Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni anan... so ba zaka damu ba idan naci wadannan kafin yazo, don bani da komai a jiki na yanzu amma ina tabbatar maka shi zai biya ka idan yazo...)
Mutumin ya saka hannunsa ya danne kayan da yake shirin ɗiba, sannan da sautin muryarsa da yafi kauri a yanzu ya sake maimaita masa adadin kudin.
"24 dollors." (Dubu goma.)
Har ya haƙura ya ɗauke hannunsa yana shirin juyawa sai kawai mutumin dake tsaye a bayansa yace.
"You're holding up the line, man! If you can't pay just leave."
(Malam kana riƙe mana layi, idan baza ka iya biya ba ba ka bar wajen mana.)
A sakannin da mutumin ya rufe bakinsa, a sakannin wani irin naushi ya ziyarci fuskarsa, naushin da ya kusan kaishi har kasa, ya ɗago jini na fara zuba ta hancinsa lokacin da wata mata a gefensu ta ƙwalla ƙara shi kuma ya furta kalmar zagi yana share jinin, kuma baiyi wata-wata ba ya nufo kansa da nasa naushin shima dsya haddasa fada a tsakaninsu ba shiri, kuma kowannensu yaji lokacin da mai kantin ya kwalla ƙara yana faɗin.
"Someone should call the police!" (Wani ya kira ƴan sanda!)
****
British Transport Police Station
No. 2 Melton St, London NW1 2BW, United Kingdom.
"Kun tabbata dukkan waɗannan bayanan file ɗin gaskiya ne?"
Ɗan sandan ya tambaya daga tsallaken teburin da Ishaq ke zaune tare da wani ma'aikacin asibiti a gefensa.
"Da gaske muke ranka ya dade, mara lafiya ne ya fito ba tare da an sallame shi ba, kuma a yanzu haka ma ba'a hayyacinsa yake ba."
Ɗan sandan ya kalli ma'akacin asibitin da yayi magana, ya kara kallon ID Card ɗinsa da ya mika masa sannan ya gyada kansa yana sake kallon cikin file ɗin.
"Naga dukkan wasu bayanai na cewar yana da matsalar kwakwalwa, amma banga wani bayani ko sau daya na abinda ciwon ke saka shi ba..."
"Ai da yake yallabai, mu a asibiti cutar kawai muke bayani ba abinda zata haifar ba."
Jin haka yasa Ɗan sandan ya dawo da hankalinsa ga Ishaq dake zaune yana kallon can gefe inda aka ƙulle tarin mutane a cikin wani budadden cell da aka zagaye da karafa kawai.
"Kai ɗanuwansa ne ko? Zaka iya gaya mana abubuwan da yake yi, don mu san cewa ba da gangan yayi abinda muka kama shi yanzu ba?"
Ishaq ya gyara zamansa bayan ya dawo da hankalinsa nan, sannan cikin harshen turanci shima yace.
"Yayi abubuwa da yawa yallaɓai, waɗanda suka fi wannan ma, ba tun yanzu ba..."
"Misali..." Ɗan sandan ya katse shi. "Misali zaka bani ba wani bayani ba."
Jin haka yasa Ishaq haɗiye yawu ba shiri, ya juya ya sake kallon idanun da suke kallonsa daga cikin cell ɗin sannan ya gyara zamansa kaɗan, muryarsa can kasa yace.
"Yallabai, a karo na ƙarshe da ciwonsa ya tashi saura kaɗan yayi kisan kai."
Idanun ɗan sandan basu canja ba, ya cigaba da kallonsa na wasu sakanni kawai kafin ya gyaɗa kai, sannan ya nuna file din dake hannunsa.
"Zan baku belinsa ne yanzu saboda wannan kawai, amma ku tabbatar bai sake barin asibitin nan ba sai da cikakkiyar lafiyarsa. Idan ba haka ba idan muka sake kama shi, mu zamu riƙe shi har sai ya warke."
Dukkaninsu suka gyada kai alamun sun fahimta kafin ya juya ya kira wani ɗan sanda dake ƙoƙarin wucewa.
"Stone! bring the Black one out." (Stone! Fito da baƙin cikinsu.)
Stone ɗin baya bukatar wani karin bayani don wanda aka nuna masa shi kaɗai ne baƙi a cikin tarin turawan cell din, don haka ya zaro muƙullai daga jikinsa ya nufi wajen.
Ɗan sandan ya sake kallon file ɗin hannunsa a karo na ƙarshe, idanunsa suka sauka akan sunan dake rubuce a jiki.
Ma'aruf Mansour Bakori!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA BIYU.
~~~~
"Kowanne ɗan adam yana da tarin ƙalubale a rayuwarsa, amma ga wanda suke da cutar 'Bipola disoder' nasu ƙalubalen daban ne. Bipola disoder cutar ƙwaƙwalwa ce dake canja yanayin mutum a lokaci guda, ta canja ƙarfinsa, yanayin tunaninsa har da ɗabi'arsa. Cuta ce dake iya taba rayuwar mutum ta bangaren aikinsa, karatu, zamantakewa har ma ta iya dakushewa mutum hanyar cigaba a rayuwarsa, don tana yawan tashi ne akai-akai.
Cutar tana farawa ne daga lokacin ƙuruciya, kuma duk da cewar babu takamaimai maganinta ana samun saukinta ko kuma ƙaruwarta idan har ba'a bin ƙaidojin magani daidai. Tana da matakai huɗu kuma na ƙarshen da ake kira da "Mania" shi yafi kowanne hatsari.
A matakin 'Mania' mara lafiya yana jin tsananin ƙarfi da jin cewa zai iya komai, da kuma tsananin fushi da yawan tunanin abubuwa barkatai, wanda ke jawo mutum ya harzuƙa ta yadda babu mai iyawa dashi, mara lafiyar yana samun ƙarancin bacci da kuma rashin nutsuwa sannan wasu ƙwaƙwalwar su tana buɗewa ta yadda za su yi abinda idan a lafiyarsu ne baza su iya ba. Matakin dake bi wa wannan kuma shine 'HypoMania'...."
Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga wata Tv dake kafe a saman harabar wajen, ƙaton wajen jira ne na asibiti inda tarin ma'aikata ke wucewa wajen wasu gadaje daga can baya da aka kwantar da marasa lafiya, labulayen da aka sassaka a tsakanin kowanne gado sune kadai abinda ya raba gadajen.
Bayanin dake fitowa daga Tvn, na irin rashin lafiyar ƙwaƙwalwar da ake dubawa a wannan ɓangaren asibitin ne, masu jiran kuma na zaune suna saurarar bayanan da ake yi mai dauke da hotuna don sauƙin fahimta ga marasa lafiyar da kuma masu jinyar, Ishaq yana ɗaya daga cikin masu jiran, yana zaune daga karshen kujerar kamar mai jiran ƙiris! Ya mike, kafarsa ta bangaren dama yake faman bubbugawa yayin da gefen bakinsa yake a cije.
A bayyane yake ga duk wanda ya kalle shi cewa jira kawai yake likitocin dake tsaye a wajen gadon ɗan'uwansa su fito daga bayan labulen da aka zagaye gadon dashi. Sun taru kusan su bakwai a ciki har da Nurses don hankalinsu ya tashi jin cewar daga police station aka taho dashi bayan an neme shi an rasa.
Ya sani cewar dukkaninsu tsoro suke yi game da ciwonsa, don Ma'aruf ya riga ya kai mataki na karshe a ciwon ƙwaƙwalwar tasa, ya riga ya kƙure komai a Bipolar Disoder, don idan har akwai wani mutum a duniya da baya taimakon kansa to Ma'aruf ne. A shekaru goma da cutar nan ta same shi babu irin fadi tashin da ba'ayi ba daga kowanne ɓangare na iyaye da kuma ƴanuwansa amma rashin tasa tallafawar ya haɓɓaka ciwon har sai da ya ƙaraso matakin ƙarshe, 'Mania Stage'.
A baya bai fi ƴan awanni ko kwana ɗaya zuwa biyu ba yake yi idan ciwon ya taso masa, amma a yanzu sati guda cur, har suka zo ƙasar nan Ma'aruf ba'a hankali sa yake ba, hakan yasa dole aka kwantar dashi a asibitin da alluran bacci wanda suka taimaka, ya farka cikin hayyacinsa yanzu.
Don duk da cewar a police station suka je suka same shi, idanunsa kawai ya kalla ya san cewar ya dawo hayyacinsa tun kafin likitocin ma su gane, shi yasa ya matsu da fitowarsu a yanzu don yaje ya same shi, ya sauke maganganun dake zuciyarsa tun daga ranar da Mami ta kira shi muryar ta na rawa taje ya taho gida Ma'aruf ya shigo musu da gawar wani.
Likitocin duka fito a daidai wannan lokacin, kuma bai tsaya jiran komai ba ya zagaya ta ɗaya hanyar da wandanda ba ma'aikata ba ke wucewa ya nufi wajen gadon.
"Minti biyar! minti biyar kawai na fita Ma'aruf amma kayi tsalle daga asibitin nan zuwa police station!"
Ya faɗi hakan da harshen hausa daidai sanda ya bankaɗa labulen da aka zagaye gadon. Dama abinda Ma'aruf ɗin yake jira kenan, ya riga ya sani cewar ya daɗe a waje yana kaɗa ƙafa yana jira likitocin su fita ya shigo da tarin ƙorafinsa, don haka hankalinsa a kwance ya ɗago da idanunsa ya kalle shi.
"Kaima sani bana iya rike yunwa, na tafi in samu abinda zanci ne and you left me with nothing, ba dole su kaini police station ba."
Ishaq ya girgiza kansa.
"Ma'aruf ba a Nigeria muke ba, ko baka gane bane da ka farka? me kake tunani idan suka kama ka a ƙasar nan?"
Maimakon ya bashi amsa kai tsaye, sai ya koma da baya a jikin gadon, ya zura hannayensa duka biyu cikin gashin kansa sannan yace.
"Na sha gaya maka kana damuwa da yawa Ishaq, kana damuwa akan abubuwan da suke faruwa dama wanda basu zo ba."
"Kuma matsalar kenan, kai da baka damuwar, baka damuwa da kanka balle kuma na kusa da kai, shi yasa har muka zo wannan matakin Ma'aruf! Mania!"
Ya faɗi sunan mataki na karshe a cutar da Ma'aruf ɗin ke fuskanta, kuma ga mamakinsa, a lokaci guda Ma'aruf ɗin ya juyo ya kalle shi, sannan a cikin sakan biyu idanunsa suka haska da wani abu da Ishaq ɗin zai rantse da ubangijin dake busa musu numfashi cewar bai taba gani a idanunsa ba. Tsoro da kuma fargaba! Sai kawai ya girgiza kansa sannan ya cigaba da faɗin.
"Shekara biyu da suka wuce a asibitin nan ko HypoMania test ɗinka basu kai ba, baka da lafiya amma babu wanda ya sani babu mai ganewa, muna ɓoye komai daki-daki don rayuwarka ta tafi daidai. Amma yanzu ka gaya min me kayi kafin mu taho nan Ma'aruf? Daniel ka yiwa dukan da har ya suma akan baiyi maka submitting takardu a office ba, ka dake shi har ya suma Ma'aruf sannan ka sako shi a mota ka kaishi gida, ka shiga dashi har falon Baffa kana gaya masa wai ka kawo shi ya kore shi daga aiki!" (Mahaifinsa.)
Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da ɗaukacin jama'ar da suka sanka, waye bai san kana fama da ciwon ƙwaƙwalwa ba Ma'aruf?
Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da duk ɗaukacin kewayen da mutane suka sanka, waye a yanzu bai san cewa kana fama da matsala a ƙwaƙwalwa ba? Waye bai san cewa kana da wannan nakasar ba Ma'aruf?"
Muryar Ishaq ɗagawa take a lokacin da yake fadar hakan, sautin ta na fitowa cike da wani irin daci da takaicin duk abubuwan da yake faɗa din, kuma har a lokacin yana ganin adadin kifta idanun da Ma'aruf ke yi alamun cewa kowacce kalma tana bada ma'anar da yake son ya gane a ƙwaƙwalwar sa. Bai ce komai ba ya cigaba.
"Ka san me ya fitar dani ɗazu? Ka san abinda yasa na bar ɗakin har kaje ka aikata abinda kayi?..."
Ya tambaya kamar yana jiran ya bashi amsa.
"... Office din likitan ka naje, shi ya kira ni personally Ma'aruf! Yayi min dukkan bayanin halin da kake ciki, kuma albishirin ka abinda kake so zai faru, idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf! Kana gab da rasa komai gabaɗaya..."
"And so what idan na rasa?!"
Yadda Ma'aruf ɗin ya katse shi a lokaci guda da tasa sautin muryar ya bashi mamakin da har sai da ya haska a idanunsa. Kallonsa yake har a lokacin da nasa idanun da suka canja, yanayinsu na kara lumshewa kamar kodayaushe idan yana cikin ɓacin rai.
"Nace sai me idan na rasa komai? Idan dai har ragowar lokacin da nake dashi zai bani dama na iya cimma abinda ke gabana sai me idan na rasa hankalina?"
Sai ya girgiza kansa kawai yana cigaba da kallonsa.
"Nasha gaya maka Ma'aruf ya mutu shekaru goma da suka wuce Ishaq, kaƙi ka yarda dani ne, amma Ma'aruf ya riga mutu, babu shi anan."
Ya ƙarasa yana nuna ƙirjinsa, daidai lokacin da labulen dakin ya buɗe, wani bature ya leƙo fuskarsa a murtuƙe yace.
"What the in the world are you two talking abou..."
Bai karasa ba sakamakon kallon da su duka biyun suka juyo suna yi masa kowanne ransa a ɓace, sai kawai yayi sauri ya maida labulen ya juya, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya alokaci guda.
Shiru ya ratsa wucewar sakan ɗaya, biyu, uku... kafin Ishaq ya ƙaraso a hankali ya zauna a gefen sa.
"Kwana na nawa a asibitin nan?"
Ma'aruf ya katse shirun da sautin muryarsa da ya koma daidai, mai zurfi dake fitowa can kasa.
"Huɗu, you were unconscious for three days a Nigeria kafin mu taho."
A hankali ya haɗiye yawu cikin maƙogwaronsa sannan ya ƙara tambaya.
"Me Baffa yace?"
"Ransa ya ɓaci sosai, ransa ya ɓaci fiye da duk yadda kake tunani, kullum sai ya kira waya ya tambaya idan ka farka, kuma yace da zarar ka dawo hayyacinka mu koma gida."
Yaji lokacin da ya zuƙi numfashi ya fitar sannan ya koma da baya ya jingina da gadon bai ce komai ba, don haka shi ya cigaba da cewa.
"Mami kusan duk bayan awa guda take kira Ma'aruf, suna can ne amma hankalinsu anan yake, kowa ya damu, Hajiya tace hatta Abdurrahim jiya gidanka ya tafi ya kwana, dan Allah Ma'aruf, dan Allah ka taimaka ko don waɗannan mutanen ka tallafi rayuwarka, dan Allah."
Kai tsaye maganganun suka shiga har wani waje dake can ƙasan zuciyar Ma'aruf, kuma yana jin yadda tasirin su ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinsa yana tafiya tare da gudun jinin cikinsu, sai kawai ya sake cusa yatsunsa cikin gashin kansa sannan ya runtse idanunsa.
Ishaq yana kallonsa, yana jin yadda tausayinsa ke bin zuciyarsa kamar kullum, ba sauki bane rayuwa da irin wannan cutar ya sani, ba sauki bane daurewa irin abinda ke zuciyar Ma'aruf din, ba sauki bane yadda yake iya daurewa abubuwa tsawon shekarun nan, ba sauki bane ba zama Ma'aruf din da yake gabaɗaya ya sani... Shi yasa fatansa a kodayaushe bai wuce Allah ya tallafi rayuwarsa ta wata hanya daban da take sabuwa ba, domin Allahn ya sani cewa su sun gwada duk wata hanyar da take a tunaninsu amma babu wani sauki.
Ya haɗiye yawu a hankali cikin maƙogwaron sa yana cigaba da kallonsa yace.
"Nayi mana booking flight, gobe zamu koma."
Kuma ba don kallonsa yake ba ya tabbata ba zai ji sanda ya amsa da 'Allah ya kaimu' ba.
Saboda haka kai tsaye sai ya sake tambaya.
"Yaya kake ji?"
Ma'aruf yasa yatsu biyu ya shafo saman hancinsa har a lokacin bai buɗe idonsa ba yace.
"Ina ji ne kamar zan mutu saboda yunwa, nace ka taimaka min da abinci amma kana ta masifa, Idan na sake fita daga nan kar barni kawai kar kaje beli na."
Ba shiri wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskar Ishaq ɗin na tabbas ɗin da yake dashi cewar ya dawo daidai, don har abada irin Ma'aruf guda daya ya sani a duk tsayin rayuwarsa.
Ma'aruf yaji lokacin da ya fita amma duk da haka bai bude idanunsa ba, hoto ɗaya ne ke yawo a cikin kansa, hoton ɗakin bincikensa, yana hasko tarin takardu da kuma hotunan da suke cikin ɗakin nan, sannan yana hasko yadda hanya ta ƙarshe da yake tunanin zata kai shi ga nasara bayan shekaru huɗu ta rushe har garinta, wanda takaicin haka shine sanadiyar tashin ciwon nasa da abinda yayi har suka taho nan.
Wata jijiya daga gefen kansa ta bullutso cike da wani sabon takaicin da ya sake ratsa shi, sabon takaici... Don wannan ɗauke yake da wani layi na fargaba da kuma tsoro, tsoron da bai taba ji a ransa game da ciwon nasa ba tsawon shekaru goma da suka wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa.
...idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf!
***
Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi a garin Kano tare da ƙaninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da daɗewa amma mahaifiyar su tana raye.
Alhaji Mansour Bakori yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha ɗaya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa ba tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ƙalau.
Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya, ɗanta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma'aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra.
Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don faɗa ko da na rana guda bai taɓa haɗa su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu kaɗai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su ɗin kishiyoyin juna bane idan ya gansu tare.
Ita ta raini Ma'aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta karɓe sshi bata ƙara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma'aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da ɗa ke samu daga mahaifiyarsa.
Ita ta raine shi da ƙarfin jikinta da kuma na zuciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai nasa, duk da ƴadda wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin daɗin su akan hakan a yanzu da ya zama shine kaɗai namiji babba a gidan.
Ƴaƴan Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da raɗin suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba shi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo 'Fatima' kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka.
Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ƙafafu bayan ta haifi ƴarta ta ƙarshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba'ayi ba a ƙasashe daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo.
Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ƙaton gida ne mai ɗauke da bangare-bangare, akwai ɓangaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ƙaton falo da ɗakuna hudu kowanne da banɗakinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai ɗauke da ɗakuna biyu da falo da kuma wajen meeting ɗinsa inda yake ganin baƙi a gida.
Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ƙaton falo, ɗaki ɗaya da kuma toilet, sai ɓangaren ƴan aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen hagu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu kaɗan ya koma, don haka wajen a ƙulle yake babu kowa.
Ishaq abokin Ma'aruf ne kuma ɗan'uwansa, don da Mahaifiyar Ishaq ɗin da Hajiya Maimuna iyayensu ɗaya, asalin mahaifinsa ɗan Kaduna ne kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya daɗe da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami'a ne sannan Allah ya ɗauki ranta, don haka da shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma'aruf ke kokarin shiga Jami'a.
Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma'aruf sauki akan halin alhinin ɗanuwansa da har a lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq ɗin Baffa ya ɗauki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar ɓangare daban-daban suka karanta. Ma'aruf ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci ɓangaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro.
***
Washegari...
No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Qauters.
.07:30 Pm.
Tun daga ƙofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gidan an watse, don hatta gate din a bude yake gabaɗaya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa.
Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko'ina hanya ta kai ka har ɓangaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ƙaton falon ɓangaren da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gabaɗayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ƙamshin turarukansu ya haɗe da ƙamshin daddaɗan abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma a can gaban Tv stand na ɗakin akwai wasu manya-manyan flasks cike da snacks kala-kala ga duk wanda yake so ya diba.
Sai dai duk wannan ba shine abin kallo a dakin ba, tarin akwatunan dake zube a makeken carpet din tsakiyar falon ne, an buɗe kowannensu dake cike da kaya fal.
Lefen Babbar ƴar Hajiya Maimunan mace da suke kira da Shukra ne, amma ba zaka banbance adadin yawan ƴanuwan Hajiya Maimunan ko kuma na Hajiya Kilishi a falon ba, sun riga sun zama ɗaya dukkanninsu don ko a sati biyu da aka karbi lefe biyu na ƴaƴan Hajiya Kilishin Safiyya da Salma, duk sune dai a wajen, shi yasa a yanzu ma rabi hirarsu ta shirye-shiryen bikin da aka saka nan da wata guda mai zuwa ce.
Hajiya Kilishi ta ratso ta cikin mutanen, sanye take da wata doguwar rigar lace daya sha adon stones sai wulgawar kyalli yake a cikin hasken fitulun dakin, ta karaso inda Hajiya Maimuna ke zaune akan kujerar Wheelchair dinta tana hira da wata ƴaruwarta, ta sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan tace.
"Hajiya su Ma'aruf sun iso, yanzu na tura Malam Sani (direba) ya ɗauko su daga airpot, mukullin store dinki zan karba na ajiyemusu abinci ɗazu, Hajiya Madina ce tace zata tafi nace idan direban nata ya sauke ta sai ya karasa ya kai musu abinci don na san baxa su shigo yau ba."
"Toh Alhamdlilah, Muƙullin yana hannun Sameera ita ta karba dazu wai sun ajiyewa ƙawayenta abinci su ma."
Hajiya Maimunan ta amsa a hankali itama. Dukkaninsu sun sani cewa a duk tarin jama'ar gidan babu wanda bai san abinda Ma'aruf ɗin yayi ba da kuma cewar baya ƙasar don labari baya taba ɓuya, amma duk da haka gwara ace basu fallasa zancen ba duk kuwa da cewar duk ƴanuwa ne a gidan, amma hakan ba zai hana cece-kuce ba.
Daga nan ɓangarenta ta nufa, inda babu mutane sosai, kuma ƴanmatan gidan da wasu kawayensu suka tare suna ta hayaniyar da jiran a ragu don suma suje su buɗe nasu babin kallon kayan. A falo ta tarar da Zahra da Sahla ƴan autan gidan kuma sa'annin juna sun baje litattafansu suna ta aiki kamar basu san da bidirin da ake yi a gidan ba, dama yayyensu sun riga sun manna musu sunan Allazi boko 1 da kuma Allazi boko 2, don mayun karatu ne kamar ba gobe, yanzu suka shiga SS1 amma abinda suka sani ko Abdurrahim da yake SS3 bai sani ba, kwanaki har Surayya dake level three suka koyawa wani abu a Biology.
Har Hajiya Kilishin zata yi musu maganar abinci sai ta kula da plate din snacks dake tsakiyar litattafansu, ta sana aikin Mama Rabi ne hakan, wata dattijuwa ma'aikaciyar gidan da har yanzu bata daina kula dasu ba kasancewar ita ta yaye su tun suna ƙanana.
Don haka ta amsa sannu da shigowar da suka yi mata kawai ta wuce. Ta nufi kofar dakinsu Salma inda ƴanmatan suke, hayaniyarsu tun daga falon zaka ji ta, cike da raha da kuma nishadi kamar an fara bikin, kuma duka hirar da suke ta tsare-tsaren bikin ce da suka daɗe suna yi tunda wannan shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidan, kuma har guda uku a lokaci guda.
"A'a ranar kunshi ne fa za'ayi style iri daya, ranar Kamu kamar kowa zaiyi style dinsa ne ko?"
Muryar Munaya ta tambaya cikin hayaniyar.
"Ranar kunshi fa shi babu anko Munaya kin manta ne kowa kayansa zai saka, da Kamu ne za'ayi har style ɗaya."
Wata kawar Salma, mai suna Aysha ta bata amsa.
Hajiya Kilishi ta buɗe kofar dakin daidai lokacin da Munayan ke gyara glass din

Please Login or Register in order to submit comment