Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne idan ta nuna musu wannan takardar dole ne auren ba zai yiwu ba.
A hankali ya sake rufe idanunsa yana tuno dukkan irin matakan dake rubuce a jikin takardun asibitinsa, Allah ya sani a baya baya taba damuwa da ciwonsa, yana ajiye shi ne a can ƙarshen lissafinsa, amma a yanzu... yanzu bai san me yake ji ba, tsoro ko kuma taraddadin cewa abubuwa zasu iya ƙwace masa kafin ya kai ga cimma manufarsa? A cikin duhun idanun nasa ya hango a inda yake manufar tasa, abinda shi kaɗai ne abu guda a duniyar nan da baya taɓa haɗawa da kowa, ɗakin bincikensa yake hangowa, tunda ya dawo bai buɗe shi ba don haka a yadda ya tafi ya barshi yake hango shi... Yadda yayi kaca-kaca da takardu cikin takaicin da shine linzamin dukan da yayi wa Daniel.
"... Kaga Rabi ma ƴar wajen Baɗɗejo, yarinya ce mai hankali, ga kyau..."
Muryar Inna ta shiga kansa da wani irin tasirin da ya doka a ƙirjinsa, tasirin da yasa ba shiri ya buɗe idanunsa yana kallon Innar da kuma Ishaq din dake cigaba da gyada kai yana shan furarsa, sai dai ba saurarar abinda suka cigaba da cewa yake ba, muryar Inna ta shekaru goma da suka wuce ce ta shiga haskawa a cikinsa, shekaru goma cikin wannan ɗakin.
Kuma bayan muryar sai hoton ma ya canja a idanunsa, yaga yadda tsufan Inna ke raguwa da shekaru goma da yadda komai na ɗakin ke canjawa da abubuwan da suke a mazauninsu a shekaru goman da suka wuce, sannan a lokaci guda Ishaq ɗin ma ya bace, siffar Jamal ta maye gurbinsa yayin da yake zaune a gaban Innar yana dariya.
"Ga Halima ma ƴar gidan Baffayo, yarinya ce mai hankali, ga kyau, ga kyau..."
Ya ga yadda Jamal ke girgiza kansa yana dariya kafin yace.
"Akwai abubuwa da yawa a gabana yanzu Inna, ki ajiye maganar yaran nan... Akwai abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan kafin ma in fuskanci aikina..."
Kuma a lokaci guda ƙwaƙwalwar Ma'aruf ta tsinto kalamai biyu a cikin zancen...
Abubuwan da nake son daidaitawa a cikin gidan nan... Abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan...
Tabbas! Ya akayi bai taɓa tunawa da wannan lokacin ba? Me yasa ƙwaƙwalwarsa bata taɓa hasaso masa wannan ranar ba? Babu shiri idanunsa suka shiga hasko masa tarin abubuwan dake ɓullewa ga wannan maganar, yaji su suna sauka a cikin kansa kamar zubar ruwan da aka tunkuɗo da ƙarfi.
"B, Yaushe zaka fita?"
Muryar Ishaq ta janyo shi daga tunaninsa, sai kawai ya lalubo wayoyinsa a gefe da mukullin motarsa ya mike tsaye.
"Yanzu." Ya bashi amsa idanunsa na muna tsantsar nazarin abubuwan da shi kaɗai yake hangowa.
Kuma da haka bai jira komai ba yayi waje, yana ji Inna Danejo na ƙokarin tsaida dashi amma bai tsaya ɗin ba, ya fita yana jin tasirin idanun Ishaq da ya biyo da kallo.
A harabar gidan ya gano Munaya tsaye tana waya, duk ta rikice kamar yadda take kullum sai faman gyara glasses ɗinta take alamun bayani ake mata ta cikin wayar, don haka bata ma ganshi ba har ya buɗe motarsa ya jata ya bar cikin gidan, kuma zai iya rantsewa zuciyarsa na lissafa kowanne wucewar lokaci kafin ya isa gida.
A ƙofar gidan ya ajiye motar don ƙwaƙwalwar sa ta gaya masa cewa ba zai iya jira har maigadi ya buɗe masa gate ɗin ba.
Ya shiga har ciki zuwa ɗakinsa, ya buɗe ƙofar da ko waye ya shigo ɗakin zai ce wardrobe ce. A ciki komai yana nan kamar yadda yake hango shi kafin tafiyarsa.
Tebura ne da duruwoyi masu cike da files ɗin takardu da kuma hotuna, ga tarin printers da photocopier a gefe, sannan bayan kayan rubutu akwai allo har kala uku ɗaya na rubutu biyun kuma ya manne su da takardu da kuma hotuna. Ɗaki ne da ko makaho ya shafa zai danganta shi da kalmar binceke balle kuma ga mai ganin da kallo ɗaya da zai yi masa zai bashi amsar da ba sai ya tambaya ba.
A jikin allon nan bayanai ne da kuma hotunan mutanen da Jamal yayi mu'amala dasu tun daga lokacin da ya dawo daga karatu har zuwa ranar mutuwarsa, kuma a jikin kowacce takarda da hoto Ma'aruf ya zana tambarin × da jar marker alamun abinda yake nema bai ɓulle ga wannan hanyar ba, kusan hakan ne ma a jikin kowacce takarda dake barbaje a ɗakin har kuwa da waɗanda aka yayyaga.
A wata durowa daga can ƙarshen ɗakin ya shiga fito da duk takardun cikinta har hannunsa ya kai kan wani file daga can ƙasa.
A cikin file ɗin tarin takardun Jamal ne wanda suka haɗa da duk certificate dinsa na gama makaranta da kuma takardun ɗaukarsa aiki a matsayin sabon ma'aikaci a kamfanin Baffa, takardun ɗaukar aikin ya shiga buɗawa ɗaya bayan ɗaya idanunsa na nazarin komai sai dai har yaje ƙarshensu bai ga komai ɗin da yake nema ba, ya zauna daga tsugunnen da yake, ya sake bin komai dalla-dalla, amma har a lokacin babu komai ɗin.
Hannayensa duka biyu ya cusa cikin gashinsa yana fitar da iska ta hancinsa... Tunani da yawa ke tsere a cikin kansa, yana ji yadda yanayinsa ke ƙoƙarin canjawa, ciwo na harbawa a cikin kansa yana gaya masa cewa zai koma halin da baidade da fitowa ba.
A lokacin ne kuma idanunsa suka hango masa wata ƴar mitsitsiyar takarda da alamun ta faɗo daga cikin file ɗin ne ba tare da ya kula ba, ya miƙa hannu da sauri ya ɗauko ta...
Rubutun Jamal ne, hanwriting ɗin sa...
Mamaki ya kama shi tun kafin yafahimci me aka rubuta, don yasha buɗe file ɗin nan ya zazzage shi amma bai taba ganin takardar ba. Kuma mamakinsa bai karu ba sai da hankalinsa ya gane masa me Jamal ɗin ya rubuta a jiki.
Amina Sulaiman.
Gadon ƙaya.
***
Me kuke tunani ya haɗa marigayi Jamal da Amina?
Me Hajiya Kilishi ke yi da magungunan Ma'aruf?
Me yasa Ma'aruf baya son hayaniyar yara?
Me Ma'aruf yake son cimma ne game da bincikensa?
Waye ya saka kansa a takalmin Amina?😅
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.


BABI NA SHIDA.
~~~~~~
Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ƙofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun daɗe suna hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin ɗin, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ƙato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ƴar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewar an samu baki fiye da mutanen gidan.
A tsakar gidan Amma ce tare da ƴanuwanta su uku da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye.
Yayarta mai suna Zahra'u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Amman da ta fito daga kitchen riƙe da ƙaton tire ɗin data yanko kankana tace.
"Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta ɗinka a cikin lefen?"
Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace.
"Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi ƴar gidan Kawu Mallam wancan satin suka ɗiba suka kai mata wajen mai ɗinkinsu, har da na fitar bikin."
Tanti ta gyada kanta tana faɗin.
"Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta karɓi zancen auren nan amma banda a al'amuranta wallahi."
"Kinga ko jiya..." Ɗaya ƙanwar Amman mai suna Ma'u ta shigo zancen.
"... Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daidai."
Ɗayar da take ƴar autarsu Safiya tace.
"Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin faɗan da banyi mata ba wancan satin amma ƙiri-ƙiri ce min tayi ita ba abinda ke damunta."
"Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yaushe za'a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen."
Aunty Zahra'u ta tambaya tana rufe ƙaton kwalin da ta gama tara ƴan ƙananun kayan kitchen a ciki.
Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ranar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon zaɓawa ƴarsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ƴarsa mara hankali ba kamar yadda Amman ta kira lamarin.
Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al'amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an karɓi kuɗin aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gidan Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al'amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za'a kai Aminan a cikin gidan da suke ne.
Sannan a jiya ta aiko da ɗan aike ya kawo tulin wasu katinan ɗan aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta karɓi al'amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ƴan kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka haɗa masa, yayin da ita da ƴanuwanta mata ke iya nasu ƙoƙarin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin.
Sai da al'amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi tanadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan.
"Yawwa master, nagode sosai..."
Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fadin babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba'asin abinda zai ce.
"Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na karɓo a wajensa."
Ya faɗa cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma'u tace.
"Na ga ranar da zaka yi al'amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba."
"Ameen wallahi..." Cewar Aunty Safiya.
"Amma da ƙyar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne."
Ya ƙaraso ciki da dariyarsa yana shirin buɗe babin shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi.
"Zaka koma ne?" Ta tambaya.
"Eh yace in ɗebi kati in kai masa."
Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga ɗakinsu a lokacin riƙe da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data ɗebi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma'un duk sun zo da ƙananun ƴaƴansu, suna ta dabdala a ɗakin.
Riga ce ƴar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda daɗin ɗaurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman ɗankwalinta dake zamewa.
Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali.
Sai ta juya ta koma ɗakin a lokacin da wata ƴar Aunty Ma'u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta.
"Me kike nema anan Yusrah?"
Yarinyar ta juyo ta kalle ta.
"Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi."
"To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo... Kije ɗakin Amma ki ɗauko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?"
Ta faɗa sanin cewar Hafsan da ƴar gidan Tanti da kuma ɗaya yayar Yusran basu daɗe da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa'ansa ɗan gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma.
Ta tsugunna tana ƙoƙarin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yayin da hayaniyar ƴan ƙananan yaran da suka ɗane katifar Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ƙara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ƙaiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga gaɓar da zata ƙare.
Musamman wannan haɗuwar ta ƴanuwan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan haɗuwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su haɗu har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen haɗuwa yanzu yana ƙara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta daɗe da kafa layin cewa ba wani taro za'ayi mai yawa ba, ko ƴanuwansu a can Niger tace duk a waya za'a shaida musu kawai, sai dai idan maza zasu zo ɗaurin aure don ya zama shaida a wajensu.
Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan ɗaurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke gani sai nata sunan dake ƙasan rubutun Ma'aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ƙirjinta.
Ta rufe idanunta ta buɗe tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin buɗe shafin kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta ɗanɗani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe gargaɗin da yayi mata.
Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma 'yaron kuwa yazo?' sai da ta ƙware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma'aruf ɗin da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ƙaddara ta haɗa su. Gani take yi kamar za'ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne kaɗai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za'ayi a kaita ɗin kawai, acan zata tsara matakan da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace.
'Dama na gaya miki Amina'
Fatima ma tace.
'Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?'
Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa.
'Ko ba komai kin ƙoƙorta Amina.'
Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu'o'in da wataƙila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa.
Ta kai ƙarshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe ɗin ta juyo tana korar yaran zuwa waje. A lokacin Ummi ta ɗage labulen ɗakin ta shigo.
"To amaryar ƙulle, kina nan mu munje mun samawa kanmu mafita.."
Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa.
"Amina ruwa dan Allah, wallahi mun ɗebo rana."
Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta ɗauko jug ɗinsu na roba haɗe da kofinansa ta ɗebo musu ruwa sannan ta dawo.
"Wai daga ina kuke?" Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan.
Ummi ta miƙo mata ledar kusa da ita tace.
"Buɗa ki ga."
Ta karɓa kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta maƙogwaronta, tun lokacin da aka kawo kayan lefen nan su Ummi suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ƴar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam ɗin, don haka sai rawar ƙafarsu ta ƙaru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne.
"Kowacce dubu ɗaya kenan da ɗari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki taɓa cewa roba bace."
"Wai na meye?"
Momi tace.
"Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu ƴan ayi sha'ani ne babu ta yadda za'ayi muyi biki lami ko amaryar bata so."
Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa.
"Ina Fatima? Ga guda ɗaya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ƙawayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ƴan kwanaki, waɗannan kuma ƙawayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu."
Sai a lokacin ta ɗago ta kalli ƙawayen nasu da murmushi a fuskarta tace.
"Allah ya saka da alkhairi, nagode." Ummi ta kalle ta tace.
"Su da kuɗinsu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu."
Da haka ta ja ta suka fita daga ɗakin, a tsakar gida su Amma duk sun shige can ɗakinta suna cigaba da haɗa kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta ɗaga yaran nan sama suna dariya.
A ƙofar ɗakin Baffa suka tsaya Ummin tace.
"Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan da kike ɓoye mana, kin sani ni da Momi ƴanuwanki ne kuma sa'aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki."
Amina ta haɗiye wani abu, duk kauɗin su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can ƙasa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ƴan uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da ɗokin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu kamar yadda Baba ya shar'anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta faɗawa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta.
"Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban taɓa kawowa kaina aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri."
Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gyaɗa kanta tace.
"To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati ɗaya na san zai tafi, don duk da haɗa ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi....Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu kuɗin walima..."
Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisafin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa.
"Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku haɗu kafin wani satin sai ki karɓo a madadinmu, idan ba haka ba kuma ni zan karɓi lambar wayarsa na tambaya da kaina."
Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace.
"Kar ki damu baza'a kai hakan ba ma."
Ina zata kai kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa'a ce babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai.
"Amina auren masu kuɗin nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci kuɗin gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya buɗa miki ba."
A yanzu ta dawo Ummin data santa, ƙanwar ƴanmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta faɗaɗa murmushin ta tana fadin.
"Toh shikenan."
Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ƙawayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da dariyar da har ƙasa suke kaiwa wajen ƙyaƙyata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ƙaton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata.
Maryam ma ta dawo ita da ƙawayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads ɗin da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ƙaru don tace tayi kalar beads ɗin da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za'ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ƙara mata kuɗi zata siyo kayan da zata yiwa ƙawayenta 'takeaway'.
"Tun safe Fatee, tun ɗazu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?"
Ta faɗa lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ƴaruwarsu.
Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace.
"Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu."
Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin ɗiɓan ruwa a buta suka yi soro.
"Amina dama wanda zaki aura da kika ce min ɗanuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?"
Sai da gaban Amina ya faɗi duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron.
"Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?"
"Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali."
Sai ta girgiza kanta.
"Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaɗaya."
Fatima ta girgiza kanta.
"Amina baki san me tace min bane..."
Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faɗin.
"Mutane sun iya yaɗa irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..."
"Yana da wa sunansa Jamal?"
Fatiman ta katse ta, ba shiri ta ɗago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya.
'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa ɗaya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce...'
"Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta.
"Me ta faɗa miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba.
"Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal ɗin shekaru goma da suka wuce!"
****
"Kar ki ɓata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shaiɗan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?"
Muryar Hajiya Kilishi ta faɗa cikin shirun ɗakin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace.
"Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuɗin da na zuba na neman tafiya a banza."
Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani ɓari na sirrin mafi yawan nasarorinta.
"Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata ɗorewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai ɗore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta?
Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana ɗaya da na taba

Please Login or Register in order to submit comment