Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki duba ki zaga a fakaice,don Uwarki ta Silar wa na fara shaye_shaye idan ba Mahaifiyarki ba,wacece Silar Lalata man Rayuwa? To ki bini a sannu yanzu ko na farka maki ciki idon ƙwayata ta Motsa,na gwada maki nima fa na balaga a harkar shan ƙwaya, kinsan koda ban shan ƙwaya bani da kirki ballantana yanzun da na fara shanta, don nan gaba saura Sholisho da Wiwi," Raheenatu ta faɗa tana dukan ƙirjin Sabreen





Murmushin ƴan duniya Sabreen tayi tana faɗin "To Allah ya baki haƙuri ni bada faɗa na tsokaneki ba hasalima shawara zan baki,"



Kallonta Raheenatu tayi tana faɗin "idan ta kirki ce a bani idan kuma bata kirki ba ce, ki bani Cocain nasha don ita zata fiye man Alkhairi,"



Zama Sabreen ta gyara tana faɗin "dama idan bazaki damu ba mi zai hana na temakeki Abbana ya Sakeki,kizo muci duniyarmu da tsinke,don Wallahi yadda kike haɗaɗɗiyar nan zakiyi farin jini kota ina,"



Kallonta Raheenatun tayi tana faɗin "da ko kin taimakeni da jarabar tsohonki daman kinsan na gaji da Kibiyarsa,ina son jin ta sabon jini,ke ni kima yi Mani hanyar da zan shiga Bariki,"




Murmushin jin daɗi Sabreen ta saki tana faɗin "komai yazo ƙarshe ki ajiye kamar anyi an gama," tana gama faɗa ta fice




Da harara Raheenatu ta rakata tana faɗin "Wallahi duk zaku ci Ubanku daga ke har Mahaifiyar taki sai kun gane sakani gurɓatacciyar Rayuwar da kukayi,da sannu sai kun girbi Abinda kuka shuka,"













*Jogu*



Tsaye suke su biyu sun ɗaɗɗaure Uwar giya da wata sarƙa mai tartsatsin Wuta,sai gana mata Azaba suke,ihu da kururuwa take tana faɗin "Jogu Naseer haƙiƙa kunyi man tsantsar butulci da yaudara,kunci Amanata dukda irin taimakonku da nayi,ku sani nice na dace na zama Shugabarku,muddin ina Raye bazan taɓa bari waninku ya hau karagar mulki ba,nice na bama Dodon tsafi Farjinta yai amfani da shi,karku ci amanata," tana kaiwa nan ta dinga wani gurnani mai firgita mai sauraro




Su Jogu dariya suka fashe da ita suna faɗin "nema duniya shi zaisa mu kauda ke a duniyar,ke kanki baki san iya adadin waɗanda kika ƙwacewa iko ba,don haka yanzunne ƙungiyarmu ta hau Matakin Nasara,kuma baza mu, lamunci Mace ta Mulkemu ba,idon muna son shahara a duniya dole ne mu kawar dake,"



Wayansu Ruwa suka ɗakko suna watsa mata a jiki waɗanda duk wannan tamojin na jikinta suka dinga ɓaccewa a hankali ta koma kyakkyawar Dattijuwa, kamanninta na Asali na fitowa,

Da sauri Jogu yaja baya yana nunata da yatsa yana faɗin "Saddiƙa dama ke ce Uwar gijiya,me yasa zaki haka ki shiga harkar tsafi? Gashi du yanda muke jini ɗaya nida ke bazan barki da Rayuwarki ba,duk yadda nake ƙaunarki bazan taɓa barin Rayuwarki ba,





Hawaye take tana kallonshi take faɗin "Jogu nasan tabbas daman ko ka gano, ko wacece ni sai ka kasheni,kasan tun ina ƙarama banida burin da ya wuce nai gadon Mahaifina na Tsafi,Don tun ina ƙarama na ƙware a harkar tsafi,a haka na dinga samun nasarori da dama,har nakai ga na kashe Mahaifimmu don na cimma nawa ƙudirin, a haka na buɗe tawa ƙungiyar wacce harta kai Maza da Mata na shiga,kaima ka shiga ba don kasan koni wacece ba,ashe bansan kuskure na aikata,Ni da kaina na kassara Rayuwar ƴar ɗan Uwana......✍️








Wannan kenan






*Comments, Share fisabilillah*




Waɗannan su ne ƙwarin guiwata









*By Mariam sani*










✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️








*08109554986*
[12/18, 7:37 AM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*
By
*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Bismillahirrahmanirrahim*




*Page* 60&61



_____________✍️"Ni da kaina ka kassara Rayuwar ɗan Uwana koda ka kasheni ka sani kaima da sannu zaka girbi abinda ka shuka,"
Tan kaiwa nan tai tsit


Kallonta Jogu yayi jikinsa yai sanyi ya ce "Saddiƙa dukda Son da nake maki na ƙanwata hakan bazai hanani kasheki ba, don cikar burina,kema kin kashe Mahaifimmu kin hau nima zan kasheki na hau karagar mulkin tsafi," yana kaiwa nan shida Naseer suka cigaba da surkullen tsafi suna ƙara azabtar da ita,saida suka tagayyara da ita yadda bazata iya komai ba sannan suka ƙyaleta,wani,


Haka suka dinga gana mata azaba har tsawon kwana Ukku, a cikon Kwana ukku ne suka kuma shirya kasheta,

Wani ihu take da gurnani kafin daga bisani kuma ta fashe da dariya ta ce "Jogu haƙiƙa kashenin da zakuyi shine wanda zai tasgarar da rayukanku, sannan zaku girbi Abinda kuka shuka, Sannan Raihanatu da kuka mallake na cire wannan Mallakar yanzun bata cikin ikonku,sannan Ruhin da kake taƙama dashi na Mayar ma maishi a gangar jiki,sannan ko ba komai jinanan da kuka zubda maisu zasu dawo ɗaukar fansa," tana gamawa ta kuma fashe da kuka mai haɗe da sautin dariya




Hankali tashe suke kallonta,cikin Matsanancin tashin hankali Jogu ya dubeta yana faɗin "Saddeƙa me yasa zaki lalata man dukkan wasu ayyuka da na daɗe ina yi? Ki taimaka ki gyara man,"




Tsagaita kukan tayi tana kallonshi da jajayen idanunta take faɗin "Jogu kace na gyara maka aikin da na ɓata maka? hmmmm kasani ni yanzun Mutuwata ce kaɗai abinda nake jira,babu abinda zan gyara maka,"




A zuciye Naseer ya zo yana watsa mata wasu baƙaƙen Ruwa,wata ƙara ta ƙara saki wacce saida ɗakin ya girgiza,daga bisani kuma tai tsit tana kallonsu da ɗai_ɗai ta ce "Fansa!!! Fansa!!! Fansa!!! Saina ɗauki fansar abinda kukayi man yadda kuka ci amanata bazan taɓa barinku jin daɗi ba nayi Imani da Mahalliccina bazaku taɓa jin daɗin Rayuwa ba, har ku koma ga mahaliccimmu," tana gama faɗar hakan Rai yayi halinsa



Tashin hankali wajen su Jogu kam ba'a cewa komai, kallon Naseer Jogu yayi yana faɗin "Naseer me kayi? ai bai kamata ka kasheta ba,kamata yayi saita gyara mana abinda ta ɓata sannan,kana jin ta ce ya ɗebe Mallakar da mukayiwa Raihana,yanzun ya zamuyi kenan?"
Shiru Naseer yayi yana faɗin "Jogu kabar komai a hannuna kada ka tada hankalinka,"











*ABBA*


Tunda suka koma Abuja hankalin Sadeeq ya kwanta don ganin yanda Abba ke samun kulawa tako wane ɓangare,Matar Modibbo ma,tanada kirki ta ɗauki Sadeeq tamkar ɗanda ta haifa,don dukda ta manyata bata taɓa haihuwa ba da ta samu ciki yake zubewa, ga maganin gargajiya da akeyiwa Abba kullum Modibbo cikin Neman masa magani yake,


Tunda Modibbo yazo kusa da Abba ya riƙe hannunsa yake hawaye yake faɗin "Nuraddeen waye cikin su Yaya Sa'adu ya aikata maka haka? Sun cuceka sun zalunceka, wannan wace irin rayuwa ce muke ciki da ɗan uwa ke Hassadar ɗan uwansa na rasa gane kansu Sa'adu su kullum cikin ƙyashinka da Hassadarka suke,dukda kuna ciki ɗaya,amma kullum burinsu suga bayanka sun rabaka da Matarka,mai ƙaunarka sannan yanzun sun illata maka Rayuwa,yanzun babu wanda yasan makomar rayuwarka wataƙil Rayuwa ko Mutuwa don da Rayuwar da kake ciki ƙara Mutuwa kasan Mutuwa kayi, Rayuwa ba tabbas duk yadda kake Rayuwa bazaka taɓa gane Mai ƙaunarka ba,sai wata Matsala ta sameka,sannan zaka tabbatar da me ƙaunarka," Hawayen da suka biyo kuncinsa ya share

Wata muguwar tsana Sadeeq yaji yayiwa dangin Abba don ko ma miye sune Silar jefasu cikin wannan hali,sune maƙasufin lalata Rayuwar Raihana




Katsina kam ba'a cewa komai wajen dangin Abba,don kowa baƙincikin yadda Modibbo ya tafi da Abba yake, sun so ace Modibbo ya bar Abba nan ya Mutu a wulaƙance,dan yadda suke ƙin Mutuwarsu haka suka ƙi Abba saboda tsantsar Hassada,shiyasa kullum cikin yi ma Abba aiki suke don koda Modibbo ya samar mashi da magani aikin nasu ya lalatashi,shiyasa suka haɗe kansu suke masa aiki,Baba Sa'adu kam yafi kowa dagewa don yafi tsanar Abba fiyeda kowa












*Nuraim*

Nuraim kuwa kullum cikin binciken Iyayen Mommy yake, wajen binciken Nafisa kuwa ya gano Abubuwa da dama da take,kamar Safarar miyagun kwayoyi da take,har Safarar Makamai,take ga bin Mazan da take,ranan da yasan waɗan miyagun halayen Nafisa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba,da yayi niyyar tunkararta Jabeer y dakatar dashi, ya ce masa tabbasa idan ya tunkareta yanzun itama zatayi wani abun don ganin bayanshi saboda tafishi Makamai,komai tana iyawa don ganin ba'a gano halayenta na ainahi ba,Abinda ya dace kawai ya dinga kaffa_kaffa da ita don gujewa shiga tarkonta,haka ya ɗauki shawarar Jabeer,yaci gaba da hulɗoɗinsa, koda ya faɗa ma Mommy yaga bata wani nuna mamakinta saima cewa da tayi kaɗan ya gano a aiyukanta ya sake wani binciken kar ya tsaya,komai cikin ƙudirar Ubangiji yana tafiyar masa dai_dai





Kamar yau zaune yake yaci wani uban gayu sai zuba ƙamshi yake, yard ne arsh Color wanda ya amshi fatar jikinsa ga sumar kanshi taci uban gyara sai sai ƙyalli take,haɗaɗɗen rolex ne ɗaure a tsintsiyar hannunsa,haɗaɗɗiyar wayarsa ce ta ɗauki Ruri,ɗauka yayi yana yamitsa fuska don a tunaninshi ko Dada ce,ɗauka yayi ya duba yaga ashe Dady ne ke kira, cikin girmamawa ya gaisheda Dady shima cikin sakin fuska ya amsa,sannan ya ce yazo nan ɓangaren Dada na nemansa,ɓata fuska yayi ya ce "To Dady" sannan ya katse kiran yana miƙewa tsaye,ya fito yana fitowa yaci karo da Nafeesa,ɗauke kai yayi don ko ƙaunar ganinta ma baiyi,don da ya tuna cin amanar auren da take wani uban takaici ke kamashi ji yake kamar ya shaƙe mata wuya ta mutu kowa ma ya huta,tahowa tayi tana binshi da wani mayen kallo daka kalleta kai kasan wutar Jaraba ce ke ɗibarta,cikin shagwaɓa ta ce "Honey wai ni me na aikata maka ne? Kullum kake guje man a shimfiɗa duk lokacin da nazo maka ina buƙatarka saika kawo man Matsalarka, idan Abar matsala ta samu b saika faɗa na samo mata magani ba,don bazan iya jurar rashinta ba," ta faɗa tana Sakar masa kukan kissa

Kallonta kawai yayi baice mata komai ba ya fice,da wani Mugun kallo tabishi tana faɗin "Nuraim kenan kasani dukkan Abinda kake a tafin hannuna yake,mu juri zuwa rafi wata rana Tulu zai fashe," tana gama faɗa ta saki wani Miskilin Murmushi






Shi kam Nuraim na fita kai tsaye Part ɗin Dada ya nufa,da Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga,amsa mashi Dada tayi cikin sakin fuska tana faɗin "ƙaraso ka zauna ɗan Albarka," ta faɗa tana washare masa haƙora,

Zuwa yayi ya zauna yana wani ciccin magani ya gaisheta,sannan ya ƙara gaisheda Dady,Kallonshi Dady yayi yana faɗin "Nuraim Dada ce ta tada Rigima Umra take son tayi,shine nace zan biya mata amma tace ita kai take son ka biya mata saboda kai mata Alƙawari,shine na kiraka na ce kazo ayi komai a gabana,"



Zama Nuraim ya ƙara gyarawa sannan ya ce "eh Dady da nayi mata Alƙawarin Hajji da Umara amma yanzun na fasa,kuɗin da zan biya mata na kaisu gidan Marayu na kuma yi sadaka da wasu,duk sun ƙare shiyasa banma ƙara mata maganar ba,saidai Dady kai ka biya mata," ya faɗa yana gallawa Dada harara



Sheƙeƙe Dada ta kalleshi tana faɗin "yoo ni Nuraim idan baka biya ba sai me,kawai dai ka ce ka fasa biya dama tun fil'azam bakai niyyar biya man ba,saboda haka riƙe kayanka nayi zuciya bani buƙata,kuma kasani gaba ce tsakanina da kai da ganan har Mahadi ya bayyana bazan sake koda kallonka ba," ta faɗa a hassale tana miƙewa ta wuce bedroom d'inta,da kallo Nuraim ya bita yana taɓe baki sannan ya miƙe,yaiwa Dady Sallama,kai tsaye Part ɗin Mommy ya nufa, da Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga,da murmushi ɗauke a fuskar Mommy ta amsa masa,zama yayi suna gaisawa da Mommy sannan suka taɓa hira ta tsakanin ɗa da Mahaifi,tashi yayi yana faɗin "To Mommy ni zan wuce," kallonshi tayi tana Murmushi ta ce "Son kodai wajen Surakata ta biyu zaka je ne? Don wannan Murmushin da kake ta zabgawa nasan ba banza ba,ga fuskarka nan sai fitar da annuri take," ta faɗa da ƴar dariya




Shima ƴar dariyar yayi yana faɗin "Mommy koma dai miye idan tai tsami kinji," haka suka dinga Raha da Mommy kamar ba ɗa da Uwa ba, har Abdurrahim ya shigo ya iske su kallonsu yayi cikin so da ƙauna ya ce "Ohhhh ni Mommy tunda na shigo nake jin kunata Raha keda Bro," ya faɗa yana zama kusa da Nuraim



Kallonshi Mommy tayi tana faɗin "Abdurrahim idan banyi raha da ƴaƴana ba dawa zanyi? Kune kaɗai kuka rage man a halin yanzun,kuma da janku da nake a jiki zan fahimci dukkan wata matsala taku, babban kuskuren da mu iyaye Mata muke fuskanta akan ƴaƴammu shine wai wata uwar bazata zauna ta dinga jan yaranta da wasa da dariya ba,gani take idon tayi hakan yaran zasu rainata, to sam ba haka bane jan ƴaƴanki a jiki shine zaisa ki fuskanci dukkan wata damuwa ta ƴaranki,sannan ki ɗebe masu wannan damuwar tasu cikin dabara,da ƙara jansu a jiki,kina nuna musu hanya Madaidaiciya, su kuma a sannan ne zasu ji kamar duk duniya babu wanda ya kaisu sa'ar Mahaifiya,bawai yaronki da yazo zai baki labari ba ki kwatseshi kina faɗin yai maki shiru baki Son surutu,to ƙara ki tsaya ki saurareshi a cikin wannan surutun nashi zaki gane wata damuwa tashi,ko abubuwan da yake fuskanta, amma iyaye da dama basa hakan saima da yaro yayo wata kwaramniyar sai zagi da la'anta wanda wannan ba ƙaramin kuskure mu iyaye muke tafkawa ba,wanda wannan la'antar ita ke taka Muhimmiyar rawa akan taɓarɓarewar ƴaƴammu"



Dukkansu wata ƙaunar Mahaifiyarsu suka ƙaraji shiyasa kullum suke ƙara godewa Allah da ya basu Mahaifiya ta gari,nandai Mommy ta zauna tanata musu hira da nasihohi sannan Nuraim yai musu Sallama ya fice






*Raheenatu*

Raheenatu kuwa harkar shaye_shayenta yai nisa a hankali kuma saurin su Hajiya Bilkisu yai tasiri a jikinta,wanda taji gaba ɗayan gidan Alhaji Bashir yai mata ƙunci ji take idan bata shiga harkar karuwanci bama bazata taɓa samun Salama ba,




Kamar yauma Zaune take tanata bulbulawa cikinta kayan shaye_shaye a hankali ta tashi tanata tangaɗi da surutan Maye ta nufi Bedroom ɗinta kwanciya tayi taji baccin gaba ɗaya ma be ɗauketa ba aiki kawai take buƙatar yi

Tashi tayi ta Tattaro kayan wankinta, sannan taje ɗakin Sabreen ta Tattaro kayan wankin Sabreen harda wankakki sannan ta zo ta shiga Falon Hajiya Bilkisu tana shiga cikin Muryan Maye take faɗin "Bil....ki, kina....ina...ne? Fito...ki bani...kaya.....wankinki...na wanke maki," ta faɗa tana ɗaga murya


Da sauri Hajiya Bilkisu ta fito ganin Raheenatu cikin wannan hali ba ƙaramin faranta mata yayi ba,tafiya tayi ta kwaso mata kayan wanki masu uban yawa ta tilka mata,ɗauka tayi tafi can garden taci gaba da yin wanki tun Azahar take Abu guda har la'asar tayi bataji ko alamar gajiya ba, saida takai Magriba ta gama sannan ƙwayar ta saketa


Wanka ta fara yi da salloli sannan ta zauna tana ta lazimummuka da istigfari ta daɗe tana lazimummuka sannan ta miƙe tana tunanin Rayuwarta yadda ta taɓalɓalce Tabbas tasan rashin uwa babban giɓi ne tasan da ace da Mahaifiyarsu a kusa dasu Rayuwarsu bazata lalace har haka ba,ranar ta ci kuka ta kuma ji ta tsani dangin Mahaifinsu tsana mafi Muni















*RAIHANA*


Tunda aka gama zaman Makokin Aslam na yanke hukunci nesanta kaina daga zama cikin mutane don bana Son ƙara ɗaukar wani zunubin,gashi kullum da Tunanin Hamma nake kwana nake kuma tashi dashi kullum ina jiran tsammanin kirana da zaiyi,saidai tun ina sa ran kiran harna haƙura,saidai kwatsam rana guda naji gangar jikina ta fara sauya naji kamar an maido man da wani sashe na jikina,a hankali hankalina kuma ya fara tashi ji nake kamar akwai fansar da nake Son ɗauka wacce bazan iya dakatawa da ita ba




Kamar koda yaushe zaune nake nayi zugudum inata tunanin Rayuwa,ji nayi anata kiran sunana da Muryar da bazan manta da ita ba wato Hamma,wani Murmushi na saki ina miƙewa a hankali na rufe idona ina waɗansu surutai,ji nayi wani ƙamshin turare ya ziyarceni saurin buɗe idona nayi ina kallonshi

Tsaye yake hannuwanshi zube a Aljihunsa yanata sakar man wani lallausan murmushi mai tafiya da imanin mai kallonsa,nima Murmushin na sakar masa a hankali ya ci gaba da takowa har yazo dab dani har muna iya jin Numfashin junanmu kafeni yayi da mayatattun idanunsa ji yake kamar ya lasheta don tsananin ƙaunarta da yake,da sauri nai Saurin ɗauke idanuna ina kauda fuskata nake faɗin "me ya kawoka nan gurin? a halin yanzun,"
"Ganinki nazo yi da kuma taimako" ya faɗa yana mai ɗauke idanunshi a kanta



Kallonshi Tayi ta ce "Saidai a koda yaushe ina sake tunatar da kai da kabi komai a sannu don zaka iya rasa Rayuwarka abinda bana fata,don tani da ka janye temakon da kayi niyyar yi man don a halin yanzun Rayuwata fansa ce ga abinda aka aikata,"


A hankali ya zaro hannunshi daga Aljihu ɗauke da wannan ƙanƙarar da sauri ya kamo hannunta na haggu yana Manna Mani
Wata uwar ƙara na saki da wata kalar Murya nake faɗin "Fansata kada ka lalata man shiri Tabbas kayi hakan zakayi ta rayuwarka ka barni na ɗauki fansar Raina da suka ɗauka ni kuma zan bar gangar jikinta.......✍️









*AlHAMDULILAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTATAFIN RUSHEWAR RAYUWA BOOK 1*

*Tofa ana wata ga wata,wai meke shirin faruwa da Raihana? Kardai ace Uwargijiya na jikin Raihana don ɗaukar fansar su Jogu,idan kuwa hakan ya kasance shin wane Hali Jogu da Alhaji Naseer zasu shiga? Kuma idan suka ida tabbatar da babu ikonsu a kan Raihanatu wane mataki zasu ɗauka,Shin Nuraim da yake son Raihana idan yaji cewar tanada aure wane hali zai shiga ya zaiyi? Nafisa ta gano Nuraim ya fara sanin sirrinta shin wane mataki zata ɗauka, Raheenatu kuwa da aikin su Hajiya Bilkisu ya fara aiki a kanta shin zatayi karuwancin kuwa? Waima su waye su Raheenatu miye mafarin shigar Raihana wannan Rayuwar me ya faru da Ammi harta Mutum,su waye dangin Abba dasu Raheenatu suka tsana,shin waima waye Modibbo dasu Baba Sa'adu,shin baku ganin halin da Raihana ta tsinci kanta yanada nasaba da Dangin Mahaifinta, shin wai ina mutanen London wace rayuwa suke gudanarwa, hmmmm akwai amsoshi da dama da zasu fito a Book 2 kudai ku biyoni a ciki don sanin amsoshinku,sannan indai har bansamun Comment zan maida Book 2 na kuɗi masu man Comment ne kaɗai zasu karanta kyauta,sai mun haɗe a Book 2 insha Allah*










Wannan kenan






*COMMENTS, SHARE FISABILILLAH*


waɗannan sune ƙwarin guiwata










*By Mariam sani Riamcool*





✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️






*08109554986*
✍️✍️✍️✍️✍️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment