Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

CIRANIN AMANA Complete Hausa Novel Document by CIRANIN AMANA


CIRANIN AMANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 99891



CIRANIN AMANA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 8061929616, 08033933642, 09032409668, +227 90795939

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 523.35 kb

File Type: txt

Views: 795+

Download: 2233+

Last download: 4 days ago

Description/Story: Compiled by Umar Dalha Funtua.


✳CIRANIN AMANA✳


1-5



By
AsmaBaffa




BISMILLAHI



INA MIKA GODIYATA GA DUBBAN MASOYANA ,DA FATAN ZA KUJI DADIN WANNAN NOVEL KAMAR YANDA KUKA JI A MA'AIKACIYAR GOMNATI READERS,ALLAH SA A FARA LAFIYA MU GAMA LAFIYA.




Sanye take cikin wata jemammiyar rigar atamfa ko kugu bata kai ba,ga wani wandon yadi ja ajijinta dogo,ta nannade kafa daya iya gwiwarta,wata dagargajajjiyar p cap ce a kanta,tafiya take tana bouncing har wani dinginsa kafa daya takeyi,irin tafiyar nigogi maza takeyi tana shan kamshi tare da dauke kai sama tana hura hanci,tafiya takeyi tare da sa hannayenta a aljihunta tana bouncing tare da yin doro tana kwobarewa hadi da budawa.

Bata kula kowa kawai kwana take sha,wata dandazon majalisa ta maza tazo,tana zuwa aka fara ihu da tafi sai Amana,kallonsu tayi tare da kara kwobarewa tace sai Baba,sa'a dai sa'a dai tayi Gaba bata kara yin magana ba tafiya kawai takeyi,wani yaro taci karo dashi,sai da ya buya a lungu yace Maza Mazaje Cike da bala'i ta dago kanta aifa sai ta hango yaron,da gudu yaron ya zura,ta bishi itama sai da ta kure masa gudu har cikin gidansu yaron ta kamoshi a gaban Uwarsa ta hau jibgarsa kamar Allah ya aikota,mutane sun taru amma ba Wanda ya riketa saboda kowa yasan halinta,in tayi fushi ba a iya tsaidata,suna ji suna gani ta farfasawa yaron nan jiki sannan ta gyara p cap dinta sosai ta da kyar take gani tsabar janyo hular da tayi, gaba tayi tare da bouncing,ta kusa zuwa kofar fita daga gidan tayi tsalle tayi ball da wani baho da ta gani a hanyar kofar fita daga gidan sai da bahon yayi raga raga,sai da ta fita ta bar gidan sannan mutane suka sami bakin tsine mata tare da Allah wadai da zuriyar Gidan baki gaba dayansu,kowa da abinda yake fada akan wannan matashiya da sauran yan uwata tare da iyayensu.

Har kofar wani gidan kasa tazo kato da alama shine gidansu,Babanta ta gani a waje tare da mutane a kofar gidan Sallama tayi musu tare da cewa Allah barmana Baba,sai me gida wlh,tayi cikin gida,da wani gurjejen namiji ta hadu da gani katon dan Wiwi ne,lips dinsa sun nuna da tafin hannunsa,cije baki yayi tare da karkace shi gefe,ke dan Uwarki daga Ina haka?hannayenta biyu a Aljihunta tana hura hanci tare da ja baya,ta kara yin doro tace kafa ja girmanka Hamza,dan zan iya takeshi kasan da wa kake magana dan tsab zan Zagi Amarya uwarka,kasan Halina ko?

Jinjina kai Hamza yayi tare da cewa zan tattakaki in bakiyi hankali ba,bani da mutunci,to ni din an fada ma mutuncin gareni cewar Wacce aka Kira da Amana.tsaki taja tare da banke Hamza tayi cikin gida,tana shiga Ashar ce take tashi a gidan ana ta dambe tsakanin yan mata gidan,
Iyayensu ma sai dirko ashar sukewa junansu,ruwan Ashariya kala kala ce ke tashi a gidan,nan take ran Amana ya baci ko kallonsu batayi ba ta wuce cikin dagargajejen dakinsu,Wanda yake daf da ruftowa.

Sallamar megidan sukaji da alama shine babansu,shima Ashariya ya Shiga dannawa yaran tare da iyayen su hade da kallon wata yar yarinya bata wuce 7yrs tana gatsine da harara yace tafi can shegiya da kai kamar kuda,kallon sauran matan nasa yayi da yaransa maza da mata yace wacce bata fasa ba taci ubanta shegu tsinannu,tambadaddu,bakin da aka sauka a gidan ne suka fito daga masaukin da aka basu suna bada hakuri,
Matan ne sukayo kan bakin da masifa kamar zasu cinyesu da zagi na tashin hankali.

Me gidan ne yayi tsalle ya dire yace kar tsinanniyar data kara zagar min bakina,bakin Alkhairi,dole kuma na dinga saukar baki a gidana,wlh babu yar wata katuwa da ta isa ta taka min birki.
Wata ce a cikin matan nasa tace tambadadden dan iska dama dole kace haka munafuki,Allah ya isa duk ka tarwatsa mana yara,ka lalatasu,dayar ma tace an dai ji kunya kwarton Banza,wata tsohuwa ce tukuf itama ta fito tana ba kwarto bane yaro na,kar ku kara zagar min da shegu jarababbu,haihuwar Asara.
Watace ta zaburo itama a cikin matan ta nuna me gidan,tace ga tsohon haihuwar asara kwarto maci amana.Amana ce ta fito daga dakin tana budawa tare yiwa mutan gidan kallon banza,tace kuna yawa fa,kuna da matsala,dan Allah ku rufe mana baki wlh ko yanzu ayi abin kunya a nan wajen nan ko Baku gane bane eh?

Me gidan yace yawa Yar Amanata kiyi maganinsu,sai Baba kaima fa Baba kana da Matsala fa,ka dinga kiyayewa duk kabi ka jona mana masifa da irin abinda kakeyi a gari.

Baba ne ya kalleta zaki ci Ubanki kema shegiya me suffar maza,jibi yanda kikeyi, wa zaki samu ya aureki haka? Shi yasa baki da mashinshini,kinyi kwantai anyiwa kannenki aure ke kina shirme a gari,
Cike da takaici ta kalli kanta tare da sa hannu daya a Aljihu tare da cewa Baba ni ba gudun maganarka nakeyi ba,bana tsoronku ku kanku kun sani,kawai biyayya nake ma amma dole a fadama gaskiya ka gane Tsoho kana yawa wlh,wannan abin da kakeyi ba me kyau bane,shi yasa muka lalace,dole na fada ma gaskiya,ka gyara badan mu ba ko dan Allah kaji tsoronsa.
Rufe min baki shashasha ubanki nakeyi? Hmmm Allah baka Hakuri Baba nasan yanzu zaka iya tsine min.
Ta inda kikafi yan uwanki hankali kenan akwai biyayya ga iyaye,ga sallah akan lokaci,cewar Baba Dariya amana tayi kadan tare da fadin Allah barmana Baba,ammafa Baba Allah shirya mana kai.ki kiyayeni Amana cewar Baba,sorry Baba Amana ta fadi,
Baba yau ba dan tsire ne?cewar Amana, Babane ya watsa mata harara tare da cewa ubanwa zai sai miki tsire maganin me kike min a gidan nan,ke ba saurayi ba bare nasa rai zan samu kudi,tafi kiban waje shashasha.bouncing ta kama yi tare da kwobarewa tana kunkuni,wofi banza da baki kamar gidan tsutsa cewar Baffa.Anayin kiran sallar Magriba Amanace ta Riga kowa yin Alwala da Sallah a gidan.

Ummanta tana zaune tana tace gasarar kokon siyarwa na safe,bata da niyyar tashi tayi Sallah,Amana ta kalleta a hankali sannan tace Ummammu Anyi fa Sallah ni halina dake kenan wlh anata ta Sallah ke baki da Niyyar tashi,
Wacce aka kira da Umma ce ta daure fuska ke jarababbiya sauraramin,niba uwarki bace zaki dinga gaya min magana inda kika ga dama?,ko ni sa'ar ubankice,har ni zakiyiwa wa'azi kamar kanwar uwarki,sai da safe ki taso sakalo sakalo na sammiki koko,kin dauki aikin banza a kanki,kin rasa me sonki tallanma kinki yi kince ke boko zakiyi ayi mugani ai duniya ce,
Haba Umma daga cewa kiyi sallah shine kike min baki?kin San ma'anar duniya ce,ku gidan nan Baku da aiki sai zage zage,duk kun gama kwashe mana Albarka,taya zamu samu miji,kuma boko tun daga primary waye yake daukan nauyina?itacen kara nake yowa a kauyen nan haka gashi har ina ss2,ai abin ku jinjina minne amm kullum kunfi so kuga na shiga duniya dan na samo muku kudi haba Umma,ya kike haka ai gwara idan bake kika haifeni ba ki fada min nasan matsayana tun wuri.
Ke tashi ki bani waje jakar banza.wani bakin cikine ya cika zuciyar Amana,Sam basuyi dacen iyaye ba,yo ni da za a dinga min fada wani ciyar dani akeyi?sutura ake min ko sabulun wanki bare na wanka ba ayi mana a gidan nan,kuma sai a bimu da zagi nifa bazan dauka ba cewar Amana tare da ficewa daga gidan.

kowa a gidansu babu na gari a cikinsu,gaskiya Allah kawo min sanadiyar tafiya Cirani na yi wajen kudu,na huta kawai da bala'in gidan nan,Allah sa Baba ya turani cirani nima irin su Hamza na tafi na huta da masifar gidan nan.

Wannan wanne gidane kenan,da alama babu me tarbiyya a gidan kaf. bari muji tarihinsa.


GIDAN BAKI kenan gidane Wanda me Gidan yake saukar mutane Baki idan sunzo gari suna Neman masauki sai ya saukesu amma iya mata banda maza,baya saukar maza a gidansa,shine dalilin da ake kiran da gidan Gidan Baki.

Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download CIRANIN AMANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album