Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu kawar da Uwar gijiya daga karagar mulkin can, dan bazata yiyu ba ace mace ce ke mulkarmu, kuma bai kamata ace duk Wahalar da muka sha na tsawon Shekaru Bama gani Dodommu, yanzun abinda nake so daku shine ina son mu taru mu haɗa ƙarfi da ƙarfin tsafikammu mu buɗe Ruhikan data kulle da sune kaɗai zamu iya kawar da ita,"


Jogu ne ya ce "To amma kadai san kamata yayi muyi komai da gaggawa dan bamu da isasshen lokaci ina guje mana ta gano Abinda muke shirya mata dan kasan ba ƙaramar shu'uma ba ce, ga kuma kai yarinyar can ga dodon tsafi,ina son kafin ta kaita mu fara kaita,mu, dan yau ya kamata mu fara shiri, don gaba da gaba da wannan 'Shu'umar macen ba ƙaramin Artabo bane,"


Nan Dukansu sukai na'am da zancen Jogu,



*Nuraim*

Tunda ya shiga ya kwanta ya rasa mike masa daɗi,juyi yake ya rasa yanda zayayi, ga Soyayyar data Addabi Zuciyarshi, wanda koshi kanshi baisan wa yake ma wannan son ba, ya kamu da Son Yarinyar da bai san Asalinta ba baisan ina zai ganta ba ballantana har ya taimaketa, kullum da Tunanin Hanyar da zai Taimaketa yake,dan baisan yanda zai ɓullo ma lamarin ba,

Tashi yayi ya shiga Toilet ya ɗan watsa Ruwa da Alwalla ya fito koda ya fito bai samu Sabreen ba Nafisa kaɗai ya gani tana Sallah, Murmushi ya saki ya fice kai tsaye Masallaci ya nufa

Yana fitowa kai tsaye ɓangaren Mommy ya nufa yana zuwa ya sameta zaune ta zuba uban tagumi ga Abdurrahim zaune a gefanta,da Sallama ɗauke a bakinshi ya shiga

Ɗagowa Mommy tayi tana amsawa, kusa da ita shima ya dawo ya zauna ya kwantar da kanshi bisa kafaɗarta ɗagowa yayi yana faɗin "Mommy yau nake son ki bani Tarihinki dana Abba ina son nasan Asalinki ko kema zan ƙwato maki ƴanci a gidannan,"


Gaban Mommy ne ya faɗi shin tayaya zata faɗa mashi Abinda ta aikata tsawon shekaru?......✍️





Wannan kenan






*Comments, Share fisabilillah*


Sune ƙwarin guiwata






*By Mariam sani*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[11/29, 6:02 PM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 29&30

_____________✍️Gaban Mommy ne ya faɗi shin taya zata faɗa mashi abinda ta aikata tsawon shekaru? Amma idan bata faɗa masu abinda ke damunta ba tsawon shekaru wa zata faɗa mawa? Ƙara ta faɗa masu ko zuciyarta zata samu salama,


Shafa kan Nuraim da Abdallah tayi tana dubansu tace "tambayar da kuke yi man na jin son ina ƴan uwana da Mahaifana suke insha Allah yau zan baku Tarihina,"


Zama suka gyara dukkansu da Son jin tarihin mahaifiyar tasu


*WAIWAYE*
Asalin Mahaifana ƴan ƙasar ETHIOPIA ne Alekxendra shine sunan Mahaifiyata Mahaifina kuma JOHN dukkaninsu auren soyayya sukayi, saidai Mahaifiyata Alekxendra Akwai tsantsar dukiya dan tafi Mahaifina,dukda shima ba daga baya ba,sunyi shekara biyu da aure Mahaifina ya gwada Son musulunta ba ƙaramin daru aka sha ba wanda Alekxendra ta ƙeƙashe ta ce ita bata ba zama da Musulmi ƙara yai haƙuri subi Addinin su, shi kuma ya gwada mata ƙara su rabu, saboda tsananin ƙaunar da take ma Mahaifina ne ya sanya ta yarda ya musulunta Amma bisa sharaɗi muddin ta haifi ɗa namiji babu shi babu bin Musulunci,idan kuma mata ne ta yarda su bi addinin Musulunci,mahaifina da ya koma Muhammad ya Amince da wannan sharaɗin nata,a haka rayuwa ta dunga tafiya har suka kwashe shekara Biyar, Sannan Allah ya basu cikina ba ƙaramin Murna da farinciki suka nuna ba cikin tsantsar kulawa suka cigaba da renon cikin har Allah ya sa aka haifeni, Alekxendra ta so ta samu namiji saidai Allah ya bata mace, amma dukda haka bai hanata farinciki da murna ba, mahaifina da kanshi ya raɗa man suna Fatima wanda faɗa maku irin ƙaunar da yake nuna man bazai musaltu ba, dukkansu suna gwada man kulawa da tsantsar ƙauna, a haka har nayi 5 yrs Sannan Allah ya sake basu wani cikin shima cikin kulawa suka reneshi Har Allah yasa aka haifi ƴa mace a wannan karin ma, shima Alekxendra bata gwada wata damuwa ba dukda ta ƙwallafa rai Allah ya bata ɗa Namiji, wannan karin shima Mahaifimmu ya raɗa ma jaririyar suna Sajeeda, tunda Aka haifi Sajeeda nake tsantsar ƙaunarta wacce koda ƙuda ne bana son ya raɓeta, dukkanimmu mun taso cikin so da ƙaunar junammu tsakanina da Sajeeda,wanda mahaifammu ba ƙaramin daɗi hakan ke masu ba, babu yadda Muhammad baiyi ba akan Alekxendra ta Musulunta ta ƙi saida shi a kullum bai gajiya da ƙara nuna mata hanya dukda taurin kai irin na mahaifiyarmu,a haka rayuwa ta cigaba da tafiya, lokacin da nake da 15 yrs dukkanin wani girma na ƴa mace ya bayyana a gareni,ita kuma Sajeeda lokacin ne take da 10 yrs saida Bama kama da Sajeeda dan ita Mahaifiyarmu ta biyo, Ni kuma Mahaifimmu na biyo, inada 20 yrs na kammala karatuna a lokacin ne kuma mazajen aure suka dinga fitowa dan a zamanin Ni ba ƙaramar kyakkyawa bace,saidai dukkan haɗuwar mazajen Turawa babu wanda yai man,a haka rayuwata tai tafiya, ana cikin haka ne na Haɗu da Mahaifinku wanda kasuwanci ya kaishi can, saidai tunda na ɗora idona akan Mahaifinku naji duk duniya babu wani mahaluƙin da nake ƙauna sama da shi, nai zurfi cikin ƙaunar shi wanda shi kuma Sam a Zuciyarshi ba haka bane, Ni ce na liƙe ma Mahaifinku wanda har takai ga Yaman Alƙawarin aure, Ni kuma a lokacin ne naje ma Mahaifana da batun son Auren Mahaifinku, a lokaccine Mahaifina ya ƙeƙashe ƙasa yace babu abinda zai sa na auri ɗan Nigeria dan da na aure shi ƙara na Mutu banyi aure ba, ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba, dan jin furucin Mahaifina, wanda duk son da yake yaga nayi aure amma ace yau shine ke iƙirarin ƙara na Mutu banyi aure ba da na auri Haris, ji nayi tsab zan iya rabuwa da kowa nawa dan na zauna da Haris ji nake koda na rabu da Mahaifana tsaf zan samu farinciki wajen Haris......✍️




*Gaskiya saboda rashin Comment ya sani nake maku gajeran Typing labarinnan da nayi niyyar yin shi dogo amma rashin Comment zai sa nayi shi gajere saboda kwata_kwata banjin daɗin rashin Comment*


*Amma masu yi man ina godiya dan duk yadda nai zuciya da kar na cigaba da post da na tuno daku sai in cigaba😀 ngd sosai*




Wannan kenan



*Comments, Share fisabilillah*


Waɗannan sune ƙwarin guiwata



*By Mariam sani*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️




*08109554986
[11/29, 6:02 PM] Riamcool: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl


*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 31&32


____________✍️Ji nayi tsab zan iya rabuwa da kowa nawa dan na auri Haris dan koda na rabu da Mahaifana tsaf zan samu farinciki wajen Haris, bana kokwanton Rabuwa da iyayena,Saidai kuma Sajeeda fa ya zanyi da ita anya zan iya tafiya na barta,saboda tsananin ƙaunarta da nakeyi,

Koda na faɗa ma Haris abinda iyayena suka yanke naga be wani nuna alamun damuwa ba,hakan ya ƙara ɗaga man hankali,kai tsaye na nuna mashi nason mu gudu Nigeria kawai muyi auremmu, shima kai tsaye yayi na'am da wannan shawarar,


Saidai na gwada ƙara tuntuɓar iyayena da maganar, amma abinda suka faɗa man muddin na ƙara tuntuɓar su da maganar basu yafe man ba, Ni kuma kai tsaye na ce masu koda zasu yi man tsinuwa kwando_kwando babu abinda zai hanani Auren Haris dan ƙara na gudu na barsu,jin furucina ne yasa Mahaifiyata ta fusata wanda kai tsaye ta Nuna kasheni ya kamata tayi kawai, saida Mahaifina yaga da gasken Kasheni zatayi sannan ya ƙwatan, tunda akayi wannan kullum sai na musu zancen Haris dukda cewa basu yafe man ba




Babu abinda basu ce zasu mallaka man ba amma na ƙi, da suka ga haka suka yanke Shawara da aura man wani ɗan Maƙwabcimmu Abdulhameed wanda ya daɗe yana sona, Ni kuma hankalina ya ƙara tashi da naga gadan_gadan aurena za suyi, Ni kuma a lokacin ne nace ko su fasa ko kuma na kashe kaina na kashe Sajeeda idan basu janye auren ba,jin furucina ya sa suka tsorata dan sun tabbatar da gaske nake, haka suka janye auren kai tsaye na nuna musu Nigeria zan gudu nai aure wanda tun Alekxendra na dukana harta kai ga tana kuka da roƙona," Mommy na kaiwa Nan ta fashe da kuka tana faɗin "Tabbas nasan Alhakin iyayena ne ke bibiyata wanda kullum na kwanta babu abunda nake tunawa sai roƙon da mahaifiyata keyi da kukan da takeyi, ashe wahala suka hango man shi yasa suka ƙi amincewa,"


Dogon numfashi ta ja taci gaba da cewa "Alekxendra dukda taurin kanta akan bata son musulunta Amma saida ta roƙe Ni indai zani fasa tabbas zata Musulunta, musulunta kuma harta abada,haka na ƙeƙashe nace mata babu abinda zai hanani,wanda mahaifina daga nan ya kamu da ciwon zuciya, duk hakan bai karya man zuciya ba, kuma a hakan na ɗauki Sajeeda muka taho tare wanda, nayi da nasanin baro ƙasata na biyo Mahaifinku wanda ashe bansan babban kuskure na aikata ba na biye wa son zuciya, banyi tunanin halin da iyayena zasu faɗa ba Ni a lokacin nawa farincikin kawai nake nema, farincikina kawai nasani bani buƙatar na iyayena ,


Saidai tunda muka shigo Nigeria Haris ya janja man Abu kaɗan zanyi sai daka tsawa,ban kawo komai a raina ba, har muka iso gidan su da kenan Jigawa, saidai ina doso gidan gabana ya cigaba da faɗuwa, haka muka shiga har ciki, Saidai muna shiga muka iske Mahaifiyar Mahaifinku muna shiga ta tambayi Haris ina ya samo masu mutane masu jar fata, nan yake faɗa musu wai hatsari iyayena sukayi shine bamu da kowa shi kuma yaji Tausayimmu ya ɗakkommu Ni kuma a lokacin bani jin Hausa shi yasa ban fahimci abinda take faɗa mata ba,na dai ga tana kallommu tana faɗa da Yaren Hausa, koda na tambayi Haris sai faɗa man yayi wai Tausayimmu taji a kan Mahaifana sun hanani auren shi shine take faɗa

Ban takura da sanin dalili ba, gurina kawai a lokacin naga munyi aure,

Tunda muka shigo muke fuskantar matsala a gidan dan saida ga baya na fuskanci Haris yana da mata Saratu naji takaici nayi kuka a lokacin ne kuma na fara danasani danasanin da bashi da amfani,a lokacin Haris ya bijora ma mahaifiyar shi da Son aure na,lokacin Dada tai tsalle ta dire ta ce ita ɗanta bazai auri ƙabilar yahudu da nasara ba,saida Kakanku Malam Ali yai mata da gaske sannan akayi auren,kuma lokacinne dukkanin ƴaƴan Dada ko wane ya ƙara tsangwama ta da kyara daga Mazan har Matan da zuri'ar su, babu kamar Sharifa Da Shafa'atu sune ƴaƴan Dada Mata dan sunfi tsangwamata, wajen Mazan kuwa su shidda wajen Mutum Biyu nake samun Salama Baba Habibu sai Salihu,

Haka duk wata shara ta gidan aka tattaro Ni ake watso mawa,tun ina kuka, harta kai ga na daina ita kanta Sajeeda bata huta da Azaba ba dan Azabar yau daban ta gobe daban,

Ana haka ne Saratu ta haihu, dukkan wani aiki na gidan ya dawo kanmu nida Sajeeda, tunda Saratu ta Haifi Muhseena Haris ya sake canza man Abu kaɗan zanyi sai bugu da zagi na cin mutuncin, haka Haris ya maida Ni jaka yadda kasan auren bariki, sai daga baya nagane mahimmancin iyayena wanda daga baya ban fahimta ba,

Haka rayuwa ta dunga tafiya har Allah ya bani cikinka wanda baƙinciki kamar ya kashe Dada da kingin ƴan gidan,haka Har Allah yasa na haifeka saidai Sak kamaninka Ni ka biyo wanda tunda na kalleka ka tuno man da fuskar Mahaifina, tunda Dada ta ganka ta ce kai ba ɗan Haris bane nasan inda na kwasoka, hankalina ya tashi, da ƙyar aka samu wutar ta ɗauke, haka Mahaifinka ya raɗa maka Suna Muhamman Nuraim,wanda tunda kazo Duniya Sajeeda ta nuna maka ƙauna da Soyayya wanda nasan tabbas koni da na haifeka bani gwada ma Sajeeda ƙaunar da nake maka..........✍️




Wannan kenan




*Comments, Share fisabilillah*



*By Mariam sani*





*08109554986*
[11/29, 6:02 PM] Riamcool: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl



*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 33&34


___________✍️Tunda kazo duniya Sajeeda ta nuna maka ƙauna da soyayya wanda nasan tabbas koni da na haifeka bani gwada ma Sajeeda ƙaunar da takeyi maka,komai naka Sajeeda ke yi maka, Haka rayuwarmu ta dunga tafiya cikin ƙunci ba baƙinciki, nayi Kuka marar adadi ba baƙinciki na Rushe Rayurmu da kaina, n kuma danasanin Soyayyar da nake ma mahaifinka wacce bata da Amfani,Saidai na Tawakkali da Allah da Manzonsa, wanda nasan Tabbas wannan ita ce ƙaddarata, saidai ace komai yana da Sanadi,



Lokacin da Sajeeda take da 18 yrs Mazajen aure suka dinga fitowa lokacin ta gama Secondary school,Dada ta Matsa lamba sai Sajeeda ta auri Sabi'u ɗan Aminiyarta, ita kuma lokacin Sajeeda ba Sonshi take ba, babu izayar da Dada bata nuna mata ba dan ta Amince,




Ranar da bazan taɓa mantawa ba Shine ranar da na wayi gari Sajeeda ta ɓata, hauka ne kaɗai ke banyi ba, ga wani ƙarin kayan takaicin shine Dada da ta dinga yaɗa labarin cewa Sajeeda Saurayi tabi suka gudu yawon iskancin, ga Mahaifinku shima babu kalar gorin da baiyi man ba, wajen Saratu kuwa ba'a cewa komai dan dama tunda na haifeka taga ɗa namiji ta ƙara tsananta da liƙa man sharrika wajen miji kala_kala


Haka Rayuwata ta dunga tafiya an ƙara gwada man izaya duk nabi na lalace kai ba kace daga ƙasar ETHIOPIA na fito ba, a hakan har Allah yasa kakai Shekara biyu sannan na yayeka, bayan na yayeka da 2 Month Saratu ta sake Haihuwar ƴan biyu dukkanninsu Mata wannan karinm baƙinci kamar ya kasheta,duk Sanda ƴan uwanta suka zo ina babu irin maganganu da habaicin da basuyi man, dan Sosai Saratu take ganin gata wajen Dada ko dan tana ƴar ƴar uwarta ne


Haka aka raɗa ma yara suna Khadijah da Safiyya
Lokacin da kaje wajen Khadijah da Safiyya zakayi masu wasa Saratu takan dake ka tundaga lokacin ka daina zuwa ka zama Miskilin ƙarfi da yaji wanda lokacin ko Mahaifinka baka yarda dashi,haka zalika Dada mai zare maka idanu, kakanka kaɗai kake yarda dashi Malam Ali,lokacinne mai bi ma Mahaifinka Kabir ya ƙara aure ya auri Mahaifiyar Nafisa Jamila

Tunda Jamila ta shigo wajenta ne kaɗai nake samun Salama, haka harta Haifi Nazir lokacin Kanada 3 yrs lokacin Allah ya bani cikin Abdurrahim saida ya Shekare Sannan na haifeshi, shima da aka ga Namiji ne Dada har yunƙurin Sace Abdurrahim tayi bata samu dama ba wai Acewrta duk ku zaku cinye mata kuɗin ɗa, Saratu kuwa dagana ko a hanya bata nuna ta sanni tsakanina da ita sai zagi

Abdurrahim nada Shekara na ƙara samun wani cikin,lokacinne Mahaifinku ya bijoroman da Son a zubar da cikin, naƙi Amincewa shine ya dinga gana man azaba, daga nan kuma ya ɗauke yiman wani Abu, koda yaushe cikin Azabtar dani yake haka Har Allah yasa na Haifi Ni'imatu lokacin komai Ni keyi maka,a lokacinne kuma Malam Ali Allah yai mashi rasuwa wanda ba ƙaramin girgizani tayi ba,

Bayan komai ya lafa ne kana da 6 yrs lokacin ka fara fahimtar wasu abubuwan hakan yasa komi ka samo burinka ka bani, lokacin Abinci ma gagararmu yake sai na fita na buɗo na kawo maku kunci kuɗaɗen da na ibo na iyayena naba ma Mahaifinku ya hanani a lokacin kuma arziƙin Mahaifinku ya ƙara bunƙasa amma idan ka ganni kai baka ce Matarshi ba ce Sai kai Tsammanin ƴar aikin gidan ce, lokacin Su Muhsina ke Mani rashin kunya da fitsara, dan tun suna ƙananu dama basu ganina da ƙima da arziƙi,


Haka rayuwa ta dunga tafiya kullum cikin ƙunci kana girma kamanninka da na Mahaifina na ƙara bayyana, kanada 8 yrs ka sauke Alƙur'ani mai girma dan tun kana ƙarami kake nutsatse, Saɓanin Abdurrahim dake da shegen rashin ji da shiririta, bayan kun gama Primary ne Mahaifinku ya ɗauki Muhsina ya kaita can London tayi karatu kai kuma ya barka tanan,


Sai a lokacinne Jamila ta sake Haihuwa ta haifi Nafisa,wanda tunda ta haifi Nafisa ka koma can ka tare,a lokacinne na gano zagon ƙasa da Jamila keyi man, nagano Abinda yai matuƙar girgizani wanda tabbas kowaye na faɗa mawa bazai taɓa yarda ba hakan yasa nai nesa da ita kaima kullum nake kwaɓarka akan kayi nesa da ita, a lokacin ne kuma cikin Hameed ya ɓullo man wanda kamar Saratu tayi bindiga, bata ida tada hankali ba saida taga na sake haihuwar ɗa namiji Sannan,hankalinta dana Dada ya tashi dan babu kalar bokayen da basu bi ba amma Allah ya tsareku,komi Dada ta gani lokacin sai ta dinga janku a jiki wanda lokacin hankalina bai kwanta da ita ba,


Damma a lokacin Abdurrahim da Ni'imatu suna tare man wani Abun dan ba ƙananun masifaffu bane, dukda suna ƙananu, girmanka ya sani na ɗan huta da fita nemo mana Abinci, dan Kanada shekara goma sha biyar ka fara zuwa gareji kana biɗo mana na Abinci,dukda cikin Ni'imar da Saratu take hakan bai hanata yin baƙincikin da Mahaifinku ya sa ka daina zuwa gareji ba,dan ita ta tura Mahaifinku akan idan ka gama Secondary ya kaika can Canada kaima kayi karatun dan ita a ganinta idan kayi nesa dani zan ida shiga cikin ƙuncin rayuwa, saidai Ni da naji hakan ba ƙaramar godiya nai ma Ubangiji ba,dan inaji wata hanya ce Allah ya kawo man ta fita cikin ƙuncin rayuwa


Haka Mahaifinka ya turaka University of Toronto Canada wanda kake karantar business,lokacin kuma Abdurrahim shima yana ɗan taimaka man da wani Abun haka rayuwa ta dunga tafiya wanda Wahalhalu da dama suka ɗan rage man Sakamakon kuɗin da kake turo man duk wata wanda ka ce tunda kaje ka haɗu da Abokinka Jabeer ba zaman karatu kaɗai kuke yi a can ba harda ɗan kasuwanci kukeyi wanda Allah ya Albarkace shi Sosai, ganin na rage Wahala ne Mahaifinku ya tuhume Ni ina nake Samun kuɗin, lokacin na faɗa mashi komai shine ya ce daga lokacin ya janye Hannunshi daga karatunka tunda har kana da kuɗin da kake ɗauke man buƙatuna, zaka iya biya ma kanka kuɗin karatu,hankalina ya tashi saidai tunda na faɗa maka kake cewa baban Jabir ya ce zai ɗauki hidimar karatunka hankalina ya kwanta



A lokacin ne babanka ya shahara wajen dukiya saidai babu abinda ya janza zani wajen gana man azaba,lokacin da Salihu zai auri Huraira lokacinne Mahaifinku shima ya ƙara auro Halima,babu yadda Saratu batayi ba akan Su haɗe man kai da Halima amma ta ƙiya haka yasa itama Dada take ɗan musguna mata,


Cikin ikon Allah Rayuwata ta fara canzawa dukda matsin da kake ciki hakan bai hanaka ɗauke Abubuwa ba dan tun daga lokacin ne komai kai keyi mana nida kingin ƙannenka





Wannan kenan



*Comments, Share fisabilillah*






Waɗannan sune ƙwarin guiwata





*By Mariam sani*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️




*08109554986*
[11/29, 6:02 PM] Riamcool: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl



*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 35&36


___________✍️tundaga lokacin komai kai keyi mana nida kingin ƙannenka, Rayuwata ta ɗan Fara canzawa Saratu tayi danasanin ba ma Mahaifinka Shawarar kaika ya kaika karatu tayi ƙulli Mahaifinka yasa ka dawo amma Allah bai yarda ba,haka rayuwa taci gaba da tafiya wajen dangin Mahaifinka babu abinda ya canza zane,hantara da kyara wacce har na riga da na saba, kaiko a hankali kasuwancinku yaci gaba da haɓɓaka Allah ya Albarkace shi har ka bani jari nakan Saro atanfofi na siyar da wannan ne nasamu na fara fita cikin yanayin Rayuwa Nuraim niko babu Abinda zance dakai sai Allah sa Albarka,dan kayi man dukkan wani Abu da ɗa ya kamata yai wa Mahaifiyarshi,"



Numfashi tasha taci gaba da cewa "daganan ne kuma Mahaifinku ya Arziƙinshi ya ruɓanya nada dan duk cikin Jigawa babu wanda bai san Haris Ali ba,daganan Mahaifinku yasayi fili a Abuja ya gina mana Haɗaɗɗiyar Estate gaba ɗayan Ahalinshi ko wane da part nashi haka muka Tattaro muka baro Jigawa muka dawo Abuja lokacinne ashe kuma inada ciki har yakai Wata bakwai bansani ba sai daga baya nagane, dukda babu Abinda Mahaifinku ke man hakan bai hanashi nuna ƙin cikin dake jikina ba Wanda harta kai shi ga yiman saki ɗaya, dukkanku babu wanda yasan da wannan daga Ni Sai Ni'imatu, Haka har na Haifi Hameeda auta,


Bayan ka kammala Degree ɗinka ne kace Abdurrahim ya taho nan yaci gaba da karatu kai zaka ɗauki nauyin shi haka zalika lokacin ka buɗe man Plaza a nan Abuja wanda lokacin kasuwancinku yakai ga har kun gina katafaren Company a nan Abuja

Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin ikon Allah komai nawa ya canza ga Ni'imatu da Hameed da ya ɗan fara girma suke tayani harkar kasuwancina


A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya wanda Nafisa tun lokacin da ta fara wayo bata da aiki sai koda yaushe ta Zauna Hamma Nuraima, ban kawo komai a raina ba dan a zatona ƙauna ce irin ta ƴan uwantaka,


Bayan Ni'imatu ta Kammala Secondary school ne itama kace ta taho nan tayi karatu duka ƴan uwan Mahaifinku babu baƙincikin da basu nuna ba, sun buga sun buga sun ƙyaleni haka,tunda Ni'imatu taje can ta haɗu da Jabir ƙauna mai tsabta ta ginu tsakanin su


A hankali nima na ɗan fara jin daɗin Rayuwa saidai har na Mutu bazan taɓa Mantawa da abu Ukku a rayuwata ba wanda kullum dasu nake kwana na tashi da su, Mahaifiyata Alekxendra da Kuma Mahaifina Muhammad sai Sajeeda waɗanna shine nauyin da yadanne man ƙirji wanda ko wane fitar Numfashi nawa nakan tuno dasu


Bayan ka Kammala Degree ɗinka na biyu ne kake ta shire_ shiren dawowa, lokacin shi kuma Abdurrahim ya kusa kammala na farko, Ni'imatu ma na hanyar kammalawa




*Kuyi haƙuri da wannan aiki yai man yawa wannan ma a tsaitsaye nayi maku shi*


*Masu yi man sharhi ina godiya waɗan basayi kuma ina miƙo gaisuwa*



Wannan kenan



*Comments, Share fisabilillah*



*By Mariam sani*





✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*08109554986*[11/29, 7:17 PM] Riamcool: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl




*RUSHEWAR Rayuwa*


*NA*
*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*Bismillahirrahmanirrahim*


*Page 37&38*




______________✍️Bayan ka Kammala Degree ɗinka na biyu ne kake ta Shire_Shiren dawowa lokacin shi kuma Abdurrahim ya kusa kammala na farko, Ni'imatu ma na hanyar kammalawa, a haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin ikon Allah komai ya canza ta sanadinka, Dada kam ji take kamar ta caka man wuƙa a maƙoshi dan baƙinciki, lokacinne ta fara sauyawa ta daina azabtar dani ta hanyar aiki Saboda jan

Please Login or Register in order to submit comment