Join Our WhatsApp Group

RAINON DAWA Complete Hausa Novel Document by RAINON DAWA


RAINON DAWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 62391



RAINON DAWA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 25, Aug 2023

Author: Mammy Kabir ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Elegant online writers????????

Author Phone : 08148360851

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 327.95 kb

File Type: txt

Views: 2891+

Download: 1511+

Last download: 20 hours ago

Description/Story:


🎄RAINON DAWA🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free page

1/2


Bismillahir rahmanir Rahim.
Ina farawa da sunan Allah,mai kowa mai komai,wanda ya bani ikon kammala littafin MACIJE NE lafiya,sannan yanzu na fara sabon book dina,RAINO DAWA.ina fatan Allah yasa yadda na fara lafiya ingama lafiya.

Wannan littafin mallakina ne,banyarda wani ko wata ya juyamin shi ta ko wacce sigaba,saida izinina.dan haka akiyaye.

Sannan ga masu bukatar biyan kudin wannan littafin zaku biya kamar haka.

Normal group 300₦
Update biyar a sati.

Special group 500₦ update bakwai asati, kuma zaku iya samun update biyu arana.

Sannan akwai manyan mata,wadanda ke bukatar atura musu private,Ina sane daku hajiyoyina.
Zaku biya 1000₦

Duka zaku turo kudinku ta wannan acc. Din.
Saratu Kabir.
U.b.a
2215749011.

Saina jiku masoyana na Amana Ina sane daku.




_____________Dajine mai cike da tarin bishiyu,dogaye masu yawan gaske,hakan yasa ta wani bangaren na dajin yake da duhu da sarkakiya,wani gurin kuma zaka ganshi akwai wadatar haske.

Dajin yana da matukar girma,wanda ke dauke da halittu kala-kala.baka jin komai sai sautin kukan tsuntseye kala daban -daban.

Kasancewar yanayine na damuna,hakan yasa dajin yayi lub-lub dashi,gaba É—aya bishiyu dake cikin dajin sunyi ganye koraye shar dasu kwanin sha'awa.
Wasu daga cikin ganyayyakin har ruwa zakaga yana diga daga jikinsu,alamun raba.

Kai tsaye zamu iya cewa dajin yana da yanayi na ban tsoro,wanda bazaka taba tsammanin akwai wata halittar dan Adam dazata iya rayuwa cikinsa ba.saidai hakan bai hana dajin kyau da kawatuwa a idon duk wanda ya kalleshi ba.

Akwai birrai da yawa cikin dajin,sannan ana tunanin akwai mugayen namun dawa dake rayuwa cikin dajin.

Can gefe guda na hango wasu bishiyu kusan guda goma,acure guri É—aya,kamar wanda aka hada kansu,suna da tsayi amma ba kamar sauran ba,da alama dai kamar yankesu akayi.

Daga kaina nayi É—an kallon iyakar tsayin bishiyun,saidai ga mamakina wata bukka na hango asaman bishiyun nan É—onono,da alama kuma akwai mutum dake rayuwa cikin wanann bukkar. Dan kuwa kana iya hango abubuwa irinsu kwanuka,abin zuba ruwa,daga gefe kuma ga wani guri mai tudu wanda ke nuna alamun gurin kwanciyane.

Daga can gefen bishiyun nan na hango wata yarinya tsugunne gaban wata yar korama dake dauke da ruwa mai kyau da haske,gefenta kuma zagaye da yan kananan shuke shuke,yarinyar ta juya bayanta,kuma ba kaya ajikinta,dan daga ita sai wani dan karamin towel data ɗaura shi asaman ƙirjinta,da alama dai wanka take,dan kuwa ruwa take diba tana watsawa ajikinta.

Ahankali yarinyar ta mike tsaye tare da tattare uban gashin daya zubo gadon bayanta ta nannadeshi kamar gammo. sannan ta janyo wani dan zani ta daure kan nata dashi.juyowa tayi ta fara tafiya cike da kuzari atare da ita. Ta nufi jikin bishiyar nan.
Masha Allah !!!shine abinda bakina ya iya faÉ—a,sakamakon arba da kyakykyawar fuskar yarinyar da akalla shekarunta zasu kai sha takwas,doguwace mai matsakaici jiki,bazamu iya kiranta da Siriya ba,sannan bazamu ce mata mai jiki ba kai tsaye.tana da kira mai kyau da É—aukar hankali, daga kasanta abaje take sosai,tana da hips,sannan tana da albarkatun kirji,jikinta shar shar yake,ita ba bakaba kuma ba fara ba,irin choculate colour É—in nance.
Tana da rawn face,dauke da madaidaicin hanci mai kyau,idanunta dara dara ne farare tass dasu,bakinta dan karami,mai dauke da pink lips,ataƙaice dai zamu iya cewa kyakykyawar yarinyace ta gani afada.

Hankali kwance take takawa cikin É—an sauri ta nufi saman bishiyar nan, abin mamaki tana zuwa naga ta kama bishiyar cikin wani irin salo da kwarewa ta fara hayewa kamar wata biranya.kawai kama jikin bishiyar take tana É—an tsalle sai kaga tayi sama.
Cikin abinda bai wuce dakika biyar ba naga ta haye saman bishiyar nan.

Zama tayi tare da janyo wani abu mai kama da akwati,saidai kuma da itace akayishi.

Budewa tayi tare da ɗauko wani irin kaya masu kama da fatar damisa ta sanya ajikinta.riga ce doguwa,wacce duka duka bata wuce iyakar gwaurinta ba.sai wani wando irin skin tite dinnan shima iya gwuiwa,gashinta ta ware tare da ɗauko wani mataji mai ƙarfi dan da alama da katako akayi shi.

Taje kan tayi sannan ta rabashi gida biyu ta daure.bayan ta kammala daure kan nata,saita dauko wani ƙaton zani ta lulluɓa ajikinta,ga mamakina saina ga ta tada sallah,saidai kuma haka tayi sallar nan gwauri a waje,kuma akwai kurakurai sosai cikin sallar.tana idarwa ta cire zanin sannan ta dauko wata ƙatuwar kwari da baka ta rataya awuyanta, sannan ta dauki wata yar karamar wuka,ta soke jikin rigarta,inda ta janyo wata jela jikin rigar ta daure ta abaya.kanta ba ko dan kwali haka ta kama bishiyar nan ta sauko kamar yadda ta hau.

Tsayawa tayi tare da kallon gefen ta,kafin ta sanya hannu abakinta,harshen ta ta lankwasa sannna ta huri iska,nan take wani sauti mai kara ya fara fitowa daga bakin nata,kusan second biyar tana fidda wannan sautin, kafin ta dakata.saman wata bishiya naga tana kallo,fuskarta É—auke da murmushi.cikin tsalle da gudu naga wani biri dan madaidaici yana sakkowa daga bishiyar.kai tsaye akafadunta yayi masauki bayan ya gama sakkowar.
Dariya tayi tare da shafo jikinsa tace "janbu, zamu fita yau da wuri nake son muje mudawa,dan haka ka dage sosai yau kaji"ta fada cikin harshen Hausa tana shafa birin,

Shikuwa birin wani dan ƙara yake yi,alamun yaji abinda ta fada kenan,kafin ya sauko daga kafaɗunta.

Wani bakin abu mai kama da fata naga ta janyo daga jikin bishiyar da ta sauko,daurawa tayi akanta yayi kamar bandana,kafin ta fara tafiya,cikin azama birin yana Binta,suka nausa cikin dajin.

Masu karatu ina zata da wannan kayan haka?

Wacece wannan yarinyar.

Muje zuwa .

Anty mammy ce

Mrs babi💘💘

Share as much as you can.fisabilillah.[29/12, 6:41 pm] Mamy Kabir: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄




🎄🎄RAINON DAWA🎄🎄



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free page

3/4

Ga masu son karanta wannan littafi,zaku biya kamar haka.


Normal group 300₦
Update biyar asati.

Special group500₦
Update bakwai asati.

Gareku manyan mata,masu so ta pc.
1000₦

Zaku turo kudin ku ta nan.
Saratu kabir
U.b.a
2215749011


Evidence of payment
08148360851.







______________Tafiya take cike da izza,sam ba wata alama dazata nuna maka cewar tana cikin yanayi na tsoro.domin kutsa kai kawai take cikin dajin,yayinda baka jin komai sai sautin kukan tsuntsaye da kwarina.
Wannan birin da ta kira da jambu yana biye da ita,cikin dan gudunsa mai haÉ—e da tsalle.

Suna cikin tafiyar ne,ta hango wasu zomaye guda biyu.da sauri ta dakata,tare da daga wa birin nan hannu, alamun shima ya dakata,aikuwa dakatawar yayi tare da kamewa guri É—aya.

Kwarinta ta dauko da baka,ta sanya kibiyar cikin bakar,sanan ta É—ameshi sosai ta saita daya daga cikin zomayen nan ta sakar masa kibiyar.aikuwa cikin sa'a kibiyar ta caku acikin wannan zomon, nan da nan zomon ya fadi yana burbuwa, yayin da guda É—ayan ya zura da mugun gudu,yayi cikin wani rami.

Da gudu birin nan ya karasa gurin da zomon ke kwance yana burbuwa,daukowa yayi tare da dawowa gurin yarinyar.ita kuma yana zuwa ta karɓe zomon tare da yin Bismillah ta yanka wuyansa.
Zomon katone sosai,dan haka suna kamashi tace da jambu cikin muryarta mai daÉ—in sauti"jambu mu koma gida kawai,wannan ma ya ishemu "tana faÉ—in haka ta juya cikin takunta mai cike da burgewa,kamar tarwaÉ—a haka jikinta ke rausayawa.

Suna cikin tafiya ba zato ba tsammani wani ƙaton biri mai girma ya dira agabansu,birin baki ƙirin dashi,hakoransa jajaje, mai matukar muni.
Da sauri jambu ya dare kan kafadarta yana ihu,da neman inda zai boye ajikinta.

Ita kuwa cike da rashin tsoro ta ja ta tsaya,tare da kafe birin nan da ido,tana gyara tsayuwa.
Wani ƙara birin yayi tare da girgiza,kafin ya nufota da gudu.

Ja tayi da baya tare da zaro wukar data soke ajikinta itama ta nufi birin nan da gudu.
Abin mamaki suna haduwa tayi tsalle tare da darewa bayan birin ta soka ma wukar nan akafaÉ—arsa.
Wani ƙara birin ya sanya tare da yin wani juyi ya wurgar da ita can gefe.
Faduwa tayi tare da buga kanta jikin wata bishiya,ƙara ta sanya tare da dafe goshinta wanda ya fashe, da gudu birin nan yayi kanta baki buɗe yana ihu shima.
Saidai yana kusantowa gareta,wata irin bakar guguwa ta tashi,nan da nan gurin yayi duhu matuka,baka iya ganin komai sai karan birin nan dake tashi cikin guguwar nan,janbu ne ya garzayo gareta tare da tabata,yana É—an kara,ganin har lokacin tana kwance dafe da kanta.

Tashi tayi da sauri tana mai rungume janbu ajikinta,tare da zuba wa wannan guguwar ido,wacce ke kadawa aguri É—aya tana ta juyi,yayinda karan birin nan ke kara tsananta cikin guguwar.

Kusan minti biyu kafin guguwar ta lafa, sai kuma gurin yayi haske,can gefe suka hangi birin nan,cikin wani irin mugun yanayi,kwance yake gaba É—aya jikinsa jini ke zuba.

Tashi tayi tare da maida wukarta, tana bin wani farin haske da ido, sannan tayiwa janbu alamun su bar gurin.
Cikin hanzari suka bargurin tare da komawa inda bukkarta take.
Cikin salonta na kuzari ta haye saman bishiyar nan,tare da zama tana mai dafe kanta,dan kuwa ta bugu sosai.
Janbu ne yazo jikinta yana kallonta tare da dan karansa.
Kallonsa tayi kafin ta É—anyi murmushi tace "karka damu janbu,ba wani zafi fa,zai warke,ka kwantar da hankalinka"ta fada tana shafa bayansa.
Shikuma yana kara maƙalewa ajikinta.

Kamar wacce akace ta duba gefenta, kawai tana juyawa taga wannan zomon da suka kamo dazu, ajiye kusa da ita.
Sam batayi mamaki ba dan dama irin hakan tana faruwa,duk lokacin da wani abu yayi nufin cutar da ita,to wannan guguwa zatazo ta taimaketa, kuma bata taba barin Abunta awani gurin ba,kuma ta dawo makwancinta bataga abin nan ba.dan haka ta riga ta saba da irin hakan tun tasowarta cikin dajin nan.
Murmushi ta sake yi akaro na biyu kafin tace "janbu kamar dai kullum yauma kaga zomon da muka bari agurin can, ankawo mana shi"ta fada tana janyo zomon gareta.
Cikin kankanin lokaci ta fara gyara zomon nan da wukar da taje farauta, Ni dai bansan inda ta samo wuta ba,kawai naga wuta tana ci daga gefenta.murmushi naga tayi kafin taci gaba da aikinta, cike da rashin tsoro ko fargaba.haka ta gama hada naman nan taci wanda zata ci,ita da janbunta, sannan ta kwanta.kwanciyarta kenan barci yayi gaba da ita,yayinda janbu ma kwanta kusa da ita.
Iskace mai sanyi ta fara kadawa cikin dakin na tsawon minti biyu,kafin wani haske ya bayyana gefen da yarinyar ke kwance.ahankali hasken ya rikiÉ—e ya koma wani kyakykyawan saurayi,fari mai matukar kyan idanu,kallon yarinyar fuskarsa É—auke da murmushi,kafin ya buÉ—e rafin hannunsa,saiga wani dan karamin abu mai haske ya bayyana cikin hannun nasa,budewa yayi tare da lakuto wani jan abu adam yatsanshi,agishin yarinyar ya fara shafawa ahankali yana kallonta.

Gama shafawarsa keda wuya,gurin ya koma yadda yake ba ciwon,kamar ma bata taɓa jin wani ciwoba.

Haka wannan saurayin ya mike bayan ya gama shafa mata maganin,sannan ya zama farin haske yayi waje.
Wannan kenan.

Abuja birnin tarayya.
Da misalin ƙarfe uku na rana,cikin anguwar maitama, wani rantsatstsen gida na hango,mai matukar kyau da ɗaukar hankali, kaida ganin gidan kasan cewa,ko cikin masu kudin ma,to ba kowaba.dan tsayawa fadar kyan da gidan kedashi ma bata lokacine.

Kai tsaye na kutsa kaina cikin gidan domin dauko maku rahoto.

Wata hamshaƙiyar Hajiya na hango,zaune kan daya daga cikin rantsatstsun kujerun da sukayiwa falon ƙawanya,tana zaune da waya akunnenta,cikin wata hadaɗɗiyar kwalliya mai cike da kyau da tsari,irin ta manyan mata masu ji da gayu dakuma Naira.

Fara ce, amma ba irin can ɗin nan ba, kyakykyawar mace mai cikar haiba da zati,waya take, cike da nishadi,tana faɗin"yanzu Aslam ka kammala karatun ka,tun last week,Amma kaki dawowa gida,me yasa kake son zama cikin masu jan kunnen nan ne?ga kakarka nan kullum zancen ta daƴa Aslam. Gaskiya ya kamata ka dawo gida, muma muna bukatar ka kusa damu"ta kai ƙarshen zancen ta cike da nuna zallar son ganin wanda take wayar dashi.

Daga can daya bangaren,naji wata murya mai cike da izza,wanda kana jin muryar nan kasan ma'abocinta zaiyi son girma da rashin don raini.
"Ki kwantar da hankalinki,mommy zan dawo very soon,akwai Abinda Ya tsayar dani anan din amma dana kammala I will be back home soon kinji mommyna"ya ƙarasa cikin sigar rarrashi.

Ajiyar zuciya matar tayi kafin tace "shikenan Aslam,Allah ya dawo da kai gida lafiya,kannanka ma suna kewarka sosai"ta fada tana canza tasha da remot din dake hannunta.

Murmushi yayi kafin yace "ki sanar dasu,nakusa dawowa,saidai ina nan kamar yadda suka Sanni,dan haka saisu kula su nutsu,dan ba sassauci ga wanda yayi ba daidai ba"ya faÉ—a cike da salonsa na son girma.

"Ai sun sani,Bama saina ƙara faɗa musuba, yaran da idan kana guri ko ƙwaƙwƙwaran motsi basa iyayi,basu ba ma, hatta Aman baya wargi idan kana guri"ta faɗa cike da son tunasar dashi,ƙannan nashi fa basu manta halinsa ba.
Murmushi yayi yana kada kafa, haka yake so,ace duk iskancin mutum to yaji tsoron Aslam,Dan Aslam yana son raini ko kaÉ—an.sun jima suna hira ta waya da mahaifiyarsa,cike da nuna kulawa da kauna, har saida taji tsayuwar motar mijinta kafin sukayi sallama ta kashe wayar.

"Alhaji yanzu goben zaka tafi can Niger É—in, Kenan?"mommy ta fada,bayan mijin nata ya fito daga wanka,tana zaune abakin gado.

"Ina sha Allahu Madam,gobe zan tafi,akwai bukatar zuwana Niger gobe,saboda in duba abubuwa yadda suke tafiya acan,kinga shi Aman makaranta yake zuwa,dama da ace Aslam ya dawo ne to shi zan tura,amma tunda baya nan dole in je da kaina"ya faÉ—a yana goge kansa da towel.

"Shikenan, Allah ya kaimu,Amma dai ya kamata Ku tafi tare da Aman tunda kace amota zaka tafi,dan nikam ina tsoron wannan dajin dake tsaninmu da nijer,dan ance akwai abubuwan cutarwa cikin dajin"ta fada cike da nuna fargaba.

Murmushi Alhaji yayi,kafin yace "banda abinki ai komai nufin Allah ne,duk abinda ya faru da mutum dama can Allah ya nufa,dan haka karki damu,zamu tafi tare da Aman É—in,tunda gobe week end ne"ya faÉ—a lokacin da yake sanya kayansa.

Murmushi Mommy tayi kafin tace "Allah ya tsare hanya Alhaji"
"Ameen yace kafin ta zuba masa abinci yafara ci.


Misalin ƙarfe biyar yaran sukan dawo gida.cike da tabara suka shigo falon,
Cikin sakalci jannat ke kiran "Mommy mun dawo,wllh na gaji "ta fada tana jefar da jakarta aƙasan falon.

Hanan ma cike da sakalci ta jefar da jakarta tana zama ragwab akan kujera"wash Mommy ruwa zansha"ta fada tana turo baki tare da jingina kanta jikin kujera.
Mommy kuwa saukowarta kenan daga É—akin ta,tajiyo hayaniyar yan shagwabar ta ta,girgiza kai tayi tana zama akan kujera kafin tace"nikam zanga randa zaku girma wllh,sakalcinku yayi yawa,yanzu duba kigani jannat anan kika jefar da school bag din ki,kuma bazaki daukeba, sai dai adauke miki.
Ke kuma wai ruwa zaki sha,gaki ga fridge Amma jira kike adebo miki Kisha,Gaskiya lamarinku sai du'ai wllh"Mommy ta fada cike da jin takaicin sakalcin yaran nata.

Turo baki jannat wacce ataƙaice zata kau shekara kusan ashirin aduniya tayi,kafin yace "haba Mommy ɗaga dawowarmy,zaki fara mana faɗa,shiyasa wllh nake son Daddy ba ruwansa da faɗa"ta fada tana barin gurin ba tare da ta dauki jakarba.

Hanan ma tashi tayi tana kwalawa mai aikinsu kira"ramatu, maza ki kawomin ruwa dakina, bana son mai zafi "ta fada tana wajewa sama ita.

Girgiza kai Mommy tayi kafin tace "Allah ya shirya minku"
Aman ne ya shigo dakin da sallamarsa,yana kada keys É—in mota,zama yayi kusa da Mommy yana faÉ—in"ji Mom ya gida"
Murmushi tayi tare da shafa kan Aman tace "Aman ka dawo ?sannu"ta fada cikin murmushi.

"Na dawo mom inna granny ?ko bata dawo ba"ya...


Read / Download RAINON DAWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album