zama sai anyi kwanaki ukun da yake bayarwa kafin a bar wajensa, don haka inda suke ɗin dakuna ne a jere kamar asibiti, sai dai bayan su ɗin wani ɗaki ne kawai daga can gefe inda aka sauki wani yaro da nasa iyayen suma da suka zo daga Kaduna.
A jiya su biyar Amma tace mata sun zo, bayan ita da Aminun da kuma Baba, sai kuma Fatiman da ta kawo su gidan da kuma wani ɗanuwanta Yusuf da a jiyan su suka koma, dama an taho dashi ne don yayi mata rakiya tunda ita ba kwana zata yi ba.
Sai ta mike a hankali ta shiga neman inda ta ajiye mayafinta a dakin lokacin da Aminu yace.
"Anjima su Baban Kurnan zasu tafi Amma?"
"Eh, Babanku yace da sun dawo daga masallaci zasu kama hanya, su zasu tafi da waɗannan kayan da Amina ta kawo ma don mu sami sauƙi jibin."
Kalmar 'waɗannan kayan' ita ta tsaida kafafun Amina cak a inda taje, don ta san waɗanne kaya take nufi, kayan abincin da suka fito daga hannun Hajiya Kilishi.
"Wallahi matar nan tana ƙoƙari Amma, Allah dai ya saka mata da alkhairi."
Taji Aminun ya sake faɗa kuma ga mamakinta sai taji Amman tayi shiru bata ce komai ba, zuciyarta ta buga a kirjinta, ta juya da sauri a lokaci guda ta kalle ta, kanta na kasa a yanzu tana ninke wasu kayan Aminun, fata take ta fadi wani abanin tunanin sauran mutanen ko ta sami kofar da zata iya tunkararta da zancen da bata san ita ina fara ba, amma ga mamakinta sai tayi ajiyar zuciya sannan tace.
"Amin ta kyauta kam, haka Babanku ma yayi ta fada."
Sai kawai tayi saurin sunkuyawa ta damƙo mayafinta dake ƙasa sannan ta haɗiye abinda ke bakinta da karfin da zata iya kafin ta muryarta ta fito wani iri.
"Bari naje Amma."
Da haka ta tura ƙofar net ɗin ɗakin ta fita, tana jin kamar tana ɗauke da nauyin duniya ne bakiɗaya a kafaɗunta, Amma ce kadai fatanta amma ko ita bata san ta yadda zata fara gaya mata komai ɗin ba.
Abinda bata sani ba shine, idan ubangiji ya amsa addu'ar bawa, sai komai yazo masa a bazata, don wajen karfe ɗaya Aminu ya samu bacci, Baba kuma tun bayan tafiyarsu Baban kurna ya fita zuwa cikin gari. A lokacin ne Amma ta kira ta zuwa waje, kasan wata katuwar bishiya daga cikin gidan suka zauna inda aka shimfiɗa wata tsohuwar tabarma, kuma kalamanta na farko suka gutsirtsira duk wani saurin ƙarfin gwiwa da take jin cewa tana dashi na iya fuskantar wannan tashin hankalin.
"Amina a wannan zamanin mafarki baya tabbata, kin sani ba zan taɓa yarda cewa lafiya kike zaune a gidan nan ba ko?"
Lokacin da ta faɗi hakan kallonta take da ƙwallar data cika idanunta taf, amma sai ta girgiza mata kai ta cigaba da cewa.
"Ni uwa ce ina kallon abinda ya shige wannan zahirin, dukkan kalamanki da kuma abinda ke faruwa basu isa su sa in kasa hango damuwarki ba... Watakila a kwanakin baya muryarki a waya taso ta ɓoye min wani abu tunda ba ganinki nake yi ba, amma a yau kallonki kawai na yi Amina, na zaƙulo tarin abubuwan da ban sanki dasu ba fal."
Sautin muryar Amman ya fito da ɗimbin abubuwa masu yawa, masu yawan da a cikinsu babu wanda bai sake karya zuciyar Amina ba, yana tuna mata da rayuwarta ta baya data shuɗe cikin wani kankanin lokaci, lokacin da Hajiya Kilishi bata yiwa Baba wannan kiran ba balle har a fara ƙulla zaren ƙaddarar ta, lokacin da bata kirga damuwa a cikin lissafinta tana kwana tana tashi ne kawai da mafarkin abinda gobe zata haifar.
"Me suke yi miki Amina? Ki faɗa min abinda yake ƙasan wannan kyautatawar..."
Ba shiri leɓɓenta ya tale cikin kokarin yin kuka yayin da take cakuɗa yatsunta cikin juna, kuma kaf a cikin bayanin da bakinta ya fara, layi biyu ne kawai ya sa fuskar Amma haskawa da tsananin mamakin da ko na nesa zai ganshi karara, amma bayan wannan layi biyun, saurarar bayanin ƴarta tata take yi da dukkan wata nutsuwar da take da ita a duniya... Nutsuwar da take da ita ta Halimatus- Sadiyar ta, sannan nutsuwar da a cikinta ta shafe shekaru ashirin da ɗoriya a gidan aurenta ba tare da wani mahaluki a duniyar nan ya taɓa jin kanta game da mijinta ba.
Nutsuwar da a cikinta ne idan za'a taro duk mutanen da suka santa a rayuwa, ƙaryane a samu mutum guda da zai tabbatar da wani aibinta baiyananne... Nutsuwar da a cikinta wasu tarin abubuwa suka faru da idan da za'a buɗewa Hajiya Kilishi su, zata yi dana sani sau dubu na inda ta kawo kanta, zata raina duk wani tunaninta dama wayonta, zata san cewa tayi kuskure wajen amfani da ƙwaƙwalwarta wajen cimma munafunci, mugunta, yaudara har ma da zalunci.
Zata gane cewa ba an halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta fitar da da kaidi kamar yadda take taƙama ba, zata san cewa Allah ya halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta samarwa kanta duniya da kuma lahirarta a tafin hannunta kamar yadda ita tayi.
Kuma a karo na farko tun bayan tsawo lokaci wani murmushi ya suɓuce a fuskar Amman, ita ta sani ba'a banza jikinta ya bata cewar bata son kai ƴarta cikin wannan gidan ba, ashe wata halittar ce mai ɗauke da irin ƙwaƙwalwar ta a wajen, banbancin kawai shine ita waccan ƙwaƙwalwar cike take da duhu tata kuma fara ce kal!
Idan kissa da dabara Kilishi ke taƙama dashi, tazo wajen da yake daidai ita, hausawa sunce karen bana maganin zomon bana! wasan nasu ne yanzu, kowa zai yi nasa cizon da sunan ceto! Kuma Amina da Ma'aruf ɗin data zaɓa dasu za'ayi wasan! Wasan da a karshensa Sarki ɗaya zai tsaya a wani matsayi da ita ta riga ta saba dashi.
Don mutane ukun da ta ga ƙarshen makircinsu a rayuwarta, bata jin Kilishi ta ko kamo yatsan ƙafarsu, kuma kamar yadda ta nuna musu, haka zata tabbatarwa da Kilishi itama yadda cikakkiyar macen data amsa suna da matsayinta ke amfani da ƙwaƙwalwarta a bigiren da ubangiji ya halitta mata ba bigiren shaidan ba, zata nuna mata irin yadda tayi asarar nata tunanin a duniyar nan!
A hankali ta gyara zamanta sannan ta furta.
"Daga yau kar na ƙara ganin hawaye a fuskarki kamar yadda baki taɓa ganinsa a tawa ba...!"
Waɗannan kalaman su suka zama na farko da ta shiga sauke ƴarta daga raunin da ta hau kai zuwa dakakkiyar Aminarta da ta san ta baro hannunta da ƙwarin gwiwar cewa zata iya tunkarar yaƙin dake gabanta saboda mahaifinta.
Banbancin shine wannan karon zata sa ta fuskanci yaƙin ne saboda kyautatawar rayuwarta... a tafin hannunta zata ɗora mata rayuwar gidanta sannan a ɗaya tafin, zata ɗora mata Kilishi bayan sun sa ta biyo ta kan matattakalar...
'Ɗan hakin da ka raina...!
***
Haseenah Guest Inn, Jigawa.
04:30pm
"Gidan da ka dauko Hamidan zaka koma Ma'aruf, a cikin mutanen gidan na san baza a rasa wanda zai tsaya maka a matsayin shaida ba, na gaya maka kuɗi kawai zaka basu har sai kayi limiting iya wadanda kake so, don wannan ita kadai ce hanyar da nake ganin zamu bi."
Muryar Ishaq ta faɗa a cikin wayar dake kare a kunnen Ma'aruf wanda ke tsaya a barandar wani ƙayataccen Guest inn dake cikin garin na Jigawa. Hannunsa ɗaya ya zura a cikin gashin kansa kasancewar ya cire hular kansa ya baro ta a cikin mota.
"Na gaya maka babu shaidar da zan gabatar Ishaq, ka barsu suyi dukkan abinda zasu yi, I have my ways akanta ita Ruƙayyan ita ta sani."
"Ka shirya faɗuwa kenan tunda ka san kotu ita da shaidu take dogaro ko?"
Ya cije leɓɓensa kaɗan.
"Ko hakan ne zai faru let them Ishaq, na san abinda zanyi. Kar ka tanadi komai kawai ka cigaba da harkokin ka, Allah ya kaimu ranar."
Da haka suka yi sallama a wayar da wataƙila itace ta huɗu tsakaninsu a yau kaɗai, ya kashe wayar daidai lokacin da wani ma'aikacin Guest inn ɗin ya ƙaraso inda yake.
"Yawwa yallaɓai, gashi an kammala komai."
Cewar matashin yana miƙo masa wani muƙulli.
"Nagode sosai."
Ya faɗa da murmushi yana karbar muƙullin ya zura a aljihunsa, kuma a cikin wayar tasa ya sake nemo nambar Hajiya Kilishi.
A wanna lokacin Hajiya Kilishi na ɗakin Baffa wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi zuwa Kaduna, shayinsa take ƙoƙarin hada masa yayin dashi kuma yake daga can kan kujera yana shafa man robb akan kafarsa don fitowarsa daga wanka kenan a lokacin.
Fuskarta ɗauke da faffaɗan murmushi ta ɗaga wayar tana fadin.
"Mai gaskiya na, kun taho ne?"
Ma'aruf ya girgiza kansa lokacin da yake tafiya wajen motarsa.
"A'ah Mami, yamma tayi sosai, so zamu kwana ne sai gobe, yanzu ma zanje in dauko ta daga can."
A lokaci guda irin wannan shirun dake biyo bayan walƙiya bayan haskawarta kuma kafin zuwan tsawa ya ratsa ƙwaƙwalwar Hajiya Kilishi da ta tsaya daga kokarin ɗebo madarar da take yi tana jinsa.
Biyu kenan! Sau biyu kenan a jere Ma'aruf ya yanke irin wannan hukuncin ba tare da tuntubarta ba, na farko tafiyar tasu zuwa Jigawan da kai tsaye yazo yake gaya mata tare da kowa, a yanzu kuma kwanansu a garin? Me yake shirin faruwa ne?
Ta girgiza kanta a fili lokacin da shi yake cigaba da gaya mata wani sabon labari na cewar baya son tuƙin dare ne, ba sai wani satin ba kamar yadda ta tsarawa Awwalu, a gobe ko jibin nan Ma'aruf zai sake komawa cikin ciwonsa. Ba ta yin saken da abubuwa ke cakuɗe mata, dole ne ta kwantar dashi don ta fahimci duk abubuwan data gano cewa suna ɗagewa daga cikin tsarinta.
Wani abu da bata sani ba shine, abubuwa ma basu fara ɗagewa ba ko kaɗan!
***
Kun fahimci cewa kowa ya shirya a wannan Babin??😅😅
To su waye zasu yi nasara? su waye zasu fara su kasa? Su waye kuma zasu faɗi kasa wanwar??
Me kuke tunani game da Amma da kuma ƙudirinta?😀
Kar ku manta kuma, zamu yi kwanan Jigawa....😍😆😆
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.

BABI NA SHA BIYAR.
~~~~~~~
This could be the start of something new.
-High School Musical
"Ina zamu je?"
Aminah ta tambaya lokacin da Ma'aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta miƙewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar.
"Wani waje." Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba.
Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruɗanin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa.
"Nayi zaton gida zamu tafi."
Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saɓanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure.
"Dare yayi kuna bana son tuƙin dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna."
Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haɗiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ƙasa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta roƙe shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya ɗauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma.
Amma duk da haka sai taji wani ɓangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take ɗauke dashi a ɗazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al'amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ƙara buɗe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaɗaya ita bata hango su ba.
Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma'anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ƙarfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ƙofar nasarar su.
"Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buɗe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faɗa akwai sauran ƙurar da dole na san ta lulluɓe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bunƙasar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba..."
Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ƙara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama'a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ƙara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu'a.
Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taɓa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma'aruf game da ita ba, don haka ba zata taɓa iya ɗorar da komai ba a wannan fannin.
Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buɗe su tana ƙoƙarin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ƙarfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take taƙama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata ɓullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan.
"Kilishi bata fi kowacce mace ba a duniyar nan Amina, yadda take takama da wayo da kuma dabararta, haka Allah ya halittawa ƙwaƙwalwar dukkan mata don ita mace uwa ce, an halicci mutane da yawa da zasu rayu a ƙarƙashinta wanda kowanne da irin ƙalubalen rayuwarsa, shi yasa Allah ya buɗe ƙwaƙwalwarta ta yadda zata iya samar da mafita kala-kala a fannin rayuwa.
Wasu matan basa gane hakan ne har suyi yunƙurin sanin abinda zasu iya, matan kuwa da kika ga suna zaune lafiya tare da mazajensu ƴaƴansu harma da duk wanda zai raɓe su, sune wanda suka iya buɗe wannan baiwar tasu, Mata irin Kilishi kuma sune wanda suke amfani da wannan baiwar ta hanya mai munin da har suke ganin cewa sun fi kowa.
Yanzu girma yazo kanki da gaske Amina, kin fara ganin hakan tun daga ranar da kika bar karƙashinmu, kuma hausawa sun ce aure yakin mata, yaki ne da kowacce mace akwai kalar nata, don haka kema dole ne ki bude ƙwaƙwalwar ki, ki karɓi wannan girman sannan ki fuskanci naki yaƙin Amina..."
A daidai wannan lokacin suka shigo harabar wani haddadden gini mai tarin fitulun dake ta haske suna maraba da daren da bai kai ga ƙarasowa ba. Ma'aruf ya tsayar da motar a jerin motocin dake tsaye a wajen daidai lokacin da idonta ya zare akan sunan wajen.
Haseenah Guest Inn.
***
"Mene ne total charges for Adjustment and Uncollectables?"
Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar da yake yi daga cikin dakin, yana zaune ne akan wani dan karamin dining table dake can karshen dakin yayin da hannunsa ke rubutu a cikin notepad din dake kan teburin. Kayan jikinsa wata loose T-shirt ce da ya siyo da kuma wani gajeran wando kalar grey.
"Next..."
Ya sake faɗa bayan mai maganar na ciki ya gaya masa wani adadi da ya rubuta a cikin wayar.
"Ka gaya min Net Patient Revenue din?"
"Na gaya maka yallabai, shine na biyu bayan total charges na Patient Care gabaɗaya."
Mai maganar daga cikin wayar ya fada, sai ya gyada kansa yana bude shafin baya, ya karanta abinda ya rubuta sannan ya sake dawowa inda yake yace.
"Operating Expenses din fa?"
Mutumin na ciki ya sake faɗo masa wani adadi da ya shifa rubutawa.
"Sannan sir akwai Bad debts ɗin wancan..."
"Sai kuma Natural Expense ɗin?"
Ya katse shi ba tare da ya saurari abinda yake cewa ba, mutumin ya ɗanyi shiru kafin ya faɗo wani adadi na makudan kudin da saida Ma'aruf ya jinkirta kadan yana saurarar sa kafin ya rubuta.
"Yallaɓai ka saurare ni akan zancen bashin nan, bamu da wata hanya ne dole..."
"Just tell me the total Sadiq." (Kawai ka gaya min jimlar komai gabadaya Sadiq.)
Muryarsa ta fito a hankalin da take tun bayan sallar magariba da yayi buda baki.
"Wallahi yallabai zai fi kyau ka duba Report ɗin gaba ɗaya tukunna gabadaya 42 pages ne, idan ka karanta komai you will realize that..."
"Ka gaya min total din kawai Sadiq."
Yadda sautin muryar tasa ta fito wannan karon ita tasa Sadiq din sarewa daga dukkan ƙokarin da yake fanin zai iya shawo kansa, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya fadi wasu makudan kudade da shi kansa Ma'aruf ɗin ya sani idan za'a bincike account dinsa na bankuna tsaf a tattaro komai baza 'a taba samun wannan adadin ba, don haka bai ma rubuta ba, wani guntun murmushi ne ya suɓuce a lebbensa yayin da yayi baya ya jingina da kujerar da yake kai yana kallon gabansa tamkar Sadiq ɗin ne a wajen.
"Wallahi yallabai..."
"Sadiq"
Ya katse shi, sautin muryarsa can ƙasa amma kuma a kausashe.
"A rufe asibitin, a tsayar da komai, kwana kaɗan na baku, I'm coming in few days, ku san yadda zaku gyara wannan abin in a reasonable way kafin zuwa na. Idan ba haka ba, na rantse da Allah wasu ne zasu ci muku abinda kuka ɗiba ba ku ba, and just dare me and see.!"
Yana faɗin haka ya kashe wayar, ya cilla ta kan teburin da karfi har sai da screenguard ɗin dake kanta yayi wata katuwar tsaga guda daya, sannan ya cusa hannayensa duka biyu a cikin gashinsa yana ƙoƙarin saita numfashinsa, ransa ne yake shirin baci ya sani, amma yana kokati da dukkan iyawarsa ya danne hakan kamar yadda ya saba yanzu a kwanakin nan. Bakinsa ya shiga karanto hasbunallahu wa ni'imal walkil daidai lokacin da kofar toilet din dakin daga can gefe ta buɗe bayan abinda zai iya kira aƙalla minti talatin.
Ya sauke hannayensa daga fuskarsa kafin ya juyo ya kalle ta, tana tsaye daga kofar kamar zata koma ciki ne ta sake rufewa, babu shiri yaji dukkan abinda ke cikin kansa na sulalewa yana bin iska, rigar da ya siyo ita ta saka, kusan iri daya ce da wadda ya taɓa gani ta saka a gida ranar da tashi cikin daren nan, me tsawo daga baya amma ta gaba kuma iya gwiwa take kawai, kuma yadda idanunsa suka riƙe hoton siraran kafafunta a wancan lokacin shi yasa kai tsaye yace a mayar da wanda ya ɗauko a ciro masa ita.
Daga yanayinta kawai ya san ta saka ne don bata da wani zaɓi, tunda wani mai wanki da guga na Hotel ɗin yasa yazo ya karɓi kayansu don ya wanke zuwa gobe, idanunsa kallonta kawai suke tun daga nan, ta yafa bakin mayafinta da bata bayar dashi ba akanta amma duk da haka gashinta na fitowa kamar ɗazu da safe.
Daga inda Amina take tsaye, cakuɗa yatsunta kawai take yi cikin junansu saboda rawar da hannayenta ke yi musamman a yanzu da take ƙara ganin wautarta na fitowa a haka, amma ya zata yi, har tawul a cikin toilet din ta ɗauko ta ɗaura taga abin bai dace ba ta cire shi.
A ajiye ma zancen ƙafafunta dake waje a gefe, tunda take bata taɓa lissafawa cewa zata yi kwanan hotel a rayuwarta ba idan har ba wai Makkah ko wata kasar taje ba, wanda shima ba'a irin wannan yanayin take hango shi ba, shi yasa tun da suka shigo zuciyarta ke rabewa gida biyu tana sake haɗewar da har a yanzu ta kasa samun sauƙi duk kuwa da ƙarfin halin da ta tattaro a ranta.
Ganin yadda yake kallonta yasa ta juya da sauri ta ƙarasa jawo ƙofar toilet ɗin ta rufe sannan ta shiga tahowa cikin ɗakin. Wani abu ya zarce maƙogwaron Ma'aruf da yake kallonta tana tahowa sai mutstsika yatsunta take yi cikin junansu yayin da siraran ƙafafun nata ke tafiya.
Tare da Ruƙayya yasha tambayar kansa meye babban interest dinsa game da mace, sai dai a lokacin ya kasa tsaida zuciyarsa akan komai banda kyawunta don ita ɗin kyakkyawa ce, amma a yanzu ya samu wannan amsar da ya daɗe yana nema, don yadda zuciyarsa ke sake ɗaukan hoton ƙafafun Amina tana masa kyakkyawar ajiya, a wani yanayi ne da wataƙila ko bayan ransa ba zai manta ba.
Ta ƙaraso kamar mara gaskiya ta wuce shi ta nufi wajen wani ɗan ƙaramin table da ma'aikatan wajen suka kawo musu abinci kamar yadda ya basu umarni.
Kuma sai a sannan tayi magana, tun bayan da suka idar da sallar isha da ya bata wayarsa ta sake kiran mahaifiyarta ta shaida mata cewa basu bar garin ba sai gobe tukunna.
"Wanne abincin zan zubo maka?"
Yaji ta tambaya daga bayansa inda taje ta tsaya, sai kawai ya ture komai a ransa ya taso ya taho inda take, ta juya bayan nata kamar yadda ya zata tana ƙoƙarin buɗe plates ɗin masu wasu irin manyan-manyan murafe kamar na abincin sarakai, a hankali ƙafafunsa suka tako ta kan carpet ɗin dake shimfide a wajen ya ƙaraso ya tsaya dab da bayan nata idanunsa na nazarin ɗan karamin jikinta dama siraran hannunta, bayan haka tsawonta ma gabadaya iya kafaɗarsa ne, ya san yana da tsawo don shi da Jamal ana cewa duk tsawon Hajiya Maimuna suka yi, amma bai taɓa tsayawa yayi nazarin yadda yafi wani tsawo irin haka ba sai akanta, don ko Ruƙayya ya sani ne cewa da kaɗan yafi ta.
Kuma wataƙila shirun da yayi ne yasa ta juyowa a hankali hannunta rike da murfin da ta ɗauko guda ɗaya, idonsa ya sake kaiwa kan kafafunta a yanzu data juyo,

Please Login or Register in order to submit comment