Join Our WhatsApp Group

ACP MUBEENA Complete Hausa Novel Document by ACP MUBEENA


ACP MUBEENA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28327



ACP MUBEENA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 17, Feb 2024

Author: Dr Xee-nice ,Himlat ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Xee's Pen

Author Phone : 09038727860, 09161738928

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 163.33 kb

File Type: txt

Views: 630+

Download: 362+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: *X££l@hs pen*...............................✍️✍️✍️✍️

****ACP mubeena****
****Paid book📚 ****

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

Page1

Tsayawar motar keda wuya cikin katafaren gida Wanda ya tsaru ya Kuma gaji da tsaruwa,cikin zafin nama aka mude murfin motar wata mace ce kyakyawar gsk ta fito cikin kakin Yan sanda ajikin tag din rigar an rubuta *Asp Mubeena Muhseen* gaba tayi cikin tafiyar Nan tata ta dakakun mata wacce ta samu horo sosai akan aikinta ta doshi kofar shiga main parlor din gidan cikin sauri daya daga cikin yaran Yan sanda ya Bude mata kofar parlor din tasaka kanta inda sauran Yan sanda suka biyo bayanta.

Zaune suke gaba daya family din Sir Muhammad yaseer suna Hira cikin kwanciyar hankali Mubeen ne ya fara dago kanshi idonshi ya sauka akan Asp Mubeena Wanda fuskar Nan tata take a daure kamar wace aka aikowa sakon mutuwa cikin fara a yace welcome dear you are home early" tace yeah wani aiki ne ya kawoni! Cikin dakiya da dacin rai tajuya ta Kalli surukinta Papi tace Sir Muhammad yaseer you are under arrest!!! Cikin wani irin kidima dukan su suka mike uncle Abbass yace are out of your mind Mubeena.... Arrest him for what? Fuska adaure ta Kalli uncle Abbass tace for the death of Alhaji Muhseen tafida my father!

Wani irin kallon kallo akafara mutanen parlor din Mubeen ne yace ke Mubeena banson shashanci fa wane irin kisan Kai papi din ne zai kashe daddy? Cikin wata irin murya Mai tattare da bacin rai tace pls Mubeen allow me to do my job,matsawa tayi Kusa ba papi ta Ciro handcuffs din tamika hannu ta kamo hannushi papi kuwa cikin kidima da tashin hankali yake kallonta zufa Tako Ina ta jikeshi sharkaff dakyar ya Bude Baki yace mu muuu muu Beena me kike kokarin aikatawa ne? Bata dago ta kalleshiba ta Saka mishi ankwa din tana fadin "you have the right to remain silent every word you said will be use against you in the court" tana gama samishi ta juya cikin sauri tana ba Yan sanda umarnin tahowa da shi.. innalillahi waina illahi raju'un Mami tafada da karfi ta zube akasa!


Ka ka ka Ra ka ka......muje zuwa !!!!!! ‎



Daga Alkalamin✍🏻


*X££l@hs pen*✍️✍️✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81W
*X££l@hs pen....................*✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ


******ACP mubeena*******
******Paid book 📚********

Page2

Ko waiwayen inda ake ihun faduwar mami bataiba hannun data sanya ma papi handcuff kawai ta ja sukai hanyar ficewa daga palon baki daya

Fadin irin tashin hankalin da wannan ahalin ke ciki ba abune mai yiwuwa ba most especially mubeen da xuciyarsa ta kusa bugawa

Wannan wata irin baqar rana ce agareshi wanda ko a mafarki bai taba hango xuwanta ba

Ace matarsa ce tai arresting mahaifinshi a gabanshi ba tareda ya iya aiwatar da komai ba
Wannan wata kalar qaddarace hk
Ko a duniyar daba tashiba bai taba xato ko tunanin mubeenar shi xataima papin shi kwatan kwacin irin toxarcin hk ba duba da yanda ya daukakata fiye da sauran yaranshi da ya haifa ya kyautata mata fiye da yanda yk kyautatama yaranshi tun ma kafin tasamu kanta har xuwa lokacinda ya hada aurenshi da ita yasa shi kuma dole yasota
Sannan bai taba daukarta matsayin Sirika ba saidai ‘ya wacce yk ji da ita sama da komai a duniyar shi

Amma yau an wayi gari itace tai masa wannan qasqancin da hankali ya kasa dauka

Ihun da easher ta qwalane ya dawo dashi daga duniyar Tina in daya shiga

Waigowa yyi yana kallon easher dake qwalla ihu tana kiran sunan mami
Xagaye suke da ita ainda suka kwantar da ita saman doguwar kujerar 3seater

Sun rufar mata akai ta inda ko iska baya shigarta km a cikinsu bbu Wanda yyi hausar yayyafa mata ruwa tsabar rudun da suke ciki

Jiki ba qwari mubeen ya nufi friedge din dakin ya bude yadauko ruwa mai dan sanyi amma ba sosai ba ya nufi inda suka xagaye mamin

“”””ku matsa baya””””
Ya fada in his deep voice

Matsawan sukai batare da sunce komai ba
Ya qaraso inda mamin ke kwance hadi da bude gorar ruwan daya dauko ya fara yayyafa mata a jikin ta da fuska

A firgice ta farko hadi da kiran sunan Muhammad a bkn ta,

“”””””””””a bangaren mubeena mubeena kuma bayan fitar su daga palourn inda sukai parking motomsu suka mufa ainda papi ya fara shiga daga ciki ita kuma ta xauna kusa dashi
Bbu mai magana a cikin su kowa da kalar tunanin da yake yi

Ko kadan papi baiji haushin abin da mubeena tai masa ba sam domin shi papi mutum ne dabaida son xuciya samm kuma ya dade da kwana da shirin xuwan irin wannan rana tunda dadewa

Dama duk boye boyen mutum dole watan watarana xata bayyana ita gaskia dayace
Kuma har wannan lokacin babu abinda ya canxa na son da yakema mubeena patansa da kuma burinsa shine Allah ya dafa mata

Daidai nan suka shigo police station din wannan lokacin ita ce ta fara fita daga motar kafin papi ma ya fito har kuma lokacin hannunta na riqe da handcuff din papi
Direct cikin cell ta sanya shi hadi da sa key takulle qofar

Cikin Dan daga murya ta fara magana

“Kaga saka makon aikin da kadade kana binnewa a tunaninka gaskia baxai taba bayyana ba ka muntada duk abinda ka shuka shixaka girba ko ba jima koba dade wannan kadan ka fara gani sauran sakamakon naka na nan tafe
Waikai da a tunanin ka jinin mahaifina xai tafi ne a iska,kaida a tunanin ka duk alwashin da nake dauka kawai cika baki ne kawai baxan iya aiwatar wa ba
Kayi kuskure alhaji Muhammad yaaseer
Kasan menene kuskuren ka????
Kuskuren ka shine na taba jinin *ACP mubeena* the worst part you are the murderer of my beloved father and it was a promise that I won’t spare you

Ta kai qarshen maganar da qarfin gaske

Yanxu aka fara wasan mutanen mu ku biyo mu danjin yanda xata kaya

Written by X££l@hs writersss

Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan numbern
*XEEl@hs pen....................*✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

***ACP mubeena****

Page 3

Har wannan lokacin babu alamar bacin rai ko kadan akan fuskar papi wanda hakan ya fara bani mamaki ~ace surukarka na ci maka mutunci haka amma ko ajikin ka wani irin xuciya ne ajikinka ne papi🤔~

“”””””””wel well well you made a good work my dear *ACP mubeena* haka akeson jami in Dan sanda ya kasance duk lokacin da aiki ya biyo ta kan kowa babu dagin qafa’kai dole ma kisamu promotion saboda namijin qoqarin da kikayi na kama hamshaqin Dan ta adda Wanda yai silar rasa adali kuma jajirtaccen Dan sanda Wanda qasa ke alfahari dashi *sir muhseen* saboda son xuciya irin nashi kuma harda aurawa dansa yar wanda ya kashe a tunaninshi watan watarana irin haka baxai zoba””””

A cewa lawal usman wanda shidin ogane ga mubeena

Dan waigowa tai tana kallonsa da wani shuumin murmushi kwance akan fuskarta tace
“”””thank you sir”””
Hadi da qamewa
“”Permission to carry on sir”” yace permission
Nan take ta juya ta fita daga cikin station din baki daya


••••••••••••Anyi sa’ar farfadowar mami da sunan papi a bakin ta,mubeen ne ya kira family dr dinsu wanda baadauki tsawon lokaci ba ya qaraso ya dubata inda ya gane bawata babbar matsala bane kawai shuck ne da tashiga yasata suma
Allurar bacci yai mata saboda ta samu tadan huta sai yan magunguna daya bata

Cikin qanqanin lokaci kuwa bacci yai awon gaba da ita a nan babban palourn mubeen ne ya bada umarnin kowa ya fita abarta ta huta nan take kowa ya fice jiki a mace bbu mai walwalah a cikin gidan

Yooo Ina su kaga ta wata walwala andauke jigo kuma shugaban gidan an garqame shi a cell ai bbu wata maganar walwala a gunsu
Shima ficewa yayi daga dakin ya koma part dinsu dake gefen nasu papi din

Bayan wasu yan mintuna mami ta tashi daga baccin daya dauke ta babu alamar wata babban damuwa a kan fuskarta sai ciwo da qunar xuciya wanda dama dolene wannan
Ta tashi da mummunar qudirin korar mubeena daga gidan tunda dai gida bana ubanta bane yau dole tabar musu mansion din

Tana qoqarin sauke qafarta qasa kenan easha tai sallama ta shigo dakin

“”””mami barkanki da tashi ya qarfin jikin naki””
“”””da sauqi alhmdllh,yarinyarnan ta dawo kuwa”””
“””aah bata dawo ba tukunna mami””
“””good””
Mami ta fada hadi da yunqurawa ta miqe tai hanyar barin parlourn easha na biye da ita a baya dukda batasan inda suka nufa ba

Part dinda mubeen yashiga daxun nan naga suma sun shiga

Xaune yake a cikin katafaren parlournsu wanda tsayawa fadin kyau da dukiyar da aka barka abune da baxai yiwuba ga wani qamshi dake tashi a palourn na burner da sanyi
Xaune yake akan kujera 2seater ya hade kai da gwiwa abun duniya ya gama isar shi yana rasa wani irin tunani xeyi da xaisa xuciyarshi tadan sassatau daga xafin da tai
Haqiqa ranar yau ta kasance ranace wadda aka kafa wani mummunan tarihin da bai taba xaton xai kasance a kanshi ba

Ko sallamar dasu mami sukaita qwalawa baisan ma su nayi ba saida mamin taxauna Dan dashi hadi da bubbbuga bayanshi sannan yai firgigit ya dawo hayyacinshi

Sassauta murya mamin tai ya fara mgn kamar wata munafuka ni karan kaina banji abinda take cewa ba


*ACP mubeena*
Bayan fitowarta daga cikin station dinsu inda tai parking motarta ta nufa, cikin wata danqareriyar mota naga tashiga wanda kaidagani kasan ba qananan kudi akasa akasiya ba saboda tsabar haduwarta
Bayan ta rufo motar takai more than 30 minutes bata tada motar ba tana xaune sai saqe saqe takeyi sai daga baya ta tayarda ita ta kama hanyar komawa gida

*papi mansion*
Horn tai a katafaren gate din gidan nan da nan gate man ya wangale mata gate tasa kai cikin gidan a parking space tai parking motar ta ta nufi part dinsu

Tsayawa tai cak gab da xata shiga part din nasu su mami ne dasu matar uncle abbas harda matar khilil babban wan mubeen
Da sauran yammatan gidan gefe daya kuma mubeen ne yai folding arms dinshi kai da ganinshi kasan ba qaramin bacin rai yake cikiba

Dukda a yanda ta gansu taso ta Dan tsorata sai ta hana kanta hakan tare da qarfafama kanta gwiwa ta cigabada tunkararsu
“”barkanku da yamma ptan nasameku lpy “”
Ta fada tareda cigaba da tafiya xata wucesu , mamice ta hankadota baya tare da fadin
“””gidan ubanwa xaki je ne eh, nace gidan ubanwa xaki, for your information bakida wata mafaka ko gurin xama a wannan gidan domin dai bana ubanki bane na wanda kika wulaqantane Dan haka banga amfanin xamanki a gidanba
Anty balkisu matar uncle abbas ta daura da
“””qyale yar marasa kunya ta qara one step daga inda take taga yanda xamu sauya mata kamanni

Wani banzan kallo Mubeena ta watsa masu tare da Sakin wani shu'umin murumshi tace kuyi hakuri fah Amma ai banida gidan zuwa sai Nan gidan mijina Kuma gidan makashin mahaifina idan kunga na bar gidan Nan to an hukunta Mai laifine wato an bimin hakkin kisan mahaifina beside ma Ina kukeso naje da igiyar aure na ai zama darammm..... Mami wacce ta kullu iya kuluwa ta Kai iya wuya sai numfashi take mayarwam kamar mesa tace Mubeen kana Jin abinda wannan yar iskar matar taka take Fadi ko to wallahi sai ka saketa yau din Nan ba sai gobe ba,ynzu ke Dan kin cika butulu ki rasa wazaki lakabawa sharrin kisa sai papi kisan ma na Amininshi kaii kaico Mubeena kaico nayi takaicin kasancewarki matar Dana tirrr da wnn mugun halin naki da kika koya silar wannan bakakaken kayan naki Mai suna kakin yansanda da nasan wannan ranar zatazo da ban goyi bayanki kin shiga wannan aikin ba Ashe da biyu kika shiga kin zame manh mage Mai kwanciyar daukan rai!! Mami takarashe tana Sakin wani kuka Mai cin rai.Mubeen da ke tsaye agefe gaba daya duniyar ma juya mishi take har yanzu ya kasa yarda wai matarshi masoyiyarshi abun kaunarshi itace ta kama hannun mahaifinshi ta buga mishi ankwa tajashi tafita dashi a matsayin waiii me laifin kisa....kaiiii inah!! Duk yanda akayi Mubeena Bata cikin hayacinta kokuma dai shaye shaye ta fara ne ban sani ba,Yana cikin zancen zuci tazo wucewa tagabanshi dama ga kukan Mami da gaba daya yake Ji kamar ana soka mishi mashi azuciya azafaffe ya fizgo ta ajuyata suna facing juna yamata wani irin roko na jaruman Maza gaba daya idonshi ya Bude akan nata ya Bude Baki cikin dacin rai yace "ke Mubeena bari kiji nagaya Miki idan ma shaye shaye kika fara to kinsha tagayamiki karya wlh kinyi kadan da wani karamin matsayinki na yar sanda ki kama papi akan kisan dady Wanda ni dake munsan papi bazai taba iya aikata Hakan ba ko a mafarki balle azahiri don haka ki gayamin meye hujjarki ta kama mahaifina!


Hujja Hujjah Hujjah!!! To yanzu dai banida lokacin tsayawar gayamaka ko baka Hujjah tah saidai kasani inada hujja Mai karfin da bazan iya cigaba da zama Ina kallon makashin mahaifina na yawo free ba!!!!


Anan X££l@hs pen writers muka aje alqalaminmu.........✍️✍️

Tofa jama’ah mubeena ta taro match fa in Allah ya kaimu gobe xamuga yanda xata kaya

Daga Alqalamin✍️
*X££l@hs pen*✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81Ws

*X££l@hs pen....................*✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ


******ACP mubeena*******
******Paid book 📚********

Page2

Ko waiwayen inda ake ihun faduwar mami bataiba hannun data sanya ma papi handcuff kawai ta ja sukai hanyar ficewa daga palon baki daya

Fadin irin tashin hankalin da wannan ahalin ke ciki ba abune mai yiwuwa ba most especially mubeen da xuciyarsa ta kusa bugawa

Wannan wata irin baqar rana ce agareshi wanda ko a mafarki bai taba hango xuwanta ba

Ace matarsa ce tai arresting mahaifinshi a gabanshi ba tareda ya iya aiwatar da komai ba
Wannan wata kalar qaddarace hk
Ko a duniyar daba tashiba bai taba xato ko tunanin mubeenar shi xataima papin shi kwatan kwacin irin toxarcin hk ba duba da yanda ya daukakata fiye da sauran yaranshi da ya haifa ya kyautata mata fiye da yanda yk kyautatama yaranshi tun ma kafin tasamu kanta har xuwa lokacinda ya hada aurenshi da ita yasa shi kuma dole yasota
Sannan bai taba daukarta matsayin Sirika ba saidai ‘ya wacce yk ji da ita sama da komai a duniyar shi

Amma yau an wayi gari itace tai masa wannan qasqancin da hankali ya kasa dauka

Ihun da easher ta qwalane ya dawo dashi daga duniyar Tina in daya shiga

Waigowa yyi yana kallon easher dake qwalla ihu tana kiran sunan mami
Xagaye suke da ita ainda suka...


Read / Download ACP MUBEENA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album