Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

IBTISAM Complete Hausa Novel Document by IBTISAM


IBTISAM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24341



IBTISAM

Reading Time: 2 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Ayusher Muhammad ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07043079282 , 07065283730

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 134.15 kb

File Type: txt

Views: 2009+

Download: 1078+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: IBTISAM......
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai....
Daga gareshi muka zo gareshi zamu koma, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani jama'a ya kuma tsareni da rubuta abinda zai gurbata al'umar ma'aiki Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wa Salam....(Ameen)


*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Available product👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀�?

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549

Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode🤝

Shafi na Farko. 🤸🏼‍♂�?

     KANO STATE (BUK NEW SITES)

  Sanye take da doguwar rigar abaya, ta yane kanta da mayafi dark purple, hannunta dauke da handbag irin babbarnan, wacce ke cike da litattafai, kafarta wani flat shoe ne kalar mayafinta. Doguwa ce sai dai ba irin cancan ba, fatarta ba mai haske bace haka kuma bamai duhu bane, batada jiki dan a koda yaushe Mamanta fada take mata akan rashin maida hankali gun cin abinci, tana ganin kamar shi yasata rama.
Gefenta kawayenta ne wanda da alama tare suka fito daga lectures, suna tafe ana hira ana dan shewa, suna kokarin shan kwana tai trus taja ta tsaya tare da kurawa wani bangare daga can nesa kallo da idanunta. Runtse idanunta tai a kuma take yanayin fuskarta ya canza, kallan gun sukai suka kalleta sai suka sheke da dariya a tare harda tafa hannu. Fuskarta a daure tace "Dalla dariyar ku kuma ta menene?" Wacce ke kusa da ita tace "Ibtisam anya mutumin can ba ya wadudu kikamai ba? Mutum kamar mara aikinyi sai bibiyarki?" Dan karamin tsaki taja tace "Ainah bansan iskanci, dadinta dai yayana ne in ma da biyu kikai maganar."
Dayar ta sa dariya tace "Wannan ko cikinku daya ai cewa zamuyi bashida lafiya balle kiri-kiri duk munsan sanki yakeyi." A ranta tace ni wannan soyayyar tun kafin ma aje ko ina ta isheni. A fili kuwa kallansu tai kawai tai dan murmushin yake, dan batasan ma me zata kuma ce musu ba.
Fara tafiya sukai tare da daga mata hannu alamar bye-bye, itama dan daga musu tai tace "Sai gobe in Allah ya kaimu."
A hankali ta fara takawa zuwa inda yake sam fuskarta babu fara'a, hannunta yadan daga ya rike jakar dake kafadarta, hakan yasa dan saman hanunta ya fito.
Shikam tunda ta taho ya kafe ta da ido yana jin wani azabar santa na sake ratsashi, idanunsa ne yakai kan hannunta sake waje, a take ya daura fuska tamau, harta karaso gun bai dauke ido daga kanta ba.
Cikin dan sanyayen murmushi wanda kana gani zaka fahimci bai kai zuci ba tace "Yaya ina wuni?" Kallanta kawai yake ya kasa amsawa, itakam wannan kallan na bala'in kular da ita, can ta daure ta sake cewa "Yaya!"
Cikin daurewar fuska ya juya ya kalli gefe da gefe ganin ba namijin dake kallanta yasa yadanyi ajiyar zuciya yace "Ba ba kiga hannunki a waje ba?"
Kallan hannun tai sannan ta saukeshi wani abu ya kara tokare mata magogwaro.
Fuskarsa haryanzu a daure yace "Na na na siyo miki hijabai kinki sakawa yanzu ina amfani haka?"
Bata tankashi ba dan batasan ranta ya baci yanzun nan.

Murmushi ya mata ganin yanda ta kawar da kanta yace " Kun kun fito lafiya?" Kai tadan daga kafin su fara tafiya a tare, ba wanda yai maganar sai tafiya kawai da sukeyi, can ta daure tace "Yaya nikam me yasa kullum kake jirana? Baka tsoron randa Abba yaji ya maka fada? Yace baka maida hankali kan aikinka?"
Tafi kowa sanin halinsa magana baya yinta mai tsayi sai azabar zuciya kamar me. Cikin dan maganarsa mai dan in-ina kadan yace " Ib Ibtisam hankalina ba-baya kwanciya in ba zuwa nai na rakaki gida da kaina ba."
Wannan abu itakam ya isheta, da batasanshi ba wlh da tuni sun hau sama sun fado, ace namiji tunkafin ya aureka yabi ya takurawa rayuwarka? Matsalar daya dan uwanta ne tana tunanin abinda zaije ya dawo, dan a yanda yake ba abinda bazai iya aikatawa ba in ta wulakantashi.
Sun dan yi tafiya kadan, suka iso gate din makaranta, daga baya taji ana kwalla mata kira, kafin ta juya shiya fara juyawa, fuskarnan tasa a daure kai kace makiyinsa ya hango. Juyawa tai tadan fara komawa kadan tana kallan saurayin dake gudu yana neman tarosu.
Dan hannu ta daga mai kadan alamar ya tafi a hankali, nan ya karaso yana hakki fuskarsa dauke da dariya yace "Book dinki." Yai maganar yana mika mata, ta amsa tana dan murmusawa tace "gudun duk na menene? Ka jira gobe ka bani mana?"
Dan bayan kansa ya dan sosa yace "Ban isa ba, kin ban aran note dinki ai dole na dawo dashi da wuri dan a sake bani aro nan gaba."
Zata sake magana ya kalli saurayin da ya hade fuska a bayansu kamar mai shirin dambe harda dunkule hannu, yace "Hmmm! Wannan saurayin naki har tsoro yake ban, ji yanda yake kallona kamar wanda nake kokarin kwace masa ke." Bata kalleshi ba tace " Nagode! Sai gobe."
Ta juya ta fara tafiya, tana isowa inda yake ta kalleshi tace "Yaya mu wuce?" Ai kamar ta taboshi nan fa ya fara zabga mata masifa kamar zai daketa, "Ke baki da aiki sai yiwa maza dariya? Sannan uban wa ya hanashi yin note? Bama wannan ba meyasa bazai ari littafin a gun namiji dan uwansa ba? Kina irin wannan ta ina zan yarda dake? Ta ina zan kwantar da hankalina? Ni wannan makarantar ta isheni sam ta hanani sukuni kullum tunanina me kikeyi? Da wani namijin kike magana, haba! Ni na gaji wallahi da kin aureni kafin ki fara bazan ma soma barinki ba."
Baki kawai ta bude tana kallansa, yau kam ankaita makura, ko mahaifinta bai taba tsareta yana watso mata tambayoyi haka ba, wato da alama wannan in akai auren ma bazai barta ta gama karatunta ba.
Cikin matukar kunar rai tace "Yaya ni na tilasta ka soni? Ko kuwa rokanka nai? Akan me soyayyarka zata nemi haukatani? Ka hanani sukuni, kawaye wannan bana zama dasu muyi magana, kullum kana tsare dani, biki wannan ko ziyarar kawayena ban isa nai ba sai dai ka tasani a gaba kamar 'yarka, taya mahaifina bai tsawalawa rayuwata ba saurayin da ba mijina ba zai takuramin? Wannan ko na aureka zargi ma bazai bar auranmu yai kargo ba........."
"NI KIKE WA MAGANA HAKA?"
Yanda ya daka mata tsawa ne yasa ta kasa cigaba da magana. Kallansa tai yau itama takai iya wuya tace "Dan Allah ka saukakemin wannan soyayyar na gaji haka nan, wannan ko auranka nake zan nemi ka sauwakemin balle....."
Abinda ta fada kenan ta fara tafiya, tana mita, "Haka kawai? Wannan wani irin masifa ne? So ya zama hauka, gaba daya rayuwata an lalatata banda zabin kaina ko ra'ayina?"
Shikam yana tsaye a gun ya dunkule hannunsa, saurayin daya kawo mata book dazu ya kalla, wanda yake ta tafiyarsa, da gudu ya bi bayansa, shikam tafiya yake baimasan ana binshi ba.
Ibtisam ganin shirin yayi yawa yasa tadan juya dan ta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download IBTISAM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album