Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka shi, to tsaya kaji karnukan nan dole ne dukkammu sai mun kusance su in har dai muna son samun nasara,"




Dariyar samun nasara Jogu ya saki yana fad'in "to shikenan Naseer amma yanzu da wane lokacin ne ya kamata mu had'u kuma 'a ina zamu had'u dukkammu,"?


Nan dai Alhaji Naseer ya fad'a mashi inda zasu had'u da lokacin shiga aikin,

A' ranar ne Jogu suka aiwatar da aikin nasu





*************
Raheenatu taci gaba da cewa "Raihana inga wiwin da aka baki har yanzun bata sake ki ba,"

"Ke ce yau da bakinki kike ik'irarin zaki iya kashe rai, ran ma kuma har da na mahaifinki, wallahi Raihana duk abinda Abba kemana ban tab'a tsanar shi koda na second guda ba, tabbas har yanzun ina jin k'aunar mahaifimmu da kuma tausayin halin da aka jefa shi ciki",








Wannan kenan






*Comments, Share and Like*






Wad'annan sune kwarin gwiwa ta






*By Mariam sani🌹💗*





✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl


*RUSHEWAR RAYUWA😓💔*





*By Mariam sanee🌹*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, faɗakarwa ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa*
(R.S.W.A) Ruwa kaɗai ke maganin ƙishi


*Alƙalaminmu ƴancinmu*



*Bismillahirahmanirrahmanirrahim*






*Page 9&10*



______________Suna gamawa dukkan su suka yi sujjada (wa'iya zubillah)wata guguwa ce ta taso.


Ba'a d'au lokaci ba sai ga wannan yabid'ad'd'iyar tsohuwar ta bayyana.


Tana bayyana wajen yai tsit sannan ta bushe da wata shaid'aniyar dariya wacce babu dad'in sauraro, kafin tai shiru tace "dukkan ku na tara ku ne bisa wani dalili, dalilin da yasa na tara ku shine dukkanku kuna son kawo wa ƙungiya casgaro, kuna son kurusa min shiri na tsawon shekaru to bazan laminta ba kar ku manta akwai wad'anda nace su kawo min matan su, wasu kuma d'iyansu, da hakan ne k'ungiya zata samu nasara, sannan JOGU na baka nan da sati guda rana ita yau nake son sadaukarwa ka,

sannan Yarinyar nan iya adadin da zan iya d'ibar ma, shine wata hud'u , saboda ita ce matakin nasarar k'ungiya da ita kad'aice dodon tsafi ya yadda yayi mu'amala da ita, sai yayi mu'amala da ita k'ungiya zata ida samun nasara,


idan hakan ta faru zaka samu babban muƙami a cikin ƙungiya, sannan kuma da ita ce zaku samu dukkan abinda kuke so, ku sani ita ce nasararmu da ƙimar mu", ta fad'a tana bushewa da wata irin shaidaniyar dariya.






*B'angare guda kuwa*



Tunda wannan d'an baturen ya tafi ya barni nan tsaye naƙi matsawa dan wata irin k'iyayyar shi ta d'ar su a cikin zuciyata bansan miyasa ba naji na tsane shi, da haka naja ƙafafuwana na tafi gida.


Ina zuwa na iske Raheenatu da saddeek suma kukan suke, dafa su nayi ina fad'in "meya faru ne?"


Raheenatu tace "mutuwar Sayyadi Hafizu ashe da gaske ya rasu? danni ba wanda yafi ban tausayi irin matar shi,"

"Allah ya jiƙanshi dan shi ba abunda yafi buƙata sama da addu'a," na fad'a ina shigewa bedroom.

Raheenatu da kallo kawai ta bini dan taga duk na canza.


Niko ina shiga na sulale na fashe da kuka naji na tsani rayuwata na tsani kaina naji inama nice na mutu ko banza an rage annoba nan na zauna na cigaba da kukana da naga ba mai rarrashina na tashi na shiga nayi wanka.


Haka dukkammu muka yi sukuku ba mai walwala a cikin mu,



gashi ni ba damar nayi Azkar ballantana naji sauk'i , haka dai mukai ta zama ba mai ce ma wani "eh bare 'a'ah

muna nan zaune sai ga Islam ta shigo tana ta yatsina fuska tace "kuje Abba na neman ku,"

Yarinya ce bazata wuce 15 yrs ba fari ne kawai ya ceceta ita ce d'iyar Aunty Amarya ta fari a gidanmu tana da 'yan mata kamar mu guda biyu su babansu daban.


Raheenatu cikin daka tsawa tace "ke Islam uban wa kike yatsina ma fuska? kamar kinga Kashi to ni zanci uwarki na tattaka ki anan danni ko uwar ki bata isa ta yatsina min fuska ban d'auki mataki ba ballantana ke, wuce ko nayi ball dake yanzun"


"To sabon salo," Islam ta fad'a tana ficewa Raheenatu ko tsayawa ta d'auki mayafi bata yi ba ta fita tana fad'in "billahillazi yau sai anyi ta ta ɗare dan ba 'yar iskar da zata kawo min wargi banyi fatali da 'yar iska ba,"
tana shiga ko sallama batai ba ta tsaya tana ta mazurai kowa da ido ya bita ba wanda ya tanka mata.


Tana fita na miƙe na d'auki zumbulelan hijab na zira sannan na nufi side d'in Abba da sallama na shiga saidai ba wanda ya amsa sai Raheenatu kaɗai ta amsa tana fad'in "shigo ki zauna 'yar uwa rabin jiki ",

Ji mukai an bushe da dariya ba kowa bane Mufida da Mubeena ne .

Raheenatu ce ta ƙule tace "wai ni uban me kuke wa dariya naga dai ba mahaukata kuka gani ba ballantana ayi mana dariya,"

Mubeena ce tace "kusan hakan muka gani Raheenatu ita wacce kike kira da 'yar uwa ai ƙara mahaukaciya da ita saboda ƙara hauka da ka zamto maye,"


Raheenatu zata yi magana Abba ya kwashe ta da mari yana fad'in "ke dan ubanki bansan shashancin banza ina zaune zaki tada min fitina a cikin gida dan iskanci kin mari Islam sune suma gabana zaki ƙara yin wata rashin kunya nemi wuri ki zauna ko na shaƙeki ki mutu uban kowa ya huta sau nawa RAIHANA, RAHEENATU, SADDEEK,zance bani sonku bani ƙaunar ku amma kunk'i ku gane,"

Raheenatu ta share hawaye ta zauna tana fad'in "Abba kamar yanda baka d'aukemu 'a matsayin 'Ya'ya ba nima zan cireka 'a matsayin mahai.......," Da sauri na dod'e mata baki ina fad'in "Raheenatu miye haka? karki ida", na fad'a ina share hawaye



Sai yanzun wata hamshaƙiyar mata wacce ta gaji da haɗuwa da gani ba zata wuce 37 yrs ba cikin isa da taƙama tace "ya kamata Alhaji ayi abinda ya kawo mu,"


Zama Abba yayi ya ce "bawani abu bane ya sa na kirawo Raheenatu da Raihana kuma na tara ku anan sai dan sanar daku gobe war haka Raihana da Raheenatu zan d'aura masu aure da.....," cikin kid'ima na miƙe tsaye ina fad'in "aure kuma Abba? dan Allah kowane hukunci kayimin amma bazan lamunci a d'aura mana aure ba, Abba kada kasa na aikata abinda banason aikatawa ka taimakeni Abba ka temaki rayuw.....," tsawa ya daka min wacce tasani dole yin shiru.


Raheenatu kam ta kasa kukan ta kasa magana saidai bin kowa da ido ji take da rayuwar wasu mutanen hannu ta take ba abinda zai hana ta zare rayukan su a yau d'innan.


Abba ya ce "naga ba amfanin da kuke yi ne shiyasa zanyi auren biyan bashi daku ga abokan kasuwancina duk kuma wacce ban isa da ita ba ta kwatanta yiman ba daidai ba taga idan ban tsine mata ba,"


Raheenatu ce ta mik'e ta ce "Abba ba zamu bijere ma umarninka ba ballantana har takai ga ka tsine mana Allah ya sa hakan shine yafi zama Alkhairi," ta fada tana sakin murmushin takaici sannan ta fice.



Tana fita na tashi na fita nima nabi bayanta ina shiga Falo naga Sadeek da akwati hannunshi ga jikar goyo a bayanshi da sauri na tare shi ina fad'in "Saddeek ina zaka tafi haka da kaya nik'i_nik'i?"


"Gidan zan bari", shi kad'ai ya furta da sauri na kalleshi ina fad'in "Saddeek bangane gidan zaka bari ba? kaiman bayani dalla_dalla yanda zan fahimta,"


Share hawaye yayi ya ce "Adda Raihana Abba ya koreni daga gidannan bansan inda zan nufa ba amma ko ina nake kuna a cikin Raina saidai ina tsoron ranar da rayuwar mu zata rushe ni na tafi had'uwar Alkhairi," da sauri na rungumeshi ina kuka Raheenatu ma dake tsaye tazo ta rungume shi tana kukan da bata samu tayi shi tun d'azun ba.











*NURAIM*



Yana dawowa daga katsina kai tsaye part ɗinshi ya wuce yana shiga ya ga bai iske Nafisa ba , to ina take? ya tambaya ganin ba mai bashi amsa yasa shi kai tsaye yaje ya wanka yana fitowa ya nufi part d'in Dada


yana shiga ya iske Dada ita da Muslima mai aiki suna fira, murmushi yayi ya zauna bisa kafet yana furta "Dada barkanki da hutawa," da sauri Dada ta juyo tana fad'in "Nura yaushe ka shigo? ka ganni nan Musulma ta d'auke min hankali da fira,"


Murmushi yayi yana fad'in "Dada yanzun ni dai yunwa nake ji kisan yanda zakiyi dani,"

Kujimin mutum ina matar taka ta tafi ta barka da yunwa? ke musulma d'ebo mashi abinci yaci kar yunwa ta kashe shi idan kin kawo mashi ki fita dan na sanki da shegen son gulma," ta fad'a tana b'antarar goro


Muslima na kawo Mai yaci ya k'oshi sannan ya dubi Dada ya ce "Dada waini Abdurrahim ya zo nan ne kuwa?",


Kamar jira Dada take tace "ohhhhh ni Saude na shiga Aljanna ban fito ba ka jika dasan k'arin zance Nura Abdurrahim d'inne zai shigo nan gurina yoo ko,dan Hasiya ai baya zo ba yanzun nan Musulma take fad'a man wai Hasiya ke son shi wai harma sun shirya kansu shine nake jiran Harisu ya dawo daga k'asar masu Jan kunnan can muje k'auyen su Hasiya a nema mashi auren ta,"


NURAIM ya nisa ya ce "Amma Dada kin tambayi shi Abdurrahim d'in kinji ta bakin shi?" "yooo na tambaye shi Nura ai zancen banza ne danni Hasiya tayimin auren Abdurrahim da Hasiya ba fashi kamar..........,"Ihun da akayi ne yasa Dada yin shiru tana kallon Abdurrahim sororo tace "Abdurrahim lafiya ne zaka shigo mana gida da ihu ko dan murnar zamu je gidan su Hasiya nema maka auren ta ne?," ta fad'a tana washe hak'ora


"Kut Dada wai ni zaku aura wa Hasiya mai aikin ki Hasiya ta k'auye ashe kau zaku ja na canja mata kamanni k'ara ku bar zancen nan,"


K'ank'ance ido Dada tayi tana fad'in "Abdurrahim ban san kwashewar Albarka yanzun nan Musulma take fad'a min wai kai da Hasiya son junan ku kuke harma kun daidaita shine zaka zo kai min maganar banza maganar wofi dan iskanci ni zaka ji ma kunya,"

A hassale Abdurrahim ya ce "Dada waini wace ma 'yar iskar ce ta fad'a maki ina son Hasiya ni kamata na rasa wacce zan so sai Hasiya, Hasiyar ma 'yar k'auye haba Dada ko sadaka aka bani ai kince na mayar,"


Dada ta ce "ko k'arya Musulma zatai ma ne ba har zance kake zuwa wajen Hasiyar ba kaji min Munafikin Yaro kana zagayawa kana zance sai yanzu zaka zo ka wani zazzare min idanu yaro sai shege felek'en tsiya,"



Zaman dirshan Abdurrahim yayi yana fad'in "Dada yau da alamun zaki kai Hasiya wajen mai d'ori dan idona idon hasiya saina karya ta, yanzun abinda za ayi ki aika a kira maki Muslima da Hasiya su fad'a maki gaskiya".

Dada najin haka ta mik'e ta kira Huwaila, ta kira mata Hasiya da Muslima ko 5 minutes ba ayi ba saiga Muslima da Hasiya sun shigo


Tunda suka shigo Abdurrahim ke kallon Hasiya bak'a ce sosai sai uban k'aton baki da k'aton hanci gata wata zallak'a guda
Dada ce ta katseshi tana fad'in "Amma Abdurrahim kai ba k'aramin munafiki bane ji yadda kake aika mata da kallon soyayya amma zakaima munafurcin banza,"

Hasiya najin ance Abdurrahim na mata kallon soyayya ta d'ago fici_ficin idanun ta kamar na 'yan China ta sauke su a fuskar Abdurrahim tana washare mashi hak'oran ta masu tsatsa ga bakin sai uban wari yake tai mashi wani fafarrr da idanu...✍️






Wanna kenan






*Comments, share and like*





Wadannan sune qwarin gwiwata





*By Mariam sanee*







✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️






*08109554986*[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 21&22


___________✍️Taɓe baki Dada tayi tana faɗin "barshi Faɗima ya gaya min maganar da yake so,idan baiyi sannu ba wallahi ko sati baza'ayi ba zansa a ɗaura mashi aure da Hasiya", ta faɗa tana banka ma ABDURRAHIM harara kamar Idonta zai faɗo,

Shima kuwa hararar ya banka mata dan ba ƙaramin haushi ta tusa mashi ba, kafin ya ce "Dada Allah baki sa'ar sakawa a ɗaura min Aure da Hasiya da wallahi saina shayar dake mamaki,don kuwa saina baki kunya,daga ke har Hasiyar saina shayar daku baƙa......," Bai idasa ba Mommy ta buge mashi baki tana faɗin "wai dan gidanku ba yanzun nayi maka magana ba shin Dada sa'ar ka ce? bansan shashancin banza dana wofi kabini a sannu," ta faɗa fuskarta da Alamun ɓacin rai,


Sadda kanshi yayi ƙasa yana faɗin "Mommy ayi min afuwa hakan bazata sake faruwa ba," murmushi Mommy tayi tana faɗin "A kiyaye gaba Son bansan rashin tarbiyya,"

Ƙara taɓe baki Dada tayi tana faɗin "idan kun gama gulmar taku sai ku saurareni,zuwa nayi inji shin ko bazaki je sunan Samira ba, dan nasan kaɗan daga baƙin halinki kice bazaki je ba," ta faɗa idanunta ƙur a fuskar Mommy, cikin ɗan shakku Mommy ta ce "Dada da Dadyn su ne zai dawo yau to shine zai hana ni zuwa wajen Sunan amma tunda ga Hameeda da Ni'imatu sun tafi lafiya lau sun wakilceni,"

Cikin kallon ƙasƙanci Dada ta ƙare ma Mommy kallo sannan ta ce "sannu mai miji saboda Harisu zai dawo shine ke bazaki je suna ba, naga alamun Faɗima raini ya shiga tsakanina da ke shiyasa", maida kallon ta tayi ga ABDURRAHIM tana faɗin ya tashi yaje ya kira mata Halima da Saratu, (wato Abokan zaman Mommy)da kamar bazai tafi ba saidai kallon da Mommy ta jefe shi dashi ne yasa shi tashi ya tafi.


Yana fita ko 10 minute ba'ayi ba sai gashi ya shigo da wasu Hamshaƙan mata masu ji da kansu,da sallama suka shigo ɗayar na ta yatsine_yatsinen fuska ta shigo,ɗayar kuwa fuskarta fall da fara'a ta shigo, sallama suka yi suka samu waje suka zauna,kallonsu Dada tayi fuska fall da fara'a tana faɗin "lale maharbin da matan arziƙi, mata bana gadon tsiya ba, kun fi ƙarfin wulaƙanci," ta faɗa tana kallon Mommy dan taga yadda zata yi,saidai Mommy ko a fuska bata nuna alamun ɓacin rai ba,hasali ma Murmushi take saki wanda ya ƙara ƙayata kyakkyawar fuskar ta, ta ƴan ETHIOPIA, hakan kuwa ya ƙara tunzira zuciyar Dada dan ba haka taso ba itakam,



NURAIM kuwa tunda Dada take ma Mommy cin fuskar nan yaji ɓacin rai,saidai abinda ya ƙara ɓata mashi rai bai wuce yadda tace ma Mommy gadon tsiya ba,a fusace ya tashi zai fita Dada tai wuf ta miƙe tana faɗin "Kai NURA ina zaka tafi?harda wajenka nazo fa inji batun zuwa Hajji da Umara,amma zaka wani tafi," ta faɗa tana washe haƙora dan Dada badai son banza ba,


Yafi ƙarfin minti biyar kafin a hankali ya buɗe bakin shi ya ce "Dada baki buƙatar Hajji da Umara saboda ta tsatson tsiya zai fito kinga kuwa babu wani amfanin zuwanki," ya faɗa yana ficewa daga ɗakin

Baki sake Dada take kallon shi,ƙwafa tayi ta samu waje ta zauna, kallonta ta maida ga Halima, (wato Ummi)cikin sakin fuska take faɗin "Dama kiranku nayi inji da gaske Harisu ne zai dawo kokuwa, ƙaryar faɗima ce dan ta samu mafaka," cikin sakin fuska Ummi ta ce "Eh Dada yau ne zai sauka,nasha da kukayi waya ma ya faɗa maki,"

Haɗe fuska Dada tayi ta ce "ya kuwa faɗamin tunda bai ɗauke ni a bakin komai ba,"

Sai yanzun matar nan mai yatsine_yatsinen fuska ta ce "wai ni Dada dama kan wannan maganar ce kika wani tado mu daga inda muke, ni wallahi shiya sa ko kiranki wani lokacin bani zuwa,"


Dukda girman Matar Hakan bai hana Dada sakar mata dundu a baya ba tana faɗin "Saratu kinci Ubanki Sadiƙu, kamar ni ina surukar ki zaki dubi tsabar idona ki faɗa min magana,"


Taɓe baki Umma tayi tana faɗin "nifa Dada ba faɗa maki magana nayi ba kawai dai gaskiya ce na faɗa maki,"

Zama Dada tayi tana ta sababin bala'i wai surukanta sun riga da sun rainata, saida ta gaji dan kanta sannan ta koma ɓangaren ta,


Mommy kuwa kamar yadda tayi tsammanin Dady idan ya dawo ba zai kulata ba haka kuwa ta kasance,yana dawowa saima kwandon tujara da wulaƙanci da ya sauke mata,






*RAIHANA*

Tunda muka shiga Jirgi ko kallon Alhaji MUTTAƘA banyi ba ballantana ya samu Arziƙin gaisuwa,shima kuwa ko kulani baiyi ba, haka har muka sauka aka zo ɗaukar mu,tafiya muke amma hankalina sam baya ga hanyar da muke tafiya, tunanina kawai taya zanyi zaman Aure da wannan tsohon, ko bama tsoho bane banji zan iya zama dashi ba,ina tunane_tunane har muka iso wani katafaren gida wanda faɗa maku shi ma ɓata lokaci ne,wangale mana ƙatoton get ɗin akayi muka shige, "Dallah Malama fito!!!!," Alhaji MUTTAƘA ya daka min tsawa, jiki a sanyaye na fito, haka ya dinga tafiya ina binshi yadda kasan Zariya,


Da sallama ɗauke a bakina na shiga Falon,wata babbar mace ce zaune a ɗakin fuska murtuke ba Alamar fara'a ga kuma mata guda shidda sai Maza ukku,suma fuskar su babu Alamun fara'a,saidai tana ɗaga kanta ta ganni ta miƙe tsaye tana faɗin "Alhaji badai wannan kyakkyawar yariyar ba ce a kayi maka biyan bashi da ita ba?".





*RAHEENATU*



Itama tunda suka shiga jirgi ta gaishe da Alhaji Bashir taja bakinta tayi shiru,har suka sauka aka zo ɗaukar su,

Kai tsaye Unguwar VICTORIA ISLAND suka nufa shima gida ne haɗaɗɗe dan za'a iya cewa yama fi na Alhaji MUTTAƘA,


Kai Tsaye suma sashen Uwar gida suka fara nufa.........✍️




Wannan kenan



*Comments, Share fisabilillah*



Sune ƙwari guiwata



*By Mariam sani🌹💗*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR Rayuwa😓💔*



*By Mariam sani🌹💗*








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Bismillahirrahmanirrahim*




*Jinjina da gaisuwa taban girma gareki Aunty Rumaisa Aliyu Inuwa ke ta musamman ce a cikin raina, Allah ya bar zumunci*





Page17&18


_______________✍️Sai yanzun zaki fito kina wani huhhura min hancinanki masu kama da gajeren wandon Salihu, to bari kiji ni bazan ɗauki sabon salon iskancin nan naki ba wallahi," ta ƙarashe zancen da buga ma Baba Harisu wata uwar harara,



"Dada ba fa Abinda kike tsammani bane muka aikata, kawai dai nayi suracen masassara ne, amma kinsan babu yadda za'ayi hakanan mu ƙyaleki," Baba Salihu ya faɗa yana zama bisa 2 seeter,


Sheƙeƙe Dada ta kalle shi tana faɗin "Salihu ni koma raya sunnar zaku yi miya ɗauke ni ya ɗaɗa da ƙasa? kawai dai haushina ɗaya ne a ce kamarni har na tako ƙafafuwana nazo nan a ce wai Huraira ta tafi ta barni a nan,"


Huraira ce tace "wallahi Dada bawai hakanan yasa na tafi na barki ba, naje ne na taimaka mashi ne, amma kiyi haƙuri idan abun ya ɓata maki rai baza'a kuma ba in sha Allah,"


Taɓe baki Dada tayi tana faɗin "yoo ni Huraira meye na bani haƙuri kuma? tunda ba Idi mai fata da Indo kika zaga ba, yanzun dai abinda ya kawo ni nan dama na zazzaga ma Salihu masifa, domme zai hana ki zuwa sunan Samira?idan banda rashin son zumunci a ce ɗiyar ƴar uwarka ta haihu amma bazaka bar matarka taje ba to bansan haka Salihu, ka barta ko yanzun na saɓa maka kamanni wallahi,"


Sadda kanshi Baba Salihu yai yana faɗin "Dada ba wai hakanan kawai yasa na hana Huraira zuwa ba, don kawai banjin daɗi ne shiyasa,kuma kinga su Rafi'atu sun tafi su, shiyasa na ce ta haƙura ko bayan suna sai taje,"



Fuskar tausayi Dada tayi tana faɗin "Ayya Autalle sannu ashe baka jin daɗin jikin, kuma ɗazun Huraira da ta shigo bata faɗa min ba, kaga da banzo na sauke maka kwandon masifa ba,"


Huraira ce ta ce "Dada mantawa nayi shaf shiyasa ban faɗa maki ba amma ga shinan yanzun ai da sauƙin,"


Miƙewa Dada tayi tana faɗin, "to Allah Ubangijin ya sawaƙe Auta, yanzun bari na tafi part ɗin Harisu," ta faɗa tana ficewa



Koda Dada taje zaune ta iske NURAIM da ABDURRAHIM, a falon Mommy, sallama kawai tayi ta zauna tana ta ƴan ɗage_ɗagen hanci sai yatsina fuska take, ga su Nuraim koda suka amsa sallama babu wanda ta kalla,



Ƙura mata idanu suka yi suna ta kallon ikon Allah dukda wannan ba sabon abu bane a wurinta, gaisheta suka yi babu wanda ta kalla cikinsu,da taga kallon da ABDURRAHIM ke mata ne ya ƙara hassala zuciyar Dada, a hassale ta ce "kai ABDURRAHIM kaci ubanka da kallona nace tunda na shigo ka ƙura min idanu kana kallona, to idan kai maye ne kasani kurwata tafi ƙarfinka, dan saidai ka cinye uwarka, mai zubin ɗiyar Roba," ta ƙarashe zancen da zabga ma Nuraim Harara, dan tunda ya gaisheta bai ƙara kallonta ba,


Cikin ƙuluwa ABDURRAHIM ya ce "to waini Dada ya kike so muyi? mun gaishe ki kin ƙyale ba dole mu zuba maki idanu ba,yanzun kuma kallon da nayi maki kin danƙara min zagi kin ci mutumcin mahaifiya ta,"


"Kai zan maka dukan tsiya fa, dan ubanka dan nace ma uwarka ɗiyar roba shine zaka zo ka gaya min magana," Dada ta faɗa cikin hasala da ƙunar rai,



ABDURRAHIM ya ce" Dada dan fa kece, amma da wata ce da tuni na zubar mata da haƙora," banza Dada tayi mashi da taga zaman ba yayi ne yasa tace "kai muskili tashi kaje ka kira mani uwarka, ka wani zo ka tare a nan kamar wanda bashi da mata," ta faɗa tana banka ma Nuraim uwar harara kamar idanunta zasu faɗo,


Mommy ce ta fito tana faɗin "wai ni Nuraim hayaniyar me nake ji.....?" shiru tayi sakamakon ganin Dada, zaune a falo.





**************



Na ɗan jima kwance ina tunanin kalar rayuwar da zanyi nan gaba, gashi yanzunnan naji babu abinda nake kwaɗayi da marmarin sha irin jini, da sauri na kawar da wannan tunanin,ga duk da halin da nake ciki bai hana ni tunanin inda Sadeek yake ba hawaye na share, ina faɗin "ya Allah ka kawo mani ɗauki bisa wannan ƙasƙantacciyar rayuwar da nake yi, kai mani ɗauki,"

Raheenatu ce ta shigo hannun ta da zanen lalle,kallonta nayi wani takaici ya tokare min maƙoshi da ƙyar na haɗiye shi ina faɗin "ke kuma ki rasa wanda zakiyi wa lalle sai wancan tsohon? ni banga abin yi ma kwalliya ba wallahi," na faɗa ina galla mata hararar wasa,



"Ke fa banza ce taya zanyi ma wancan kwalliya, kawai dai dan Aunty Amarya tace ta kira mai lalle muje ai mana, ita kila a zatonta ba zamu je ba, shine ni kuma na bata mamaki dan kinga, ƙara mu rabu lafiya," Raheenatu ta faɗa tana bugun kafaɗata,



Dariya nayi ina tsokanar ta na ce "ohhh ni nasa kwalliyar Baba ce kika yi,dan cancare Amarci,"



Ɓata fuska Raheenatu tayi tana faɗin " kinga Raihana bani son haka, ki bari mu rabu lafiya danni tsakanina da shi sai dai kallo, dan bazan iya rayuwar auratayya da wancan tsohon ba wallahi, dandai Abba na mahaifine kawai ya sa na rufa mashi asiri amma ba dan haka ba da ko wanene saina mashi Abinda bazai manta ba," ta faɗa hawaye tab a idonta,


Dafata nayi ina lallashinta, kallona tayi tana faɗin "yanzun shikenan Raihana an raba ƴaƴan Ammi dukkammu bama tare, ku da Sadeek da nake kallo ina jin sanyi, shikenan dukkammu mun rabu, haɗuwarmu dake sai Allah,"


Kallonta nayi ina faɗin "ke wa ya faɗa maki an raba mu,? babu wanda ya raba mu ki saki ranki kamar kina kusa dani, dan zan dinga zuwar maki ta mafarki ke dai bari yau a ƙara tsafa ni, ni kuma nai maki Alƙawarin zuwar maki duk lokacin da tunani na ya zo maki," na faɗa ina sakin murmushi dan ganin burina ya kusa cika, yau nake son su ƙara tsafa ni,



A harzuƙe, Raheenatu ta ce "wai ke Raihana baki yi ma kanki fatan alkhairi, sai dai sharri mamadin kiyi fatan Ubangiji ya yayemaki amma sai

Please Login or Register in order to submit comment