Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAN AREWA Complete Hausa Novel Document by MATAN AREWA


MATAN AREWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 64870



MATAN AREWA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 23, Jun 2024

Author: Maimunah Tijjani Iyam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07038908713

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 334.55 kb

File Type: txt

Views: 613+

Download: 908+

Last download: 3 hours ago

Description/Story:  MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, maƙagin rayuwata. Wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da aron numfashin da ya bani na rubuta wannan littafin na MATAN AREWA. Bayan kammala littafina na SALON ƘADDARATA. Ina roƙon Allah da ya tsare mini hannayena, wajen rubuta abinda zai zamu cutar ga al'ummar musulmai tare da tarbiyar su.


Oh my fans, i'm back no more waiting, ku shirya zama don ban zo da wasa ba, wannan karon salon na daban ne kamar yanda zubin labarin yake na daban kuma na mussamman, wanda suka karanta SALON ƘADDARATA da UWATACE SANADI shaidu ne akan hakan.


Page 0⃣1⃣

Hayaniyar daya karaɗe yalwataccen filin tsakar gidan mu, da carar da zakara ya tsala, su suka zamto ababen farkon da suka fara sallama a ƙofofin kunnuwana a wannan asubahin. Mirginawa nayi ina toshe kunnuwana da hayaniyar matan gidan mu, da ya zamto tamkar ibada idan har suka kuskurewa yin sa. To sai in ba lafiya, suka cika mini ƙofofin kunnuwana, Kafin na miƙe ina sakin wata miƙa na fito daga ɗakin.

"Tun daren jiya Salma, ta sanar dani ta ga shigowar Kubra cikin gidan nan, ina da tabbacin cewar a nan ta kwana. To menene abin ɓoyewa in ma sakin ta Habibun nan yayi ai banga abi......".

Furcin Umman su Salma kenan da suka yiwa kunnuwana dirar mikiya. Yayin da nake ƙarisowa inda suke tsaye cirko cirko, duk sanyin asubahin da ake busawa hakan bai dakatar dasu daga fitowa daga ɗakunan su ba. Bata ƙarisa zancen ba Umman su Anty Kubra tayi hanzari faɗin"Bakinki ya sari gumtun kashi, karyarki wallahi Hadiza dukkan mungun nufin ki akan ki zai juye ba akan ƴaƴana ba. In sha Allahu sai Mariya ta dawo cikin gidan nan tayi zawarci kafin Kubra tayi".

"Wannan kuma ƙarya ne, hatta bokan nakin yayi ƙadan wallahi, Mariya zama a gidan mijinta daram daram, yanzu ma aka fara".

Sai da suka gama ciwa junan su zarafi, sai a sa'ilin Ummata da take tsaye daga gefe ta soma baki"Haba Umman su Salma menene amfanin hakan a gaban ƴaƴanku, ku tsaya kuna ciwa junan ku zarafi. A kan maganar yaran da ba lalle bane ya zamto gaskiya".
Harara Umman su Kubra ta watso mata haɗi da faɗin"Malama waye ya saka dake balle ki ɗauki babban kashi?, ai bamu aike ki ba balle muga daɗewar ki, ko don saboda baki san ciwon ƴaƴa ba tunda ga zarkaɗeɗiyar budurwa kin garke ta a ɗaka har yanzu babu miji dole ki faɗi haka. Duk gidan nan an sawa ƴaƴana ido".

Dai dai lokacin da lasifikan masallacin dake kusa da gidan mu suka sallame sallan asubahi, Abban mu da su Baba ƙarami suka shigo cikin gidan a jere har suna karo da juna. Ganin su ya sanya kowa shiga taitayinsa.

A zafafe Baba yake faɗin"To Allah yayi safiya gari ya waye, an fara sana'ar karnukancin ko?, ana sallan asubahi amma ku kuna nan kuna tada wa mutane hayaniya. Wai shi ku kam yaushe za kuyi hankali ne?, ga ƴaƴa guɗai guɗai a gaban ku amma har yanzu baku san annabi ya faƙu ba, nasan duk wannan fitinar daga kece Zainabu".
Ya ƙarishe zancen cikin ƙololuwar ɓacin rai, yana nuna Umman su Anty Kubra da ƴar manuniyar yatsarsa.

"A'a kar ka soma ɗaura mini laifi, daga shigowar ka baka ji ba'asin abinda yake faruwa ba kace laifina na".

Gyaran murya Abba yayi yana ɗaurawa da cewar"Menene yake faruwa?".
Cikin zafin rai Umman su Anty Kubra take faɗin"Kama Hadiza da ɗiyarta Salma nayi suna gulmar Kubra wai ta kwana a gida".
Na lura sai a sannan duk idanunsu suka sauƙa akan Anty Kubra, da take rakuɓe cikin ƙofar ɗakin su, Baba ƙarami yayi mata wani kallo yana cewar"Ke Kubra meye kawo ki gidan nan?".

"Baba ƙarami mun sama saɓani ne dashi Habibun, shine yace na taho gida".
Tsawa ya daka mata"ki tafi kai tsaye ki sanar dani abinda take faruwa kai tsaye, kafin nan kowa ya wuce yaje yayi salla".

Dukkan mu barin wajen muka yi, bayan an gama wurgawa juna harara da kallon uku kwata kowa taja zugar ƴaƴanta suka nufi ɗaka. Ummata da Anty Zakiyya muka shige ɗaki bayan mun ɗauro alwala muka yi sallan asubahi. Aikin daya kallafa a kaina na fito nayi na kowa ɗaki nayi kwanciyata. Na iske su Umma duk sun haɗo a falon Abba.

Gidan mu gidan gandu ne, daya haɗa dukkan ahalin mu waje guda tun daga kan kakanin mu har izuwa iyayen mu. Da kuma mu ƴaƴansu hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin matan gidan da kuma gasa a tsakanin mu ƴaƴan ahalin. Su biyar Abba suke a wajen iyayensu shine babba sai Baba sai kuma Baba ƙarami, ragowar biyun mata ne Goggo Suwaiba da Goggo Jummai da auran ta ya mutu ta dawo gidan da zama. Dukkanin su babu mai mata ƙasa da biyu Abba ne kawai mai mata biyu, Allah ya azurta ahalin da yalwan da ƴaƴa mata babban namiji Yaya Majid ne kawai sai kuma Nurain ɗan ɗakin su Anty Kubra, da bai wuce shekaru biyar da haihuwa ba. Mu uku ne a wajen Umman mu yaya Majid, Anty Zakiyya sai kuma ni, Daada kishiyar Umma ƴaƴanta uku Anty Maimuna, Anty Hasina da kuma Abasiya. Yayin da duk sauran ƴaƴan su Baba ƙarami da Baba ne.


Kawai gasa sosai a gidan mu da son ganin cewar kafi kowa. Al'ada ce a gidan mu duk wata ɗiya mace bata rufa shekaru goma sha biyar ake aurar da ita. Anty Zakiyya ce kawai ta kai shekaru goma sha tara ba a cikin ɗakin mijinta ba. Hakan ya zamto abin tsegumi da yafice a tsakanin mutan gidan mu. Abin nema ne ya samu wai matar ɗan doka ta haifi ɓarawo gori da shaguɓe babu irin wanda ba'a yiwa Umma da Anty Zakiyya ba.

Ina zaune a uwar ɗaka, ina biya karatuna Umma ta dawo daga zaman da suka yi tare da su Abba, da kallo na bita har ta zauna kusa dani tare da cewar"Na'ima ki tashi ki tafi islamiyya ga can su Abasiya sun shirya".
Zumburo baki nayi gaba kafin na kai ga furzo zancen cikina, ta ɗaga mini hannu alamar bata son jin komai daga gare ni, na miƙe na fice daga ɗakin a tsakar gidan nake jiyewa kunnuwana dalilin zuwar Anty Kubra gida. Wai sunyi faɗa da mijinta ne ta turo shi ta saman bene ya karairaine.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciyar da ta tokare mini ƙirjina na sauƙe, ina ƙara jinjina lamari a raina duk irin romon soyayyar da Anty Kubra suka kwankwaɗa da yaya Habibu, a lokacin bikin su har wani ji da kai Ummansu ta ƙaro tana ganin Allah yayi wa ɗiyarta ilhama zata auri mai hannu da shuni, mai gida da mota. Yanda suke soyayya abin zai ba wa kowa sha'awa amma yau ita ce da zuwan gida da sunan matsala.

Kwanon abincin da Umman su Salma ta dangwafa mini a gabana, na ɗauka na koma ɗaki kasancewar su Salman da muke ci tare yau kowa a ɗakinsu zata ci, nan na iske Anty Kubra zaune da Ummata gefe kuwa Anty Zakiyya ce tana naɗe kayan wankin da tayi. Gefe na samu nayi wa kaina mazauni ina kafe Anty Kubra da idanu da take maganar cikin zubda ƙwalla.

"Umma nasan kai kaɗai ce za ki gaya mini gaskiya a cikin gidan nan, wasu ma murnar dawowa gidan suke yi. Dan Allah abinda nayi shine dai dai ko kuwa na aikata kuskure?.Umman su Na'ima da nasan haka aure yake da banyi shi ba, akan gadona Habibu yake waya da wata yana faɗa mata wasu kalamai marasa daɗin ji da nauyi akan harshe wajen maimaitawa. Masu cike da batsa me na rage Habibu dashi da zai yi mini haka?".

Ta ƙare zancen tana kuma sakin wani kukan dake bayyanar da raunin dake cikin ƙalbinta, ina iya jiyo ɓoyayyiyar ajiyar zuciyar da Umma ta sauƙe kafin ta riƙo hannuwan Anty Kubra cikin nata ta riƙe sosai, kana ta soma cewar"Kubra shi aure ɗan haƙuri ne ko wacce kika ganta cikin ɗakinta, har ta kai wani matakin da take burge ki, take baki sha'awa to haƙiƙa haƙuri shine tsanin daya kawo ta wannan tudun. Kaso arba'in daga cikin MATAN AREWA su suke ɗaukewa kansu dukkan ɗawainiyar su dana ƴaƴan su, a gidan miji kama daga ci, sha da kuma sutura. Kaso ashirin na MATAN AREWA basa tarar da soyayya da kulawa a gidaden auren su, basa samun kulawa daga mazajen nasun saɓanin hakan ma sai dai a tarar da kishiyar hakan. Kiga aure shekara ɗaya wani baya ma rufa shekarar an rabu. Kaso talatin na MATAN AREWA basa samun biyan buƙata na auratayya daga wajen mazajen nasun
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAN AREWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album