Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kammu mu ida ƙarasa shi,"..............✍️







Wannan kenan







*Comments, Share fisabilillah*





Waɗannan sune ƙwarin guiwata








*By Mariam sani*










*08109554986*




_____________✍️
[12/6, 8:07 PM] Riamcool: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl




*RUSHEWAR RAYUWA*

*By*
*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*



https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana,fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa*
(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi




*Bismillahirrahmanirrahim*





*Page 49&50*


___________✍️Ina ganin Abinda ya dace kawai mu barshi har lokacinshi yayi, idan kuma bai Mutu ba muda kammu mu ida ƙarasa shi," Aunty Amarya ta faɗa tana kafe Mama da idanu dan jin ta bakinta,


Dogon numfashi Mama taja tana faɗin "Zainab banƙi ta taki ba,dan koni kaina ɗawainiyar da nayi da Alhaji kwana biyu na gaji, kuma dama inada wani buri akan Alhaji,shiyasa kika ga har na amince da shawararki akan ƙin tafiya da shi India, saidai Maganar mu kashe Alhaji baima taso ba,kawai mu ƙyaleshi nasan bazai kai labari ba,"



Iska Aunty Amarya ta furzar tana faɗin "Kin kau yi tunani mai kyau, amma abinda nake so na ƙara faɗa maki ki sake Tunani kodai mu haɗa kai mu kashi Alhaji ko kuma mu ɓatar da shi ga baki ɗaya,hakanne zai bamu damar cin dukiyar Alhaji cikin sauƙi,"



Numfasawa Mama ta ƙara yi tana faɗin "Zainab indai zanci dukiyar Alhaji,to ba zanyi dana sanin kashesa ba, amma da mu ɓatar da shi ina ganin ƙara mu kashesa kawai,"

Nan Aunty Amarya tai Na'am da zancen Mama



Haka rayuwa taci gaba da tafiya,har tsawon Sati guda amma babu abinda ya sauya na daga samun sauƙin Abba,dan idan ka ganshi bazaka taɓa cewa Abba bane, da shi da gawa basu da wani banbanci,banbancisu kawai shi akwai rai a tare dashi, Babu Abinda Mama ke yiwa Abba, dan tunda sukayi shawarar kasheshi,ta fidda hannunta daga lamarin Abba, komai saidai mai gadi yayi mashi,a haka Sadeeq yaji labarin Abinda ya samu Abba yayi kuka marar Musaltuwa na ganin zai rasa Abba wanda shi kaɗai ya rage masa wanda yake kalla yaji sanyi,dukda babu Abinda Abba ke tsinana masa,Haka ya shiryo zuwa duba Abba,saidai koda yazo yaga yanayin da Mahaifinsa yake ya ƙara shiga cikin wani Mawuyacin hali,dole yasa ya kwana nan gurin Abba ganin tunda yazo baiga kowa na gidan ba,ga ɗakin Abba duk yayi gaje_gaje da ka shigo zakaji wani irin wari,da Zarni, Sadeeq shine ya gyara ɗakin ya wankewa Abba jikinshi,dan Rabon da yaga Ruwa tun kafin su dawo daga Asibiti,komai na ɗakin Saida yai mashi fes,Sannan kuɗin da yake garuwa da su, sune ya ɗauka ciki ya damowa Abba Fura,yana kawo mashi ya ɗago kanshi ya dinga bashi,duk yawan furannan Saida Abba ya Shanyeta tas,dama rabon cikinshi da Abinci tun jiya,kallonshi Sadeeq yayi yana Tunanin wai yau Abba shine a kwance babu Abinda yake iyawa,bai san Sadda hawayen tausayin Kanshi da Abba ya zubo masa ba,a mamakinsa sai yaga hawaye na bin kuncin Abba shima,



Haka Sadeeq ya zauna tsawon kwana biyu wajen Abba, babu su Mama babu labarinsu, haka yake Zuwa School idan ya dawo ya fita garuwa,da kuɗinne yake Samu ya siya musu Abinda za suci,Saida yai kusan kwana biyar Sannan su Mama da Aunty Amarya suka dawo,koda suka dawo saida suka kwana biyu basu leƙo Abba ba,Cikion na Ukkun ne Mama ta shigo, tana shigowa ta dinga tattoshe hanci,harda ƙaƙarin Amai,f'ɗago idonta tayi tana kallon Sadeeq ta ce "kai duk Abinda kuke yi kaida Mahaifinka mun baka nan da kwana biyu ka tattara kaida Mahaifinka ku bar gidannan ga baki ɗaya, sannan garinnan ma ka barshi,dan wannan ne gatan da zan iya maka," tana gama faɗa tayi ficewarta,



Da kallo Sadeeq ya bita yana girgiza kansa,yana Tunanin baƙin hali irin na su Mama,da Safe Sadik ya Samu kango a nan bayan gidansu ya tattara kayanshi da na Abba ya maida can,Da Taimakon Abbukanshi aka ɗakko Abba suka dawo cikin Kangon, haka Suke Rayuwa cikin kangonnan, wanda koda yaushe suna cikin Zullumin Rayuwarsu, Sadeeq yayi kuka marar adadi,yaji ya tsani Su Maman wanda duk Sune Sanadin Rushewar Rayuwarsu,Sai daga baya yake jin Su Mama sun bar ƙasar ma ga baki ɗaya, sun koma London da zama,










*Raheenatu*




Tsawon Sati biyu ke nan tunda Alhaji Bashir ya nemeta kullum sai yazo mata da yana buƙatarta, Saidai wani abin Mamaki duk lokacin da yazo zai kusanceta,Sai bacci ya kwashe shi, kuma idan ya falka zaiga kamar ya kusanci Raheenatu ne, tun Abin na Bama Raheenatu tsoro har yakai ga yabar bata,don tasan aikin Raihana ne,shiyasa hankalinta ya bar tashi,


Sabreen ce tayi Sallama ta shigo, Tunda ta shigo ta kafe Raheenatu da idanu, tanata Saƙa abubuwa da dama a kanta,Murmushi ta sakar ma Raheenatu Tana faɗin "Ohhh ni Sabreen, Har yanzun fushi kike dani akan faɗan da Mukayi, haba Raheenatu ya kamata ace kin ɗan dinga sassauta Zuciyarki,ke Kullum cikin gaba kike da Mutum,ni fa, tunda nake Wllh babu Macen da na taɓa So kamarki,shiyasa har kika ga inata liƙe maki,"


Sheƙeƙe Raheenatu ta kalli Sabreen tana faɗin "Sabreen dan Allah idan kinga dama karki liƙe man ki barni daga yau,na riga na faɗa maki bani ba ke tun randa kika ja Ubanki ya ɗora man ayyukan gidannan a kaina, tun daga lokacin naci Alwashin ko kallona kika ƙara yi Sai na shaƙi Maƙwallatonki wllh," ta ƙarase zancen da banka ma Sabreen harara



Sabreen kuwa wani takaici ne ya turniƙeta ƙwayarta ta Motsa( kunsan ƴan shaye_shaye da saurin fushi🤣) wata Ashariya ta lailayo ta ɗirka ma Raheenatu, Tana faɗin "ke zan farka maki ƴan ciki yanzunnan na siyar da su dan Uwarki, duk girmana baki gani ba,Ni ba komai ba ne na kira a siyeki a bani kuɗinki yanzu......," Kafin ta idasa Raheenatu ta bugar mata baki tana faɗin "duk iskancinki kiyi amma karki sake Zagarman Mahaifiya,banza karya,kuma idan kika siyar dani Ubanki kikayi wa asarar hq dan da ita ne yake Samun natsuwar da wajen uwarki bai Samu,shegiya ƴar Shaye_ shaye,kawai,"

Bugu tazo kawo ma Raheenatu ta kauce,nan Raheenatu ta kamata tai Mata shegen duka,dan duk girman Sabreen babu abinda take iyawa duk ƙwaya ta riga da ta ƙarar da ƙarfin,


Saida Raheenatu taima Sabreen lilis Sannan ta jawota kamar wata tsumma ta jefar da ita


Da ƙyar Sabreen ta samu ta lallaɓa ta Nufi Side ɗin Hajiya Bilkisu, tana shiga Ta Zauna tana cizon yatsa, Hajiya Bilkisu na shigowa ta Samu Sabreen fuska duk ta kumbure,da Sauri ta ƙaraso tana faɗin "Sabreen lafiya? Naga fuskarki a kumbure,"


Wani mugun Ashariya Sabreen ta Sake kalailayowa Sannan ta faɗa ma Hajiya Bilkisu abinda ya faru tsakaninta da Raheenatu,

Ran Hajiya Bilkisu idan yayi dubu ya ɓaci,kallon Sabreen tayi tana cewa "ke Sabreen daɗina dake rashin hankali wllh ke duk abinda ƙwayarki ta faɗa maki shi kikeyi,yanzun gashi kin lalata mana shiri,yanzun abinda ya kamata tunda naga ta lalama bata yiyuwa koya mata shaye_shayen, mu Samu mu dinga zuba Mata Kayan mayen cikin Lemo, da haka suka aje Shawara duk lokacin da Hajiya Bilkisu zatayi Kunun aya ko Zoɓo sai su Samu su cika ma Raheenatu ƙwaya a ciki,ita kuma Raheenatu da shegiyar ƙwaƙwa,sai ta sha komi Hajiya Bilkisu ta kawo Mata, da tasha zata dinga yin Bacci da ta tashi sai taji dukkan wani damuwan Da take dashi,Sai taji ta yaye, Haka za taji duk lokacin da bata Sha Zoɓon Hajiya Bilkisu ba wata Damuwa ta lulluɓeta kanta yai ta Juyawa,shiyasa wani lokacin da kanta zata Nemi Hajiya Bilkisu ta bata,














*RAIHANA*



Yau tunda na tashi nake jin wani Sabon yanayi a tattare da Ni,ga wani irin kwaɗayin jini da nake ji, ji nake bani da wani Abu
wanda nake Son Sha idan banda jini, kwanciya nayi naji duk kwanciyar bata min daɗi,


Gajiya nayi da kwanciyar na fito don na Samu, koda jinin tsuntsu ne nasha ko naji sassauci, ina fitowa na ci gaba da zagaya Harabar gidan ina cikin zagaya wa ne,saiga Wani baƙin Tsuntsu ya faɗo, yana faɗowa yadda kasan wata mayunwaciyar zakanya haka na kafa ma Tsuntsunnan baki na zuƙe jininshi, ina gama Sha naji wani kwanciyar hankali ya ziyarce ni,dukda ban samu gamsuwa da wannan ba,juyowar da zanyi naga Wani ɗan Matashin yaro ya kafe wajen da na yadda tsuntsun nan, ga sawun huda a dai_dai Wuyanshi, zaro ido waje nayi Hankalina yai Matuƙar tashi ganin Tsuntsun nan ne ya koma Yaron,ja da baya na dinga yi Hankalina a Matuƙar tashe....✍️




Wannan kenan







*Comments, Share fisabilillah*





Waɗannan sune ƙwarin guiwata







*By Mariam sani*







*08109554986*
[12/7, 6:57 PM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*


*By*
*Mariam sani*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*





*Bismillahirrahmanirrahim*




*Page 51&53*



_____________✍️Zaro ido waje nayi hankalina yayi matuƙar tashi ganin Tsuntsun nan ne ya koma Yaron, ja da baya na dinga yi, hankalina a matuƙar tashe, da ƙyar na samu ina "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un," kallon yaron nake yadda naga yanata ƙaƙarin Mutuwa, tun yan shure_Shure har ya kai ga ya daina, rai yayi halinsa, zuwa nayi na duƙa a gaban gawar na fashe da kuka mai cin rai, ji nayi ga baki ɗayan duniyar ta tsayaman, dukda kisa ba baƙon abu bane a wurina, wannan shine wanda yafi tsayaman a rai, ganin ƙaramin yaro ne na kashe, naji na ƙara tsanar kaina da rayuwata, ji nayi da wannan ƙasƙantacciyar Rayuwar da nakeyi gwara mutuwa, alamar Motsi naji a baya na hakan yasa Ni waigawa, Alhaji Muttak'a ne tsaye waje guda ya ƙafe, dan tsananin tsoro ganin Abinda Raihana ta aikata.


Cikin ɗari_ɗari ya matso kusa da gawar yaron, yana faɗin "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un, Ni kam na shiga ukku naga ta kaina, tunda kin riga da kin ɗauki ran jikana don Allah Ni ki barni hakanan, ke Ni Wallahi idan ma kina son na Sakeki Sai na sake ki, kije can ki auri ɗan sawalwalin saurayi, yoo dama ke ina Ni ina ke, ke ai sai irin Hand Some guy ɗinnan shine ya dace da ke,amma Ni kina ganin Fuska duk tamojin Tsufa ya kamani,ga hancina kamar an bugan, ga baƙar fuska,kamar ta bukan gwaggwon biri,ke Ni wllh nasan koni banyi maki Adalci ba da na aureki,kuɗin da Mahaifinki ya ci na yafe mashi,amma dan Allah ki ƙyaleni nima karki kasheni, wllh ban shirya Mutuwa ba yarinya kuma wllh wannan gawar Bama zan nuna nasan wani Abu b game da gawar yaron nan,kawai zanyi duk yadda zanyi ganin ba'a gano Abinda ya kashesa ba,Zance ƙusa ce ta cakar mashi wuya kafin na kai asibiti ya mutu," ya ƙarashe zancen kamar ya fashe da kuka





Tunda ya fara Maganar nake kallonshi,wai ya sakeni, "To idan ya sakeni na tafi ina?," Na tambayi kaina, ƙala ban ce mashi ba,na tashi na wuce Side ɗina,


Tana tafiya Alhaji MUTTAƘA ya sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya,kana ya ƙura ma yaron ido,yana faɗin "Allah Sarki Sudais Ni na riga na janyo maka Mutuwa wajen shegen Rashin Mutuncina, gashi na ja maka Mutuwa," yana gama faɗar haka ya saɓi gawar yaron yana nufar sashen Zaliha, yana shiga ya dire Ma Zaliha gawar a gabanta,

A matuƙar razane ta miƙe tana faɗin "Alhaji mi ya faru da Sudais idan ba gizo idanuna keyi man ba kamar gawar Sudais nake gani,"



Mamadin Alhaji MUTTAƘA ya bata amsa kawai sai ya fashe mata da kuka,kallonshi Zaliha ta sake yi tana faɗin "Alhaji yanzun fa ba lokacin Kuka bane ka faɗa man Abinda ya faru,"

Cikin Muryar kuka Alhaji MUTTAƘA ya ce "Zaliha ba gizo idanunki ke yi maki ba, tabbas gawar Sudais ce,yana tsaka da wasa ya faɗo kan wata ƙusa ta cakar mashi wuya,ina zuwa na ɗauke shi don na kaishi Asibiti,kafin na kaishi Allah ya ƙarɓi abinsa,"


"Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un shine Abinda Zaliha ke faɗi, kallon Alhaji MUTTAƘA tayi ta ce Muttak'a kuka ba naka bane, Addu'a ya kamata kayi mashi,ka rasa iyayenka da Matarka da ƴaƴanka kayi haƙuri ballantan jikanka,yaro wanda bai san komai ba, Allah ya jiƙanshi da rahama," Zaliha ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa sosai,


Kallonta Alhaji MUTTAƘA yayi yana faɗin "Zaliha duk ba wannan ba,dole ne nayi kuka Ni kaɗai na san cikin tashin hankalin da nake ciki, ki barni kawai ki man Addu'a," ya faɗa yana miƙewa ya fice,
Kallonshi Zaliha tayi tana girgiza kai, Dan kwanannan ta rasa gane kan Alhaji MUTTAƘA,kullum idan zai fita sai ya ce tai mashi addu'a saboda Rayuwarshi na cikin haɗari,
Wayarta ta ɗauka ta kira ƴarta Mahaifiyar Sudais,tace tazo tana nemanta, bata faɗa mata abinda ke faruwa don karta ɗaga mata Hankali,koda tazo saida Zaliha tayi mata ƴan Nasihohi Sannan ta faɗa Mata rasuwar Sudais,Khausar tayi kukan Rasuwar ɗanta kamar b gobe don shi kaɗai Allah ya bata,bayan Tayi kusan 15 yrs Allah bai bata haihuwa ba,Saidai ta ɗauki komai bisa ƙaddara ne tasan Allah da ya bata yafi ta So shiyasa ya Amshi abinsa,haka akayi wa, Yaron Sutura aka kai shi makwancinsa,




Nikam tunda na shiga nake Rusgar kuka ji nake duniyar ta ƙara man ƙunci fiye da yadda take man,rabon da nace nayi wani farinciki, har na Manta,Rayuwata bata da wani ƴanci,ba dai Safiyar Allah ta fito ta koma ba,ban zubar da hawaye ba,Tunda nake kisan Mutane,ban taɓa jin wanda ya tsaya man a rai ba kamar wannan,ina ji akayi wa Yaron Sutura aka kaishi Makwancinsa,ji nake dama nice na Mutu ko zan huta da azabar duniya,ko an Samu a rage babbar annoba a cikin duniya,

Haka na kwanta,ina ƙara jin wani Sabon yanayi a tare da Ni,koda na kwanta ina rufe Idona na ganni cikin Wannan ruɓaɓen tsohon gidan da na kassara Abba a ciki, Zaune idan banda Kuka babu abinda nake,ina cikin Kukanne saiga Halittu biyun nan da nake gani sun zo man, Saidai yau harda Wata yabiɗaɗɗiyar Tsohuwa a bayansu Suna Zuwa,bisa kaina suka tsaya,ɗago da idanuna nayi da suke Zubar da hawaye na kallesu, ina faɗin "Tabbas kune Silar jefani cikin bahagguwar rayuwar nan,a cikinku akwai me amfani da Ruhina,kuma ku sani wllh yadda kuka kassara man Rayuwa ko ba daɗe ko ba jima sai na ɗauki fansa,ba don komai nake Son Zama shahararriyar matsafiya ba sai don ku,
Yadda kuka lalata man Rayuwa sai na lalata taku fiyeda yadda kukaima tawa Rayuwar,"



Wata sheɗaniyar dariya suka fashe da ita Su Ukkun,kafin su gimtse bakunansu,kallona ɗaya daga cikinsu yayi yana faɗin "Tun kafin ki fara ɗaukar fansa mu zamu ida lalata Rayuwarki ga baki ɗaya," ya faɗa yana buɗe wani tsohon ɗaki da ya riga duk ƙura ta baɗe shi,yana buɗewa wani gurnani mai ban tsoro ya dinga fitowa ta cikin ɗakin,Kallona yayi yana Umartana da na shiga ɗakin ja da baya na dinga yi ina girgiza masa kai hawaye na bin kuncina,Tunkaro Ni ya dinga yai har ya cimmani yana jawoni da ƙarfin tsiya,ina Tirjewa yana jana har ya kaini wannan ɗakin mai bala',itaccen duhu,wasu surkulle suka kama da Matar nan suna gamawa akayi wata masifaffiyar tsawa wacce tasa kunnuwan toshewa daga ji na waƴansu Second,ban gama tsorata ba,Saida naga Abu mai bala'in tsoratarwa hankalina bai ida tashi ba saida ya damƙo Hannuna da hannunshi mai masifar zafi kai kace garwashi ne,idanuwanshi kaɗai nake iya gani Jajaye kamar garwashi,gasu suna Zubar da jini,sandarewa na ƙara yi waje guda danji wani Abu mai kama da icce na ƙoƙarin shiga ta ƙasana,
Ban ida dawowa daga suman wucin gadin da nayi ba naji an tura man shi, Wata Mahaukaciyar ƙara na saki ina faɗuwa wajen Sumammiya,









*Nuraim*


Dukkan wasu Al'amurra Na Nafisa ya riga ya sa mata ido ita da Mahaifiyarta,saidai har yanzun bai gano komai ba,don Nafisa dukkan wani Motsin Nuraim tana sane da shi,


Zaune yake Nafisat na ta zuba mashi shagwaɓa da taɓara kala_kala,duk abinda take,sam Hankalinshi bai tattare da shi,mamadin ya ji daɗin Abinda take mashi,sai ma wani haushinta da ya kamashi,kwaɓe hannunta yayi da take ta shashshafa shi dashi,



Ɗago fuskarta tayi tana faɗin "Honey miye haka kuma? Ko bakaji daɗin Abinda nake maka ne," "Eh," ita kaɗai ce ta fito bakinshi yana miƙewa ya shige Toilet ya ɗauro Alwalla,Yazo yana nafilfilu da karatun ƙur'ani ,saida ya raba dare yana ibada sannan ya tafi ya kwanta,koda yaje ya iske Nafisa har ta riga da tayi bacci,ƙaramin tsaki yaja yana kwanciya,


Ana kiran Asuba ya farka yayo Arwalla, yazo yana tada Nafisa,Tana tashi yai ficewarshi Masallaci,yana fita Nafisa taja ƙaramin tsaki tana faɗin "aikin banza kawai zai zo ya tada mu daga bacci,nidai nasan koda nayi Sallar nan Bama zan shiga Aljanna ba saboda baƙaƙen ayyukan da nake aikatawa,to don mi zan ɓata lokacin kan salla? Ina Gara na kwanciyata na More duniya," tana kaiwa nan ta gyara kwanciya bacci mai daɗi na sake ɗaularta,



Shi kam Nuraim na fita Masallaci akayi Sallah ya fara karatun ƙur'ani har saida Rana ta ɗan fara fitowa sannan ya rufe,

Yana fitowa kai tsaye Part ɗin Mommy ya nufa,yana shiga ya iske Hameeda na gyara Falon Mommy, gaisheshi Hameeda tayi,da fara'a a fuskarshi ya amsa mata, yana faɗin "ina Mommy take?," "Lazimi takeyi amma nasan ta kusan gamawa," Hameeda ta faɗa tana dawowa kusa da Nuraim ta zauna itama kyakkyawar Matashiya ce, zama tayi tanata ma Nuraim surutu har sai da ya gaji ya korata,ya ɗan daɗe sannan Mummy ta fito,

Da murmushi ɗauke a fuskarta ta ƙaraso tana faɗin "Son nasan tun ɗazun kake jirana,gashi na tsayar da kai nasan kana son zuwa Office,"


Safkowa yayi daga saman kujerar ya duƙa yana gaida Mommy,

Da fara'a Mommy ta amsa mashi, sun ɗan taɓa fira sannan ya tafi,


Yana Zuwa ya iske Nafisa ta gama haɗa Break fast, wanka ya shiga yayi, ya shirya cikin wata haɗaɗɗiyar, blue ɗin Shadda,ya fito yana ta zuba uban ƙamshi,koda ya fito bai ya take cikinshi Sannan ya fita,koda Securities ɗinsa suka zo, yauma gwadawa yayi bai buƙatarsu, yai ficewarshi shi kaɗai, gudu yake ta Shararawa bisa Titi, wata kwana ya shiga wacce babu kowa a hanyar haka ya dinga gudu, har ya shiga cikin wani daji yana zuwa dai_dai yana cikin tafiya yaga kamar Mutum zaune a hanya, Horn ya dinga yi amma ko motsi batayi ba,ta haɗa kanta da gwiwa,a fusace ya fito yaga wace ƴar rainin hankali ce ta zauna kan tsakiyar hanya kuma a dokar daji,

Saidai yana tunkarar wajen yaji Zuciyarshi na ta bugawa wanda ya rasa dalili,dukkan wani tako ɗaya da zaiyi dai_dai yake da bugawar zuciyarsa,

Yana zuwa yaga yadda ta haɗe kanta da gwiwa saida ya tuna mashi da wacce yake mafarkin gani, da Samunta, "baiwar Allah, me ya kaiki zama cikin dokar daji ke kaɗai kuma ki zauna a hanya?,"


Fuskarta ta ɗago wacce tai jage_jage da hawaye ga jini ta ƙafafuwanta, kallonshi tayi hawaye na bin kuncinta,a hankali ta furta " bawan Allah kamar yadda Allah ya taimakeka ina Son nima ka taimakeni,"




A matuƙar razane ya ɗago da Fuskarshi don jin Murya da bazai taɓa mantawa ba har ya koma ga mahaliccinsa, kallon ƙwayar idonta, Muryarshi na rawa ya ke nuna ta da yatsa yana faɗin "ke ce nake gani a halin yanzun kuma a gabana?,".............✍️





Wannan kenan





*Comment, Share fisabilillah*






Waɗannan sune ƙwarin gwiwata









*By Mariam sani*








✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️







*08109554986*[12/9, 8:20 PM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*



By
*Mariam sani*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Bismillahirrahmanirrahim*




*Page* 52&53








_____________✍️A matuƙar razane ya ɗago fuskarshi don jin murya da bazai taɓa mantawa ba har ya koma ga mahaliccinsa, kallon ƙwayar idonta yake, muryarshi na rawa yake nunata da yatsa yana faɗin "ke ce nake gani a halin yanzu kuma a gabana? Na daɗe tsawon kwana da kwanaki ina nemanki, ko dan na taimakeki daga hannun azzaluman mutanen can, ashe da rabon na ganki,"



ya faɗa fuskarshi na nuna tsantsar farin ciki da annushuwa,





Kallonshi nake cikin tsantsar Mamaki, cikin raunanniyar nuryata nake faɗin "bawan Allah ni a ina ka sanni? Duka daga haɗuwarmu zaka ce kasan ni, sai dai naji ka faɗi wani sirri na rayuwata wanda ba kowa bane mutum ne daga haɗuwarmu zai san dashi ba," na ƙarashe zancen da faadeshi da manyan idanuna, waɗanda duk suka kumbura sa boda tsabar kukan da nake sha,



Cikin takunshi mai nutsuwa ya tako har zuwa gabana yana kafeni da manyan Idanunshi, Sannan ya sakar man wani lallausan murmushin da saida yasa zuciyata bugawa,da sauri nace "Astagfirillah", tunawa da nayi da aure a kaina, Saurin janye idanuna nayi daga kanshi, dan jin wani Abu na yawo a jikina





Cikin Sweet voice nashi mai fidda daddaɗan Sauti yake furta, "tsawon shekara biyu kenan da saninki a duniyar mafarkina, wanda ba lallai ke kisanni ba,Koda yaushe kikan Zo man da Kukan taimakonki,Wanda na shiga cikin matsananciyar damuwa,dukda a lokacin ban san ke ko wacece ba a cikin raina, amma yanzun tabbas kin zama wani ɓangare na jikina, kuma insha Allah kamar yadda kike faɗin ni kaɗai ne zan iya ƙalubalantarsu, to bi'izinillahi sai na ceto rayuwarki daga halaka koda kuwa hakan shine Sanadiyyar zama ajalina,"

Da sauri na ɗago na kalleshi jin maganganunshi, "Amma bawan Allah kai miye na damuwarka? da har zaka saka rayuwarka a haɗari, ina roƙonka da ka Taimaki rayuwarka karka cilla kanka cikin matsala,bana son ta sanadiyata ka rasa Rayuwarka,bana Son tasanadiyyata ƴaƴanka suyi Maraici a Sanadina Matarka tai Zawarci,Ina godiya da Son taimakon da kai niyyar yai man," na ƙarashe Zancen da hawaye tab a idona


Kallonta yake yadda take ta faman zubda hawaye ji yake kowane ɗigar hawayenta, dai_dai yake da ɗigar darma a cikin Zuciyarsa, "Amma ai Ni nayi niyyar taimakonki, ki sani koda ace ban ganki ba sai na Taimakeki," ya faɗa yana Sake kafeta da Lumsassun idanunsa,




"Komai zakayi bazaka iya taimakona ba saboda sun riga da Sun kammala aikinsu a kaina, Sun riga da sunyi Sadaukarwa dani kalli Wannan jinin da ke fita, daga ƙasana shine Sadaukarwarsu,. Daga halin yanzun kuma babu wanda ya isa ya cetoni daga Wannan hali Saboda Dodon Tsafi ya riga ya kusance Ni," na faɗa ina Sake fashewa da wani irin Matsanancin Kuka mai ban tausayi,




"Kada ki ce Haka,ki ɗaukeni a Matsayin yayanki, na riga da yi maki Alƙawarin ceto Rayuwarki,Kuma babu wani dalili da zaisa na Saɓa maki Alƙwari,Saidai ki Sani Shi kukan da kike bazai canza maki yanayin ƙaddararki ba,ko wane hali kika tsinci kanki ki dinga godewa Mahaliccinki, Sannan kada ki yanke Samun Rahama daga Ubangiji,ki Sani ko wane bawa da tashi ƙaddarar, Allah yana jarabtar bawanshi ne don ya gwada imaninshi,Annabawa ma an jarabce su ballantana kai Mutum, Ki ƙara haƙuri da yanayin ƙaddararki ƙanwata,duk yadda kike ji ki ƙara daurewa da Addu'a ki kasance mai yawaita karatun Alƙur'ani da Azkar, Sannan ki ƙara haƙuri da juriya da yanayin ƙaddararki,ki Sani shi bawa baya wuce ƙaddararsa, ki Sani Zalunci baya Nasara akan Mumini,"




Tunda yake Maganar naji wata Nutsuwa ta Sabko man,hankalina ya fara kwanciya, "Kallonshi nayi ina sakar mashi Murmushi,nake faɗin "haƙiƙa kaine zaka Maye man gurbin da na rasa tsawon shekaru, kaine a yau ka Maye Man gurbin Mahaifiyata,da ƴan uwana,yadda kayi Niyyar taimakona Ubangiji ya saka maka da Mafificin Alkhairi, tabbas bani ma da bakin gode maka,bakina yayi kaɗan da yi maka godiya," na faɗa ina hawayen farinciki,



Shima Murmushin ya Sakar man yana faɗin "Tashi muje na kaiki gida kinga bai dace ki zauna a cikin dokar daji ba,muje na mayar dake gida,"





Tashi nayi da ƙyar ina ciccije lips don zafin da ƙasana ke man, kallonshi nayi ina faɗin "karka damu dani kaje kawai inda zaka tafi,Ni da kaina zan koma inda nake, Saidai Hamma duk lokacin da kake Son ganina kazo nan ka kira Sunana Sau Ukku *RAIHANA* Ni kuma zan fito maka," ina gama faɗar hakan na Rufe idanuna, take yanke na ɓacce,



Waigawa ya dinga yi kodai dama idanuwanshi gizo suka dinga yi mashi a fili yake furta "kodai Aljana ce?," Wata zuciyar ta ce mashi ina saidai Mutum don da Aljana ce zaiji a yanayin jikinshi, ko ma dai micece ita Yaji ya gani Yana Sonta a hakan zai kasance da ita ( lallai Nuraim) zuwa yayi ya shiga Motarshi Zuciyarshi cike da Farinciki,ji yake kamar an ɗauke mashi wani Abu mai nauyi da ya danne mashi Zuciya, cike da Farinciki yake Driving,
















*Raheenatu*



Yau tunda ta tashi take jin ƙwalwarta na mata wani

Please Login or Register in order to submit comment