Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: *RUSHEWR RAYUWAA😓💔*



*By Mariam Sanee 🌹*


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*


*Wanna shine first book dina sai kunyi haquri da yi man uzuri*



*BISMILLAHIRAHMANIRRAHMANIRRAHIM*



*Page 3&4*
___________________✍️ "Shi ke nan Harisu ashe har ya haifi d'an da zai zageni da bai aure waccan ta wajen ba da bazata haifoman zabiyan yaro marar tarbiya ba ga 'ya 'yan Saratu da Halima nan ba wanda ya taba zagina" ta fada tana share hawaye har da jan majina kamar karamar yarinya.

Shi ko NURAIM baki sake yake kallonta shi bai ga abin kuka ba kuma da take cewa 'ya'yan Umma da Ummi ba Wanda ya taba zaginta kamar ba anjima za'a jisu ba shi wllhy shiyasa bai son ko zuwa wajen tsohuwan ga haushin muzguna wa Momy da take.

Ba yadda ya iya dole yace "ni fa dada ba zaginki nayi ba amma in abin ya b'ata maki rai Allah ya baki hak'uri" 'a hassale dada ta dago tana fadin "Amma kai ko Nura anyi d'an banza yaro ka dauki keyar duniya ka aza 'a kanka dan rashin kunya ina kuka iya Allah ya ban hak'uri kawai za ka ce baza kazo ka rarrashe ni ba amma nasan da Fatima ce zaka rarrrashe ta ai saboda ni iya Harisu na Haifa kai ban haife ka ba kai da uwarka kun nuna man wariyar launi fata Allah sarki Harisu na da shi ne na san da yanzun yana nan yana rarrashina har sai yaga zuciya ta wasai ba sauran abinda ke damuna Amma ni da yake ban haife ka ba Nura ni baka rarrashe ni ba Ina ganin kana da hankali kai Ashe mai wando sabule yama fika hankali wllhy Nura ka bi duniya 'a sannu" ta fada Tana sake rushewa da kuka.

"Ohhhhh ni wannan tsohuwa zata chaza man k'ai" shi ma a d'an hassale yace "wai ni dada nafa ce maki ba sunana Nura ba NURAIM din ne bazaki iya fada ba kuma da kike cewa na rarrashe ki nace maki Allah ya baki hak'uri to so kike na goya ki".

Ai dada 'a mugun hassale ta mike har zani na neman kuncewa ta daure shi gamgam Tana fadin "Nura bazan san ka gaya man magana ba sai ka mazgan" ta fada Tana bugun kirjinta "idan ko ba kai hakan ba to baka cika d'an Harisu ba jika ga Saude yar kitimurmara kuma da kake cewa idan baka ce Allah ya bani hak'uri
ba so nake ka goyani Allah ya sawwake Nura baka san Saude 'yar kitimurmara ba wllhy yanzun ne ruwa ya doki zakara d'an duk girman jikin nan naka baya hana na bugi rabona wayyo rayuwa Ina zaki damu ne wai ni yaron nan yake gaya ma magana idan ban yi sannu ba har iyayena idi mai fata da kuma Indo sai ya zaga" ta fada tana sake rushewa da kuka har da sheshsheka Tana fadin akan sunan yahudu da nasara wannan yaron yake gaya man magana.

Shi ko tunda ta fara baki sake yake kallon ta danshi abin ma dariya ya bashi dama yayi hakan ne shi ma dan ya dan cusa mata haushin da tasa mai.

Mikewa yayi yazo inda take ya duka yakama hannunta yana fadin "haba dadata ni fa duka abinda kika fadi ba haka nake nufi ba Amma Dan Allah ki yi hak'uri komai ki ke so zan maki Dan bana dake za'a sauke farali" ai dada na jin haka ta washe hakora Tana dariya hawaye na zubowa tace "ba komai jikalle na ya wuce shiyasa nake sonka wllhy Allah sarki Ashe har wannan shekarar zaka biya man Hajji Amma na zauna Ina kwashe maka Albarka kayi hak'uri Dan Allah Dan nasan da Mai wando sabule ne da yanzun ya kusa zubar min da hakoran gaba" murmushi yayi Wanda ya kara bayyanar da kyawunshi yana fadin "haba dada idan ban yi maki ba wakike son nayi mawa?" ita ma kara washe hakora tayi tace "haka ne Nura Ashe da rabon d'an Fatima zai riritani kamar uwarsa abinda ko Salihu auta be man ba yau gashi kai Nura kayi man Salihu kau shege mai kan faranti sai shegen makon tsiya Dan uban shi duk wahalar Dana Sha wajen haihuwar shi ba kamar kan Salihu shi yafi ban wuya da na haife shi nifa nasa Dan ruwa ne Al'qur'an sai daga baya na gane Salihu ba d'an ruwa ba ne da nai mashi hayaqin barkono dan ban mantawa Rabilu kanena har waka yake mai yana fadin 'Salihu Dan ruwa Mai kan Saude yar kitimurmara Nura kaji wani sharri wai ni Rabilu zai cema kaina da na Salihu iri daya ne dako iri daya ne da kakanka Malam Ali bai aureni ba yoo Allah na tuba ina dalili yana shigowa yaga rankwalelen k'ai na amsa sallama dan ni fa Huraira matar Salihu naga kokarinta data zauna dashi" ta qarashe zancen Tana fashewa da dariya.


Me NURAIM zai yi in ba dariya ba sai da yayi mai isar shi sannan yace "dada zan qara maki da umra cikin watan nan zaki tafi" ai zumbur dada ta miqe Tana taka rawa Tana cewa "Allah sarki jikana Ina kake son nasa kaina da farinciki ne".

Sai da ta gaji dan kanta ta zauna tana ma NURAIM fira shi ko in banda dariya ba abinda yake.


*****************
Mikewa tayi a matuqar firgice Tana furta "innalillahi wa Inna ilaihi raji'un shikenan Raihana dama nasan hakan zata faru" kuka muke dukkanmmu kafin Raheenatu ta tsagaita da nata kukan Tana lallashina sannan nayi shiru ga kaina dake wani irin sara man tashi tayi ta had'a man ruwan wanka Tana fitowa na mike na shiga ko da na fito ban samu Raheenatu ba a gurguje na shirya na nufi kitchen dan yin girki ko da naje yau ma iya Abu na gani har ta kammala a bakinta nake jin wai Aunty Amarya gobe zata dawo Allah ya maido ta lpia kawai nace ban qara cewa komai ba na koma bedroom na kwanta dan jin zazzabi na neman rufeni.

Raheenatu kuwa ko da ta fita ba inda ta zame sai sashen Mama tana zuwa taga Mama tayi dai daya iskar fanka da ta AC na bugunta ga fuskar ta duk tayi suntum alamun tasha kuka har ta gode Allah.

Raheenatu zama tayi ta gaisheta tana fadin ashe haka tsautsayi ya afku Allah ya kyauta gaba abu dai bai yi dadi ba Mama matsagin dare bai kyauta maki ba jibi yadda fuskarki ta koma gaskiya ki samu ki yi maganin gargajiya" ta karashe zancen da nuna damuwa a fuskar ta.

Mama ko ji take da Tana iyawa ba abunda zai hanata dukan Raheenatu yau ko ta huce bata san sadda tace "ke d'an ubanki tashi ki bani wuri yar iska kawai jira nake kawai na warke mayyar 'yar uwarki data turoman aljani ya tsargani sai ta gane bata da wayo" ta fada tana ci je lips alamar tana jin jiki har yanzun dan gefe da gefen bakinta duk an mata dogayen tsagu.


Raheenatu danne dariyar ta kawai take ta tashi tace "bari na gano Zulfa'u" da harara Mama ta rakata tana zuwa ta tura dakin Zulfa'u ta ganta ta wani bubbuda kafafu sai fifita take da sauri Zulfa'u ta had'e kafafu tana fadin "D'an uwarki Raheenatu koma fuskar tausayi tayi tace "ayya Adda Zulfa'u Ashe tsautsayi ya abka maki to Allah ya kyauta gaba Allah yasa kar haka ta daina aiki" banza Zulfa'u tayi mata Dan ba karamin haushi Rahinatu ke Bata ba gashi tayi zaune taki tafiya ta samu ta fifita ga zafi da wuri keyi mata (Dan ba Dan karamin barkono Raheenatu tasa mata ba).

Ita ko Raheenatu zamanta tayi tana fadin "ba inda zani ina nan sai na ga kwal uwar daka ai ko" zamanta tayi taki tashi

Da Zulfa'u ta ga Raheenatu taki tashi ga zafin ya isheta tace "d'an Allah Raheenatu jeki nagode haka nan" ta fada wani kululun bakinciki na kamata Raheenatu tace a'a Adda Zulfa'u anyi haka kuma kara ki bari na taimaka maki ko ruwan zafi na had'a maki ki gasa wajen kin samu sauki".
Zulfa'u tace "yawwa Raheenatu dako kin kyauta" da sauri Raheenatu ta shiga toilet ta had'a mata ruwa masu dan karen zafi tana gamawa ta fice.



Tana fita Zulfa'u ta mike ta shiga yoo ai Tana zama cikin ruwan ta kwalla uwar kara saboda azaba gashi ta kasa tashi zama tai ruwan na ta babbaka ta da kyar ta samu ta fito towel ma da kyar ta dorashi ta fito da rarrafe ko da ta fito faduwa tai dan azaba ji take kamar ana yankan wajen ihun ma ta kasa yin shi.


Ko da Raheenatu ta nufi side dinsu kwance taga Raihana hankalinta yai mugun tashi ganin yanayin 'yar uwarta taba jikinta tayi taji zafi rau kwalla ne suka cika mata ido tace "na san ko naje wajen Mama ba bani magani za ta yi ba ko mutuwa zaki amma bari na gwada na gani riko hannun ta nayi ina fadin "Raheenatu Dan Allah kar kije ki bar shi kawai kinsan ko da Abba na nan ba baki zatayi ba ni Raheenatu da wannan bahaguwar rayuwar qara mutuwa" na fada Ina zubar da hawayen bakin ciki "Raheenatu kara ki barni na mutu ko an rage annoba ni kaina naji natsani kaina" dade man baki Raheenatu tayi Tana girgiza k'ai hawaye na zuba tace "haba Raihana kamar ba musulma ba Allah yana jarabtar bayinshi tako wace hanya Kuma yana jarabtar su dan ya gwada imanin su wanda su ka yi hak'uri kuma sune masu samun babban rabo anan duniya da kuma lahira kiyi hak'uri Raihana bayan wuya sai dadi in sha Allah".


*****************

Duke yake gaban wani mummunan yabidaddiyar tsohuwa ga hakora zako-zaki idanuwan ta jajir yanda kasan garwashi da kakkausar murya take fadin "jogu mun gaji da b'ata mana aiki da kake yi waccen karamar halitta ce kakasa da ita ga har yanzun bakai sadaukar wa ba.

Wanda aka kira da Jogu jikin shi na karkarwa yace "yake uwar gijiya hakika nasan na aikata laifi Amma a gafarceni a' kara bani lokaci, ita kuma yarinyar can zan san yadda zanyi na ida janyota k'ungiya" ya karashe zancen da kai goshin sa kasa (subhanallah).


Cikin murya mai amo tace "mun baka nan da yan watanni sannan sai maganar sadaukarwa wannan shekarar k'ungiya na bukatar jinin mace mai sabuwar haihuwa sai budurwar mace.


Tunda take zancen zufa ke karyo masa ba yadda ya iya dole ya amsa da zai yi yadda ake bujata sannan ya tashi yai ta wasu surutai wanda bangane mai ya ke cewa ba sai shi da yayi zai fahimci abinsa.

Ko da ya dawo gida yana ta tunanin ina ne zai sami mace sabuwar haifuwa da budurwar yarinya dole ne ya nemo mafita.

Alhaji Naseer tabbas shi kadai ne zai nemo mashi mafita.


*Bangare guda Kuma*

Tunda take zancen nake kuka mai tsuma zuciya shin Raheenatu sai yaushe ne abubuwa zasu dai-daita ne an cucemu an cuci mahaifiyarmu da yayanmu mafi soyuwa agaremu shin kina ganin zamu manta ina ji a' jikina Ammi ba mutuwa tayi ba" na karashe zancen ina sake rushewa da kuka.

Raheenatu ma kukan take taana fadin "Raihana ki daina cewa haka tabbas Ammi ta tafi tabarmu ba abunda take bukata sama da addu'a Yaya fauzan kuma Allah ya bayyana shi duk inda yake in yana raye in kuma baya raye Ubangiji kai masu rahama shi da Ammi".

Ji mu kai an banko kofar dakinmu da sauri muka tashi jikinmu na karkarwa dan tsananin razana.


*To fa waye wannan wanda su Raihana suka tsorata shin wai su meye asalinsu ne?*

*'Bangare guda kuma ga jogu shin ina zai sami mace sabuwar haihuwa wacce yarinya ce zai jawo cikin qungiyar su hmmmm ku dai ku biyoni domin jin wadan nan amsoshin*



*Comments, share and like*

Wadan nan sune kwarin gwuiwata



*By Mariam Sanee🌹*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA😓💔*



*By Mariam sanee🌹*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Wanna shine first book dina sai kunyi haquri da yiman uzuri idan anga kuskure*



*Bismillahirahmanirrahmanirrahim*




*Page 5&6*

_____________________Ji mukai an banko ƙofar ɗakinmu da sauri muka tashi jikinmmu na karkarwa dan tsananin razana ganin Abba da Mama da sharbeben icce a hannushi, zuwa yayi ya damƙo Raheenatu ya dinga bugunta yana faɗin "dan ubanki kashe min Mata zaku yi da Ɗiyata, Raheenatu na tsani diyan Sajeeda dandai na haife ku ne bani da yadda zanyi jibi yadda kika maida min mata, sauran ke Raihana bari na gama da ita na dawo kanki, wato maitar taki tafi ƙarfin kiyita a waje har cikin gida yi kike, kin turo iska ya tsarge ma matata fuska kuma ya lahanta min 'Ya, zaki gane kema nikam Sajeeda ta haifa min bala'i", ya fada yana huci da jibgar Raheenatu.

Ni kuwa kuka nake kamar Raina zai fita ga shi sai bugun Raheenatu yake yaƙi sassautawa ganin zai kashe min 'yar uwa ya sani zuwa na durƙushe na riƙe ɗafafunsa ina roƙonsa, juyowa yai a fusace ya sauke min iccen a tsakiyar kai, wata irin razananniyar ƙara na saki dan azaba ga jini nata zubowa dukda haka na daure dan na ceto 'Yar uwata, juyowa ya qara yi da zummar ya ƙara sauke min shi, mama tai saurin riƙe shi tana faɗin "miye haka kuma Alhaji, shin kayi hauka ne zaka bugi Raihana?, sanin kanka ne duk wanda ya buge ta ranar baya kwana duniya shin kaima so kake ta kashe mana kai", ta fada tana fashewa da kukan munafurci cikin kukan take faɗin idan ta kashemana kai muke da asara dan su basuda ita", jikin shi ne yai sanyi dan Abba ba daga baya ba wajen tsoron mutuwa amma duk da haka ya matse ya ce "Dan ubanta idan ta tashi cinye ni dan Allah karta ɗagamin ƙafa, karki sassautawa kurwata", ya fada yana zazzare ido.


Nikau durƙushe nake ina kuka shin Mahaifinmu ma bai son mu ina zamu je a somu ballantana ni da nazama annoba nasan ba wanda zai soni ya ƙaunace ni, zuwa nayi na kama Raheenatu ta tashi daƙyar itama kukan take tana faɗin "Raihana wallahi guduwa zanyi daga gidannan barin shi zanyi dan wata rana Abba sai ya kasheni da bugu ni kuma ban shirya mutuwa yanzun ba".

Saurin rufe mata bakinai ina cewa "ya isa haka Raheenatu kibar maganar guduwa daga gidannan baki da inda yafi maki nan duk lalacewar Mahaifinka har abada Mahaifinka ne baki da kamar shi a duniya".

Sai yanzun Raheenatu taga jinin dake zuba daga kan Raihana da sauri ta riƙe ni tana faɗin "Raihana ashe Abba yaji miki ciwo tashi muje nakai ki ko chemist ne".

Murmushi kawai nai mata nace "kedai kiji da jikinki kiyi ta kanki kar ki damu dani", hannu nasa daidai ciwon na shafe saiga wurin ya koma lafiya jinin ya ɓace kamar ba ai min komi ba.


Raheenatu da tsantsar mamaki take kallona tana faɗin "Raihana dama ko ciwo kika ji tsab zaya hade?".

Murmushi kawai nai mata nace "yanzun dai tashi kije ki gasa jikin kikisha magani".

"Ni ba abinda nake ji irin Abba tunda ake buguna ba wanda ya taɓa fito min da jini a jikina wadanda da ma iyakar su bugu ne an kashe su inaga wanda ya fitar min da jini", na ƙarashe zancen da damuwa a fuskata.



*****************
Da yaga dai Dada zata tsaida shi ne ya tashi yai mata sallama.

Kai tsaye part ɗinshi ya wuce yana shiga ya iske Nafisa ta caɓa uwar kwalliya ba laifi tayi kyau amma dukda haka saida yaji wani uban haushi da takaici tunawa da yayi ta zubarmai da ciki.

Itako tana ganinshi ta taso cikin karairaiya da takun manyan mata tana zuwa ta rungumeshi ta saki kukan kissa tana faɗin "dan Allah honey kayi haƙuri ni kaina nasan nayi kuskure wallahi sharrin zuciya ne in sha Allah Allah zaibamu wani nan bada jimawa ba kayi haƙuri".

Duk wani haushinta da yake ji da tijarar da zai mata yaji ya kau a zuciyar shi saima wata irin ƙaunar ta tasake wanzuwa a cikin zuciyar shi, anya zai iya rabuwa da ita kuwa?, zai iya son wata mace bayan ita?, bubbuga bayanta yayi yana fadin "it's ok don't mind beby just forget".

Shiru tai tana share hawayen ƙaryar da tayi tana faɗin "to honey muje yanzun na taimaka ma kayi wanka sannan kaci abinci".

"No bashshi kawai zanyi wankan da kaina jeki ki hada min ruwan wanka kawai", ya faɗa yana jan kumatunta, turo ɗan ƙaramin bakin ta tayi tana faɗin "honey baka haƙura ba?".
Ɓata fuska yayi ya ce "bansan wannan zancen ya wuce", to tace sannan ta tafi ta haɗa mashi ruwan wanka.

Koda ya fito tana nan zaune bakin gado tashi tayi tazo ta shirya shi kamar ƙaramin Yaro haka takama hannu shi ta kaishi har dinning zaunawa tayi da kanta tai feeding ɗinshi suna gamawa ya rungumeta yana faɗin "Allah yai maki albarka Nafeesa haƙiƙa yau kin sani cikin farin ciki faɗa min me kike so?, komai kike so zan baki matsawar bai fi ƙarfina a duniyar nan ba".
Cikin iya yi tace "haba my honey idan bansaka farin ciki ba a halin yanzun wa zansa ni kawai abinda nake so kayimin alƙawarin bazaka taɓa yiman kishiya ba shine kawai zai sani cikin farin ciki".

Gabanshi ne yai wata irin mummunar faɗuwa jin ta ambaci yai mata alƙawarin bazai mata kishiya ba cikin dauriya ya ce "haba Beby kema kinsan daga ke ba ƙari ina maki so na haƙiƙanin gaskiya son da bazan iya rabuwa dake ba".

Cikin tsantsar farin ciki ta sake rungumeshi tana faɗin haƙiƙanin gaskiya na yi dace da miji, miji na nunawa tsara bazan so kowace mace taraɓe ka ba ina tsantsar kishinka duk wacce tai ƙoƙarin raɓar ka kuwa tabbas zatai tsantsar nadama a rayuwar ta".

Jin anata danna door bell yasa su sakin junan su tashi tayi taje ta bude

Tana buɗewa taga Abdurrahim ta ɓata fuska
shiko baima wani tsaya bi takan ta ba ya shigo kyakkyawan matashin saurayine ya sha wankan sugar sai wani bubbuɗawa yake yana bouncing da gani a shekaru bazai haura 30 yrs ba yana zuwa ya samu wuri ya zauna suka gaisa da NURAIM

Nafisa kuwa baki sake take kallonshi tana zuwa itama ta zauna kusa da NURAIM ganin karta sa masa shakku a ransa yasa ta ƙaƙalo murmushin dole tace "kune ake gani a gidanmu ?",

ƙara tsuke fuska yayi ya ce "zuwan ma dan ya zama dole ne da ko ƙeyata bazaki gani ba".


NURAIM ne ya ɓata fuska ya ce "Abdurrahim bansan shashancin banza kazo har gidana ka gaya wa matata magana ina kallonka da ka shigo ko gaisheda ita baka yi ba kuma kazo kana gaya mata magana a kiyaye gaba",


Sake ɗaure fuska yayi tamau ya ce "Amma ai bro naga dai na tsaya nai magana da macen da ba muharrama ta ba bai kamata ba kuma kasan yanda nake da mace kamar annabi da kafiri, ni duk inda mace take ma indai ba 'yar uwa ta bace bani zama wajen".

NURAIM yasan halinshi da kafiya da taurin Kai shiyasa ya ƙyale shi ya ce "fadi abinda ya kawo ka".

Gyara zama yayi yace dama maganar ma'aikata n compa...... Sai Kuma yai shiru yana cewa wai Ashe wannan mujiyar nanan ke dallah tashi baki San kiga za ai sirri ba ne ke kitashi yafada yana sake doka mata wata uwar tsawar.

Ai da sauri nafisa ta tashi har tana tuntube ta nufi bedroom Tana shiga ta zauna Tana fadin kash Abdurrahim zai rushe man shiri ne naso naji bayanin company dinne ko Yaya ne Dan nasanp yanda zan bullo wa lamarin gashi ko na tambayi NURAIM zai zargeni ga shi ba fada man zaiyi ba dole nasan yanda zan bullowa lamarin.



*Bangaren jogu*



Yana tuna Alhj naseer ya lalubo number shi y doka mashi Kira yana fadin yana buqatar suyi haduwar sirri dashi daga dayan bangaren bansan me aka ce ba naji jogu yace su hadu a, gidan hutawar shi.


Yana Gama wayar ya miqe Kai tsaye gidan hutawar shi ya wuce koda yaje yadan jima kafin Alhaji naseer yazo


Yana zuwa ko bari su gaisa baiyi ba yake fadin naseer akwai matsala wannan Karin qungiya ta bijoraman da buqatar ta kaban shawara ya zanyi ya qarashe zancen da damuwa.

Alhaji naseer yace jogu kwantar da hankalinka mana Kai Mani bayani dalla_dallah


Ina nufin qungiya tace man nasamo mata macen da Bata kwana da haihuwa ba sai budurwar mace wannan Karin jinin su take buqata sannan Kuma waccan yarinyar nasan yanda zanyi na ida jawo ta qungiya saboda yarinyar ce zata ida Kai qungiyar mu matakin nasara shine nake neman shawararka

Mamadin yaji Alhaji naseer yabashi amsa sai yaji ya sheqe da dariya yana fadin jogu wannan qaramin aikin ne saika nemi shawarata abinda za ayi kawai kabari zan samo maka macen dabata Dade da haihuwa ba Kai Kuma kasamo budurwar.

Jogu yace to shikenan naseer Amma taya zangane budurwar virgin ce kasan yawancin 'yam matan yanzun ba sosai ake samun virgin ba.

Alhaji naseer yace Dan samun budurwar mace bazai ma wahala ba tunda

Please Login or Register in order to submit comment