Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ido da kuka yi mata da kanka ka Samar man House made, daganan na samu salama daga masifarta saidai gori da yaɓa baƙaƙen maganganu



Da taga ba Sarki sai Allah ya sa dan dole ta dunga janku a jiki, wanda a lokacin da batayi haka ba, haka dai rayuwa taci gaba da tafiya cikin ikon Allah kuka kammala Karatunku lafiya kaida Jabir, lokacin da ka dawo nayi farinciki marar misaltuwa ganin yadda ka zama babban mutum ga kamanninka da na Mahaifina sak babu wani banbanci, tunda ka dawo Nafisa tabi ta tare part ɗina kullum tana nan, tun abun na ban mamaki har ya daina bani,dan kafin ka dawo babu wani abun dake kawo Nafisa Sai idan mun haɗu a ɓangaren Dada tambayeni kai lokacin ta kammala Secondary school ɗinta





Bayannan Shaƙuwace mai ƙarfi ta shiga tsakaninku wanda saida naji tsoron hakan dan ko kaɗan bansan haɗa zuri'a da Jamila ko bani ba ina gujewa wanda zai haɗa zuri'a da Jamila saidai ƙaddara ta riga fata, a haka har Soyayya ta shiga tsakaninka da Nafisa wanda Dada najin hakan ta ce ba zai saɓu ba ace jikarta ta auri dangin tsiya, da ƙyar iyayenku suka samu suka shawo kanta, wanda hakan baiyi man daɗi ba, bayan Ni'imatu ta dawo aka tsayar da naku da nata rana ɗaya,

Saidai a cikin biyu na rasa wane zanyi tsakanin baƙinciki ko Farinciki sakamakon auren Ahalin sheɗanu da zakayi, saidai duk sanda nai yunƙurin faɗa maka wacce Jamila da ƴarta nakan kasa, haka na barwa Allah komai dan nasan ban isa nayi Abinda Allah baiyi shi ba,


A haka aka zo akayi aurenka da Nafisa wanda tun kafin ayi auren ta ɗauke yi man magana ita da Mahaifiyarta har kukayi aure ko gaisuwa bata gibtawa tsakanina da ita sai idan taga idonka ne take darattani a haka har kukayi shekara da aure sannan Ni'imatu ta haifi Amir lokacin Nafisa nada ciki 3 Month sai ji nayi kace ka kamata ta zubar maka da ciki lokacin hankalina ya tashi dan nasan tabbas da wata manufar tayi hakan bawai don bata son cikin bane saidan duniya ta riga da ta ruɗesu basa tunanin komai sai na samun duniya wanda duk iya abinda ka samu nan zaka tafi ka barshi sai iya ayyukan ƙwarai ne kaɗai zaka tafi da abunka, lokacin babu wani sirri na Jamila da ban sani ba,"

Mommy na kaiwa nan tayi shiru Hameed da Hameeda da ke tsaye suka tafo suka rungume mahaifiyarsu suna jin tausayin Mahaifiyarsu najin gwagwarmayar da tasha




Nuraim ne ya ɗago ya kalleta yana faɗin "Mommy me yasa kika ɓoye mana? Yanzun da ban riga na tambayeki ba haka zaki ta zaunawa da damuwa a ranki,"


Murmushi Mommy ta sakar mashi tana ta ce "Nuraim lokacin ina jin kunyarku na faɗa maku abinda aikata dukda nasan wannan ita ce ƙaddarata,"


Kallonta Abdurrahim yayi ya ce "Mommy insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe muddin Mahaifanki na raye mu kuma munyi Alk'awarin nemo maki su muddin suna raye,"


Zama sukayi suna yima Mahaifiyarsu Hira mai sanyaya zuciya don Son kwantar mata da mikin da ya tashi,



Bayan Nuraim ya tabbatar sun kwantar mata da Hankali ya miƙe yayi wa Mommy Sallama Zuciyarshi cike da tunanin Maganar da Mommy ta faɗa akan Nafisa da Aunty Mahaifiyarta, kanshi ya kulle ya rasa ta inda zai fara, ga nemo yarinyar da ya ƙwallafa rai a kanta wanda shi inba duniyara mafarki ba ma bai santa ba, gashi yanzun dole ne ya fara bincike a kan Nafisa da Aunty, amma ta ina zai fara? Dole ne ya sanyo Jabir cikin lamarin.






**************


Yaro ne ɗan kimanin 16 yrs da kurar ruwa yana turawa ga wata irin rana da ake ƙwalawa a haka ya dinga turawa har yakai kurar ruwan wani gida ya fito ɗibo waƴansu saidai yana tafiya yaji an ce "Sadeeq," juyowa yayi ganin Suhailat kallonshi tayi daga ƙasa har Sama sannan ta bushe da dariya tana faɗin "Niko naga Rushewar Rayuwa kai ka bige da garuwa kingin ƴan uwanka an siyar da su tabbas kukau kuka ga haza hada hazihi dan Bama kuga komai ba insha Allah sai munga bayanku banzaye ƴaƴan tsintacciya marassa galihu," tana kaiwa nan ta kashe shi da Mari


Dafe kuncin yayi Hawaye na bin kumatunshi dan marin bai mashi zafi ba kamar yadda ta kira Mahaifiyarshi da tsintacciya kuma take faɗin an siyar mashi da Adda Raihana da Raheenatu, dukda dauriya irin ta Sadeeq bai hana shi fashewa da kuka mai ban tausayi, yanzu shi kenan ina zai sake ganin ƴan uwanshi waɗanda tunda ya tashi dasu ya tashi baida wani bayan su kaɗai yake raba yaji sanyi.....✍️






Wannan kenan




*Please masoya Comment, Share fisabilillah*



Waɗannan sune ƙwarin guiwata




*By Mariam sani*






✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[11/29, 7:17 PM] Riamcool: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl


*Rushewar Rayuwa*

*NA*

*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*





*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*Page 39&40*

___________✍️Fashewa yayi da kuka mai ban tausayi, yanzu shi kenan ina zai sake Ganin ƴan uwanshi waɗanda tunda ya tashi dasu baida wani bayan su, su kaɗai yake raɓa yaji sanyi, gashi yanzun an mashi iyaka da su, yanzun shikenan a haka rayuwarsu zata ƙare,indai baka da uwa a cikin gida bakada wani ƴanci na rayuwa,ace su ga shi rashin uwa yaja masu dan tabbas da Mahaifiyarsu nanan bazata taɓa bari Rayuwarsu ta tagayyara ba,


Hankaɗa shi Suhailat ta ƙara yi tana barin wajen ta baɗe shi da ƙurar Motar ta, kakkaɓe jikinshi yayi yana miƙewa ya tafi dan sake ebo waɗansu Ruwan,




*GORIBA ROAD*


Zaune yake yana karanta News a jarida, Shigowar mama ce tasa shi dakatawa, yana sakar mata Murmushi, Saidai ganin yadda Fuskar mamar ke haɗe yasa shi haɗiye Murmushin sa,fuska murtuke tazo ta samu waje ta zauna, kallonta Abba yayi ya ce "Safara'u lafiya na ganki haka babu walwala,"

Cikin tujara Mama ta hayayyaƙo masa tana faɗin "Kaga Alhaji bansan jan zance Magana ce ta kawoni wakenka, dan na faɗa maka wllh Zulfa'u bazata taɓa auren wanda ka zaɓa mata ba, dan bazai yiyu kayi wa ƴata auren dole ba, bazan lamunta ba,sudai waɗancan da kayiwa sune dai_dai kuma ƙasƙantattu,"



Kallonta Abba yayi yana faɗin "Safara'u kenan Ni ban isa nayi iko akan ƴaƴa na ba,bani da hurumin da zan duba Mijin da ya dace na aura masu bisa sharaɗin addinin Musulunci,



Tashi Mama tayi ta wuce Fuuuu kamar zata tashi Sama,da kallo Abba yabita yana miƙewa dan jin wani kalar barci dake fisgar shi, Saidai yana miƙewa yaji Bama zai iya ko tafiya ba danjin baccin na wani irin fisgarshi Sulalewa yayi nan ƙasa ya kwanta,wani kalar nannauyen bacci ne ya ɗauke shi,


yana kwanciya yaji ana kiran Sunanshi bin hanyar da ake kiran Sunanshi yadinga yi, tun yana tafiya a hankali harya kai ga ya galabaita dan yayi tafiya ba kaɗan ba,haka ya dinga tafiya harya isa wani ƙungurmin daji da baka ganin komai banda tsirrai da itatuwa ga wani irin duhu da ya Mamaye dokar dajin,haka ya dinga keta itatuwan Wajen yana bi, yana zuwa dai_dai wani ɗan kurkun gida dashi kaɗai ne cikin dokar dajin ya tsaya,jin wata Azababbiyar ƙishirwa, har zai wuce wajen yaji an doka mashi tsawa ana faɗin "Dakata anan,'!!!! A hanzarce ya juyo gani tsohuwar da ta doka mashi tsawa,



Dudduƙe take tafiya harta ƙaraso wajenshi,kallonshi tayi da rikiɗaɗɗun idanuwanta tana "faɗin kai ina zaka wuce nan ya kamata kazo kasha Ruwan, dan duk tafiyar da zaka ƙara gaba bazaka taɓa samun rafi ba nan ne kaɗai zaka samu ruwan da zai kore maka ƙishi," ta faɗa tana zuba mashi idanunta masu kama dana Mage


Tunda ta fara zancen Abba yake kallonta cikin Tsoro saidai yanayin Muryarta da kalar idanu tabbas ya sansu saida ya rasa a ina ya sani,


Cikin tsoro ya shige cikin ɗan Akurkin gidan, yana shiga tabi bayanshi,wani ruɓaɓɓen tsohon ɗaki ta shiga,tana shiga ta dawo hannunta ɗauke da tsohon kofin Silver da ruwa a cikinsa, miƙo mashi kofin Silver tayi tana kafe shi da idanunta,jiki na rawa Abba ya karɓa yana sha, dan ji yake idan bai sha ba zai iya mutuwa,



Yana amsa ta saki wani Shu'umin Murmushi,Abba na Sauke kofin ruwan yaji Zuciyarshi an ɗaureta,wani kalar tari ya fara, tun yana yi a hankali harya kai ga yana yi yana aman jini gundari_gundari, da ƙyar tarin nan ya tsagaita,



ɗagowa Abba yayi yana faɗin "wacece ke?,"

Wata kalar sheɗaniyar dariya ta saki tana faɗin "ko baka tambayeni wacece Ni ba zan sanar da kai, tana gama maganar ta girgije sai gashi Tsohuwar nan ta koma RAIHANA

"Raihana,"shine abinda Abba ya furta yana faɗuwa ƙasa dafe da saitin Zuciyarshi, Wata kalar Dariya ta sake kecewa da ita wadda tasa ga baki ɗaya gidan ya dinga girgiza, tsagaita dariyar tayi ta haɗe fuska, takowa tayi harta ƙaraso inda Abba yake duƙawa tayi tana faɗin "Abba saida na gargaɗeka akan kada ka kuskura ka ɗaura man igiyar aure, amma gashi bakaji ba, tabbas Abba ka kassara Rayuwarka da kanka,ka kuma jazawa Wanda ka aura man dan shima bazai sha ba," tana kaiwa nan ta miƙe tana ɗakko wata ƴar tsana,

Kallon Abba tayi hawaye na biyo fuskarta tana faɗin "Abba yadda zan karya dukkan wata gaɓa ta jikin ƴar tsanar haka kaima taka zata daina aiki,"


Fashewa Abba yayi da Matsanancin kuka, itama Raihana haka ta dunga hawaye, ɗaga ƴar tsanar tayi ta kalli kudu tana waɗansu surutai,sannan dukkan wata gaɓa mai amfani ta dinga Binta ɗaya bayan ɗaya tana karyawa,dukkan wata gaɓa da ta karya ta jikin ƴar tsanar nan saida ta Abba ta karye tun yana ihu da kururuwa na ceton Rai harya kasa, haka ta ida karyawa sannan itama ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai,








*Raihana*

Firgigit na farka daga wannan mafarkin da nakeyi fuskata shaɓe_shaɓe da hawaye,a take na tuno da Abinda ya faru, "innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un," shine Abinda na furta ina fashewa da wani matsanancin kuka, ji nayi na tsani kaina na tsani Rayuwata dan tabbas da zanga mutuwa da kaina sai na tunkareta, ƙara mutuwa da gurɓatacciyyar Rayuwar da nakeyi na kashe Rayukan Al'umma, "wai Ni Raihana da kaina na kassara rayuwar Mahaifina shikenan yanzun Abba tashi ta ƙare," na faɗa ina mai rushewa da kuka, saida nayi mai isata Sannan na tashi na wanko fuskata na dawo na zauna,







*Raheenatu*



Tunda Alhaji Bashir ya kamata ta mari Sabreen ya ɗora mata dukkan wasu ayyuka na gidan komai ita keyi,da kamar bazatayi ba sai kuma ta tuno da Allah ya isar Abba, hakan yasa ta keyi,



Yauma kamar kullum uban aiki ne take ta uban yi, saboda Hajiya Bilkisu zatayi baƙi, sauri take tayi ta kammala, da sauri ta kammala wankin da takeyi ta tafi ta ɗora girki,



Tana zuwa ta kunna gas ta ɗora ruwa tana ɗorawa ta kamfato shinkafar da ko wankewa batayi ba ta antayata cikin tukunyar, sheƙewa da dariya Raheenatu tayi tana faɗin "Zaku ci ubanku dukkanku dan ina tsoron Allah ya isar Abba ne da babu abinda zai hanani casgaraka Alhaji Bashir, dan yau duk sai na horaku da yunwa," ta faɗa tana ƙara sakin wani Murmushin Mugunta






Haka ta bari shinkafar ta dinga dahuwa harta ƙone tana ƙauri ga shi tai wani ƙiri_ƙiri saukewa tayi ta sami haɗaɗɗun Warmers ta zuba


Sannan ta ɗora miya itama haka ta barta ta ƙone ga miyar ta cika mata uban manja da Attarugu, sai uban yaji,



Haka ta kammala taje ta jera a kan dinning, idan ka kalla sai ka wani ce wani haɗaɗɗen Abinci ne aka jera amma sai ka buɗe zaka wani ji uban ƙauri ya ziyarce ka, kallon dinning ɗin tayi tana faɗi "Zaku ci girkin Amarya daga ku har baƙin da zakuyi sheggu masu kan farenti," ta faɗa tana wucewa Side ɗinta



Tana shiga ta faɗa wanka tana fitowa tayi Sallah, tana gamawa taje ta gyara ta ɗan shafa powder da kwalli Sai lip gloss da ta ɗan shafa red,cakarewa tayi cikin wani haɗaɗɗen leshi, tayi ɗaurin ture kaga tsiya da ɗan kwalin, juyawa ta dinga yi gaban Mirror tana faɗin "kan uba daga zuwa Lagos har na koma hajiyar Lagos," ta faɗa tana sake jujjuyawa, haka ta zauna ta dinga shirmenta,


Tana zaune saiga ƴar aiki Hajiya Bilkisu ta aiko wai taje zasu gaisa da Baƙinta, tashi tayi ta biyo bayan ƴar aiki




Tana shiga dukkan Hajiyoyin Falon Sukayi Mata ca da idanu, waje ta samu ta zauna tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Sannan ta gaishe su dukkansu da fara'a a fuskokinsu suka amsa,





Wannan kenan





*Comments, Share fisabilillah*


Waɗannan sune ƙwarin guiwata





*By Mariam sani*





✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️






*08109554986*
[12/2, 8:21 PM] Riamcool: [11/30, 9:59 PM] Mariam sani: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl




*Rushewar Rayuwa*

*NA*
*Mariam sani*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*Bismillahirrahmanirrahim*


*Page 41&42*


_____________✍️Tana shiga dukkan Hajiyoyin Falon Sukayi Mata ca da idanu waje ta samu ta zauna tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya Sannan ta gaishe su dukkansu da fara'a a fuskokinsu suka amsa,Hajiya Bilkisu ce ta kalli Raheenatu cikin Haɗe rai ta ce "ke tashi ki fice hakanan tunda kun gaisa, ko kafin ki fita ki kwaso Abincin da kikayi daga dinning ki kawo masu nan,"


Tashi Raheenatu tayi taje ta kwaso Abincin da ta girka ta kawo masu nan, tana kawowa Hajiya Bilkisu ta buɗa Saidai tana buɗe shinkafar wani uban ƙauri ya ziyarceta, miyar ma da ta buɗe itama wani ƙauri da ƙarni take, a fusace Hajiya Bilkisu ta ɗago ta kwalfa ma Raheenatu Mari a kunci, miyar ta ɗakko ta sheƙa mata shi bisa farin Lace ɗinta,cikin Masifa ta ce "ke wace irin kidahuma ce? Dan Ubanki a gidan Ubanki haka kike girki Wato sainan zaki zo ki Mani Almabazzaranci a gida to Wllh Abincinnan duka Sai kin cinye shi, watakam dan kinga ina maki da sauƙi Shine zaki rainani, banza Jakka Tinkiya," Hajiya Bilkisu ta ƙarashe zancen da masifa




Kallonta Raheenatu take yi Idanunta duk Sun kaɗa sunyi jajir kallon Hajiya Bilkisu tayi ta ce "Wllh bashi kika ɗauka dan banga macen da ta isa ta taɓa kuncin Raheenatu ta zauna lafiya, wllh bashi kika ɗauka sai kinyi dana sani,"tana kaiwa nan ta fice zuciyarta na Mata ƙuna





Tana fita Kingin Hajiyoyin da suka kafe Raheenatu da idanu wato Hajiya Turai da Kuma Hajiya Madina Sai Hajiya Rabi, Hajiya Turai ce ta kalli Hajiya Bilkisu tana faɗin "Haba Bilki bai kamata ki biyo mata ta haka ba kamata yayi ki bita ta lalama dan tunda naga wannan yarinyar na ayyana abubuwa da dama akanta, kuma da na tsaya na natsu na karanci yarinyar akwaita da tsarin ido,dan na fi son ire_iren su masu tsaurin ido,"


Hajiya Bilkisu ta kalli Turai tana faɗin "me kike Nufi? Kwata_kwata ban fahimce ki ba ki fahimtar dani,"


Turai ta kalli Hajiya Bilkisu tana faɗin "Ina nufin yarinyar nan ita ce wacce muka fi son ire_irensu wajen kasuwancimmu, Wato Safarar ƴam mata da mukeyi itama zatayi Kasuwa wajen Mata da Maza saidai ita ba zamu Sayar da ita ba, kawai zamu maidata Ƙaruwar Ƙasa ce, dan koni da naga yarinyar nan saida ta tada man da ƙishina to inaga sauran Maza da Mata, Wannan ko a garin Lagos ta tsaya a harka zamu samu," ta faɗa tana kallon Hajiya Bilkisu don jin ta bakinta, cikin Gasgata zancen Turai Hajiya Bilkisu ta ce Amma wani hanzari ba gudu taya zamu maida ita karuwa? Baya ga aure da take da shi,"


Hajiya Madina ta dafa kafaɗar Hajiya Bilkisu ta ce "ke Bilki kamar ba mace ba shin ke ba mace ba ce baki san yadda zaki shirya Tuggu da makircinki na mace ba,kuma kamar mijin naki ba'a hannuki yake ba kina juya shi,"


Hajiya Madina tace "Ni abinda nake gani yanzun abinda ya kamata ta fara jan yarinyar a jiki dan yarinyar nan fa kar take, yadda ko ta shirya Tuggu baza'a zargeta ba,kuma fa wannan aikin ba namu ba naki bane kaɗai sai kin haɗa da Sabreen Sarkin makirci, dan nasanta akan makirci ba ƙarama ba ce, kuma yanzun abinda kika yi mata kije ki rarrasheta, sannan bayan kin janyota jikinki sai ki sa Sabreen ta fara koya mata Shaye_shaye da ganan kinga kangarar da ita bazai maki wuya ba, sannan kuma duk wani tuggun da zaki shirya baza a gane ki ba,"



Hajiya Rabi ta ce "tabbas Madina ta kawo shawara wannan ita ce Shawarar da ya dace ki bi,Sannan kuma duk wani jaraba naki da kwaɗayinki sai kin riƙe kayanki, karki fiddo maitar ki farko yadda za'a fahimceki, Sannan saurin fushi ba naki bane," cikin gamsuwa da zancensu ta ce "haka ne kun kawo man shawara mai kyau,"


Turai ta kalleta ta ce "Sannan wannan ɗan banzan kishin naki dole sai kin barshi,dan kota halin yaya kisa Alhaji Bashir ya kusanceta tunda daga gani ba'a taɓa yarinyar can ba,kisa shi ya taɓa ta yadda zata san namiji tunda wuri, kinga shiga karuwanci bazai mata wuya ba,kamata yayi yau ɗinna ma kisaka shi ya kusanceta,"


dogon numfashi Hajiya Bilkisu taja tana faɗin "indai duk wannan zai sa mu samu nasara duk ba komai bane dan Ni Akan kuɗi babu abinda bazan iya ba," ta faɗa tana sakin Wani Shu'umin Murmushi da ita kaɗai tasan ma'anarshi,

Haka dai suka zauna sunata Shawarwarin yadda ya kamata su jawo Raheenatu harkar karuwanci,bayan sun ɗan jima suka ko waccensu ta tafi,



Raheenatu kuwa tunda ta shiga ta rasa me zatayi ma Hajiya Bilkisu ta huce, dan ita ko baɗe mata fuska da niƙaƙƙen Tarugu tayi bata huce ba,

Dafa wajen tayi tana faɗin "Hajiya Bilki kenan baki san wacece Raheenatu ba marin da kika yi man bashi kika ɗauka kuma tabbas sai kin biya shi," tana faɗin hakan ta shige Toilet ta Sake wani Wanka tana fitowa ta Samu wasu arnayen kaya waɗanda Alhaji Bashir ya siya mata da zasu tafo,Crazy Jeans ne black sai Riga red mai yankakken hannu, Wacce babu abinda ba'a gani,dukkan wata sura ta jikinta ta fito,ƙara gyara gashinta tayi tayi parkin ɗinshi Sannan ta samu waje ta zauna ta aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya tan kaɗata





*Ɓangare guda kuwa*


Dady ne gaban Dada, Kallonshi Dada tayi ta ce "Harisu daman abinda yasa kaga na kiraka kan Maganar Abdurrahim ce, ace kamar Abdurrahim ya zama garjejan Saurayi amma ko budurwa bashi da ita to na gaji wllh Ni da kaina na riga na samar mashi Mata na gaji da Halin Abdurrahim dan Haka yanzunna kirawo man shi yasan na zartas dashi wanda ko kai Ubanshi baka isa kaja dani ba," ta faɗa tana maida goron da ta ɓantara a haɓar zani ta ɗaure,


Dady baice komai ba ya ɗaga Waya ya kira Abdurrahim, Yana ɗagawa Dady yace "Kazo Part ɗin Dada ina buƙatar ganinka," bai tsaya jin Amsar shi ba ya kashe wayar,



Ba'a fi 5 Minute ba saiga Abdurrahim ya shigo bakinshi ɗauke da Sallama fuska a kumbure dan ji yake kamar ya ɓalla Dada gida biyu Uban kowa ma huta da jarabarta, ga daman bala'in haushinta ya keji najin Wahalar da ta Bama Mahaifiyarsa, yana shigowa fuska a kumbure ya gaishe da Daddy Dada kuwa ko kallo bata ishesa ba,

Cikin Tuƙuƙin baƙinciki Dada ta ce "Abdurrahim idan bansa Harisu ya tsine maka ka ce ban haihu ga Idi mai fata ba da kuma Indo, Kai zanci fa Ubanka dan duk girmanka bazai hana naci Ubanka koda da Muciya ne, kaiko Harisu kana ganin yadda Abdurrahim ya rainani amma ka kasa ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran mataki," ta faɗa tana banka ma Daddy Harara

Kallon ABDURRAHIM Dady yayi ya ce "Abdurrahim me yasa waikai baka daratta Dada ne ko bata haifeni ba ai ko dan Darajar faurfurarta ka daratta ta ka kiyaye Ni,"



Taɓe baki Dada tayi ta ce "Harisu barshi indai duniya ce ta ishi kowa riga da Wando indai nice Abin rainawarshi yayi,

Kuma Harisu ba Abdurrahim kaɗai nake Buƙata a wajennan ba harda *NURAIM* nakeda bauƙata, Dan nasan yafe me wando saɓule hankali, kuma ko kai da ka haifeshi yafika Fahimtar Mutum shiyasa nake Son sanya shi cikin lamurrana,"

Babu musu Dady ya ɗaga waya ya kira Nuraim ba'a wani daɗe ba sai ga shi ya shigo, cikin Nutsuwa da Takonshi na ƙasaita ya Shigo ya samu waje ya zauna, cikin Nutsuwa ya gaisheda Dada da Abba, amsawa sukayi cikin sakin fuska,

Dada ta kallesu ta ce "to Alhmdllh tunda dukkanku kun taru kaida Abdurrahim, shine ina Son Sanar da ku na Samo mashi Matar aure tunda shi Tsohon iskancin ya hana shi raya sunnar ma'aiki,"


Cikin hassala Abdurrahim ya ce "Dada wllh bani kika samowa Mata ba,dan kika aurota saidai ke ki zauna da ita......," Daka mashi tsawa Dady yayi yana faɗin "kai banson Shashancin banza da na Wofi Mahaifiyar tawa kake faɗa ma haka, ka sani dukkan hukuncin da ta zarce ya zartu," shiru Abdurrahim yayi yana jin kamar ya Shaƙe Dada ta Mutu


Shi kam Nuraim ƙanzil bai ce ba Saidai ya dinga binsu da idanu yana kallo,

Sheƙeƙe Dada ta kalli Abdurrahim ta ce dan Allah Abdurrahim idan an ɗaura maka aure ranar da aka ɗaura auren nake Son kayi ma Matar saki ukku, karka fasa Ni kuma sannan ne zansan Faɗima ta haifeka, kuma ba ko wace ba ce Matar face Sabreen ƙawar Nafisa dan na yaba da Hankalinta Sosai,"



Da Sauri Nuraima ya ɗago ya kalli Dada yana Faɗin "Haba Dada keda baki tsaya kikayi wani ƙwaƙƙwarab bincike ba amma zaki ce zaki aura masa Sabreen," ya faɗa Zuciyarshi shima na Sake hassala da Halayen Dada dan Shima ba ƙaramin haushi take bashi ba,





****************

*ABBA*

A hanzarce ya buɗe idanunshi daga Mummunan mafarkin da yake ga mamakinshi Hawaye yaji nabin Fuskarshi, "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un," shine Abinda yake furtawa dan jin wani uban raɗaɗin azaba na bin dukkan wasu gaɓɓai na jikinshi, yunƙurin tashi yayi Saidai yaji kwata_kwata lakka jikinshi bata aiki komai na jikinshi baya motsawa, dan ko wuyanshi baya iya motsawa gadai shinan ya zama Mutumi Mutumi , sake yunkurin tashi yayi, Wata uwar ƙara ya Saki wacce ta janyo hankalin su Mama da su Suhailat, da gudu suka shigo Falon Abba, Saidai kowa yayi Saranda suna kallonshi cikin tashin hankali ganin yadda jini ke fitowa ta bakinshi da Hanci ga wani ta ƙasanshi yana bi......✍️






Wannan kenan





*Pls Masoya Comment, Share fisabilillah*




Waɗannan sune ƙwarin guiwata






*By Mariam sani*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️






*08109554986*
[11/30, 10:06 PM] Mariam sani: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl


*Rushewar Rayuwa*

*NA*
*Mariam sani*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*Bismillahirrahmanirrahim*


*Page 41&42*


_____________✍️Tana shiga dukkan Hajiyoyin Falon Sukayi Mata ca da idanu waje ta samu ta zauna tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya Sannan ta gaishe su dukkansu da fara'a a fuskokinsu suka amsa,Hajiya Bilkisu ce ta kalli Raheenatu cikin Haɗe rai ta ce "ke tashi ki fice hakanan tunda kun gaisa, ko kafin ki fita ki kwaso Abincin da kikayi daga dinning ki kawo masu nan,"


Tashi Raheenatu tayi taje ta kwaso Abincin da ta girka ta kawo masu nan, tana kawowa Hajiya Bilkisu ta buɗa Saidai tana buɗe shinkafar wani uban ƙauri ya ziyarceta, miyar ma da ta buɗe itama wani ƙauri da ƙarni take, a fusace Hajiya Bilkisu ta ɗago ta kwalfa ma Raheenatu Mari a kunci, miyar ta ɗakko ta sheƙa mata shi bisa farin Lace ɗinta,cikin Masifa ta ce "ke wace irin kidahuma ce? Dan Ubanki a gidan Ubanki haka kike girki Wato sainan zaki zo ki Mani Almabazzaranci a gida to Wllh Abincinnan duka Sai kin cinye shi, watakam dan kinga ina maki da sauƙi Shine zaki rainani, banza Jakka Tinkiya," Hajiya Bilkisu ta ƙarashe zancen da masifa




Kallonta Raheenatu take yi Idanunta duk Sun kaɗa sunyi jajir kallon Hajiya Bilkisu tayi ta ce "Wllh bashi kika ɗauka dan banga macen da ta isa ta taɓa kuncin Raheenatu ta zauna lafiya, wllh bashi kika ɗauka sai kinyi dana sani,"tana kaiwa nan ta fice zuciyarta na Mata ƙuna





Tana fita Kingin Hajiyoyin da suka kafe

Please Login or Register in order to submit comment