Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RUSHEWAR RAYUWA Complete Hausa Novel Document by RUSHEWAR RAYUWA


RUSHEWAR RAYUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 54232



RUSHEWAR RAYUWA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 11, Jul 2024

Author: Mariam sani Riamcool ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 08109554986

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 301.01 kb

File Type: txt

Views: 810+

Download: 654+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: *RUSHEWR RAYUWAA😓💔*



*By Mariam Sanee 🌹*


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*


*Wanna shine first book dina sai kunyi haquri da yi man uzuri*



*BISMILLAHIRAHMANIRRAHMANIRRAHIM*



*Page 3&4*
___________________✍️ "Shi ke nan Harisu ashe har ya haifi d'an da zai zageni da bai aure waccan ta wajen ba da bazata haifoman zabiyan yaro marar tarbiya ba ga 'ya 'yan Saratu da Halima nan ba wanda ya taba zagina" ta fada tana share hawaye har da jan majina kamar karamar yarinya.

Shi ko NURAIM baki sake yake kallonta shi bai ga abin kuka ba kuma da take cewa 'ya'yan Umma da Ummi ba Wanda ya taba zaginta kamar ba anjima za'a jisu ba shi wllhy shiyasa bai son ko zuwa wajen tsohuwan ga haushin muzguna wa Momy da take.

Ba yadda ya iya dole yace "ni fa dada ba zaginki nayi ba amma in abin ya b'ata maki rai Allah ya baki hak'uri" 'a hassale dada ta dago tana fadin "Amma kai ko Nura anyi d'an banza yaro ka dauki keyar duniya ka aza 'a kanka dan rashin kunya ina kuka iya Allah ya ban hak'uri kawai za ka ce baza kazo ka rarrashe ni ba amma nasan da Fatima ce zaka rarrrashe ta ai saboda ni iya Harisu na Haifa kai ban haife ka ba kai da uwarka kun nuna man wariyar launi fata Allah sarki Harisu na da shi ne na san da yanzun yana nan yana rarrashina har sai yaga zuciya ta wasai ba sauran abinda ke damuna Amma ni da yake ban haife ka ba Nura ni baka rarrashe ni ba Ina ganin kana da hankali kai Ashe mai wando sabule yama fika hankali wllhy Nura ka bi duniya 'a sannu" ta fada Tana sake rushewa da kuka.

"Ohhhhh ni wannan tsohuwa zata chaza man k'ai" shi ma a d'an hassale yace "wai ni dada nafa ce maki ba sunana Nura ba NURAIM din ne bazaki iya fada ba kuma da kike cewa na rarrashe ki nace maki Allah ya baki hak'uri to so kike na goya ki".

Ai dada 'a mugun hassale ta mike har zani na neman kuncewa ta daure shi gamgam Tana fadin "Nura bazan san ka gaya man magana ba sai ka mazgan" ta fada Tana bugun kirjinta "idan ko ba kai hakan ba to baka cika d'an Harisu ba jika ga Saude yar kitimurmara kuma da kake cewa idan baka ce Allah ya bani hak'uri
ba so nake ka goyani Allah ya sawwake Nura baka san Saude 'yar kitimurmara ba wllhy yanzun ne ruwa ya doki zakara d'an duk girman jikin nan naka baya hana na bugi rabona wayyo rayuwa Ina zaki damu ne wai ni yaron nan yake gaya ma magana idan ban yi sannu ba har iyayena idi mai fata da kuma Indo sai ya zaga" ta fada tana sake rushewa da kuka har da sheshsheka Tana fadin akan sunan yahudu da nasara wannan yaron yake gaya man magana.

Shi ko tunda ta fara baki sake yake kallon ta danshi abin ma dariya ya bashi dama yayi hakan ne shi ma dan ya dan cusa mata haushin da tasa mai.

Mikewa yayi yazo inda take ya duka yakama hannunta yana fadin "haba dadata ni fa duka abinda kika fadi ba haka nake nufi ba Amma Dan Allah ki yi hak'uri komai ki ke so zan maki Dan bana dake za'a sauke farali" ai dada na jin haka ta washe hakora Tana dariya hawaye na zubowa tace "ba komai jikalle na ya wuce shiyasa nake sonka wllhy Allah sarki Ashe har wannan shekarar zaka biya man Hajji Amma na zauna Ina kwashe maka Albarka kayi hak'uri Dan Allah Dan nasan da Mai wando sabule ne da yanzun ya kusa zubar min da hakoran gaba" murmushi yayi Wanda ya kara bayyanar da kyawunshi yana fadin "haba dada idan ban yi maki ba wakike son nayi mawa?" ita ma kara washe hakora tayi tace "haka ne Nura Ashe da rabon d'an Fatima zai riritani kamar uwarsa abinda ko Salihu auta be man ba yau gashi kai Nura kayi man Salihu kau shege mai kan faranti sai shegen makon tsiya Dan uban shi duk wahalar Dana Sha wajen haihuwar shi ba kamar kan Salihu shi yafi ban wuya da na haife shi nifa nasa Dan ruwa ne Al'qur'an sai daga baya na gane Salihu ba d'an ruwa ba ne da nai mashi hayaqin barkono dan ban mantawa Rabilu kanena har waka yake mai yana fadin 'Salihu Dan ruwa Mai kan Saude yar kitimurmara Nura kaji wani sharri wai ni Rabilu zai cema kaina da na Salihu iri daya ne dako iri daya ne da kakanka Malam Ali bai aureni ba yoo Allah na tuba ina dalili yana shigowa yaga rankwalelen k'ai na amsa sallama dan ni fa Huraira matar Salihu naga kokarinta data zauna dashi" ta qarashe zancen Tana fashewa da dariya.


Me NURAIM zai yi in ba dariya ba sai da yayi mai isar shi sannan yace "dada zan qara maki da umra cikin watan nan zaki tafi" ai zumbur dada ta miqe Tana taka rawa Tana cewa "Allah sarki jikana Ina kake son nasa kaina da farinciki ne".

Sai da ta gaji dan kanta ta zauna tana ma NURAIM fira shi ko in banda dariya ba abinda yake.


*****************
Mikewa tayi a matuqar firgice Tana furta "innalillahi wa Inna ilaihi raji'un shikenan Raihana dama nasan hakan zata faru" kuka muke dukkanmmu kafin Raheenatu ta tsagaita da nata kukan Tana lallashina sannan nayi shiru ga kaina dake wani irin sara man tashi tayi ta had'a man ruwan wanka Tana fitowa na mike na shiga ko da na fito ban samu Raheenatu ba a gurguje na shirya na nufi kitchen dan yin girki ko da naje yau ma iya Abu na gani har ta kammala a bakinta nake jin wai Aunty Amarya gobe zata dawo Allah ya maido ta lpia kawai nace ban qara cewa komai ba na koma bedroom na kwanta dan jin zazzabi na neman rufeni.

Raheenatu kuwa ko da ta fita ba inda ta zame sai sashen Mama tana zuwa taga Mama tayi dai daya iskar fanka da ta AC na bugunta ga fuskar ta duk tayi suntum alamun tasha kuka har ta gode Allah.

Raheenatu zama tayi ta gaisheta tana fadin ashe haka tsautsayi ya afku Allah ya kyauta gaba abu dai bai yi dadi ba Mama matsagin dare bai kyauta maki ba jibi yadda fuskarki ta koma gaskiya ki samu ki yi maganin gargajiya" ta karashe zancen da nuna damuwa a fuskar ta.

Mama ko ji take da Tana iyawa ba abunda zai hanata dukan Raheenatu yau ko ta huce bata san sadda tace "ke d'an ubanki tashi ki bani wuri yar iska kawai jira nake kawai na warke mayyar 'yar uwarki data turoman aljani ya tsargani sai ta gane bata da wayo" ta fada tana ci je lips alamar tana jin jiki har yanzun dan gefe da gefen bakinta duk an mata dogayen tsagu.


Raheenatu danne dariyar ta kawai take ta tashi tace "bari na gano Zulfa'u" da harara Mama ta rakata tana zuwa ta tura dakin Zulfa'u ta ganta ta wani bubbuda kafafu sai fifita take da sauri Zulfa'u ta had'e kafafu tana fadin "D'an uwarki Raheenatu koma fuskar tausayi tayi tace "ayya Adda Zulfa'u Ashe tsautsayi ya abka maki to Allah ya kyauta gaba Allah yasa kar haka ta daina aiki" banza Zulfa'u tayi mata Dan ba karamin haushi Rahinatu ke Bata ba gashi tayi zaune taki tafiya ta samu ta fifita ga zafi da wuri keyi mata (Dan ba Dan karamin barkono Raheenatu tasa mata ba).

Ita ko Raheenatu zamanta tayi tana fadin "ba inda zani ina nan sai na ga kwal uwar daka ai ko" zamanta tayi taki tashi

Da Zulfa'u ta ga Raheenatu taki tashi ga zafin ya isheta tace "d'an Allah Raheenatu jeki nagode haka nan" ta fada wani kululun bakinciki na kamata Raheenatu tace a'a Adda Zulfa'u anyi haka kuma kara ki bari na taimaka maki ko ruwan zafi na had'a maki ki gasa wajen kin samu sauki".
Zulfa'u tace "yawwa Raheenatu dako kin kyauta" da sauri Raheenatu ta shiga toilet ta had'a mata ruwa masu dan karen zafi tana gamawa ta fice.



Tana fita Zulfa'u ta mike ta shiga yoo ai Tana zama cikin ruwan ta kwalla uwar kara saboda azaba gashi ta kasa tashi zama tai ruwan na ta babbaka ta da kyar ta samu ta fito towel ma da kyar ta dorashi ta fito da rarrafe ko da ta fito faduwa tai dan azaba ji take kamar
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RUSHEWAR RAYUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album