Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu hada iri ai da ba ayadda akai auren ba dada kam kuka tafashe dashi Tana cewa shikenan harisu Ashe har ya haihi Dan dazai dunga zagina da bai aure waccan tawajen ba ai da bazata haihoman zabiyan da marar tarbiya ba ga ya'yan kishiyoyinta tanan bawanda yataba zagina tafada Tana share hawaye harda Jan majina kamar qaramar yarinya.



Wanna kenan



*By Mariam sanee🌹**


[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA😓💔*




*By Mariam sanee🌹*


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



*Bismillahirahmanirrahmanirrahim*




*Page 7&8*


*______________✍️* Itama Raheenatu ba a barta a baya ba, haka muka dunga jibgar Suhailat baji, ba gani kamar Allah ya aiko mu, Saida mukayi mata lik' is barkonon da tazo dashi muka bad'e mata idanu dashi, sannan muka jawo ta har side d'insu muka kaita.

Koda muka dawo ban huce ba, dama can ni ban iya zuciya ba, muna zaune Saddeeq ya shigo koda ya zauna ya ce "waini Sister ya naga bakin Raheenatu ya kumbura ne?," "wllhy Abba ne yai mata haka na fad'a da damuwa 'a fuska ta,"

Saddeeq ya ce "Amma wane laifi tayi wa Abba har yai mata wannan uban dukan? "nan nakwashe abinda Raheenatu tayi wa zulfa'u , na fad'a mashi"

"Ohhhh ko shi yasa naga an d'akko Adda Zulfa'u za'a kaita asibiti nasa ma ni, ko masassara take dan ko magana Bata iyawa," Sadeek ya faɗa yana nuna damuwa a fuska,


"Ashe Bata iya magana kaga ni bansani ba Wallahi Dan duk abinda taiman tabani tausayi sainaji duk banji dad'i ba," na faɗa da nuna damuwa,


Raheenatu tace "to sannu sarkin 'yan tausayi ke duk abinda taimaki baki gani ba, kinsan ta warke idan bamuyi sannu ba sai munzama abin kwatance , Dan Haka gara ki farka tun wuri ki gane me kike, Danni Wallahi yanzun na d'auri aniyar d'ammara ba 'yar iskar da zata takani da Amman yanzu bazan jura ba ke in zaki jura sai ki zauna ai kina ganin akai wannan Amma gobe gudar makirar matar can zata dawo, ni fa aka takura man gidannan guduwa zanyi ba abinda zaisa na tsaya k'ara na shiga duniya Wallahi , Dan muka zauna gidannan sai an d'auki gawar mu," tafaɗa da hawaye taf a idonta


Tunda take maganar nake kallon ta dafata nayi Ina fad'in "Raheenatu abinda kika fad'a gsky ne Amma maganar ki shiga duniya bai taso ba kar, ki biyewa son zuciya, ki rushe rayuwar ki, da kanki kada ki d'ebe duk wata daraja ta d'iya mace da Allah ya baki, kibar wannan zancen baki da inda yafiye maki nan,"


Hawaye ta share Tana fad'in "Raihana na gaji da abinda 'ake mana gidannan ace rayuwar gidanku baku da galihu k'ara naje nasan 'eh ni keda kaina Dan na zauna nan ko ni ko, su Wallahi.


Sadeeq ne ya ce "to Adda da Raheenatu idan kin gudu kije Ina, mu da bamusan 'yan uwan Ammi ba ba wanda muka sani ballantana mu ce muje can ga 'yan uwan Abba babu masu sonmu,"


Dafa shi nayi nace "karka ce haka Sadeeq suna sommu mana ba Wanda ya tsane mu , yanzun kutashi muje mugano Zulfa'u kar muqara wani laifin Kuma,"

Raheenatu ce ta maka man wata uwar harara Tana fadin "wllhy saidai su kashe ni Dan naje ni saina ƙara illata ta Dan wannan dukan da akai man saina fanshe shi wajen su," tafad'a Tana tashi fuuuu ta wuce

Girgiza kaina kawai nayi Dan Raheenatu halin ta sai ita bansan wannan halin Ina ta d'akko shi ba jin ana Kiran sallah yasani tashi ,naje nai sallah, Ina gamawa sai ga Hinde ta shigo wai mama tace nayi masu girkin dare, inyi ma zulfa'u kunun gyad'a idan nagama nak'ara gyara
sashen aunty amarya


Baki sake nake kallonta ace duk y'an aikin gidannan a rasa Wanda zaiyi sai ni wahala ake son ta kashe mu, rashin uwa ma masifa ne nasan da mahaifiyar mu nanan bazata bari muyi wannan banzar rayuwar ba hawaye na share na ce mata "shike...........,"kafin nak'arasa Raheenatu tai wuff tace "keeee!!! Hinde je kice mata 'ance baza 'ayi ba idan bazata sa suhailat tayi ba ko 'yar aiki tabar shi 'ai ba uwar mu zamuyi mawa ba,"


Hinde da gudu tafita Dan gani take ta tsaya tsaf Raheenatu zata daketa


Raheenatu ta dawo kaina Tana fad'in "ke Kuma har kin wani ce to shikenan kamar wata uwar ki ke ni danice ke wllhy dukkansu sai na zuqe masu jini uban kowa ya huta,"

Sadeeq yace "ai ni wllhy wani lokacin adda Raihana na ban haushi saboda wannan salihancin nata wllhy ki ka tsaya idan baki sannu ba sai sunbi ta,kanki ni, baki ga ba ma cikin su ba Mai shiga shirgina ba," ya fada'a yana wani karkace baki.

Ni da, gashi har Raheenatu dariya ma suke ban, k'yale su nai kawai suna mitar su, tashi nayi zanyi girkin Amma raheenatu fafur tace bazanyi ba ba yanda banyi da ita ba tace ko nayi sai ta b'arar da shi, nasan zata aikata shiyasa ma na haqura kawai.



Hinde Tana fita ta nufi sashen mama Tana d'ari_d'ari ta fad'a mata ai ko ta na gamawa mama ta kwashe ta da mari Tana fad'in, "ke har kin isa su baki saqo kizo ki maimaita man to yau Dan uwar ki ke zakiyi aikin gidannan duka shegiya Mai idanun gojiya,"mama ta, inda take shiga batanan take fita ba, yadda kasan hinden tai mata.


Hinde ko sai hawaye take a ranta Tana fad'in "Allah ya isah muguwa kawai insah Allah sai kinga sakayya tun a duniya,"



Saida mama tagama masifar ta sannan tace ta tashi ta Kira Inna Abu tai girkin ita Kuma ta gyara sashen aunty amarya idan ta Gama ta ba ma shehu Mai ba ma flowers ruwa ya Kai mata asibiti, da sauri hinde ta tashi tafita Tana ta ja ma mama Allah ya isah




Mama kam haushi da takaici kamar ya kaita kushewa ga bak'in cikin Raheenatu ta lahanta mata 'yar ta Dan zulfa'u najin jiki sosai , ga takaicin tasa su aiki suna bijere mata ita da take son su dunga bin ta sau da k'afa amma dole ta sake shiri a kansu Dan idan batayi sannu ba dukkan Shirin ta na tsawon shekaru zai lalace Tana ji Tana gani.




Zaunawa mukayi muna ta hira a bakin Sadeeq nake jin wai saura sati biyu muyi family meeting , shima a bakin Na'im d'an baba rabi'u yake ji shiru nayi Dan nasan naje nazama abun tsoro da hantara, Kuma gashi idan banje ba nasan wani laifin zanyi wajen Abba shiyasa na shiga zullumi




*Washe gari*



Koda muka tashi muka ga ana ta girke_girke kala da kala, na tarbar aunty amarya da zata dawo daga Canada.


Bamu bi takansu ba muka shirya zuwa islamiyya gabana na d'ar_d'ar saboda abinda zanje na tarar





*************

Tunda ya tashi yake jin jikin shi ba dad'i Amma dole ne yaje katsina yau dandai bashi da yanda zaiyi yana son duba company shi nacan tashi yayi 'a hanzar ce ya ida shishshirya wa, koda ya fito Nafeesa na zaune a dining ta Sha uwar kwalliya sai zuba qamshi take yana zuwa ta sakar mashi murmushi Tana fad'in "morning honey," "morning too beby, hope dai kin tashi lpia,"yafad'a yana sakar mata kiss a kumatu murmushi tai Tana fad'in "lpia lou,"

Zama yai ta cika mashi qundunshi da abinci sannan yai mata sallama , ya shiga part d'in momy yana zuwa Kai tsaye bedroom d'inta ya shiga ya iske Abdurrahim da mom da sallama ya shiga ya gaida mom yai mata sallama sannan daganan Airport yawuce yabi flight.





Koda ya je ya dubo ya d'an rage wasu ayuka


takaddu ya ke cike wa jin ana Kiran sallah ya sashi tashi ya tafi masallaci , ana idar da sallah ya fito

tafiya yake cikin sauri yaji yaci karo da mutum d'ago kanshi yayi itama lokacin ta d'ago nata idanun da suka Sha kuka
Gabanshi ne ya fad'i ganin Abinda ya matuƙar ruɗashi,


Ja da baya yayi yana kakkab'e jikin shi yace ke baki da hankali kiga babba ya wuto baki San ki bashi hanya ba ko Kuma kin buge ni bakisan kibani haquri ba ga ki k'arama sai shegen girman Kai.


A hassale na d'ago idanuna Ina fad'in "ni dakai waye yafara buge wani Kai ya kamata kaban haƙuri , Amma ka wani tsare ni da fad'a naqarashe zancen da huci harda girgaza jiki,"


Baki sake ya ke kallonta tun da tafara ga takaicin yarinya ƙarama ta gaya mashi magana bud'e baki yayi cikin bala'i ya ce "wai uban mi kike taƙama dashi ne, ni zaki na,gaya wa wannan maganar kin wani yiman fik'i_ fik'i da idanu, nonsense kawai,"


Yana Gama fad'a ya wuce cikin qunar Rai Dan dukan mace ba halin shi ba ne da ba abinda zai Hana shi dukan ta.





*B'angaren jogu*


Dunyar shi yake ci ba abunda ke damun shi yau ne za suje k'ungiya Dan k'ungiya na buk'atar ganin su.



Gudu yake ta shararawa har ya isa wan ƙungurmin daji Kai baka ce 'a kwai wasu halittu a ciki ba yana zuwa dai_dai wani waje ya tsaya yai 'yan surutai sai ga gida ya bayyana Kai tsaye ya shiga ciki.

Abinda zai baka mamaki duk mutanen ciki manyan Alhazawa ne da 'yan siyasa.

Jogu na shiga aka buk'a ce su da su shiga d'akin taron

Suna tashi wani qaramin d'aki ne suka fara shiga dukkan su tsirara sukayi suka dunga gewaye wata babbar tukunya sai da suka gewaye ta yakai sau bakwai sannan suka d'ebi abinda ke ciki suna zuba ma jikin su shima sai da sukayi sau 7 sannan suka Sha sau 7 shima sannan suka d'aura jajayen zannuwa .

Suna gamawa suka hadu dukkansu suka jera layi kamar masu neman sadaka Wasu surutai suka dinga yi Wanda bazaka fahimci abinda suke cewa ba



Suna gamawa dukkansu suka zube dukkansu sukai sujjada dukkansu wata guguwa ce ta taso

Ba a d'au lokaci ba sai ga wannan yabid'ad'iyar tsohuwar ta bayyana..✍️




Wannan kenan







*Comments, share and like*



Wadannan sune qwarin gwiwata✊🏿




*By Mariam sanee🌹*





*✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️*





*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai
*RUSHEWAR RAYUWA




*By Mariam sanee🌹*





بسم ألله الر حمن الر حيم





*Page 11&12*



__________________✍️Ga bakin sai uban wari yake tai mashi wani fafarrr da idanu.


Abdurrahim kau wani uban takaici ne ya turnik'e shi, ganin yadda ta kemashi, baisan sadda ya buga mata uwar tsawa ba, yana fad'in "ke Dan ubanki fad'a masu gaskiya ko yanzun na tattaka ki a nan,"


Dada tace "Kai Abdurrahim bansan iskanci kana son yarinya kana wani b'ob'b'oyewa yanzun fa, naga har wani fafarniyar soyayya taima da idanu, Kuma da Alamu ta shigeka idan zaka fito fili ka fad'a mana, 'a Sha biki kawai Amma ka wani tsaya sissinne mana Kai,"

Hasiya najin ance fafarniyar soyayya ta shiga Abdurrahim ta k'ara washare hak'oran ta masu d'an banzan wari tanafad'in "Kuma Alk'ur'an dada da, naimahi, baake sakar man murmuhin soyayya ba," tafad'a tana rausayar da Kai


Wani bahaggon bugu Abdurrahim yazo kawo wa Hasiya NURAIM ya tare, yana fad'i " baka da hankali ne zaka daki mace?macen ma k'aramar yarinya,"



Abdurrahim ya ce "bro kabar ni ko Yaya ne na zubarma wannan yarinyar hak'oran gaba ko Yaya ne, Dan baccin rainin hankali, kamar ni zata ce wai na ce Ina sonta to Dan ubanki idan baki gaya masu gaskiya ba saina ci buhun ubanki yanzunnan na karya ki Dada takai ki d'ori 'yar banzar munafuka,"



Hasiya naganin Abdurrahim ya birkice Kuma tasan halin shi yanzun nan zai iya karyata, cikin inda inda tace "zan... Zan...fad'i gaskiyar lamari Dada aradun Allah Dada Abdurrahim bai ce yana Sona ba ni dai, ce nake sonsa tun tuni to hine nace masu Muslima Abdurrahim yana Sona don har mun daidaita kammu hine ita Kuma bak'ar Algunguma zata zo ta tona man Asiri, nima dada zan tona mata Asiri yanzun," tafad'a tana hararar muslima dake wutsil wutsil da idanu kamar wacce tai ma sarki k'arya.


Dada tai caraf tace "keko Hasiya anyi bak'ar munafuka yanzun da shi Abdurrahim d'in baice yana sonki ba? Amma kika zo kika sharara ma Musulma k'arya ita Kuma da yake 'yar banzar gulma na cinta tazo tafad'a man
Kuma da kike cewa zaki tona ma Musulma Asiri wane asirin musulma ne ban bankad'o ba?indai game da satar nama ne wannan ko kura ta shafa mata lafiya,"


Hasiya zatai magana Abdurrahim ya buga mata tsawa yana fad'in "ke Hasiya idan baki rufe mana wannan d'an bazan bakin naki ba saina karyaki, Kuma ki fad'a Mani dalilin da yasa kika ce kina Sona tunda har raini ya shiga tsakanina da ke, ke baki San dubunki sunyi sungama ballantana ke kucaka 'yar k'auye, tashi ki b'ace mana da gani ko nayi ball dake yanzunna,"


Da gudu Hasiya da Muslima suka fita, Dada ta kalli Abdurrahim ta ce "Allah ya, taimake ka wannan fafarniyar soyayya da tayima Bata tafiyar ma da zuciya ba, yooo Ina dalili ku dinga haihuwar d'iya masu k'urma k'urman goshi,"

Abdurrahim ya ce "Dada Dan Allah ki daina ma wannan zance ni fa kinsan mace ko kallo Bata isheni ba ballantana har akai ga maganar aure ke mutum bai da damar shigowa nan sai kin mashi maganar aure nifa shiyasa kika gani ko shigowa na gaisheki banayi,"


Dada ta tab'e baki Tana fad'in "Abdurrahim idan baka shigo ba ai baka Hana d'iyan Halima da Saratu su shigo ba, tunda Kai, da Hameed Fatima ta Hana ku shigowa, nasan 'a b'oye ka shigo yanzun ma,"


Abdurrahim baice mata komai ba ya fice, Dada ta waigo taga NURAIM baya nan, tab'e baki tayi Tana fad'in "kunji da bak'in halinku irin na uwar ku,"


Shiko NURAIM tun sadda
Su Hasiya suka fita shima ya fice Kai tsaye part d'inshi ya nufa

Yana shiga falo yaji k'amshin girki ya San Nafisa ce, wuri ya samu ya zauna, Nafisa ce tafito Tana fad'in "honey yaushe kashigo ?"murtuke fuska yayi yana fad'in " Ina kikaje? baki gaya man zaki fita ba Kuma kinsan nayi tafiya zandawo,"

Marairaice fuska tayi Tana fad'in honey ba wani waje, naje ba wajen Aunty naje fa.
Nuraim ya ce to 'a kiyaye dai yafada yana ficewa daga palon

Yana fita Nafisa ta dafe kirji Tana fad'in "wai Allah ya tsareni bai d'ago ni ba,"





*B'angare guda kuwa*


Haka muka dinga kuka bamai rarrashin wani sai da muka gaji Dan kammu sannan mukai shiru, muna ji muna gani muka rabu da d'an uwammu gashi bawanda ya San inda ya nufa shikuma yace bazai zauna garinnan ba, sai Raheenatu ce ta bashi number wayar ta.

Koda muka dawo falo muka zauna kowa da abinda yake sak'awa a ranshi, ganin Shirin bayai yasa nace ma Raheenatu "miye mafitar wannan auren da za'ai mana? kina ganin fa Abba biyan bashi yayi damu yanzun ko auren a kayi kinsan kamar yanda muka zama bayi gidannan, can idan muka je bautar da zamuyi sai tafi Haka,"

Raheenatu tayi murmushin takaici ta ce "Raihana to idamma bautar zamuje muyi da sauk'i, waye yaja mana?idan ba mahaifinmu ba, ni yanzun Raihana duk yanda rayuwa tazo man karb'ar ta zanyi, idan Allah ya k'addara muji dad'in rayuwa zamuji,kinsan kowane bawa da irin tashi k'addarar mu tamu kenan,mafita kawai Raihana muyi ma Abba biyayya,"

Hawaye na share Ina fad'in "yanzun Raheenatuda k'ananun shekarummu 18 yrs fa duka za'a kashe Mana rayuwa,miyasa zulfa'u da suhailat su bai masu ba? sai mu da baya k'auna shin k'iyayya hauka ce idan baya son ganimmu ya kore mu daga gidan mana,"

Shiru Raheenatu tayi bata ce ƙala ba,




Mama kam farinciki kamar ta kashe kanta Dan murna burinta ya cika na, naganin, hukuncin da Abba ya zartar, ba abinda take gurin gani sama da taga rayuwar su Raihana ta tagayyara, Bata k'aunar ta bud'i ido taga y'ay'an Sajeeda.


Aunty Amarya kuwa kadaran, kadahan Dan gaban Abba Bata nuna farinciki ba Bata Kuma nuna bak'inciki ba.
Ji take duk duniya ba Wanda ya fita tsanar su Raihana tabbas yau idan tace batai farinciki ba tayi k'arya, da


Duk ilahirin su Mama da Anty Amarya dukkansu farinciki suke da hukuncin da Abba ya zartar.



Mu kau yau Haka muka k'arashe rayuwar mu cikin k'unci, to dama kullum rayuwar mu cikin k'unci take saida na yau yafi na kullum.




*WASHE GARI*


Tunda muka tashi muka ga y'an aiki na ta hada hadar girki kala_kala, jikina yai sanyi Dan duk inda muka wuce 'yan aiki sai sunyi zund'en mu suna dariya, Inna Abu ce kawai ta taya mu jimami.


Mama da su aunty Amarya kuwa sun cakare cikin leshi tsadadde dukkansu ka kalli fuskokin su cike take da farinciki

B'angaren Abba kuwa yana ta sabgogin gabanshi Dan shi ji yake zai rabu da k'aya.


Karfe 2:30 daidai Aka d'aura auren RAIHANA da Alhaji MUTTAƘA Raheenatu da Alhaji Bashir kowa ka gani cikin Alhazawan nan dukkansu bakunan su bud'e yake Dan su arha b'agas anyi masu biyan bashi da tsala_tsalan 'yam mata kamar su RAIHANA.


Muna nan zaune sai ga Hinde ta shigo Tana fadin Abba na naiman mu part d'inshi.

Tashi mukayi muka zira hijab d'immu ga fuskokin mu duk sun kumbura saboda kukan da muka sha.


Da sallama muka shiga kawunan mu 'a k'asa bisa cafet muka zauna muka gaishe da wasu dattijai guda biyu da suka k'ura mana ido tunda muka shigo

Abba ne yace to raihana ga mazajen ku nan, ke raihana ga wannan Alhaji muttak'a, ke Kuma raheenatu Alhji Bashir

Dukkan mu d'agowa mukayi muna kallon wad'annan dattijan da sukayi jikoki damu





*Jogu*




Jogu kuwa bashi da burin da ya wuce yaga yajawo wannan yarinyar ya kawo ta ga k'ungiya.

Gashi nan da sati ake son yakai sadaukarwa shi dole ne ya tuntub'i Alhaji naseer yaji miye mafita yanzun.




Wannan kenan





*Comments, share fisabilillah*




Wadannan sune qwarin gwiwata


*By Mariam sanee🌹*





✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl

*RUSHEWAR RAYUWA😓💔*



*By Mariam sani🌹💗*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


*Bismillahirrahmanirrahim*




Page 13 &14


__________________✍️Da kallo Nafisa ta bishi tana sakin wani shu'umin murmushi, kafin tace, "da sannu sai na mayar da rayuwarka a tafin hannuna,*Nuraim* duk son da nake maka baya hana na aikata k'udirin da nai niyya, da kasan ni kowacece da bakai fatan kasancewa dani ba, ni Kura ce lulllub'e da fatar Akuya, kayi kuskuren fahimta ta", murmushi ta k'ara saki tana mik'ewa ta shige bedroom d'inta,





Nuraim kuwa yana shiga ya kwanta bacci, ko 5 minute ba'ayi ba, ya ganshi cikin lambu mai ciki da yalwar itace, ga wani sassanyar iska dake kad'awa, a hankali ya dinga jiyo sautin kuka, hanyar da yake jin kukan nan yabi, kamar kulum yau ma ta kifa kanta a gwiwoyinta tana kuka, a hankali ya tako ya iso gabanta ya dafa kafad'ar ta yana fad'in "baiwar Allah wacece ke meye damuwarki"??, shiru tai na tsawon mintuna biyar, kafin a hankali ta d'ago fuskar ta dake cikin nik'ab wacce ba abinda ake iya gani sai idanunta,


Cikin wata kalar murya mai dad'in sauraro tace "kayi min Alk'awarin zaka taimakeni ka ceci rayuwata daga wad'ancan Azzaluman," ta fad'a tana nuna mashi wasu kalar halittu dake tunkaro su, "tabbas nasan kai kad'ai ne wanda zai iya ceton ruhina daga hannunsu, kayi min alk'awarin duk runtsi zaka taimakeni" ta fad'a tana mai zubar da hawaye,


A hankali ya kama hannuwanta ta mike, kallonta yake cikin k'auna da shauk'i har na tsawon minti goma, kafin cikin nutsatstsiyar muryarshi ya ce "tabbas zan taimake ki ta ko wane hali, idan kinga ban taimake ki ba sai dai idan bana raye, ki sani raina fansa ne ga abinda nake tsananin so da k'auna,"


Sake kallonshi tayi tana sakar mashi wani lallausan murmushi, kafin tace "kayi min abinda bazan tab'a mancewa da kai ba, sai dai tabbas zanyi nesa da kai ba zaka k'ara ganina ba a halin yanzu, sai dai ko ba komai rabo zai sake had'amu", ta fad'a tana mai b'acewa daga gurin.


Da Addu'a d'auke a bakin shi ya farka' daga wannan sababben mafarki daya saba, a hankali ya bud'e idanuwan shi, kafin ya tashi yana fad'in "wacece ita, shin su waye wad'annan mutanen da ta nuna min,"??, Kusan shekara biyu yana mafarkinta, amma bata taɓa yi mashi magana ba sai yau, shin wai ma ina zai sake ganinta? tabbas akwai lauje 'a cikin nad'i, yanzu yaji yanada burin taimakon ta koda ta hanyar ne zai rasa rayuwar shi, tausayin ta da wata zazzafar k'aunar ta d'arsu a cikin zuciyar shi, baiyi tunanin bayan Nafisa akwai wata ya macen da zai duba ba, a matsayin wai yana sonta, saidai kash, gashi ya kamu da son wacce bai ma san a ina take da zama ba, "wacece ita,"? duk bai sani ba, lumshe lumsassun idanunshi yai yana fad'in tabbas "ke kad'ai ce wacce nake ma so na hak'ik'anin gaskiya, duk inda kike ina son Ubangiji ya bayyanar min da ke,"







***************


Raihana ta cigaba da cewa "Abba tabbas nasan lokaci na nan zuwa, wanda ko baka mutu ba zaka d'and'ana,"


Tana kaiwa nan ta fice, kowa da kallo ya bita, Raheenatu jiki a sanyaye ta tashi tabi bayanta, tana shiga ta iske ta ta kifa kai da gwiwoyin ta tana ta uban kuka, hawayen tausayin 'yar uwarta suka zubo mata ta share, tana fad'in "haba Raihana miye na ki zauna kita kuka, ki sani ba kuka fa ya kamata kiyi ba addu'a ya kamata kiyi,"


D'ago fuskata nayi ina kallonta, kafin ince "Raheenatu kenan, kina tunanin zan manta abinda Abba yai mana?, tabbas nasan ko nace zan manta a halin yanzu nayi maki k'arya, shin Raheenatu ina Abba yake son mu saka rayukammu?, ni yabar ni da annobar da nake ciki, gashi ya k'ara tsunduma ni cikin wani halin ha'u la'i, tabbas inaji a jikina akwai abinda zai sami Abba,na lokaci kad'an ake jira, nasan ko basu kashe shi ba sai sun kassara rayuwar shi",






Raheenatu tace "in sha Allah Raihana babu abinda zai sami Abba saidai Alkhairi, yanzun dai ki cire damuwar komai a ranki, k'ara ki rungumi rayuwar ki ta gaba,tunda baki san kalar zaman da zakiyi da iyalin wancan bawan Allah ba,"





Kallonta na sake yi ina fad'in "Raheenatu wace rayuwa zanyi baya ga wadda zan runguma?, nasan can d'imma ba wai zaman jin dad'i zanyi da iyalinshi ba, Raheenatu abinda na d'auka da can, yanzun bazan d'auke shi ba, zuciyata ta k'ek'ashe da rashin tausayi da Imani yanzun, ji nake babu wani sauran tausayi daya rage min a halin yanzun, tun lokacin da aka d'aura min aure da wancan tsohon naji babu ran da bazan iya kashewa ba, ciki kuwa har da mahaifin da ya haifeni, to kinga kuwa zare rayukan iyalan Allhaji Muttak'a ba zai sa naji wani Abu ba, dan tabbas nasan na zauna dasu kaf sai na k'arar dasu, nikuma bani son k'ara d'aukar wani Alhakin",





Baki sake Raheenatu ke kallona tana fad'in "anya Raihana kina da hankali kuwa?, dan ina tunanin D'an Cakara ya baki k'waya kema kin cakare".




***************



*Jogu*


Numfasawa Alhaji Naseer yai yana fad'in "Jogu nariga da na fad'a maka dole sai munyi aiki 'a kanta, dole ne yau mu shiga aiki 'a kanta".



Numfasawa Jogu yai yana fad'in, "Naseer wallahi sai yanzun hankalina ya kwanta, amma kana ganin wannan aikin da zamu yi shine mafita?",




Duban shi Alhaji Naseer yai yana fad'in "Jogu wannan aikin da zamu yi shine dai_dai, yau nake son mu shiga mu gama aikin tunda kaga gobe war haka za'a daura auren, amma kafin nan sai mun samo bak'ak'en karnukan da zamu yi amfani dasu",



Jogu yace "amma Naseer miye amfanin karnukan da za' a samo,"?

Alhaji Naseer yace "Jogu kai har yanzun baka kware 'a harkannan ba, ace shekara kusan nawa amma har yanzun wani abun saina yi

Please Login or Register in order to submit comment