Join Our WhatsApp Group

ANGULU DA KAN ZABO Complete Hausa Novel Document by ANGULU DA KAN ZABO


ANGULU DA KAN ZABO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39749



ANGULU DA KAN ZABO

Reading Time: 3 Hours

Added On: 06, Oct 2023

Author: Badi'at Ibrahim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gawurtattu Biyar

Author Phone : 0702 616 6536, 0706 860 6171

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 220.79 kb

File Type: txt

Views: 655+

Download: 286+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*

1_2
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
Ina miƙa godiyata ga Allah subuhanahu wata ala, sarkin da babu irinshi, daya bani damar rubuta wannan littafin mai suna a sama. Wannan littafin tsumagiyane ga mata harda mazan ma. Wannan labarin labarine wanda ya faru a gaske, babu abunda na ƙasa bisa labarin. Hatta garurruwan ciki ban sake komai ba, unguwanni kawai na sassake, sai kuma sunayen jaruman labarin. Ku biyoni da sannu zaku gane me labarin ya ƙunsa.


Kano:

Anguwar Court road:
High court
"Bayan sauraron wannan sharia da kotu ta yi, tare da gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a gaban wannan kotu mai alfarma, tare da takaddar asibiti data tabbatar mana Hauwa Sada a cikin hankalinta take, bi ma'ana bata d'auke da matsalar data shafi k'wak'walwa. Kotu ta yi ma Hauwa sassauci sabida bata wahalar da sharia ba, wajan amsar laifin data aikata. Kotu ta yankema Hauwa hukuncin d'aurin rai da rai a gidan kaso." Damm Damm ya buga gudumar kotu wacce take nuni da an gama wannan case d'in.
Hawaye nake zubarwa sosai, tashin hankalin da nake ciki a dai_dai wannan lokacin, ba abu bane da zai fad'u balle harya rubutu masu karatu su fahimta ba.
Aminu na kalla, idanunshi sun k'ada sun yi jawur tabbas yama fini shiga tashin hankali. Dubana ya sake sauka akan yarana mata, wanda naja musu abun fad'en da har abada baza'a dena nuna su dashi ba. A gefe kuma ga k'annena wanda na kasance musu uwa da uba, kasancewarmu marayu, duk da ko wacce a cikinsu a k'ark'ashin inuwar Aure take. Mak'otana wad'anda akai zaman mutumci na kalla.
Duniya kenan, yanzu rayuwata a killace a waje guda zata k'are babu wani motsi?" wata gandiroba macece ta iso cikin d'an akwakun da nake tsaye, hannayena sanye da ankwa, ta ingiza k'eyata tana wani mun muruzai."
Kaina a k'asa muka sakko, 'yan sanda kuwa ta gaba da bayana duk gasunan, sabida tsaro. Ina jiyo sautikan koke_koken dangina da masoyana, a cikin kunnena. Amma in d'ago in kallesu na kasa. Hantar cikina sai rawa kawai take yi, hakan ya yaifar mun da zazzab'i me mugun zafi, da jiri da naji yana shirin ka da ni. Ga k'irjina da nake ji tamkar yafi komai nauyi a jikina, tun sanda wannan k'addarar ta faru na soma jin wannan ciwon k'irjin, wanda ban tab'a samun sauk'inshi ba."
muna fitowa bakin k'ofar kotu, nan fa manaima labarai suma suka kunno dan gudanar da aikinsu, wannan gandiroba dake rik'e dani sai naga taja ta tsaya." Nan suka shiga jero mun tambayoyin da bansan ma ta ina zan soma amsasu ba."
"Ku yi hak'uri ba wani abu da zata iya cewa a halin yanzu, dan Allah ku barmu haka nan muji da abunda ke damun mu" Cewar Aminu kenan Baban su Mardiyya."
Gandirobarnan ta jani har zuwa gaban motar da zata sada ni da gidan yari. Duk da dai kwanana biyar a cikin gidan yarin, ina jiran sharia. Amma a waiting room nake ba asalin cikin yadi ba." Waiting Room wani dogon ɗakine wanda anan ake ajjiye masu laifin da suke jiran shari'a.
Jikina da 'kafafuna na rawa na d'aga k'afata na shiga cikin motar na zauna.
D'ago kaina na yi da sauri dan yima Ahalina kallon k'arshe.
Aminu na gani a gaba, sai Mardiyya d'iyata tana rik'e a hannunshi. Idanu ya k'ura mun cikin rauni da sarewa yace."
"Wannan itace k'addararki Hauwa ki yi hak'uri, sannan kiy ta yin istingifari, Allah mai sauraron kukan bawane kuma maji roƙone."
Sabbin hawayene suka zubo mun. Hak'ik'a nayi rashin Aminu. Da yarana, ta tabbata na bar ahalina."
K'ofar motar Aka rufe Direba kuma ya ja motarshi ya fice a cikin kotun."

Aminu
Dauriyace kawai ya ke yi, domun baya son yayi kuka a gaban yaranshi, ya sake tsinkar da zukatansu, kuka suke yi sosai. dangin Hauwa ne su ke ta rarrashinsu.
Nanfa 'yan jarida suka yi ca akan Aminu, a k'ok'arinsu na lallai _lallai sai sun ji k'wak'wab. Da kyar suka fita a cikin kotun, tare da taran abun hawa.

Jakara city Kano:
Anguwace ta talakawa masu fad'i tashin naiman na kai, dan ganin asiri ya rufu.

GIDAN IYAYEN HAUWA:
Maza ne a k'ofar gidan anata k'arbar gaisuwa, taburmai ne manya a shinfid'e, cike da dattawan anguwa. Baffa Junaidu yana ganin tsaiwar Adaidaita sahun su Aminu, saiya tsallako ya taso.
Su mardiyya kuma suka shige cikin gida, inda ya kasance shima dank'am da mata 'yan ta'aziyya. Baffa Junaidu, k'ane yake ga malam Sada mahaifinsu Hauwa, shima a cikin layin yake tare da iyalanshi, gidajensu a jere suke dana juna.
"Aminu Yaya shariar ta kasance kuma me ake ciki, sunk'i ba da belin Hauwa ko?" Aminu ya rasa me zaice, dan zazzab'ine a jikinshi yau kwana bakwai kenan, baya ko iya rintsawa tunda ya ji labarin abunda Hauwa ta aikata, a cikin tashin hankali da jinyar rayuwarshi dake shirin salwanta yake. Nunfashi ya ja yace."
"Baffa Junaidu, Hauwa dai mun yi iya yinmu, dan ganin anyi duk binciken daya dace a gudanar, dan wallahi duk inda lauyan yasa k'afa nima anan nake sawa, bamu zauna ba. Amma duk wata hujja ta tabbata Hauwa ta aikata laifinta, dama ita bata wahalar da sharia ba, a zaman farko ta sanar da gaskiyar lamarin."
Muryar Baffa Junaidu na rawa yace.
"Hukuncin kisa ne ya tabbata a kanta ko?" kai kawai Aminu ya iya gyad'awa, zuchiyarshi na tafasa sosai.
"Innalillahi wa'innailaihilrajium kaico kaico da wannan mummunan aiki da yarinyarnan ta aikata, gashi ta jefa kanta da mu kanmu a cikin damuwa.Ni wallahi wannan zaman makokin ma da akeyi wallahi kunya yake bani, dan kulma ce ta ajjiye mafi akasarin jama'ar dake zaune a wajan, ga kunyar surukanmu. Aminu ka yi hak'uri naga yanda lamarinnan ya jijjigaka fiye damu dangin Hauwa. Duk da abunda ta aikata maka amma kana cikin lammuranta dumu_ dumu." Guntun hawayene ya taru a idanunshi guda d'aya. Aminu Namijine mai zuchiya da k'wazo, ba kasafai damuwa ya cika bata dama ta rusa shi ba. Amma Hauwa ta rugurgushe mishi jarumtarshi da k'wazonshi gabaki d'aya."
"Baffa nace ko zamu je gidan yarin muje mu dubota ne?" Baffa ya yi shiru yana nazari yace. Sai daya nisa yace.
"Gaskiya ne Aminu, babu yanda zamu yi da wannan k'addarar, amma bari in kira Jamila me bin ita Hauwan sai mu d'unguma ai. Jirani ina zuwa"
A tsaye Baffa ya tafi ya bar Aminu a tsaye a rana, yanayin yana ji tamkar wani irin nannauyan mafarkine mai wuyar farkawa. k'arar kwarab'abbiyar wayarshi da ke ajjihun wandonshi ce ta dawo dashi daga zauren tunanin daya lula. Saminu abokinshine yake kiranshi.
"Assalamu Alaikum Saminu, yaya akayi?" Daga cikin wayar Saminu yace.
"Ameen wa'alaikassalam, Aminu k'arfe nawa ne zaman kotun ne?" numfasawa yayi sannan yace.
"Zaman kotu ya k'are Saminu, yanzu haka ma dubo Hauwa zanyi a gidan yari. Saminu yace.
"Au da gaske ashe rashin hankalin Hauwa yakai ta iya aikata wannan abun? Tabb lallai na tsinke da lamarin Hauwa, ban tab'a cin karo da mace mai taurin zuchiya da kafiya irinta ba" murmushin yak'e Aminu yaima Saminu yace.
"Ka fiye sharri, ka bari zamu yi magana inna koma gida, saima naje asibiti dan bana jin dad'i jiri da ciwon kaine suka sani gaba. Irinna shekarun baya.
"Aminu dama nasan za'a rina an saci zanin mahaukaciya, amma na kusan shigowa kano,tunda dai mun gama sauke lodinmu, dawowa kawai ya rage mana, dana dawo zan shigo, ka gaishe da Dada. Sallama su ka yi Aminu ya sauke wayarshi a kunne."

Cikin gidan
Su Mardiyya na shiga cikin gidan nanfa idanu ya koma kansu, sai kallonsu akeyi. Jamila ta ja hannun ummu da Nanne k'annen mahaifiyarsu da suka tawo daga maiduguri. A k'uryar d'aki suka zauna dan tattaunawa.
"Ni ummu ki sallami matannan 'yan zaman makoki da suka cika gidannan,wallahi gulmace ta kawo su ba gaisuwa ba. Tunda can ma Zaginmu suke yi balle yanzu." Hafsa tace.
"Ni fa naga har k'annen Baban shamsu, da matan yayyenshi duk sunzo suna tsakar gida, kuma fa ba shiri muke yi da su ba. Gulma ce kawai.
Nanne tace.
"Ina zuwa bari inje in sallamesu su watse.
Fita tayi ta sallami kowa.
"Dan Allah kowacce mace ta tafi gidanta mun gode da gaisuwa Allah ya saka, adda'ar bakwai an riga anyi tun asuba. Dan Allah kuje."
Nanfa wasu suka soma ya da habaici harda zagi, da d'aya da d'aya duk suka watse, sannan ta shige d'aki wajan 'yan uwanta.
Baffa ne yaga mata sai fitowa suke yi a cikin gidan suna surutai harda masu shewa. Kai kawai ya girgiza ya kutsa kai cikin gidan.
Har cikin uwar d'akin ya shiga.
"Nanne sai kuma kuka ji abunda ya faru a kotu, an yi ma Hauwa d'aurin rai da rai." Nanne ta dafe k'irjinta tare da fashewa da kuka tace.
"Bamu ji ba, kai wannan masifa da yawa take. Ni wallahi abun yayi mun yawa wallahi." Ummu tace
"Yanzu tana gidan firsina kenan? Yarinya da yarinta a jikinta bak'ar zuchiya yasa ta aikata abunda ta jefa kowa a damuwa." Mardiyya tayi maza ta fice a d'akin ta koma falo. K'annenta ne suka mara mata baya, nan suka shiga rera kuka abun tausayi.
Su Nanne ma kukan suke yi. Sai Sameera ce ta daure tace.
"Yanzu dai adda'a ya kamata mu bisu dashi kawai. A dena tono maganarnan sabida su Mardiyya. Baffa yace.
"Yaron da zai Aurenta ma yana waje a cikin 'yan zaman makoki. Jamila ki taso mu je firsinan mu duba ita Hauwan mu dawo kafin malaman da zasu raba gadon naku su iso, a raba a sauke ma Marne nauyi."
mik'ewa Jamila ta yi dama da mayafi a jikinta bata cire ba. Fitowa su ka yi falo, Mardiyya tana zaune k'annenta duk suna jikinta sun mayar da'ita uwa. Cikin rauni Jamila ta ciro nera d'ari biyu a k'ulle a bakin zanenta tace.
"Kunga Mardiyya ku kama hanya ku tafi gida ku zauna a wajan Dada. Ki daure zuchiyarki sabida k'annenki kuyi ta hak'uri. Mardiyya jikinta na rawa ta amshi kud'in ta ja k'annenta. Tare suka fito da su Baffa. Wajan Aminu suka nufa.
"Mardiyya ina zaku je? Ya jefo musu tambaya, tausayinsu da kunyarsu duk ta gama cika shi. Cikin shesshek'a mardiyya tace.
"Abba gida zamu tafi" Ajjihunshi ya laluba bashi da ko sisi yace.
"Ki kula dasu ku tafi a hankali har ku isa gida." Cike da mugun tausayinshi Jamila tace
"Na Basu kud'in abun hawa ma, su samu su isa da wuri.
"An gode Jamila" Titi suka nufa dukkansu. Su Aminu suka hau Adaidaita sahunsu, su mardiyya ma su ka hau nasu.

GIDAN D'AN KANDE
KURMAWA PRISON:

Hauwa
motarmu ce ta tsaya a wajan ajjiye motoci, gandiroba ta fito dani daga cikin mota. Zuwa ciki.
Mata ne guda uku akan layi ana musu tambayoyi akan laifin da suka aikata. Duk da suna da takaddu mai d'auke da bayanan mutum a ciki da irin laifinshi. Hakan baya sawa su kasa tambayarka ka sake jaddada laifinka a gabansu. tsawa Gandirobar da ke zaune a kujera ta daka ma wata data kira da Ramatu.
"Nace laifin mai kika aikata aka kawo ki gidannan kiyi magana."
Cike da tsoro da fargaba Ramatu tace.
"Kisa na aikata aka kawoni gidannan." Kallonta gandirobar tayi kawai tace.
"Mariya a kaita a bata kaya, Ramatu in akwai waya a jikinki ki fito da ita kafin a bincikeki. Sannan ki cire d'ankunnenki da sark'a da zobe ki ajjiye. Mariya zata kai ki block d'inku. Ke matso kefa meye laifinki?"
ni dai ina tsaye ina sauraronsu har akazo kaina."
"A'a 'yar shuwa kun dawo, hala kotu ta yanke hukunci kenan?" Kai kawai na gyad'a mata. Gandirobar da muka je kotu tare ta ajjiye takaddata. Karantawa tayi tace."
"Mariya Ga Hauwa d'akinsu d'aya da Ramatu, ku tafi tare a basu kaya." Jiki a mace dukkanmu muke binta har zuwa wani ofishi. Kaya ta mik'a mana."
"Gashi zaku rik'e a hannunku, in lokacin fitowa waje yayi sai ku saka, amma in kuna d'aki zaku iya zama da kayan gida a jikinku. Amma in zaku fito yadi ku tabbatar kunsa kayanku, dan a tantance ku. Ku yi hak'uri k'addara kowa da irin tashi. Zaman gidan gyaran hali ba zama a jahannama bane. Da sannu zaku yi walwala har nutsuwa ta saukar muku uhm?" ku muje in rakaku block d'inku."
muna biye da ita a baya. Ni dai jefa k'afata kawai na ke yi amma babu nutsuwa a tare dani. Hankalina ya na wajan Aminu da 'yan yarana."
*BLOCK B*
haka naga an rubuta a jikin bangon da muka sha kwanarshi. wani dogon coridor muka shiga mai d'auke da dakuna, amma kuma abun mamaki d'akunan a bud'e suke ba a kulle kamar yanda nayi tunaniba. Wasu sai kai kawo su ke yi a zauren, yayin da kuma wasu suke zazzaune a k'ofar d'akunansu, wasu ma suna zaune akan gadajen kwanansu.
"Sannu sir mariya." Shine abunda suke ta ce mata. da fara'a take ta amsawa. Wani d'aki muka shiga mai d'auke da gadaje shidda sama da k'asa na kwanan mai rai goma sha biyu kenan. Mata uku muka samu a zaune a d'akin. Biyun suna k'asa a zaune suna cin abinci. D'ayar kuma tana zaune a bakin gado tana sak'ar hular sanyi na jinjiraye sak'ar kwaraishe na farin k'ulu."
"Sir mariya barka da zuwa. Munyi bak'i ne?" A cewar ta zaune a kan gadonta kenan."
"Eh uwatale ga bak'inan Wannan Ramatu wannan Hauwa. Dubanmu tayi tace.
"Hauwa, Ramatu ga abokan zamanku nan, nanne dak'in naku, sai ku kula dan Allah ku saki jiki kuma"
Hawaye na soma zubarwa, take wata nadama mara amsani da saukarmun. Uwatale ce ta zaunar dani a bakin wani gado, matan da suke zaune kuma suka kamo hannun Ramatu suka zaunar da'ita.
Zuchiyata ce ta tsinke sosai.
Yanzu a cikin d'akinnan da gidannan zan k'araci rayuwar duniyata? Uwatale tace.
"Kuka ya zama dole, mu muka k'adartoma kanmu wannan k'addarar, da sannu zaku zama 'yan gida. Shekarata goma a cikin gidannan, nayi kai harna zama 'yar gari, nice shugabar d'akinnan, ko wacce anan ta same ni. Hauwa kuyi hak'uri kunji?" Murmushi mai ciwo na sakar mata, wani irin zazzab'ine ya rufemun ganina da ji na, take na soma rawar sanyi, kankace me sai Amai. matannan biyu su ka yi tsaye a kaina harda ma mak'otan d'akinmu. Uwatale kuma ta je ta tawo da Sir mariya.
Jikina ta tab'a taji shi kau da zafi sosai.
"Sannu Hauwa, zaki iya lallab'awa mu je d'akin shan magani?" Na kasa ce mata komai ma, sai uwatale ce ta taimaka mun na mik'e tsaye. Ahankali nake takawa bana ko iya gani, har muka isa d'akin shan magani."
"Sister Aisha ga mara lafiya nan ki duba ta, inna maganine sai a bata magani, in kuma na zuwa asibiti ne sai a kiran danginta." Sir Mariya ce ke magana" Wacce aka kira da sister Aisha ta soma tambayata bayan taji zafin jikin nawa."
"Yaya kike ji yanzu haka?. Cikin nauyin k'irji nace mata.
K'irjina ne ya ke yi mun kamar an d'auramun garwashi, ga nauyi, sai jijiyar bayan kunnena kuma da take yi mun ciwo, har wajan ya kumbura."
Sister Aisha tace da Sir Mariya
"Gaskiya sai an fita...


Read / Download ANGULU DA KAN ZABO

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album