Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zansa a ɗaura mashi Aure da Hasiya....✍️


More comment more Typing


Wannan kenan

*Comment, share fisabilillah*


Waɗannan sune ƙwarin guiwata



*By Mariam sani🌹*



✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️




*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 21&22


___________✍️Taɓe baki Dada tayi tana faɗin "barshi Faɗima ya gaya min maganar da yake so,idan baiyi sannu ba wallahi ko sati baza'ayi ba zansa a ɗaura mashi aure da Hasiya", ta faɗa tana banka ma ABDURRAHIM harara kamar Idonta zai faɗo,

Shima kuwa hararar ya banka mata dan ba ƙaramin haushi ta tusa mashi ba, kafin ya ce "Dada Allah baki sa'ar sakawa a ɗaura min Aure da Hasiya da wallahi saina shayar dake mamaki,don kuwa saina baki kunya,daga ke har Hasiyar saina shayar daku baƙa......," Bai idasa ba Mommy ta buge mashi baki tana faɗin "wai dan gidanku ba yanzun nayi maka magana ba shin Dada sa'ar ka ce? bansan shashancin banza dana wofi kabini a sannu," ta faɗa fuskarta da Alamun ɓacin rai,


Sadda kanshi yayi ƙasa yana faɗin "Mommy ayi min afuwa hakan bazata sake faruwa ba," murmushi Mommy tayi tana faɗin "A kiyaye gaba Son bansan rashin tarbiyya,"

Ƙara taɓe baki Dada tayi tana faɗin "idan kun gama gulmar taku sai ku saurareni,zuwa nayi inji shin ko bazaki je sunan Samira ba, dan nasan kaɗan daga baƙin halinki kice bazaki je ba," ta faɗa idanunta ƙur a fuskar Mommy, cikin ɗan shakku Mommy ta ce "Dada da Dadyn su ne zai dawo yau to shine zai hana ni zuwa wajen Sunan amma tunda ga Hameeda da Ni'imatu sun tafi lafiya lau sun wakilceni,"

Cikin kallon ƙasƙanci Dada ta ƙare ma Mommy kallo sannan ta ce "sannu mai miji saboda Harisu zai dawo shine ke bazaki je suna ba, naga alamun Faɗima raini ya shiga tsakanina da ke shiyasa", maida kallon ta tayi ga ABDURRAHIM tana faɗin ya tashi yaje ya kira mata Halima da Saratu, (wato Abokan zaman Mommy)da kamar bazai tafi ba saidai kallon da Mommy ta jefe shi dashi ne yasa shi tashi ya tafi.


Yana fita ko 10 minute ba'ayi ba sai gashi ya shigo da wasu Hamshaƙan mata masu ji da kansu,da sallama suka shigo ɗayar na ta yatsine_yatsinen fuska ta shigo,ɗayar kuwa fuskarta fall da fara'a ta shigo, sallama suka yi suka samu waje suka zauna,kallonsu Dada tayi fuska fall da fara'a tana faɗin "lale maharbin da matan arziƙi, mata bana gadon tsiya ba, kun fi ƙarfin wulaƙanci," ta faɗa tana kallon Mommy dan taga yadda zata yi,saidai Mommy ko a fuska bata nuna alamun ɓacin rai ba,hasali ma Murmushi take saki wanda ya ƙara ƙayata kyakkyawar fuskar ta, ta ƴan ETHIOPIA, hakan kuwa ya ƙara tunzira zuciyar Dada dan ba haka taso ba itakam,



NURAIM kuwa tunda Dada take ma Mommy cin fuskar nan yaji ɓacin rai,saidai abinda ya ƙara ɓata mashi rai bai wuce yadda tace ma Mommy gadon tsiya ba,a fusace ya tashi zai fita Dada tai wuf ta miƙe tana faɗin "Kai NURA ina zaka tafi?harda wajenka nazo fa inji batun zuwa Hajji da Umara,amma zaka wani tafi," ta faɗa tana washe haƙora dan Dada badai son banza ba,


Yafi ƙarfin minti biyar kafin a hankali ya buɗe bakin shi ya ce "Dada baki buƙatar Hajji da Umara saboda ta tsatson tsiya zai fito kinga kuwa babu wani amfanin zuwanki," ya faɗa yana ficewa daga ɗakin

Baki sake Dada take kallon shi,ƙwafa tayi ta samu waje ta zauna, kallonta ta maida ga Halima, (wato Ummi)cikin sakin fuska take faɗin "Dama kiranku nayi inji da gaske Harisu ne zai dawo kokuwa, ƙaryar faɗima ce dan ta samu mafaka," cikin sakin fuska Ummi ta ce "Eh Dada yau ne zai sauka,nasha da kukayi waya ma ya faɗa maki,"

Haɗe fuska Dada tayi ta ce "ya kuwa faɗamin tunda bai ɗauke ni a bakin komai ba,"

Sai yanzun matar nan mai yatsine_yatsinen fuska ta ce "wai ni Dada dama kan wannan maganar ce kika wani tado mu daga inda muke, ni wallahi shiya sa ko kiranki wani lokacin bani zuwa,"


Dukda girman Matar Hakan bai hana Dada sakar mata dundu a baya ba tana faɗin "Saratu kinci Ubanki Sadiƙu, kamar ni ina surukar ki zaki dubi tsabar idona ki faɗa min magana,"


Taɓe baki Umma tayi tana faɗin "nifa Dada ba faɗa maki magana nayi ba kawai dai gaskiya ce na faɗa maki,"

Zama Dada tayi tana ta sababin bala'i wai surukanta sun riga da sun rainata, saida ta gaji dan kanta sannan ta koma ɓangaren ta,


Mommy kuwa kamar yadda tayi tsammanin Dady idan ya dawo ba zai kulata ba haka kuwa ta kasance,yana dawowa saima kwandon tujara da wulaƙanci da ya sauke mata,






*RAIHANA*

Tunda muka shiga Jirgi ko kallon Alhaji MUTTAƘA banyi ba ballantana ya samu Arziƙin gaisuwa,shima kuwa ko kulani baiyi ba, haka har muka sauka aka zo ɗaukar mu,tafiya muke amma hankalina sam baya ga hanyar da muke tafiya, tunanina kawai taya zanyi zaman Aure da wannan tsohon, ko bama tsoho bane banji zan iya zama dashi ba,ina tunane_tunane har muka iso wani katafaren gida wanda faɗa maku shi ma ɓata lokaci ne,wangale mana ƙatoton get ɗin akayi muka shige, "Dallah Malama fito!!!!," Alhaji MUTTAƘA ya daka min tsawa, jiki a sanyaye na fito, haka ya dinga tafiya ina binshi yadda kasan Zariya,


Da sallama ɗauke a bakina na shiga Falon,wata babbar mace ce zaune a ɗakin fuska murtuke ba Alamar fara'a ga kuma mata guda shidda sai Maza ukku,suma fuskar su babu Alamun fara'a,saidai tana ɗaga kanta ta ganni ta miƙe tsaye tana faɗin "Alhaji badai wannan kyakkyawar yariyar ba ce a kayi maka biyan bashi da ita ba?".





*RAHEENATU*



Itama tunda suka shiga jirgi ta gaishe da Alhaji Bashir taja bakinta tayi shiru,har suka sauka aka zo ɗaukar su,

Kai tsaye Unguwar VICTORIA ISLAND suka nufa shima gida ne haɗaɗɗe dan za'a iya cewa yama fi na Alhaji MUTTAƘA,


Kai Tsaye suma sashen Uwar gida suka fara nufa.........✍️




Wannan kenan



*Comments, Share fisabilillah*



Sune ƙwari guiwata



*By Mariam sani🌹💗*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 23&24


_______________✍️kai tsaye suma sashen Uwar gida suka fara nufa,da sallama ɗauke a bakunan su suka shiga,

Hajiya Bilki ce ta amsa musu babu yabo ba fallasa,suna shiga jikin Alhaji Bashir ya kama kyarma kamar mazari, wuri ya samu ya zauna yana ɗari_ɗari,yake furta "Hajiya Bilkisu mai gadon zinare uwar gida ran gida Mata ga Alhaji Bashir,daga ke ba ta biyun ki," ya faɗa yana washare mata haƙora,

Harara ta dallara mashi tana faɗin "banson salon munafurci, idan ba munafurci ba kaje anyi maka biyan bashi da tsaleliyar budurwa ka wani zo kana da gani, babu biyuna, to ƙara kasani tun yanzun wallahi ba mata ka Auro ba saidai ƴar Aiki,"


Raheenatu kuwa baki sake take kallon Matar dake ta zazzaga ma Alhaji Bashir tujara,cikin Ranta take faɗin "kaiko Alhaji Bashir Anyi sallamamme anya ba Salame ta yaye ka ba,kiyi ki gama danni babu shegiyar da zanyi wa Aiki gidan Aure nazo ba gidan bauta ba," ta ƙarashe zancen da banka ma Hajiya Bilkisu harara ƙasa_ƙasa


Shiko Alhaji Bashir cikin fargaba ya ce "dama Hajiya ai zata dinga yi maki aiki,ba wai dan inyi Rayuwar aure kawai na auro ta ba,harda ta dinga kula da Sabreen,ta dinga yimaki duk abinda kike buƙata," ya ƙarashe zancen da duƙar da kanshi ƙasa,


Gaban Hajiya Bilkisu ne ya faɗi cikin Ranta take faɗin "kar dai ace ya gano Abinda nake aikatawa idan ko ya gano dole ne na canza shiri,"

Cikin yanga da kisisina Raheenatu tace "Alhaji na fa gaji so nake na kwanta kazo ka nuna man sashe na,kafin dare na ida gajiya," ta faɗa tana kallon Hajiya Bilkisu da tayi saranda tana kallon ta,

Cikin ƙuluwa Hajiya Bilkisu ta ce "ki ida gajiya ɗin Ubanki shegiya ƴar iska karuwar banza kawai, wallahi ba ke, babu zaman jin daɗi a gidannan, yanda Ubanki ya gaji ya siyar mana da ke, haka zaki ƙarashe Rayuwarki cikin ƙunci,ƴar buhun uba,"

Wani ƙululun baƙin ciki yazo ya tokare ma Raheenatu maƙoshi,jin an kirata da karuwa,jarumta ta Aro tana faɗin "Ayya Hajiya bawai gajiyar da kike tunani nake nufi ba, kiyi Haƙuri indai nice zaki same ni kamar yadda kike so,"


Murmushin jin daɗi Hajiya Bilkisu tayi tana faɗin "shikenan indai zakiyi man yadda nake buƙata ni kuma zaki same ni mai adalci a kanki," ta faɗa tana bin jikin Raheenatu da wani Shu'umin kallo,


Raheenatu kuwa cikin Ranta take faɗin "zaki ci gidanku indai nice bana yafiya duk abinda kikayi man sai nayi maki dubun shi, shegiya mayya kawai sai wani bina take da kallo tana lashe baki,shiko Alhaji Bashir mi ya haɗa shi da Auren mayya?ta je ta lashe shi a banza, danni kuma kurwa ta tafi ƙarfinta,"

Haka dai Raheenatu tai ta ganin ikon Allah, dan Alhaji Bashir gaban Hajiya Bilkisu soloɓiyo ya zama yadda kasan wani dolo,a ƙarshe dai ma ɗakin ƴan aiki aka tunkuɗa Raheenatu,kuma ita bata ma wani damu ba, dan acewar ta babu wanda ya isa ya sata tayi mashi aiki,






*JOGU*


Zaune yake idanunshi sun kaɗa sunyi Jajir Alamar ɓacin Rai,cikin takaici yake faɗin "Naseer ni har yanzun mun gaza gano wanda ya rusa mana shiri,har fa cikin jikin matata na saudaukar dukda yadda na ƙwallafa Rai a kanshi,amma duk a banza,"


"Haba Jogu bansan gajen haƙuri yanzun bata wannan ma muke ba ta yadda zamu kawar da Uwar Gijiya muke,yanzun hankalimmu yafi karkata a can,duk wannan yanzun ka ƙyale,kawai, kaga kuma ga sabon shirin da zamu canza na tsafa waccan yarinyar,ga kaita ga Dodon tsafi, kaga muna da Ayyuka a gabanmu," Alhaji Naseer ya faɗa,


Cikin gamsuwa Jogu ya kaɗa kai, yana fad'in "Naseer amma kai kana ganin kawar da wannan 'Shu'umar macen abu ne mai sauƙin,kamata yayi mu ƙara shiri dan bamu da isasshen lokaci,"


Alhaji Naseer ya ce "kawar da ita ba Abu bane mai sauƙi, dan dole mu ƙara shiri,a halin yanzu muna buƙatar jinin mutane da dama,sannan muna buƙatar tsofin Ruhikan da ta kulle, dasu ne kaɗai muke da tabbacin Nasara," "to Amma Naseer ina zamu sami tsofin Ruhikan da ta kulle wannan shine matsalar mu," Jogu ya faɗa da damuwa tsam a fuskar shi

Dogon numfashi Alhaji Naseer yaja yana faɗin "duka wannan ba matsala ba ce kaidai kawai ka zama cikin shiri," kaɗa kanshi Jogu yayi cikin gamsuwa da maganar Alhaji Naseer,




*ƁANGARE GUDA KUWA*



Mommy ce duƙe gaban Dady idan banda rusgar kuka babu Abinda take,fuskarta ta ɗago wacce tai gaje_gaje da hawaye, cikin dasassjiyar murya take faɗin "Alhaji Sakayyar da zaka yiman kenan duk son da nuna maka na ƙaunaceka a kanka fa na guji iyayena na rasa ƙanwata, nasan tabbas wannan Sakayyar iyayena ce ke bibiyata,ni kaina nasan banyi ma kaina adalci ba ban cancanci zaman jin daɗi a gidannan ba,duk abinda kayi man ni ce na jaza wa kaina,saboda ƙin bin umarnin iyaye," ta faɗa tana sake fashewa da wani sabon kukan takaicin ɗa namiji,



Cikin daka tsawa Dady yake faɗin "kee!!! Kar ki isheni ni na faɗa maki dole ki soni a lokacin ko dole nayi maki banza wacce bata ɗauki Iyayenta a bakin komai ba,dama ni ba wai Auren So nayi tsakani na dake ba nayi shi ne dan kawai guje ma aikata zina sai gashi tunda kika shigo kinƙi fita kin bi kin ƙadaddabe ni," ya faɗa yana huci yadda kasan zai daki Mommy,


Cikin jin zafin maganar Dady Mommy tace "Alhaji ka cuceni ka zalun....." Bata ida ƙarasawa ba Dady ya ɗaga Hannu ya sharara mata mari Dai_dai shigowar Nurain wanda akan idonshi marin ya sauka a kuncin Mommy......✍️





Wannan kenan


*Comments, Share fisabilillah*



Sune ƙwarin guiwata






*By Mariam sani🌹💗*






✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️






*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl
*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 25 &26



_________________✍️Bata ida ƙarasawa ba Dady ya ɗaga Hannu ya sharara mata mari Dai_dai shigowar Nuraim wanda akan idonshi marin ya sauka a kuncin Mommy


Runtse idon shi yayi da ƙarfi yana kiran ya Allah ji yake zuciyar shi na mashi wani irin zafi da raɗaɗin ganin yadda Mahaifinsa ya ɗaga Hannu ya mari Mahaifiyarshi,a hankali ya juya zai koma dan bazai iya ganin yadda Mahaifiyarsa ke zubar da hawaye ba,


"Ina kuma zaka tafi? Dawo ka zauna mana," Dady ya ƙarashe zancen da ƙura mashi idanu,

Dawowa yayi ya zauna Amma zuciyar shi na mashi wani irin zafi da ƙuna "Dama Mommy da Dady ba auren Soyayya sukayi ba, me hakan yake nufi kuma dama Mahaifanta baro su tayi ta auri Dady komi???," Duka waɗannan tambayoyin bashi da mai bashi Amsa,

Dady ne ya kalleshi yana faɗin "Son da ina kuma zaka koma?ai ƙara da baka koma ba Nuraim ka ƙullaceni a cikin Zuciyarka, wai kamar ni ace Faɗima zata cakumi kwalata ta zagar man Mahaifiya na rasa inda Mahaifiyarka ta gano wannan baƙin Halin nata," ya ƙarashe zancen da Hura iska


Mommy kuwa hawaye ta ƙara sharewa zuciyarta na mata zafi da Raɗaɗi,wai kamar ita Dady zai ce ta cakumi kwalarshi kuma harda ƙarin ta zagi mahaifiyarshi, Mutumin da ko Maganar banza bata gaya mashi tsakaninta da Mahaifiyarshi saidai Mutumtawa, dukda kuwa da irin cin kashin da ake mata a cikin Ahalinsu,


Nuraim Ne ya kalli Dady yana faɗin "Dama Dady zuwa nai naimaka sannu da dawowa Sai kuma na taradda wannan lamari, ga shi ina son zuwa Office," ya faɗa yana miƙewa, kallon Mommy yake yanda ta duƙar da kanta ƙasa tama ƙi barin su haɗa Ido dashi, cije lips ɗinshi na ƙasa yayi yana ficewa Daga Falon,ko takan Dady baibi ba,


Kai tsaye Part ɗinshi ya nufa dan baiji zai iya zuwa Office ba yana shiga ya iske Nafisa da ƙawarta Sabreen wani uban takaici ne ya ƙara kama shi zuciyarshi ta ida hassala, dan shi ko kaɗan baison ganin yarinyar nan shi kanshi baisan taƙamaiman Abinda yasa ya tsaneta ba, murtuke fuska yayi ya shiga da sallama ɗauke a bakin sa,


A razane suka juyo suna Amsa masa,wanda da ka kalla dukkansu ba'a natse suke ba,saidai shi ko kaɗan baima lura da yanayin su ba,cikin inda_inda Sabreen ta ce "Ina kwana," " lafiya," ita kaɗai ya furta mata yana shigewa bedroom ɗinshi, yana shiga kuwa suka kalli Juna suna sauke Ajiyar zuciya, sannan suka ƙyalƙyace da dariya, Nafisa ce ta ce "kinga ƙawata yanzun miye kike ganin mafita? Ni a ganina kawai da dukka mu haƙura da waɗannan kayan kinga nasanya Anyo man safarar Zafafan ƴam mata dukkansu na ba ma Hajiya Turai Ajiyarsu dan za'a samu da su sosai," ta ƙarashe zancen da kallon Sabreen, murmushi Sabreen tayi tana faɗin "maganar ki gaskiya ce inaga hakan kawai shine Mafita,amma yanzun maganin matsala ina ganin kawai ki Tura su a CHINA sai kinfi Samun kuɗi dasu Sosai tunda kin gani dukkan su siyar dasu zakiyi, su kuma da sun gama Abinda za suyi da Matan Sukan kashe su ne su cire wani Sashen na jikin su, su siyar kuma anan ma kina da wani kason naki na daban,"

Rungumeta Nafisa tayi tana faɗin "ƙawata gaskiya kin bani shawarar da zan samu kaso mai tsoka,"






*Raihana*



Niko tunda wannan Matar ta tashi tana faɗin badai dani akai ma Alhaji MUTTAƘA biyan bashi ba zuciyata ke man Zafi ga ɗima_ɗiman Matan da Samarin dake bina da uwar Harara, hakan ya sake fusata Ni dan Ni yanzun ko ni ina Bama kaina mamakin yadda Abu kaɗan ke fusata Ni

Alhaji MUTTAƘA ne ya kalli Hajiya Zaliha yana faɗin "ke Zaliha bansan rashin ɗa'a fa ko barina na zauna bazakiyi ba zaki tare Ni da tashin hankali, to wllh ki bini a sannu, kuma da kike cewa anyi man biyan bashi da tsaleliyar budurwa naga dai ko na tashi aikata Abinda nai niyya bazaki iya hanani ba, kuma da kika tara ɗima_ɗiman Matannan da Maza Uban mi za suyi maki? To kafin Raina ya ida harzuƙa maza_maza ko wace shegiya ta tashi ta wuce tafi ɗakin mijinta wanda basu da Auren kuwa ku wuce sashenku ko yanzun na dinga Ball daku dan kunsan ba ƙaramin Aikina bane," ya ƙarashe zancen da Huci kamar wani tsohon kumurci,


Niko kallon Alhaji MUTTAƘA nake yadda yake ta Uban tada jijiyoyin wuya, "kai wannan Mutumin badai bala'i ba," na faɗa cikin Rai ina banka mashi Harara ƙasa_ƙasa dan ji nake kamar na zuƙe jininshi Ubankowa ya huta,


Dukkan mata da maza ɗinnan kowanensu tashi yayi suna gunaguni suka miƙe suna fita da ɗai_ɗai
Na ƙarshen ne da yazo fita yai man wata muguwar bangazar da tasanya saida na faɗi na fashe baki idanuna ne suka kaɗa sukayi jajir ɗago idanuna nayi na sauke su Akan wanda ya bangajeni, wanda da Alamun kallon da nayi mashi ba ƙaramar Razana yayi ba......✍️




*Kuyi Haƙuri da wannan insha Allah gobe zanƙara maku yawan TYPING*



Wannan kenan



*Comments, Share fisabilillah*


Sune ƙwarin guiwata


*By Mariam sani*



✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*08109554986*[11/29, 6:02 PM] Riamcool: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 27&28



____________Ɗago idanuna nayi na sauke su Akan wanda ya bangajeni wanda da Alamun kallon da nayi mashi ba ƙaramar Razana yayi ba,


Ƙaɗa kaina nayi na miƙe ina shafe wajen daya fashe,zuciyata na tafasa, Kallona Matar Alhaji MUTTAƘA tayi tana faɗin "indai wahala ce yanzun kika saka wando ƙafa ɗaya da ita, dan wllh bake ba zaman jin daɗi a gidan,Amma Mu zuba Ni dake mu gani, A ce Alhaji ka rasa wacce zaka Auro sai tsarar auta, wllh kadai ji kunya kuma ka sani tashin Hankali yanzun za'a fara sai ma Idan Rabi da Murja sun dawo dan wllh baza muyi zaman kishi da ƴar cikimmu ba,"

"Ke wai Zaliha me yasa bakya da ladabi ke kamarni ace zaki buɗe baki kina gaya man Magana Har muryarki na kera tawa,to wllh ki kiyaye Ni dan na kusa ɗaukar babban Mataki akanki,"ya faɗa yan fisgar Hannuna da ƙarfi





Binshi na dinga yi Har ya kaini Side ɗina, koda na shiga kai tsaye Toilet na faɗa nayo wanka tare da ɗoro Alwalla, A gurguje na samu na shirya na kabbara Sallah dan lokacinta ya shige,da ƙyar na samu na Kabbara Sallah, dan jinake yadda kasan Ana babbaka Ni da wuta, ina gamawa na sauke Ajiyar zuciya,Saidai dana Rufe Ido Babu Abinda nake gani illa Abba ana gana mashi Azaba,gabana ne ya faɗi dan nasan Tabbas ba ƙyale Abba za suyi ba, dan duk yadda nake jin daga baya zan iya zuƙe jinin Abba sai naji a halin yanzun bazan iya ba, nayi Nisa cikin Tunani Alhaji MUTTAƘA ya banko ƙofa, Abinci ne ɗauke a hannun shi, "ke dallah tashi bansan Sabon salon wulaƙanci tun ɗazun da muka shigo jirgi ko gaisuwa babu tsakanina dake,ke ko kallon Arziƙi bakiyi man ba, ban san rashin ladabi ko Auren Aminci mukayi tsakanina dake bai kamata kiyi man haka ba ballantana siyenki nayi,"


Banza nayi mashi zuciyata naman raɗaɗi da ƙuna haɗe kaina da gwiwa nayi na fashe da kuka,dan ji nake idan banyi kuka ba zuciyata baza ta samu Salama ba,"yanzun haka Zanyi Rayuwa ana faɗin Mahaifina ya siyar dani? tun kafin susan Ni wace ce sun fara hantarata da kyarata to inaga sun san Ni Asalin ko wace ce," yanzun lokacine da kowa kanshi kaɗai ya sani baya Tunanin halin da ɗan uwanshi Musulmi yake,babu wanda zai dubeka yaga halin da kake ciki wani ma burin shi ya ida jefaka Halin ƙaƙa na kayi,zuciyoyin Al'Umma sun dasashe da rashin Tsoron Allah wasu duniyar kaɗai suka sa ma gaba,"

Daka man tsawa yayi yana faɗin "wai Uban mi akai miki ke banson fa taɓara daga yi maki magana sai kuka,dallah ɗauki Abinci kici banza karya,kuma ki sani wllh tunda kika ɓullo ta wannan hanya Wahala ce kin ɗaura aure da ita kenan,dan bake ba zaman jin daɗi a gidannan," yana faɗa ya kaɗa Babbar rigar shi ya fita,


Niko kukana na cigaba da yi ga yunwa da ta Addabeni, dan banji zan iya cin Abincinnan ba ko yunwa zata kasheni, miƙewa nayi na shige bedroom dan na ɗan kwanta,








*Raheenatu*


Zaune take waje guda tayi zugudum duk kewar ƴar uwarta ta isheta, ga ba wani zaman jin daɗi take a gidan ba,tana nan zaune sai ga ƴar aiki tazo wai Hajiya Bilkisu na kiranta, tashi tayi ta nufi Side ɗin, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, zaune ta iske Hamshaƙiyar (dan abinda ta raɗa mata kenan) cikin ɗan sakin fuska ta amsa mata, waje ta samu ta zauna, Kallonta Hajiya Bilkisu tayi tana faɗin " dama Daughter so nake kiyi mana girki yau muji Taste ɗin girkin Amarya,dan yau banjin daɗi,"

Kallonta Raheenatu tayi tana faɗin " gaskiya saidai kiyi haƙuri dan duka yau fa kwana guda da zuwa Amma za'a ce na fara girki to gaskiya bazan iya ba don sai nayi 2 week ban ɗora tukunya ba,"

Haɗe Rai Hajiya Bilkisu tayi tana faɗin "To dan Allah idan na baki kayan girkin kada Allah sa kiyi,"


Harara Raheenatu ta galla mata tana faɗin "nifa Hajiya ba zaman wahala nazo yi ba zaman Aure ya kawo Ni dan inba aure ba ma me zai kawo Ni Lagos garin inyamurai har kiga fuskata ki sani girki,"

"Keee!!! Har kin isa na saka kiyi man Abinda nake so ki ƙiya, to koshi mai gidan bai isa ya ƙetare Umarnina ba ballantana ke karan kaɗa miya,duk kiyi iskancinki ki gama na lokaci ƙalilan ne," ta faɗa tana tashi


Taɓe baki Raheenatu tayi ta samu waje ta kwanta,tana kwance saiga Sabreen ta shigo kallonta Sabreen tayi tana faɗin "ke lafiya zaki zo nan ki kwanta a matsayinki nawa?," "A matsayina na Matar Ubanki kinga kuwa dole nai yadda nake so a gidan mijina babu ubanda ya isa ya taka man birki,"

"Ke Ni zaki dubi tsabar idon ki zaga,To wllh zamanki anan gidan ya ƙare," dariya Raheenatu ta sheƙe da ita tana "Ni da tsoho Mutu ka raba, ke baki isa ki rabani dashi ba,"

Ɗaga Hannu Sabreen tayi ta sharara Mata Mari , bata sauke Hannu ba itama Raheenatu ta sharara mata mari har ukku dai_dai shigowar Alhaji Bashir







*JOGU*


Gudu yake shararawa a Titi har ya isa wani gidan gona, yana shiga yaga Dukansu sun Hallara shi kaɗai kawai suke Jira, kusa da Alhaji Naseer ya samu waje ya zauna suka gaggaisa,


Alhaji Naseer ya ce "To Dama dai nasan dukkanku kunsan Abinda ya taramu nan muna so ne

Please Login or Register in order to submit comment