Join Our WhatsApp Group

DA SANNU Complete Hausa Novel Document by DA SANNU


DA SANNU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 69211



DA SANNU

Reading Time: 5 Hours

Added On: 10, Sep 2023

Author: Amina Umar Farouq ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PEN WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 414.89 kb

File Type: txt

Views: 477+

Download: 320+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: ๏ปฟ๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’žNU"
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ N
๐Ÿ’๐Ÿ’ SA
๐Ÿ’ž DA"
๐Ÿ’ž
Page๐Ÿ’ 1
๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žDA"
๐Ÿ’๐Ÿ’SA
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’N
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’žNU"




NA



๐Ÿ’ *MEENAT๐Ÿ’ž ๐Ÿ’žUMAR FARUQ* ๐Ÿ’





SHIMFIDA




GODIYA


Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin halitta daya bani damar Rubuta wannan littafi, tsirada aminci su tabbata ga Shugaban'mu Annabi Muhammadu (S.A.W)
Da iyalan gidan sa Da Sahabbansa, da wayanda suka bashi gaskiya har zuwa Ranan Alkiyama Amin.



SADAUKARWA


Na sadaukar da wannan littafin ga iyayena "Alh Umar Muhammad da "Hajiya Lauratu nagode kwarai da tarbiyar da kukai Mani ubangiji yasa kugama da duniya Lafia Amin.



Wannan labarin kagaggene bawai yafaru da gaske bane, saidai nayi shine akan irin "mutanan nan masu saurin yanke hukunci batare da bincikeba, nasama wannan labarin Nawa suna DA SANNU dafatan zaya fadakar.



Sannan wannan labarin ina kirane ga masu kudi dasuyi koyi da halin irin Na Alh Ya'u Na KaKa, suka sance masu taimakama talakawa kamar yanda wannan bawan ALLAH yayi acikin wannan littafin.


Wannan shine littafina' nafarko inafata zaya fadakar daku,kuma ban rubuta shi doncin zarafin wani ko wata KO kuma wasuba, saboda haka duk Wanda yaga halayya ko kuma suna sundace dashi to arashine ba dashi akeba nagode.




_edited by Zainuddeen Zain_






-------------------------------------------
ยฎ *~PEN WRITERS ASSOCIATION~*


_PEN: THE STRONGEST WEAPON_
-------------------------------------------



Bismillahirramanirhim



Mama! Mama!! Mama!!! Ina mama kam tayi nisa domin kuwa ko motsi batayi.


Tafdijam! Babbar magana... wai Dan sanda ya ga gawar soja.


Ai kuwa tuni Abdul-jabbar ya yi kukan kura ya chakumi wuyan Dan siririn nurse da sai rabon idanu yakeyi a firgice, yana cewa "ai wallahi tun da Kayi sanadiyar mutuwar maihaifiyata, to kai ma sai nayi Ajalinka. Dan iska kawai sai na kashe ka".


ko kafin jama'a su kawoma Dan siririn nurse dinnan agaji, tuni ya fara jin kamshin mutuwa, domin kuwa bakaramin, shake sa Abdul-jabbar ya yi ba.


Dakyar wasu nurses su hudu suka kwache shi daga hannunsa, daya daga cikinsu ne yace "lafia me ke faruwa ne cayode?"



Dan siririn nurse da aka kira da suna Cayode bai samu damar bayar da amsa ba kasancewar yanachan yana kokarin nemo numfashinsa da yake Neman kubucewa daga gareshi.


Abdul-jabbar ne cikin tsananin bacin rai yace "ka duba abun da ya yi Mani", ya nuna musu in da Mama take kwance magashiyyatan



Da sauri suka hada baki suka ce "subhanallahi! Ai mu bamu kula ba sam, ya akayi haka ta faru?"



Gaba dayansu suka nufi in da take kwance. Abdul-jabbar cikin kidimewa bayan ya daga hannunta ya juyo ya kalle wadanda sukayiwo ca a kanta, yace "ta mutu"
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žNU"
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’žN
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’N
๐Ÿ’๐Ÿ’SA
๐Ÿ’žDA ๐Ÿ’ž
Page๐Ÿ’2
๐Ÿ’žDA" ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’๐Ÿ’SA
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’N
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’žN
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žNU"



NA




๐Ÿ’ *MEENAT UMAR FARUQ* ๐Ÿ’



```Dedicated to my lovely sisters may aljannah be your final destination with other Muslims ummah, Ameen.```






_edited by Zainuddeen Zain_





-------------------------------------------
*~PEN WRITERS ASSOCIATION~*


_PEN: THE STRONGEST WEAPON_
------------------------------------------



_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_





โœ๐Ÿพ





Abdul-jabbar ya zabura tareda cewa "ta mutu KO"?


Ya nufi Cayode yace ba fa zan yardaba, har ya fara cakumar wuyansa da niyyar ya kai masa wawan naushi, sai wani yace "Kai Ina fa ganin kamar bata mutu ba".



"Musa yi sauri ka kira doctor" daya daga cikinsu ya fada.



Da sauri Musa ya nufi office din har da sassarfa, sai ga su tareda doctor, da sauri yace "A'uzubillahi! Me yasa me ta"? Sukace "wallahi bamusani ba", daya daga cikinsu yace ina ganin kamar ta mutu fa", doctor yace "what"?



Da sauri ya tsuguna gabanta tareda daga hannunta, yai shiru, cen ya mike yace "Musa Kai maza ka dauko(stretcher) ayi maza a kaita emergency room, oya please hurry up"


Yace "OK sir", da sauri yaje ya dauko, har da hadawa da gudu suka nufi emergency room da ita, doctor na bin su a baya shima Abdul-jabbar yana biye da su, yace "don Allah doctor hide nothing from me, is she dea"?



Ba tareda doctor ya kalleshiba yace "no bata mutu ba", a dai dai lokacin da suka isa emergency room din, har doctor zaya shige room din sai ya juyo, ya dafa kafadar Abdul-jabbar yace "don't worry we will do the best we can to see her alive" yace "OK", da sauri doctor ya shige room din.



Yabar Abdul-jabbar tsaye cikin tsananin tashin hankali da tunani, a ransa kuwa cewa yake "shin idan har Mama ta mutu yaya zaiyi"?



Ji yayi gabansa ya fadi, da sauri ya furta "innalillahi wa'inailaihi raji'un!", yace "ya ubangiji ka ba Mamata lafiya Ameen".



Ji yake kirjinsa yana mashi zafi kansa sai sarawa yake, abubuwa sunyi mashi yawa zucci-zucci sai kai da komowa sukeyi a kansa. Ya kasa me ke yi masa dadi,ga matsalar Humaira Wacce kanta ne ya dawo Nigeria, Ga shi tun bai je ga warware matsar ba sai kuma ga wata ta bullo, duk ya rame yayi fayau dashi kamar yayi shekara yanayin jinya,
Shiru tsawon wani lokaci yana tunani, a ransa sai ya saka wannan ya kulla wanchan.



Cen sai ga doctor ya fito,
kafin doctor ya karaso gurin, Abdul-jabbar ya kare mishi kallo, Dogo ne yanada kiba kadan Wanda takarama tsayinsa kyau, wankan tarwada ne bai cika dariya ba yana saye da farar T-shirt me dogon hannu da bakin wando hannun sa yana rike da lab court, Yai ma Abdul-jabbar nuni da hannu alamar ya biyo shi da sauri, yabi bayanshi zuwa office din, mai girima ne an shinfide shi da carpet, akwai Kujeru masu laushi guda biyar da suka kewaye office din, sai wasu kananan kujeru dake gefe, table din me girmane cike yake da takardu,
Akwai laptop akai sai kuma wani Dan karamin katako me dauke da sunan shi.



Ya kalli Abdul-jabbar tareda zare dan karamin glass din dake manne a ldonshi yace "Bissimilla have a sit,"
Abdul-jabbar yazauna a hankali, tareda karanta Dan Karamin katakon Da akayima rubuta da manyan baki kamar haka, DOCTOR I. S. G. Ya tsurama Abdul-jabbar ido yace "munsamu ta farfado saidai nayi Mata alluran bacci saboda tadan samu Hutu, nan da awa daya zata farfado normal insha Allahu kar ka samu damuwa kaji KO, Saidai wane irin abu ne kai mata Wanda ya sa ta tsananin firgici, har ya sa ta tayi dogon suma haka?"
A dai-dai wannan lokacin ne aka turo kofa aka shigo office din, Dan siririn nurse din nan ne, hannunshi rike da (files) suka juya gaba daya suna kallonshi.
Yayin da Abdul-jabbar yake yi masa kallon tsana, shi kuma doctor kallon tambaya yakeyi masa, Cikin bacin rai Abdul-jabbar yace "wannan Dan iskan shi ne sanadin faruwar komai", doctor yace "kamar ya fa"?



"Muna tsaye muna jiran Result sai ga shi ya kawo yace sai sakamako yanuna cewa ina dauke da kwayoyin cutar nan me karya garkuwan jiki,
wai kanjamau shi ne ta fadi ta suma".



Doctor yace "what"?



Eh! Haka ya fada,
Yakalli Cayode da yai tsuru-tsuru da idanu kamar makaryaci.



Cikin tsananin takaici doctor yace "are you stupid
Shi ne joy chukuma"? Yayi tsuru da ido ba tareda ya bada amsar tambayar da akai masa ba,
Yadaka masa tsawa "Ina magana kayi mini shuru". Ya kalli Abdul-jabbar yace "kai ba sunan ka Abdul-jabbar
Ahmed ba"?


Ya ce "eh! Sunana kenan", ya kara kallon Cayode yace "ba nace ne ka kira shi ba Shi ne kaje Kai abun da ban sa ka ba ko? Saboda tsabar iskanci salon kabatawa mutane aiki ko"? Cayode zai yi magana doctor yace "shut up you stupid, and give me the files"ya mika masa hannu alamar ya bashi files din, Cayode ya mika masa ya karba yace "oya get out of my office, mahaukaci kawai", cikin sauri ya fita tareda cewa "sorry sir".



Abdul-jabbar ya bishi da harara yace "banza kawai Wanda baisan Aikinsa ba",
Doctor ya maida hankalinsa ga Abdul-jabbar yace "don Allah Kayi hakuri, wannan ba shi ne result din ka ba sakarci ne kawai irin Na Cayode, nace masa ne fa ya kiraka, Sha-sha-sha ne aikin da aka sashi daban Wanda yaje yayi daban, please sorry".



Yace "it's OK, dama dai Mamana nake ji", "kar ka damu zata farfado ai very soon inshaa Allahu ba tareda wata matsala ba, then, sai abu na biyu, abokina, damuwarka tayi yawa matuka, har tana barazanar haifar maka da ciwon zuciya, Wanda inhar zaka cigaba da sa damuwa acikin ranka to komai yana iya faruwa. Saboda haka ya kamata ka cire komai daga cikin ranka, Yanzu haka ma dole sai na rubuta maka wadan su magunguna Wadanda za ka samu Relief, saboda condition din da ka ke ciki yanzu.



Ko kadan Abdul-jabbar bai yi mamakin abin da doctor I .s. g. yace ba, dama yasan za'ai haka donmin shi a zaton shi ma doctor zaice masa Abdul-jabbar ai zuciyarka ta kumbura sosai saura kiris ta fashe,
Saboda tsananin tunani da damuwa to kuma sai aka samu akasin haka.
Ya kalli doctor yace "to nagode doctor kwarai da gaske, kuma in Allah ya yarda zan yi kokari nai aiki da abin da kace", yace "OK to Bari na rubuta maka maganin".



Yayi rubutu a takarda ya bashi, ya karba yace "nagode sosai fa, sai kudin Mama nawa zan bayar"?
Doctor I.s.g yayi murmushi yace "ba abin da za a bayar", "a ah doctor ayi haka"? "Eh! ka bar shi kawai ba komai," Abdul-jabbar ya sake yin godiya, A hankali aka turo koda aka shigo doctor ya kalli Wanda ya shigo yace musa ya akayi ne"? "Sir matan nan ce ta farfado", "OK to gani nan zuwa" yace "OK sir" tare sukafita da Abdul-jabbar.
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žNU
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’žN
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’N
๐Ÿ’๐Ÿ’SA
๐Ÿ’žDA"
๐Ÿ’ž
Page๐Ÿ’3
๐Ÿ’ž

๐Ÿ’ž"NU
๐Ÿ’๐Ÿ’N
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’N
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’žSA
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žDA"





NA





๐Ÿ’ž *MEENAT UMAR FARUQ* ๐Ÿ’





```This page belongs to my Aunty khadeeja lbrahim Godabe A b u Zaria, pls come back soon we miss youuu```






_edited by Zainudeen Zain_




-------------------------------------------
*~PEN WRITERS ASSOCIATION~*


_PEN: THE STRONGEST WEAPON_
-------------------------------------------



โœ๐Ÿพ



_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_




Tana zaune ta zabga uban tagumi sai kace wadda akayiwa mutuwa, gaba dayan su suka karasa wurin doctor, yace "Hajiya kin tashi" tace "umm!"




Abdul-jabbar yace "sannu Mama bata amsaba, saidai tsuramasa idanu da tayi kamar bata taba ganin sa ba.




Ya sake "cewa sannu Mama ya jiki"?



Tayi ajiyar zuciya tareda cire tagumin da tayi, tace "sannu Ina ciwo ne? Ai kai ya kamata Ayiwa sannu ba ni ba, domin kuwa Kai ke dauke da cuta. Yanzu saboda Allah abin da ya kai ka America ke nan"? Nan ta fashe da kuka tana cewa "nikam wallahi da nasan abin da za kaje kayi kenan, tovda ban yar da ka tafi ba, ga shi yanzu ka dauko wa kanka cutar da batada magani. kuma ka sani sarai ita wannan cutar in har takama Mutum to lahira ne direct ba tsayawa, amma shi ne ka kwasowa kanka saboda kasan koka Mutu ba kada hasara KO"? ta sake fashewa da wani sabon kukan"



Doctor yace "kwantar da hankali Hajiya", tace "kyaleni Likita, ai ni wannan yaron ya chuceni", yace "Hajiya da kin saurareni kiji abin da zamfada miki"



Ta fyace majina da gefen zani tareda share hawaye, tace "Ina saurarenka". Cikin shesshekar kuka.
Yace "kina ji ko"?


Ta kada Kai, yaci gaba da cewa wannan ba result din shi ba ne.


Akasi aka samu amma shi baya daukeda wannan cutar".



Ta daga Kai da sauri ta kalli doctor tace "a ah Likita kar fa ka yaudareni kar ka kuskura Kayimani karya"



Yace "Allah Hajiya da gaske nakeyi ai ba zanyi miki karya ba"



Tace "to ya akayi ya rame yayi baki? Na tabbata domin ba kasan shi ba ne kafin ya tafi shi yasa, amma ai ba haka yake ba".



Yace "zazzabi ke damun sa da ciwon Kai shi ne ya sashi ya rame" (ya fada Mata haka ne saboda hankalinta ya kwanta domin idan ya fada Mata gaskiya zata koma rikicewa ne).


Da kyar ya samu ta yarda sannan ta sauko daga kan gado, ta kalli Abdul-jabbar tace "Allah ya rufa maka asiri da yanzu sunan ka gawa".



Ta mayar da dubanta ga doctor tace "to ka bashi magani"? Yace "eh! Na rubuta masa ya siya", tace "to madallah Likita mun gode kwarai DA gaske".



Shikam Abdul-jabbar bai ce komai ba saboda tsananin mamaki, aranshi kuma fadi yake "Ashe Mama tana sonshi haka?
Ah! tana sonka mana ga shi ta nuna damuwarta a kanka,
Daga ance kana dauke da cutar H.I.V duk ta rikice".
Yayi ajiyar zuciya a hankali, hakan yasa yaji sanyi a ranshi yau Mama ta nuna masa kulawa ya saki sanyayyan murmushi.



Tace "to ai sai mu tafi ko"? Yace "to", suka fito doctor ya kara jaddadawa Abdul-jabbar kan yayi kokari ya sayi magunguna, yace "ai zan siya insha Allahu".



Mama tace "Ya sunan Likita ne"? Yayi murmushi yace "sunana Ibrahim", tace "A ah Ashe sunan Babana ne to mungode sosai Dattijon kirki".



Yace "Lah! ai ba komai sukayi musabaha da Abdul-jabbar yace sai anjima, mun gode fa doctor" yace "nima nagode", suka tafi.



Sunkusan fita daga harabar asibitin sai ga Cayode, Abdul-jabbar ya watsa masa harara.



Da sauri Cayode ya matsa gudun kada Abdul-jabbar ya sake shakesa, ita kam Mama bata kula ba har sukafita.



Yabi bayansu da kallo yace "Kai Ka ga Mutum sai karfin tsiya kamar Zaki?, yanzu ba domin su Musa ba ai da tuni na zama Dan gida a barzahu".
Yayi kwaf "Kai wannan guy din akwai shegen karfi,
a tafi dai Allah...


Read / Download DA SANNU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album