Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

IDON NAIRA Complete Hausa Novel Document by IDON NAIRA


IDON NAIRA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16225IDON NAIRA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 07, Apr 2023

Author: Mamuh Gee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 09166221261, +22799643131

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 95.96 kb

File Type: txt

Views: 5563+

Download: 938+

Last download: 3 days ago

Description/Story: hoton kyakkyawan mijinta a shafin farka na jaridar da wani me siyarda jaridu yaketa dagawa Dan a siya.

Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke tana jin sonsa me tsananin girma na sake mamayeta musamman tunaninta na koda yaushe akan nata dinne ita kadai.

Murmushin farin ciki ta sake tana sake kallon fuskarsa a jaridar tareda saka hannu handbag dinta tana lalubo wayarta Dan kiransa taji murmuyarsa.......

Dakatawa tayi daga dauko wayar cikin Jakarta tana Dan tsayar da idanuwanta akan jaridar lokacinda me jaridun ya matso har gaban gilashin motarsu Yana sake tallata sanaar tasa.....

Ras ta bude ido da kyau ta karanta bayanin dake rubuce baro baro gameda mijin nata da hotonsa yake Kai....

Duk tsananin ilimin addinin datake dashi Kuma a matsayinta na matar babban Mai ilimin addini bata iya kamo salatiba cikin tashin hankali da tsoro hannuwanta na rawa tace"

Wayyo Allah na

Nashiga uku,

Meye wanna nake gani?

Murya na Yar rawa ta kalli drivernsu tace"

Habibu karantamun abinda yake jikin jaridar Nan Dan Allah

Kaga nakasa gane mena karanta...

Me jarida kuwa yana ganin hankalinta sosai akan jaridarsa ya sake matsowa sosai Yana sake Nuno mata jaridar.

Ahankali habibu ya bude idanuwansa akan jaridar ya karanta abinda yake rubuce a gurin hoton maigidansu.

*_DR sheykh MUHAMMAD AQEEL Former COA, HN Spk/MADAME IDON NERA._*

*_Work(aiki) Or busness(kasuwanci)????_*

*_Mother(uwa) Madame haj zainab IDON NERA or Daughter ('ya) AMAL IDON NERA???_*

Sake karantawa yayi dakyau ya tabbatarda dai Maigidansu ake nufi wato Dr Aqeel sheykh..

To meya hada sunan dr sheykh da wannan hamshaqiyar matar data bawa karuwai cikakken yanci da gata???

Me ake nufi da uwa ko 'ya?.....

Cikin Yar shaqewar murya bilkees tace"

Habibu fassaramun dakyau nagane Mana

Ka karanta kayimun shiru..

Shiru yayi yana Dan kaucewa kallon jaridar a natse yace"

Hajia shirme ne da neman lalata suna irin na Yan jarida fa Amma bakomai ban.....

A rikice ta zaro kudin da batama San nawa bane daga Jakarta ta sake glass din motar ta miqawa me jaridar ta karba da qarfi tana sake ware idonta sosai akai tana sake karantawa.....

Innalillahi,kenan dai abinda ta karanta dinne da farko ba kuren karatun bane...

Innalillahi na shiga uku na lalace,

Kodai sunan SSG zasu saka suka saka na Sheykh sbd a iya saninta babbar masifar data tarwatsa farin ciki da gidan Ssg IDON NERA ne

Saidai bata saniba Yar ce ko uwar..

Mezai hada mijinta me tsananin qyanqyamin sunan zina ma bare karuwan dake aikata zinar har a hada sunansu a jarida.....

Zuciyarta taji tana doka wani irin tsalle da rawar firgici,

Zufane yaketa karyo mata tako Ina cikin doguwar jallabiyar dake rufe ruf dako Ina jikinta kasancewarta matar babban masani addini.

Ahankali numfashinta yafara yin sama sama sbd tsananin firgici da abinda takeji a zuciyarta,

Zuciyarta wata irin zafaffiyar zuciyace akan mijinta,

Tanada wani irin mugun rauni agurin kishi sbd abu kadan ne yake sakata shiga masifaffen hali sbd kishin Mijinta Wanda ya kasance wani lafiyayyen masani addini Kuma Mai tashen arziki da mukami da suna da kyau da nutsuwa....

Ita kanta tanada ilimin addinin sosai kasancewarta tun farko Yar babban masanin addinin itama Kuma ga mijinta shima Amma lokuta da dama kishinta kaman rinjayarta yakeyi shiyasa take wahala sosai da zuciyarta...

Qawarta matar aminin Dr shaykh Aqeel wato ssg babbar masifar data farraqa zaman lafiyarta da jin dadinta shine muguwar soyayyar da SSG din yakewa IDON NERA wdda ita batada sanin uwar ko Yar ce Amma dai koma wacece aciki tafi saka ran 'yar ce Dan kuwa uwar zataiwa ssg girma duk da ance tamkar qaramar matashiya take sbd hutu da zallar rayuwar jin dadin datake zubawa manyan Yan siyasa da shugabannin tsaro sun tsaya mata yanda takeso.

Ganin mawuyacin halinda tashiga yasa habibu qarawa motarsu gudu suka iso gida a rikice sbd ganin kamar zata shide bata hayyacinta.

Yana parking ko Jakarta a juye ta daukota tana tafe Yan wasu abubuwa ciki suna zubewa batareda ta ankaraba......

Kai tsaye hayar babban shashen sirikarta ta nufa idanuwan ko gani basayi sosai sbd rikici...

Daqyar da wahala ta iya Dan seta kanta kadan sbd sanin doka da halin sirikar tata na rashin son tashin hankali da rashin nutsuwa.

A Palo ta taddata zaune kan doguwar kujera tana karanta sako a waya

Kyakkyawar dattijuwar mace Mai son nutsuwa.

Kasa riqe kanta bilkees tayi sbd gab take da Dora hannu akai tayita birgima da wannan mummunan abin datake neman me yimata budadden bayani akan ba gaskia bane abinda aka rubuta din.

Hannunta na wata irin rawa ta miqawa haj maryamah jaridar hannunta tana sako wasu irin hawayen tashin hankali da shiga uku...

Kafin tayi magana Hameeda ce tashigo palon itama hankalinta atashe riqeda jaridar ko gabanta bata gani sosai itama tana cewa"

Mummy B menene yake faruwa zaa lalatawa mahaifina suna?

Wannan IDON NERA din idan natuna itace waccar hamshaqiyar karuwar me 'ya AMAL IDON NERA,

Meya hadata da daddynah?

Meya hada sunansu guri daya?

Wace tambayace suka rubuta anan din????

Wurgi tayi da jaridar tana sakin hawaye itama Dan kuwa wnnn babban alamrine ya tunkarosu...

Haj Maryamah da aduk duniya idan akwai kalmar datafi tsana a fada gabanta to itace kalmar karuwanci.,

Ta tsani kalmar sunan tsana mafi muni da qyama Wanda kusan kowa yasan hakan shiyasa shima Dr shaykh Aqeel ya tsani kalmar sunan...

Ajiye wayarta tayi agefe tareda kallonsu gabanta na Dan nauyi ganin yanda hankalinsu yayi masifar tashi

Hannu a sanyaye ta dauki jairidar ta saukar da idonta akai.

Jimmm tayi tana sake maimaita karanta kalmomin daya bayan daya kirjinta na wani irin nauyi...

Sake kallon hotonsa dake kan jaridar tayi ta tabbatarda Dr Shaykh dinne 'danta qwalli daya ake maganar menene alaqarsa da karuwa....

Innalillahi wainna ilayhirrajiuni

Innalillahi wainna ilayhirrajiuni

Balkees na ganin haka tasake shiga mummunan tashin hankali tafara nanata sunan IDON NERA a bakinta cikin rikicewa tana cewa"

Wannan haj zainab adamu idon nera meya kawosu rayuwar da take hannun riga da qazamtacciyar tasu rayuwar...

Meya hada Dr shaykh tsaftatacce tsarkakke mara qazanta dasu....

Sunan da balkees ta ambata yasa haj maryamah miqewa tsaye tana kokarin barin gurin Amma tana tsayuwa qafafunta suka kasa riqeta ta sulale zuciyarta na daukan wani irin nauyi da harbawa....

Kanta sukayo cikin tashin hankali da tsoro suna Kiran sunanta hankali tace

Saiga sallamarsa cikin nutsuwa da wata irin haiba Mai tsananin cika ido da kwarjini.

Qamshinsa daya fara gauraya iskar palon yasakasu waiwayowa su dukansu suna kallonsa kowa zuciyarta a rikice da tashin hankali neman bayani daga gurinsa Wanda shi baimasan abinda yake faruwaba.

Qarasowa yayi gurinsu cikin takun nutsuwa Yana kallon haj maryamah dake kallonsa cikin tashin hankali,tsoro,fargaba da babban tunanin Ina ya hadu Zainab qanwarta tsatsonta dasu biyu kawai mahaifinsu ya Haifa a duniya ya mutu,

Zainab itace hamshaqiyar shahararriyar matar da ake fada a tsayawa karuwanci da karuwai??

Kenan bayan tsawon shekaru Aqeel yagano maminsa zainab dayake tsananin so a mahaifiya kusan ciyeda ita data dauki cikinsa ta haifesa????

Innalillahi wainna ilayhirrajiuni

Tayaya zaace itace?

Rintse idanuwanta tayi tana cewa"

Ya Allah kada ka dawo da Zainab rayuwar tsaftataccen 'dana AQEEL,

Ya Allah ka hanasu sake haduwa sbd rayuwarsu ta bambamta,

Shi Mai tsaftane ya Allah..

Babban fatanta kada Allah yasa wannan zainab idon nera din ta kasance qanwarta zainab dasuka rufe suka binne juna daga zuciyarsu da rayuwarsu...

Kowa yaje yayi rayuwarsa da abinda Allah yabasa

Ita 'da mai tsarki itakuma 'ya Mai daudar najazar uwa karuwa Wanda itama tanada tabbacin 'yar karuwace a yanzu...

*_IDON NERA???_*

Meya kawo sunan da ko tsarki da dadin ji da fada babu acikin rayuwarsu??

Da gaske zainab qanwarta itace ta zama idon nera datake taka rawa Kai tsaye gurin tsayawa barna da karuwanci?

Dr shaykh aqeel 'danta yasan Maminsa data renesa tun Yana jinjiri itace hamshakiyar karuwa idon nera??

Shin Zainab dince ma idon nera kokuwa 'yarta data bar gida da ita??

Mezaisa Dr shaykh ya yarda ma ya kalli inda IDON NERA's din suke sbd saninin tsananin taka tsantsan dinsa da kiyayewarsa ga kusantar qazamtaccen guri???

Yasan Maminsa Zainab itace idon neran shiyasa yaje kokuwa wata qaddararce ta hadasu har ya jarida suka samu damar yada wannan mumman labarin Dan lalata sunan tsarkakken masanin addini kamarsa Kuma Wanda yakeda suna sosai a harkar foreign business dinsa harma da muqami ace angansa tareda Idon nera...

Allah dai ma yasa ba Zainab bace wannan sananniyar karuwar idon nera Dan kuwa Yana cikin babban baqin ciki idan aka amabata sunan ita din 'yar uwartace,jini daya yake yawo a jikinsu..ace Ana ambatar sunan sananniyar karuwa da sunan mahaifinsu a gaba babban baqin cikin rayuwarta ne wanan Dan kuwa ko mahaifinsu dake kwance kabarinsa wannan babban abin jin zafine.

#MAMUH#

#SISTERS#HATE#SISTERS CHILDRES#BLACK AND WHITE LOVE#

LOVE/ROMANCE

ZAFAFA BIYAR

______________________

*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

*DAUDAR GORA*πŸ”₯

*IDON NERA*πŸ”₯

*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

*KI KULANI*πŸ”₯

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

0022419171

Maryam sani

Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA...


Read / Download IDON NAIRA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album