Join Our WhatsApp Group

SULTANAAH Book 1 Complete Hausa Novel Document by SULTANAAH Book 1


SULTANAAH Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 20676



SULTANAAH Book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 24, Apr 2024

Author: Ashanty Love ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08140754777

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 114.99 kb

File Type: txt

Views: 250+

Download: 121+

Last download: 2 hours ago

Description/Story:  ♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔


ᗩՏᕼᗩᑎTY LOVE.


# WORK OF FICTION.
# ADVENTURE.
# DESTINY.
# ROMANCE.
# HEARTBREAK.
# HOT LOVE.
# MYSTREY.
# Royalty.



⚠︎: 𝑊𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑖𝑟𝑘𝑖𝑟𝑎𝑟𝑟𝑒𝑛 𝑙𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖 𝑛𝑒. 𝐵𝑎𝑛𝑦𝑖 𝑠ℎ𝑖 𝑑𝑎𝑛 𝑐𝑖𝑛 𝑧𝑎𝑟𝑎𝑓𝑖𝑛 𝑤𝑎𝑛𝑖 𝑘𝑜 𝑤𝑎𝑡𝑎 𝑏𝑎. 𝐷𝑢𝑘 𝑤𝑎𝑛𝑑𝑎 𝑦𝑎𝑔𝑎 𝑦𝑎 𝑔𝑖 𝑑𝑎𝑖-𝑑𝑎𝑖 𝑑𝑎 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎𝑟 𝑠𝑎 𝑎𝑟𝑎𝑠ℎ𝑖 𝑛𝑒.


________________❦︎_________________

𝐴𝑙ℎ𝑎𝑚𝑑𝑢𝑙𝑙𝑖𝑙𝑎ℎ ,𝑑𝑢𝑘𝑘𝑎𝑛 𝑦𝑎𝑏𝑜 𝑑𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑖𝑦𝑎 𝑠𝑢𝑛 𝑡𝑎𝑏𝑏𝑎 𝑔𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ. 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑘'𝑎𝑟𝑎𝑤𝑎 𝑚𝑎𝑛𝑧𝑜𝑛 𝑚𝑢 𝐴𝑛𝑛𝑎𝑏𝑖 Muhammad (𝑆.𝑊.𝐴)𝑑𝑎𝑗𝑎𝑟𝑎. 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑘'𝑎𝑟𝑏𝑖 𝑖𝑏𝑎𝑑𝑢𝑛 𝑚𝑢,𝑦𝑎𝑠𝑎 𝑚𝑢𝑛𝑎 𝑑𝑎𝑔𝑎 𝑐𝑖𝑘𝑖𝑛 𝑏𝑎𝑦𝑖𝑛 𝑠𝑎 𝑑𝑎 𝑠𝑢𝑘𝑎 𝑠𝑎𝑚𝑢 𝑟𝑎𝑏𝑜 𝑚𝑎𝑖 𝑔𝑖𝑟𝑚𝑎 𝑐𝑖𝑘𝑖𝑛 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑤𝑎𝑡𝑎 𝑚𝑎𝑖 𝐴𝑙𝑏𝑎𝑟𝑘𝑎. 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑚𝑎𝑖𝑚𝑎𝑖𝑡𝑎 𝑚𝑎𝑛𝑎.


❤︎ EID MUBARAK ❤︎







☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆



Chapter
1/5.




YEMEEN. NIGER


2005.



Bansan taya zan iya kwatanta muku yanayin rayuwar mu ba a wannan lokacin. Muna rayuwa ne can wani yanki dake cikin YEMEN Niger. Buzaye ne mu rayuwa muna yinta cikin kwanciyar hankali da Annushuwa. K'aramin kauye ne inda muke amma Allah ya hore mana jindaɗin rayuwa. Nasan zaku ce me ku ke dashi?. Yaruwa muna yinta cikin y'anci da kaunar junan mu. Kunsan mu buzaye yanda muke rayuwa. Bani da wasu shekaru a wannan lokacin dan shekarata 7. Zan sheda irin matsanancin kauna da iyayena da kuma mutanen kauyen mu kewa juna. D'an kowa na kowane. Muna da matsanancin had'in kai. Wannan kad'ai ya isa mu samu kwanciyar hankali. Duk inda aka ga wani abu dazai kawo mana cikas cikin kauye za'a had'u a tattauna dan samun masalah. Daga ni sai iyayena da nake matuƙar kauna. A duniya bani da wasu masoya daya wuce su. Na taso cikin gata, kauna da soyayya. Bamu da wani ilimi mai zurfi saboda yanayin rayuwar mu. Amma akwai tarbiya. Sannan duk alhamulis da juma'a har zuwa ranan lahadi mahaifina yana tara yara nan k'ofar gidanmu bakin bishiyar Mangoro da tun tasowa ta na tarar da ita. Zai ta bamu tatsuniyoyi da kuma labarai masu Jan hankali musamman na yankin kudu. Abbu na yana yawan cewa shi ba haifeffen d'an Yemen bane. Hasali ma shi dan gudun hijirane shida Innati sun baro k'asar su ta haihuwa ne saboda irin mulki na zalunci . Bansan kuma me yasa ba sam basa son fad'an wace k'asa ce asalin k'asarmu. Duk sanda na kawo zanchen sai su kauce baza su bani amsa ba. Innati tana yawan cewa

"Nadeeyah akwai wata k'asa da zakiyi alfahari da ita banda wannan da ki ka buɗe ido ki ka ganki a ciki?, wancan k'asar ba k'asa bace da za'ayi alfahari ko kwantace da ita , k'asar ki ita ce nan YEMEEN kar ki manta wannan"

Idan Abbu yana bamu labarin irin zaluncin da ake k'asar saboda mulki ba k'aramin tsoro abun yake bamu ba. A koda yaushe yana samana tsoron Allah da kuma gudun cin zarafin wani ko na misk'ala zarratan . Yakan ce duk abunda wani zaiyi muku dan zalinci ku barshi da Allah zai isar muku a duk inda kuke. Addu'a wadda aka zalunta karbabbiyace domin Allah baya yafe hakk'in wani kan wani sai in shi mutum yace ya yafe masa.



✿︎✿︎✿︎✿︎


Mummunan kaddarar da ban taɓa tunanin zata same ni cikin kuruciya ta ba ita ce ta same mu a daren yau. Hayaniya da kuma ihuce-ihuce mutanen rugar mu ta farkar dani daga barcin da nake mai nauyi jikin Innati. Cikin barci na farka ina kallon Abbu dake tsaye bak'in k'ofar d'akin mu yana k'ok'arin rufeta cikin firgici. Tunda na taso ba'a tab'a rufe k'ofar ba sai yau. Sai dai a saki asabari da zai rufe ko ina. Tunda na taso wannan al'ada ce da mutanen kauyen mu ke yi saboda halin rayuwa. Bamu da asibiti ko masallaci, ko makaranta. Dalilin da yasa bama rufe k'ofa dan wani zai iya neman taimako cikin gaggawa. Da y'ar muryar ta ta wanda ya tashi daga barci nake kallon Abbu dake tsaye jikin k'ofa cikin matsanancin tashin hankalin da ban taɓa ganin sa a ciki ba. Kallon Innati nayi data k'ara rungume ni tsam cikin k'irjin ta itama dai tashin hankalin ne kwance kan fuskarta kaman na Abbu.

"Abbu, Innati ihun mene haka naji mutane suna yi?"

Da sauri ya k'araso inda muke ya durkusa. Hannu ya tura cikin rawanin sa ya fito da wata sarka kaman ta zinare. D'aura min ita ya yi yana kallon Innati da naga hawaye masu zafi sun biyu kuncin ta. K'asan rigata ya tura sarkar sai kuma ya kunce gashin kaina da Innati ta nade min shi tsakiyar kaina kaman gammo. Shekara 5 nake amma za kayi mamakin yawan gashi na da kuma tsayin sa gashi baki sid'ik. Har wajen gwiwar kafata yake zuwa. Shi yasa duk bayan wata Innati ke rage min tsayin sa. Da ita da Abbu na rasa wana biyo gurin gashi. Danma Abbu bai cika buɗe fuska ba kullum nad'e yake da rawani ya rufe fuskarsa sai idonsa kawai ka ke gani. Idan kaga ya kwance rawanin to cikin d'aki yake daga shi sai ni da Innati idan kuwa ya kwance har kitso nake masa naita ja masa kai dan gashin sa har gadon baya yake kwanciya. To itama Innati haka. Abun tambayar shi ne meke faruwa ne? Wannan sarkar fa?. Goshi na ya sumbata idan sa tab cike da hawaye yace

"Nadeeyah duk wani bayani da zanyi miki yanzu baza ki fuskanta ba saboda k'arancin shekarunki, amma ina so ki riƙe wannan sarkar da kyau, duk runtsi karki yarda wannan sarkar. Babu wani lokaci da zan iya yi miki bayani da zaki fuskanta, amma kar ki manta a koda yaushe muna tare dake"

Shar naga hawaye sun biyu kuncinsa. Galala na tsaya ina kallon sa .sheshshek'ar kukan Innati ya d'auke min hankali na juya ina kallonta. Cikin rashin wayo da yarinta na rungume Innati na riƙo hannun Abbu shima na jawosa na rungume su kan kirjina. Hannun Innati ,Abbu ya kama yana mata murmushi. Ihuce-ihuce da guje-guje da nake ji na mutanen karkarar mu ya yi yawa ga sawon kaman dokuna . A hanzarce Abbu ya miƙe ya kama hannun Innati da nawa k'ofar da yake b'ulla tacan bayan Sahara ya buɗe. K'ofar kaman boyyayyir hanya ce da Abbu ke yawan bi idan yana san kad'ai cewa cikin sirri. Binsu kawai nake har yanzu na kasa fuskantar komai. Babu zato muka ji wata murya mai kaushi da cikin tsantsan larabci da ban iya shi sosai ba lokacin sai kuma k'arar dokuna a bayan mu.

Wani irin fisgata Abbu ya yi ya sab'a kan kafad'a ya riƙe hannun Innati muka hau gudu bana wasa ba.

Gudu muke mutanen suna biye damu har sun kusa kamomu. saboda nike fuskarta su ya bani damar ganin mutanen dake binmu kan dokuna sanye da kaya bak'ake sun rufe fuska da bakin abu. Kayan dake jikinsu kaman irin kayan nan na yaki irin wanda Abbu ke bamu labari. (Armour ). Wasu riƙe da takobi wasu kuma riƙe da mashi. Cikin wanda ke riƙe da mashin naga wani ya saita Abbu kafin nayi wani yunƙuri ya saki mashin ya tawo da mugun gudu .

Wani irin slow naga abun ya tawo na saki gigitacciyar k'ara ina kiran Abbu. Amma sai dai me Innati naga kawai ta fisge daga hannu Abbu ta tare mashin daya nufushi a guje ya huda saitin k'irji ta ya wuce. A take ta zube a k'asa tana tarin jini. Matsanancin kuka na fashe dashi ina kallon Innati dake kallon na ina sab'e kan k'afad'ar Abbu da murmushi kan leben ta dake motsi kaman mai magana.

Ganin da nayi Abbu kaman bazai tsaya ba sai sharara gudu yake ga Innati can kwance a k'asa cikin jini. Na fara buge -buge zan kwace ina kiran Innati cikin matsanancin kuka. Wani mashin suka k'ara harbowa Abbu ya yi maza ya kauce cikin zafin nama ya shige cikin ciyayi muka samu damar b'ace musu. Saida muka yi y'ar tafiya mai nisa mun shiga cikin dajin sosai babu alamun ana binmu sannan Abbu ya tsaya gindin wata katuwar bishiya.

Sauke ni ya yi yana haki ya jingina jikin bishiyar. Duk da cewar dare ne amma hasken farin wata ya haske sararin samaniya kana ganin komai tar. Sannan ina da wata baiwa koman duhun dare da nisan abu tar nake ganin sa kaman rana. Dalilin da yasa na iya hango mutanen da suka shigo cikin jejin da k'afafuwansu babu dokunan. Rigar Abbu na kama ina nuna masa da hannu. A firgice naga yana kallon inda na nuna masa d'an waige-waige ya yi ya jani da sauri ya tura tsakanin wasu ciyayi. Rawanin dake kansa ya cire ya nade fuskata dashi sai ido na kawai.

Ido na zuba masa ina kallon fuskar sa dake d'igar da hawaye da sai alokacin ma na lura dasu. Wani kuka ne ya k'ara zuwarmun mai k'arfi dan nasan kukan me Abbu yake. Sunan Innati na fara kira ina kuka sosai shima Abbu duk yanda yake daurewa kar ya yi kuka mai sauti kasa jurewa ya yi ya fashe da kuka mai k'arfi jikinsa na girgiza.

Durkusawa ya yi gabana yana sharemin hawaye murya a raunane yace

"Nadeeyah zanje na d'auko Innati kinji ko?, idan na tafi ki irga d'aya zuwa uku sai kibi nan "

Doguwar hanya ya nunamin mai tsayi daga can nesa kanajin k'arar teku.

"Kibi nan har sai kin bulle bakin gaba ki samu guri ki buya har sai na dawo da Innati kinji ko. Ki buya kar ki fito ko kinji motsi sai in na kira sunanki wanda ni kaɗai da Innatin ki muke kiran ki dashi. Gayamin sunan"

Murya na rawa nace "SULTANAAH" Murmushi Abbu ya yi ya kama fuskta yana kallona hawaye kwance kan kuncinsa

" kar ki manta har sai kinji wannan sunan zaki fito kinji SULTANAAH "

Shar hawaye suka k'ara wanke min fuska. Me yasa nake ji kaman sallama ce Abbu shima yakemin?. Goshina dake nade ya sumbata ya miƙe tsaye .

"Ina sanki SULTANAAH, INNATIN ki na sanki. A shirye muke mu bada rayuwar mu dan ceton ki. Muna tare dake a koda yaushe "

Saki na ya yi da sauri kafin nayi wani yunƙuri ya kwasa da gudu ya koma hanyar da muka biyo. Gursheken kuka nake ina k'ok'arin danne bakina. Saboda baiwar da nake da ita na samu ganin Abbu har ya b'ace daga ido na kafin ya fice daga dajin ya juyo yana kallon duhun sa bak'insa na motsi na karanta kalman da yake cewa.

"MY SULTANAAH"

Murmushi ya yi mai had'e da kuka ya juya da sauri ya fice ba tare da yaci karo da mutanen dake nemanmu ba. Kuka nake sosai na kasa motsawa daga inda nake har suka k'araso inda nake b'oye. Ido na runtse ina jin motsin su daf da inda nake .

Wai su waye wad'annan mutanen mai suke so?, mai muka yi musu da suka tarwatsa mana duk wani farin cikinmu cikin d'an k'ank'anin lokaci? . Ina jinsu suka gama zagaye- zagayen suka dumfaro inda nake boye bayan ciyayi. Numfashi na d'auke na k'ara damke ido na tsaya kam rungume da k'irjina dake bugawa. Muryar su naji a kaina da sauri na buɗe ido na na zaro su waje ina shirin kwasa da gudu.

Abun mamaki gasu dai a gaban nawa amma babu wani alamu da yake nuni da sun ganni. Ga d'aya kusa dani kaman zai tab'a ni. Baya naja da sauri ina kallon su dafe da kirji. Babu alun ya ganni ya juya da sauran mutanen sa suka koma inda suka fito. Me hakan ke nufi? Gani gasu amma basu ganni ba?.

Iska naji ta d'an kad'a mai sanyi har saida na k'ank'ame jiki. Wooshh naji iskar tabi bayan kunne na sai kuma naji kaman magana.

"SULTANAAH nan"

A firgice na juya bayana dan ganin wanda ya yi maganan. Wayan babu kowa. Matsanancin tsoro ya k'ara kamani. Iskar ta k'ara kad'awa wajen saitin kunnena na dama ta wuce Wosshh na k'ara jin wata maganan kaman daga cikin Iskar ma take fita.

"Nan SULTANAAH "

A guje na kwasa hanyar da Abbu ya nunamin yace nabi tun d'azu na kasa bi. Gudu nake ina kiran Abbu da Innati ban tsaya ba sai da na fara hango hasken ruwa da farin wata ya haske na k'ara kaimi dan sai nake ji kaman sawun mutum ne bayana idan na juya kuma bana ganin kowa.
Sai dana kai bakin tekun na samu guri na zauna ina maida numfashi. Waige-waige nake ta inda zan hango mab'oya amma babu sai cikin ciyayin dana fito. Sawun k'afafuwa da naji na mutane na yowa inda nake na miƙe a sukkuwanne da y'an kafuwana ina neman hanyar tsira sai gasu sun bullo. Ajiyar zuciya na sauke mai k'arfi ina kallon wasu daga cikin mutanen kauyen mu da yara dana shedasu a take. A guje na nufe su ina kira hakan yasa suka juyo kaina. Ido waje FAHIMA ta nufoni tana kira kaman yanda nake kiranta....


Read / Download SULTANAAH Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album