Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin juyawa kwata_kwata bata jin daɗin Yanayin da ta tsinci kanta a ciki, ta rasa gane Wannan lamarin kullum indai bata sha Zoɓon Hajiya Bilkisu ba bata jin daɗin Rayuwarta,




Tashi tayi ta Nufi Side ɗin Hajiya Bilkisu,tana shiga ta iske su zaune su duka,zama tayi tana gaishe da Hajiya Bilkisu
Da fara'a ta amsa Mata,

Ta ɗan daɗe Sannan ta ce "dama Hajiya Zoɓo nazo amsa wallahi duk lokacin da ban shashi ba,sai inji wani Abu namin yawo a ƙwalwa,nidai ko wani Abu kike saka Mashi ne mai ɗebe damuwa,"



Dariyar ƴan Duniya Hajiya Bilkisu ta fashe da ita tana faɗin "Raheenatu kenan, Wannan shi ake kira ba Shan ruwa ba ƙetara hanyar, Tabbas ina sa miki wani Abu a cikin zoɓon, Saboda ina ganinki a yanayin damuwa, shiyasa na taimakeki nake saka maki ƙwayar da ke yaye damuwa, yanzumma idan kina so zan iya baki," ta faɗa tana kallon Raheenatu





Kallonta Raheenatu tayi tana faɗin "Eh ina buƙata ki bani,"


Tashi tayi ta buɗe jikkar Sabreen tana fito da kayan Maye kala_kala,wasu ƙwayoyi ta miƙo mata da Cocain tana faɗin "indai kika sha wannan bake ba damuwa,"



Amsa Raheenatu tayi tana mata godiya Sannan ta fita,Tana Zuwa, kai Tsaye bedroom d'inta ta shige, tana baje kayan shaye_shayen kan bed, ɗaukar ƙwayar tayi Hawaye na bin kuncinta,ta sa ƙwayar cikin Lemo, tana narkewa ta kafa kai ta shanye, sannan Cocain ɗimma ta buɗe ledar tana shaƙa tana gamawa ta dinga jin duniyar gaba ɗaya na janza mata,nan take yanke bacci ya bugar da ita.......✍️







Wannan kenan








*Comment, Share fisabilillah*






Waɗannan Sune ƙwarin gwiwata








*By Mariam sani*










*08109554986*
[12/18, 7:35 AM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*
By
*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Bismillahirrahmanirrahim*




*Page* 54&55

__________✍️ Cocain ɗimma ta buɗe ledar tana shaƙa tana gamawa ta dinga jin duniyar gaba ɗaya na janza mata, nan take bacci ya bugar da ita,




Lokacin da Raheenatu ta fita, Hajiya Bilkisu ta ɗauki waya ta dannawa Turai kira,Tana ɗagawa ta sheƙe da dariya tana faɗin "Turai komai yana tafiya dai_dai, yanzun miye Shirimmu na gaba? Tunda haƙarmu ta cimma ruwa,"



Daga can ɓangaren Turai ta ce "Bilki komai fa ya tafi dai_dai ina ganin Abinda ya dace kawai wannan yarinyar sai kin haɗata da Boka,Saboda ta shiga harkar karuwanci, amma idan kika ce koda Tuggunki zata shiga karuwanci to bazai yiwu ba,yanzu Abinda ya dace ku ƙara koya mata shaye_shaye yadda idan bada ƙwaya ba bazata iya Rayuwa ba,ke har shan Wiwi ki koya ma shegiya tunda harkar Bariki zata shiga
sannan idan ta ƙware a harkar shaye_shayen ki nemeni zan faɗa maki Target ɗimmu na gaba,"

Dogon numfashi Hajiya Bilkisu ta sauke tana faɗin "To Turai duk yadda kika ce haka za'ayi amma ke a wane Bokan kikaga ya dace naje, dan kinsan wanda yayi man aikin Alhaji baya nan ya koma Nijer da zama Ni kuma ban son doguwar tafiya saboda harƙallolina,"



Turai ce ta ce "Bilki kedai kawai ki shirya, ni da kaina zan kaiki wajen Boka Sangarƙami don aikinshi kamar yankan wuƙa haka yake,"


Nan suka yanke zuwa tunda assuba za suyi sammako su tafi wajen Boka Sangarƙami,


Raheenatu kuwa ta daɗe tana bacci Don tun Azahar take bacci har sai wajen 9:30 na dare ta tashi, tana tashi tajita ta koma Normal Toilet ta shiga tayo wanka da Alwalla sannan ta rama sallolin da ake binta, kai tsaye Kichen ta shiga ta dafa Indomie ta ci, tana gamawa sai ga Alhaji Bashir ya shigo yana shigowa Raheenatu ta haɗe rai,don tasan Abinda ya kawo shi dukda idan yazo bai kusantatta saidai iyaka ya shashshafi jikinta da Breast ɗinta, wannan Abun na Matuƙar ɓata mata rai,


Yana zuwa ko gaisuwar da take mashi bai tsaya amsawa ba ya jawo hannunta sai bisa gado,shafata ya cigaba da yi,da kissing ɗinta,saidai yana zowa shigarta bacci ya kwashesa, tana ganin yayi bacci da ƙarfi ta hankaɗashi ta tashi ta mayar da rigarta da gudu ta fito Falo ta durƙushe tana sakin wani marayan kuka, ta daɗe tana kuka kafin ta koma can wajen Alhaji Bashir ta kwanta,saidai sam baccin ya kasa ɗaukarta,


Da Assuba kuwa sai ga Turai tazo don zuwa wajen Boka,dama tuni Hajiya Bilkisu ta shirya tana zuwa suka ɗauki hanya,tafiya suka dinga tsulawa yadda kasan zasu bar garin Lagos, tun asuba suke tafiya har Rana ta fito basu kai inda zasu kai ba ga ko ruwa basu taho dashi ba daji suka dinga yanka suna zuwa dai_dai wani guri Turai ta ce su Tsaya daga nan,haka Driver yai parking su kuma suka dinga yankar hanya suna keta daji,Sunyi tafiya mai nisan gaske wanda saida Hajiya Bilkisu taji kamar ta koma, sun ƙara cin uwar tafiya sannan suka hawo wani dutsi, Turai ce ta dinga ɗaga murya tana faɗin "Sandarƙami!!! Sandarƙami!!! Sandarƙami!!!!," har sau ukku ta kira sunanshi, tana gamawa wata guguwa mai ƙarfin gaske tazo ta ɗaga su sama,don tsananin tsoro sai ga Hajiya Bilkisu tana sakin fitsari zawo ma saura ƙiris ta sakeshi, guguwar nan bata ajesu ko ina ba sai kogon Boka Sangarƙami suna shiga wani uban wari da ƙarni ya ziyarce su, durƙusawa sukayi Turai ce ta ce "barka dai Boka Sangarƙami kafuri ɗan kafura, la'ananne tambaɗaɗɗe,tsinuwar Ubangiji ta tabbata gummu masu shirka,mun kawo kukanmmu gunka wanda kaine zaka share mana hawaye tsinannen Allah,"




Buɗe wagegen bakinshi yayi mai uban hamami ya sheƙe da wata irin sheɗaniyar dariya,wacce kogwon ya dinga amsawa yana girgiza daga bisani kuma ya gimtse Mummunan Fuskarshi mai kama da ta gwaggwon biri, ya ce "Bilki la'ananniyar Allah nasan dukkan Abinda ya kawoku nan, don haka jeki buƙatarki ta biya,murya na rawa Hajiya Bilkisu ta ce "Boka Sangarƙami nawa ne kuɗin aikin? ,"


Daka mata tsawa yayi yana faɗin "ke la'ananniyar Mata bazaki iya biyana da kuɗi ba, don Haka Abinda kika tafo dashi daga sarƙoƙinku da kuɗaɗenku har takalmominku sai kun ajiye,sannan ko waccenku saita cire kayanta na sadu da ita,"


Gaban Hajiya Bilkisu idan banda dukan ukku_ukku babu abinda yakeyi don duk jarabarta saida taji ta fice mata rai a yau,babu yadda suka iya dolensu tasa sukayi yadda ya buƙata,bayan ya gama abinda zaiyi dasu ne ya ce " ku tashi la'anannun Mata buƙata ta riga ta biya saura idan kin koma ki Samu naman baƙin Alade kiyi sadaka dashi Sannan ki jera sati guda baki kalli gabas ba,ku ɓace man da gani la'anannu,da gudu suka fito zani a hannu ko mayafi basu tsaya sun ɗauka ba,tafiya ce suka dasa suka dinga yi wurjanjan suka iso inda Driver yai parking,suna shiga ya dinga kallonsu don ganinsu yayi kamar tsaffin Mahaukata, "kai dalla jamu mu tafi ka wani ƙura mana ido sai kallommu kake," Turai ta faɗa a masifance, Driver najin abinda ta ce ya maida hankali a kan aikinshi.




Saida ya fara ajiye Turai sannan ya kai Hajiya Bilkisu gida,a wurjanjan ta shige cikin tana Shiga Toilet kawai ta wuce don yin wanka saboda jikinta da ke wani irin wari da hamami




Haka Rayuwa ta ci gaba da Tafiya don shaye_shaye Raheenatu ta maida shi Abokin firarta ta sanadiyyar shaye_shaye har sun jone da Sabreen, kwatsam kuma taji babu abinda take buƙata sama da shiga harkar karuwanci.












*Ɓangare Abba kuwa*

Abba ne kwance cikin mawuyacin hali kullum abinshi ƙara gaba yake mamadin yai sauƙi ga Wani lokacin basu samun isasshen Abinci daga shi har Sadeeq ɗin,duk ya ƙara komawa wani ƙwarangwal babu Abinda ke motsawa na jikinshi idan banda numfashin da yake fitarwa,shi kaɗai ne zai tabbatar maka da yana raye,



Kallon Yadda Mahaifinshi ke cikin mawuyacin Hali yake hawaye na bin kuncinsa, kullum idan ya zauna yaga Abba bashi da aiki sai kuka,duk dauriyar Sadeeq amma akan Abba ya kasa daurewa,
Kullum baya bacci yana tsaye yana kaiwa Allah kukanshi



Zowa yayi ya kama Abba ya wanke mashi fitsari da kashin da yayi,haka ya Tattaro kayan wankinsu yana yi,yana cikin yi ne ya hangi Baba Sharu yayan Abba dashi da Baba Sule shi kuma ƙanin Abba ne, tunda suka zo ganinshi so ɗaya basu sake zuwa ba wanda a da sai suyi zuwa yakai biyar gurinshi Amma tunda suka ga Abinda ya Samesu basu sake tako ƙafarsu ba sai yau, koda suka zo Suka ga jikin Abba suka tashi zasu tafi ɗari biyar Baba Sharu ya Bama Sadeeq yana faɗin "Ungo wannan ka siya maku ko fura ne ku sha, Kafin Modibbo yazo, don baisan Abinda ke faruwa ba sai ɗazun da nake faɗa mashi, idan yazo zan rakoshi har nan gurin," amsa Sadeeq yayi yana ma Baba Sharu godiya, Baba Sule kuwa ko ficika bai bada ba saima wani kallon ƙasƙanci da yake bin Sadeeq da Abba dashi


Sallama sukayi suka wuce, Suna tafiya ya ida ƙarasa wankin sannan ya je ya siyo masu furar da zasu sha,yana dawowa yabama Abba furar yasha shima yasha,bayan sun gama Shan furar ne Suka ji dirar motoci a kangwon, Da Sallama wani kamilin Mutum ya shigo da ka ganshi kaga kamilin Mutum nutsatstse shima ya kai sa'ar Abba Modibbo kenan ɗan'uwan Abba ne shima don banbansu guda dashi kuma sa'anni ne, shiyasa suka tashi tare da Abba komai tare sukeyin shi, daga bayanshi kuwa Baba sa'adu ne masifaffen Mutum wanda duniya shi baka iya mashi komai kayi masa baka birgeshi ba,Wutowa suka yi suna zama Sadeeq ya gaishe dasu suka amsa Sannan Modibbo ya ce "Sadeeq ina Nuraddeen ɗin yake ne? Ance man yana cikin mawuyacin Hali,"



Baba Sa'adu ne ya kalleshi yana faɗin "Ba gashi a gabanka ba kamar tsummakaran wanki, yoo Allah na tuba da kalar wannan wahalar a ƙara Mutuwa shi dama Mutuwar yayi an huta da jarfar wahala," ya faɗa yana ɗaɗɗage hancina



Kallonshi Modibbo yayi yana girgiza kai don Halin su Baba Sa'adu sai su daga Allah ya azirta Abba suka ɗauki karan tsana suka ɗora mashi,kamar ba ciki ɗaya suka fito ba,


Kallon Abba Modibbo yake yadda ya koma baisan sadda Hawaye suka dinga zubo mashi ba, fita yayi ya umarci Securities ɗinsa da su ɗauki Abba don bazai barshi anan ba kai tsaye Abuja zasu wuce dashi,don aka barshi anan tsaf ɗaya daga cikin ƴan uwan Abba sai sun kashe sa,don kwata_kwata basu da imani da zuciyar musulunci,don ba ƙananun shahararrun Matsafa bane, Sallama Modibbo yai ma Baba Sa'adu suka wuce Abuja,wanda baƙinciki kamar ya kashe Baba Sa'adu don takaici yaso an bar Abba anan ya Mutu a wulaƙance amma wancan Modibbo ya ɓata masa shiri












*Nuraim*

Tunda suka rabu da Raihana ya yanki Daji yana tafiya yayi nisa Sosai don kai baka ce akwai wata halitta a cikin Dokar dajin ba, tafiya yayi mai tsayin gaske Sannan ya isa wani kogo, yana shiga ya iske farin dattijon da fararen kaya yana salla kogon sai uban ƙamshi yake ga wani ni'imtaccen sanyi da ke cikin kogon, saida ya daɗe sannan Dattijon nan ya gama lazimummaknsa,yana gamawa suka gaisa da Nuraima sannan ya ce "dama na faɗa maka komin ba daɗe zaku haɗu da ita kuna haɗuwa na fahimci abubuwa da dama game da ku, yanzu ne lokacin da ya kamata ka taimaki yarinyar nan,amshi wannan ƙanƙarar ina son duk lokacin da kuka ƙara haɗuwa da ita ka manna Mata wannan ƙanƙarar a hannun haggunta," ya faɗa yana miƙo mashi wannan ƙanƙarar,


Godiya Nuraim yai ma wannan Dattijon sosai da zai tafi saida Dattijon nana ya bashi wani Zobe na kariya wanda ya ce duk runtsi kada ya cireshi saboda shine zai ƙara ma Ruhinshi ƙarfin tunkararsu, Sallama Nuraim yayi Mashi sannan ya shiga Motarshi ya ja, kai tsaye gidan Jabir ya nufa,yana Zuwa ya iske shi da Ni'imatu zaune bayan sun gaisa ne Ni'imatu ta tashi ta bar wajen don tasan Abinda ya kawo shi, kallon Jabir yayi ya labarta mashi dukkan abinda ya faru,Numfashi Jabir ya sauke yana faɗin "To Alhamdulillahi tunda ka ganta nima zan bada tawa gudummawar amma baka tunanin may be Aljana ce Tunda ka ce fa har ɓaccewa tayi,"

Ɓata fuska Nuraim yayi yana faɗin "koma wacece Ni ba damuwata ba ce,kawai Abinda nayi niyya shi zan aikata,"



Dariya Jabir yayi yana faɗin "Nuraim kayi nisa da Son Aljana baka jin kiran kowa sai nata, amma Man na fara bincike akan Nafisa na ɗan fara gano Abubuwa da dama kanta yanzun ka bari idan ka samu Nutsuwa zan faɗa maka tunda yanzun baka cikinta saboda ka haɗu da Aljana," Jabir ya faɗa yana dariya


Shima Nuraim ɗin dariya yayi, nan suka zauna suna tsokanar junansu,suna cikin firan ne kiran Dada ya shigo wayar Nuraim, ɓata fuska yayi kamar kar ya ɗauka,haka dai yai ya ɗaga kiran nata yana gaisheta,bata amsa kiranshi ba ta ce "kai Nura duk abinda kake ka baro kazo ina nemanka," tana gama faɗar hakan ta datse kiran



da kallo yabi wayar girgi kai kawai yayi don yasan wata kuma jarabar ce ta Dada ta tashi shine take Son ta maida ita kanshi, miƙewa yayi yai ma Jabira Sallama Ni'imatu ma ta fito ta rakoshi,




Yana isa kai tsaye Part ɗin Dada yayi yana shiga ya iske Dada tana ta rusgar kuka tana ganinshi sai ta ƙara Volume yatsina Fuska yayi ya zauna yana faɗin "me kuma aka miki Dada?


Kallonshi Tayi tana faɗin "Yoo Nura miye ba aminba ma a gidannan wai kamar ni Abdurrahim zaiyi wa ɗebewar Albarka daga zanyi mashi gata shine shi zai saka man da Mugunta don Allah ka faɗa man laifi ne don zan haɗa shi aure da Sabreen?shi ko wacce mace bai so na zaɓa mashi Hasiya ya ce bai so Sabreen ma ƴar gayu kyakkyawar mace ya ce bai so, to shine fa daga na ce aure shida Sabreen ba fashi yanzun ya tattaso man kamar zai dakan, Abinda yafi ɓata man rai da shi harda iƙirarin idan ban janye ba sai ya sa ƙaurayen Lagos sun sare ni kaji rashin imani ya rasa waɗanda zai saka su Sareni sai ƙaurayen Lagos waɗanda ba Allah a cikin zuciyoyinsu, shine na kiraka ka sa baki cikin lamarin wallahi ko ɓantalewa na gani a jikina da sa hannunshi," ta faɗa tana jan Majina kafin ta ɓantari goronta



Nuraim shi Dada dariya ma ta bashi kallonta yayi yana faɗin "To Dada kin dai san halin Abdurrahim da kafiya gashi baya magana ɗaya don haka ƙara ki janye da wuri,"


A hanzarce Dada ta ɗago tana faɗin "Nura ai tunin duniya na janye don nasan halin Abdurrahim da zuciya kamar ta kafuran farko,wa ni ? rufa man asiri ya je can ya ƙarata na gama saka Mashi baki cikin lamurran sa,tun lokacina baiyi ba ya ida ƙarasani,"















*Raihana*

Tunda na baro dajinnan na dawo gida na shiga Toilet nayi wanka na na gasa jikina,dawo wa nayi na dunga tuna maganganun Hamma don abinda na saka Mashi kenan,ko ba komai yau na ɗan jini ina da sauran gata nima tunda har wani yayi sadaukarwa da Rayuwarshi don kawai ya ceci rayuwata,Lumshe idona nayi ina tuna Kyakkyawan Fuskarshi, hakanan ko Tunowa nayi da shi nakan tsinci kaina a cikin farinciki,Tashi nayi na saka Babban Hijabi na wuce sashen Zaliha don yi mata gaisuwa,ina shiga dukkan idanun masu zaman Makokin suka yo kaina..........✍️









*Wannan kenan*







*COMMENT, SHARE*


Waɗannan su ne ƙwarin guiwata








*By Mariam sani*







✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[12/18, 7:36 AM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*
By
*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Bismillahirrahmanirrahim*




*Page* 56&57


______________✍️ina shiga dukkan idanun masu zaman Makokin suka yo kaina,duƙar da kaina ƙasa nayi saboda na fara tsarguwa da kallon da suke man, zama nayi nayi Wa Zaliha gaisuwa,sannan itama Mahaifiyar Sudais ne mata,na ɗan jima sannan na tafi,haka har akayi zaman Makoki aka ƙarashe, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, wanda kullum da kalar ƙalubalen da nake fuskanta na rayuwa,saidai duk yanayin uƙubar da nake fuskanta na Rayuwa, da na tuno da maganganun Hamma nakan ji dukkan wata damuwa ta kau a zuciyata,nakan ƙara tawassali da Allah da Manzonsa don nasan Ubangiji ne kaɗai zai iya fidda ni cikin ƙazamar Rayuwar nan, duk kuma yanda nake jin wani abun nakan ƙoƙarin dannewa Zuciyata wanda hakan yasa azzaluman suke ƙara azabtar dani
Nayi nisa cikin Tunanin makomar rayuwata naji an banko ƙofa da ƙarfin gaske,saurin ɗago fuskata nayi ina kafeta da idanu, harara ta banka man tana faɗin "nifa banson kallon munafurcin nan da kike yiman banza marar galihu dalla kije Mijinki na nemanki," ta faɗa tana buga tsoki Sannan ta ƙara gaba


Tashi nayi na ɗauki mayafi na yafa ina ficewa, kai tsaye part ɗin Alhaji Muttak'a na shiga da Sallama ɗauke a bakina na shiga,da sauri ya amsa man, waje na samu na zauna ina gaishe da shi tukun ya amsa yana kallona cikin shakku ya ce "am dama Abinda yasa kika ga na kiraki Saboda ina son muyi wata muhimmiyar Magana,saboda duba da nayi na ganin na tauye maki haƙƙi wanda kullum da Wannan nake kwana nake tashi,to idan bazaki damu ba ina son na sawaƙe maki, don kije ki auri zaɓin ranki," ya faɗa yana kawar da kanshi gefe don shi tsoron haɗa ido ma yake da ita,



Nannauyar Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce "dukkan Abinda ka gani zai fi maka sauƙi ka yishi kawai na baka wuƙa da nama,"



Shima wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauke gani cikin sauƙi zai rabu da ita,gyaran murya yayi yana faɗin "to nidai abinda na yanke shine zan sawaƙe maki, ki koma a gaban Mahaifinki ki zaɓi mijin da kike son aura,"
.

Miƙewa nayi ina faɗin "hakan ma yayi amma ina son ka ƙara man lokaci don ƙara tunani," ina gama faɗar hakan na fice


Da kallo ya bita yana jin kamar ya fashe da kuka,don ji yake kamar zaune yake da wata Dodanniya


Ni kam ina fita kai tsaye Side ɗina na nufa,ban ankare ba naji an fisgo ni da ƙarfin gaske da saurin gaske na juyo don ganin wanda ya aikata man hakan,idona ne sukayi man tozali da Aslam ɗan Alhaji Muttak'a,cikin ɓacin rai nai saurin ƙwace hannuna, kafin na ƙara yin wani motsi naji ya kikkifa man wasu wawayen maruka a kunci,sannan ya jawoni ta ƙarfin gaske ya cilla ni ɗakinshi, Belt ɗin jikinsa ya zaro ya ci gaba da zuba man shi ta ko ina a jikina,sandarewa waje guda nayi na kasa taɓuka komai don tsananin ɓacin rai,saida ya gaji don kanshi sannan ya ƙyaleni yana mamaki sosai,don ganin bugun da yake mata kwata_kwata bata motsa ba,cikin Daka tsawa yake faɗin "ke wai uban mi kika ɗauki kanki ne? To ki sani marin da kika man kwanakin baya shine na rama sannan sai na fanshe dukkan wani baƙinciki da kika ƙunsa man,"

Yana gama faɗar haka ya tunkarota yana tuɓe Wandonshi,hannu ya sa da niyyar taɓata, da sauri na ɗago da rinannun idanuna, wanda saida suka kusa saka shi suma don tsananin tsoro,ja da baya ya dinga yi ina tunkararsa har ya ƙure ma bango kallonshi nayi ina fashewa da wata shaiɗaniyar dariya mai fidda sautittika,kafin na gimtse fuskata,cikin Murya mai fidda sautin Mutum biyu nake faɗin "kayi kuskure mafi muni a rayuwarka wanda shine sanadiyyar Mutuwarka tabbas zakai mutuwar wulaƙanci mutuwar da zata tsoratar da dukkan Al'umma,bana Yafiya sannan kuma bana manta sharri," ina gama faɗar haka na runtse idanuna ina kalar wasu Surutai,ina gamawa na saki wani Miskilin Murmushi, buɗe idona nayi naganni cikin tsohon gidannan,ɗakin da Dodon tsafi ya kusanceni na shiga da Aslam.........✍️




*Kuyi haƙuri da wannan banjin daɗi ina ciwon kai ne*





Wannan kenan



.*Comment, Share fisabilillah*





Waɗannan su ne ƙwarin guiwata







*By Mariam sani*







*08109554986*[12/18, 7:36 AM] Riamcool: *RUSHEWAR RAYUWA*
By
*Mariam sani*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Bismillahirrahmanirrahim*




*Page* 58&59


__________✍️ina shiga wata iska da guguwa suka ɗaga Aslam sama,juyawa ɗakin yaci gaba da yi,daga bisani kuma aka sheƙe da wata Mahaukaciyar dariya mai firgita mai sauraro,kafin ɗakin yai tsit,cikin sheɗaniyar murya mai nuna zallar shaiɗanci aka ce "Haƙiƙa yanzunne zakiyi abinda ya dace yanzunne zakiyi sadaukarwarki ta farko da jinin Bil'am ɗinnan da kin Shayar da mu jininsa,mu kuma daga nanne zamu baki ƙarfin iko na karin kanki,sannan muna son sassan jikinsa guda biyar,kiyi amfani da biyu mu kuma zamuyi amfani da ukku,a ranan zamu baki iko na kanki,zamu sakar maki Ruhi,"da ganan ne ɗakin yai tsit kujerar dake gefena ce kuma taci gaba da juyawa ana sheƙa dariya,daga bisani kuma aka ci gaba da kuka.





Don tsananin tsoro Aslam bai san Sadda ya jiƙe Wandonshi da fitsari ba,yayi suma tafi a ƙilga,da ya farko zaiga jinane da halittu kala_kala, fashewa da kuka yayi yana faɗin "na roƙeki ba don halina ba ki taimaka ki ceci Rayuwata don Allah kada ki aikata abinda kika ƙudurta,ko ba komai nifa ɗan Mijinki ne,ki ceci Rayuwata ni kuma nayi maki Alƙawarin bazan sake kwatanta irin halinnan ba,ke wallahi ko sigari ba zan ƙara sha ba, ballantana ƙoƙarin keta haddin wata," yana kaiwa nan ya ci gaba da rera kuka,



Fashewa nayi da Dariya daga bisani kuma na gimtse fuska kamar ban taɓa dariya ba,cikin isa da takon Izza naci gaba da takowa har nazo gurinshi, "kada ka ƙara yunƙurin bani haƙuri don lokaci kaɗan ya rage maka,idan kuma ka sake buɗe baki wallahi ko gawarka iyayenka baza su gani ba don haka ka gimtse bakinka," ina gama faɗar hakan na dafa kansa ina ci gaba da surutan da saidai naji su a bakina ina yi,ina gamawa,wata guguwa mai ƙarfin gaske ta ɗagashi sama, ya ɓace

Dariya aka cigaba da ƙyalƙyatawa,daga nan kuma na ganni na dawo ɗakin Aslam kwance,da sauri na tashi na fita,ina fitowa naji naci karo da Mutum wanda ban tsaya tantance ko waye ba na ƙara gaba,ina shiga Side ɗina na faɗa kan kujera ina fashewa da kuka,wanda ya riga ya zame man jiki a duk lokacin da nayi kisa,Ranan kwanan zaune nayi bacci ko kaɗan ya kasa ɗaukata,ga ko wace addu'a nazo yi nakan ji kamar an ƙulle man baki,nafilar ma da nayi ƙoƙarin tashi ji nayi kamar ansaka man sarƙar wuta an ɗaure man ƙafafu da shi


Washe gari ana tashi babu wanda ya nemi Aslam don kowa ya san wani lokacin yana kusan kwana biyu baya gidan,haka kowa yaci gaba da harkar gabanshi har akai kusan 1week da gananne hankalin Mutan gidan ya fara tashi,aka ci gaba da cigiya, har aka sako Police cikin lamarin haka Alhajiu Muttak'a ya saki kuɗi ana bincike har 1 Month ya wuce amma babu labarinsa,saida akayi kusan Wata biyu sannan aka ga gawar Aslam duk an fidda hannuwa da ƙafafu sai harshensa da aka yanke,kowa yaga gawar nan sai yayi mata kuka, ba ƙaramin tashin hankali Alhaji Muttak'a ya ƙara shiga ba,ga wani tsananin tsoron Raihana da ya ƙara shigarsa,da Police sun ce baza su bayar da gawar ba sai sunyi bincike Alhaji Muttak'a ya ce babu wani binciken da za suyi kawai su bashi gawar ɗanshi,haka suka bashi azo aka kaishi Makwancinsa.






Ni kam ranan da naga gawar Aslam ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba,don tunda nake kisa ba'a taɓa ɗaukar sassan jikin Mutum ba saina Aslam,a ranan na ƙara tabbatar da ni ba ƙaramar annoba bace a cikin Al'umma tabbas kota halin ƙaƙa zan nisanci Mutane,na ƙara jin tsanar kaina da kaina

















*Raheenatu*

Zaune take ita da Sabreen suna fira kamar wasu ƙawaye dukda Sabreen ta girmewa Raheenatu nesa ba kusa ba,kallonta Sabreen tayi tana faɗin "wai ni kam Raheenatu me ya zaja miki auren Abbana? Dukda kina da damar da zaki gujema hakan,kina ƙaramar yarinyarki amma an riga an kashe maki Rayuwa," Sabreen ta faɗa da Son jin ƙwaƙwab



Kallonta Raheenatu tayi Tana faɗin "Ƙaddara ita ce ta jaza man auren Mahaifinki,kinsan ita ƙaddara bata wuce bawa,yanzun ba don auren Mahaifinki ba ni nasan koman lalacewar gidanmu bazan taɓa shaye_shaye ba," Raheenatu ta faɗa fuskarta na nuna Alamun damuwa



Taɓe baki Sabreen tayi ta ce amma dukda ƙaddara ce harda Silar Mahaifinki,don komai yana da sila,to ke taki ƙaddarar Ubanki yaja maki,"


Wata Ashariya Raheenatu ta lailayo ta ɗirka ma Raheenatu tana faɗin "ke don kutmar....... Ni

Please Login or Register in order to submit comment