Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki dinga yi ma kanki fatan tsiya," ta faɗa tana banka min uwar harara,


"Wane kuma fatan Alkhairi Raheenatu? Ai ƙaddara tariga fata, tunda ina cikin tsiyar, da ne nake dana sanin Rayuwata, amma yanzun ko kaɗan, bani dana sani, yanzun ma dai abar maganar," banza Raheenatu tayi min dan ita baƙaramin haushi na bata ba sai dai ko yayane tana bala'in tausayin ƴar uwarta,


Duk yini Ranar haka muka yi shi sukuku, babu wani mai walwala a cikimmu, dama gashi indai rayuwar ƙunci ce mun riga da mun saba ta, saidai ta yau tafi ta kullum, dan kowa yana tunanin rabuwa da ɗan uwan shi, duk da nasan ba wai zan dena ganin Raheenatu bane, sai dai ina jimamin irin yanayin da zanje mata da shi ne,



Haka dai cikimmu, kowa ya kwanta da zullumi, Raheenatu na zullumin, rabuwa, ni kuma ina zullumin yadda za'a tsafa ni,dan idan na tuna irin Azaba da raɗaɗin da naji jiya da aka saka min ƙanƙarar nan, haka dai na kwanta.



*Duniyar mafarki*




Sanye nake da jajayen kaya,ga wani uban tambari a dokin wuyana,zaune nake gaban wuta na tanƙwashe ƙafafuwana, ga waɗansu mata ɗaure da baƙaƙen zannuwa mai ɗauke da ratsin ja , sai waɗannan halittu masu kama da siffar birrai,suma hannuwansu ɗauke da wasu irin ƙahunhuna,



Wata irin tsawa a kayi da rugugin da ya sanya iska da guguwa mai ƙarfin gaske kaɗawa, yana zubar da itace dake cikin dajin, waɗansu halittu guda huɗu ne suka bayyana, suma da kalar shigar da nayi da tambari, sai Awwazun mutane, da ƙoƙon kai, suna isowa daf dani, masu ƙahunnan nan suka busa shi, wata kalar sheɗaniyar dariya suka saki, su duka, kafin su tamke fuska kamar waɗanda basu taɓa dariya ba, zama suka yi gaban wutar suma suka tanƙwashe ƙafafuwansu, kamar yadda nayi,da wata kalar sheɗaniyar murya ɗaya daga cikin su yace "RAIHANATU!!!!! da ƙarfin gaske,"




*JOGU*

A ɓangaren su jegu kuwa, suma dai-dai wannan lokacin ne suke zaune, duk sun tanƙwashe ƙafafu, saidai abinda zai baka mamaki dukkansu, yadda kasan barci suka yi ko mutuwa,amma ba hakan bane Ruhikansu sun tafi wata duniya ta daban,ga ɗakin da suke idan banda kukan waɗansu kalar tsuntsaye babu Abinda kakeji,



Wani kalar busa ƙaho a kayi wanda kai kace, ƙahon tashin duniya ne akeyi, ɗaya daga cikinsu ne ya miƙe zumbur kamar an tsikareshi, ya tashi ya shiga wani ɗan sirɗaɗen lungu,wani shirgegen baƙin kare ne ya ɗakko, sai jarirai guda, ukku suna ta canyara, uban kuka, aje karen nan yayi sannan jariran mutanen ya kwantar da su gaban wata shirgegiyar tukunya, wani surutai yakama yi, suma dukka kingin suka ɗauka,



Sunfi ƙarfin Awa suna surutan Aljannu nan, kafin su tsagaita, mutumin da ya tashi ne ya dinga ɗakko jinjiran nan da ɗaiɗaiya yana yankawa a cikin rangajejiyar tukunyar, nan a haka kaf ya yanke su,yana gamawa aka ɗauki wata uwar kururuwa, da tsawa mai tafe da walƙiya,



A daidai wannan lokacinne ita kuma Raihana ta ɗago da idanunta da suka janza kala daga blue zuwa Jajir ga jini dake zubowa daga kwarinsu, gashin kanta duk ya barbaje, wata iska ce ta taso mai ƙarfin gaske, ta ɗaga ta sama....✍️






Wannan kenan




*Comments, Share fisabilillah*




Waɗannan sune ƙwarin gwita





*By Mariam sani🌹💗*



✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





*08109554986*
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9Pl


*RUSHEWAR RAYUWA*



*By Mariam Sani🌹💗*







*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Bismillahirrahmanirrahim*




Page15&16




__________________✍️"Tabbas har yanzun ina jin ƙaunar mahaifimmu da kuma tausayin halin da aka sakashi, shin Raihana baki tausayin mahaifinki ne? kamata yayi fa ki ceto rayuwarshi ba wai ki kassara shi ba, nasan kinada right ɗin da zaki ɗauki fansar abinda akai ma mahaifimmu, kamata yayi mu haɗa ƙarfi da ƙarfi mu ceto rayuwar shi, nasan duk abin da ya keyi bayin kanshi bane, ina iƙirarin da kike yi na ɗaukar fansar mahaifiyarmu? sai dai kash duk wani mataki na ɗaukar fansa an mana iyaka dashi, nasan kece kaɗai wacce zaki iya ɗaukar fansar ran mahaifiyarmu, da ɗan uwanmu, Raihanatu ina son ki dawo cikin hayyacinki, ki daina wannan zance," ta ƙarashe zancen da sakin wani marayan kuka,



Niko kallonta nake, dan duk abin da ta faɗa batai ƙarya ba, da ina da burin ɗaukar fansar ran mahaifiyar mu, ina son ganin bayan duk wani mai hannu a cikin sakamu wannan hali, sai dai kash yanzun ji nake bani da wani burin da ya wuce, nai gadon Ahalin mahaifina, wato na zama shahararriyar matsafiya, bani da burin da ya wuce na ganni bisa karagar mulki ta matsafa,


Kallon Raheenatu nake yi yadda take ta cisgar uban kuka, sai kuma ta bani tausayi, kafaɗarta na dafa ina faɗin "Raheenatu da nake da burin haka amma yanzun wannan ya kau a zuciyata, tabbas abinda kika ji na faɗa maki gaskya ne, yanzun bana shakkar kisa, bana tsoron nai kisa duk abinda kika ji na faɗa tabbas daga zuciyata yake, ban sha sholisho ko wiwi ba, a cikin hayyacina nake, maganar da na faɗa maki gaskiya ce, tabbas ko Abba bai mutu ba, sai rayuwar shi ta kassara komin daɗewa, yanzu ne na hau ganiyar mulki, yanzun ne zani fara wasan, dan duk wanda ya shigo gonata tabbas ya gama Amfanuwa, dan sai dai uwar mutum ta haifi wani bani duba abota ko ƴan uwantaka, saina shayar da su mamaki," na ƙarashe zancen da fashewa da wata sheɗaniyar dariya,


Tsayawa Raheenatu tai cak da kukanta, dan ita ganin Raihana take ta koma mata wata ta daban, wannan ba Raihana da ta sani bace, Raihana da take shakkar wani ya daketa, dan gujema kashe shi, wacce take gudun ta aikata kisa amma yau ita ce take iƙirarin ta hau ganiyar kisa, har tana iƙirarin ta hau karagar mulkin zubda jini, me mata nasiha akan abinda Abba yake mata yau ita ce da faɗin zata kashe shi ko ta kassara rayuwarshi, wannan wace irin rayuwa ce Raihana ta ɗaukar ma kanta, dogon numfashi taja ta ce "Raihana ya kamata ki sauke wannan ƙudirin naki, kinga yanzun gidan wani fa zaki, bai kamata ki hau bisa ganiyar nan ba, kamata yayi ki rungumi rayuwar da tazo maki, kinga mun rasa mahaifiyarmu, mun rasa ƴan uwammu, kema bana son wani Abun ya sameki, dan Allah Raheenatu ki sauke wannan baƙin ƙudirin naki,"



Banza na mata dan ba ƙaramin haushinta nake ji ba, taya zata ceman wai na janye ƙudirina, "ke Raheenatu babu abinda zan janye ƙara ki ƙale ni kawai idan kinga na janye wannan ƙudirin tabbatar babu ruhi a tare dani, ki sani ni a halin yanzun bani da burin da ya wuce nai gadon Ahalin Abba, na zama cikakkiyar matsafiya, da hakan ne zanbi duk wani mataki na kassara rayukan da na riƙe a raina", ina kaiwa nan na tashi na wuce bedroom,dan wani kalar mashahurin bacci da nake ji.


Da kallo Raheenatu ta bita tana mai tausayin halin da ƴar uwarta ta shiga, amma tabbas koma minene tasan ba mai kyau bane ta ɗaukar ma kanta, ta rasa abinda take son tayi sai gadon, Ahalin Abba, amma su komi za suyi ai basu kisa,




Niko ina shiga na kwanta, ko 5 minute ba'ayi ba na ganni cikin dokar daji inbanda gudu babu abinda nake tsalawa, ga wasu kalar halittu biyu da ke bina, gudu nake na ceton rai, saidai ina zowa dai_dai wata itaciya na tsaya cak sakamakon, ganin wannan mummunar halitta, da na saba gani, kamar kullum yauma cikin shigar da na saba ganin shi, ta jan kyalle yake, saidai yau harda wani uban tambarin rubutu, a dokin wuyan shi, dan da gani kasan rubutun Aljannu ne, da yarensu, tunkaro ni ya dinga yi ina ja da baya har na ƙure ma itaciyar da ke bayana, cikin wata sheɗaniyar murya da ke nuna zallar, sheɗanci ya ce, "ba zaki iya guje ma tarkona ba dole ne yau na ƙara tsafe ki, ta yadda zaki ƙara hawa, bisa layi, kece matakin duk wata nasara tawa, kece kaɗai wacce zata iya, ɗaukar dodon tsafi, dole ne yau na ƙara cire maki dukkan wani shakku, da tsoro, tsoro ba naki bane in hardai kina son gadon Ahalin mahaifinki, kuma kina son hawa karagar mulkin matsafa, yanzunnan zan ƙara tsafe ki," ya faɗa yana mai sake fashewa da wata mahaukaciyar dariya wacce ga baki ɗaya sai da dajin ya amsa,


Niko tsurewa guri guda nai dan wani bala'in tsoro da ya ziyarce ni, haɗiye wani yawu nai da ya tokare min maƙogaro nai, cikin murya mai nuna Alamun tsoro nace, "ya shugabana haƙiƙa zan Amince ga dukkan wani umarni da zaka gindaya min, in har dai kayimin alƙawarin zamowa shahararriyar matsafiya, zan kasance maiyi maka biyayya a ko da yaushe, a halin yanzun babu abinda bazan iya ba, don ganin na cika burina na zamowa matsafiya, yanzun ne na samu amsoshina na cewa ni ba mayya bace sai dai matsafiya,"



Sheƙewa da dariya wannan mummunar halitta yayi, yana fad'in "yanzun ne na tabbatar da matakin nasara ta ta taho", wata uwar kururuwa ya saki wacce sai da dajin ya girgiza, ita ce suka dinga faɗuwa, daga bisani kuma, wasu kalar halittu suka bayyana, wanda sudai ba goggon biri ba, dan jikin su duka gashi ne, sai jajjayen idanuwansu waɗanda kasan jini, ga wasu tukwanen ƙasa a kawunan su, zagaye ni dukkan su suka yi suna wasu surutai waɗanda ba zaka fahimci abinda suke cewa ba, sai su kaɗai suka san Yaren,

Bayan sungama ne wannan mummunar halittar ya amshi tukwanen wajen halittu biyun nan, zuwa yayi ya fasa a sashen damata, sannan a sashen hagguna, yana gamawa dukkan waɗannan halittun suka zube suna masa sujjada,



Wata ƙwarya naga ya ɗakko ya miƙo min ita, dan tunda ya tunkaro ni da ita yawu na ke tsinkewa, danjin ƙamshin jini, ƙagare nake ya bani ita na kwankwaɗa, yana zuwa na karɓe kwaryar na kafa mata kai, wani zut_zut na dinga ji tunda ga ƙafafuwan har izuwa kwanyata, ga wani maganaɗisun daɗi da nake ji, saboda daɗin jinin da garɗinsa, saida na shanye shi tas har ina tanɗe baki sannan na ajiye ƙwarya, wannan halittun ne suka miƙe dukkansu, sakamakon naga tukunyar ƙasa sai naga ƙoƙon kawunan mutane bisa kansu, lokaci guda suka raba ƙoƙon kannan gida biyu, sannan wannan mummunar halitta ya ida ƙarasowa gareni yana mai tura man wata ƙanƙara_ƙanƙara a ƙasana, wani Azababben ihu na saki dan jin wata uwar azaba ta ziyarceni,

Ruwa naji an malaya man saman jiki buɗe idanuna nayi da suka ƙara canza launi, nayi na sauke a kaina
Raheenatu wacce take ta uban kuka, "lafiya kike kuka ko wani Abun Abba ya sake yi maki?" Na tambaya ina kafeta da idanu,

Rungume Ni tai tana faɗin "Raihana badai suyima Abba komai ba ko,?dan Allah kar suyi masa wani abun idan har sun ɗauki ruhin shi kiyi ƙoƙarin dawo mashi dashi bana son wani Abun ya samu Abba dan Allah ki janye mummunan ƙudirinki a kan Abba, wannan wacce kalar rushewar rayuwa ce? a ce kina ƙoƙarin ganin bayan mahaifinki,"


Baki sake nake kallonta ina faɗin "wai Raheenatu mi kika gani ne? da zaki zo kina man waɗannan surutan,ni babu wanda na kashe, na dai san nasha jini amma bansan jinin waye nasha ba, na kuma san ba jinin Abba bane nasha, dan daga jin garɗin jinin yayi kama da na jinjiri, idan ko jinin Abba ne zanji shi da launi_launi kinsan shi jinin manya yadda yake," na ƙarashe zancen da ƙoƙarin miƙewa saidai wata uwar Azaba da ta sake ziyarta ta sani komawa na zauna ina ciccije leɓe,



Raheenatu kuwa ta kasa ce ma Raihana komi, dan jin zancen take gadai shinan, "Raihana yau ita ce da faɗin jini da garɗi, lallai abin nata azimin ne", ta faɗa tana miƙewa dan kiran da aunty Amarya ke mata( su Raheenatu yau duk anyi sanyi ba'ajin tashen balagar rashin kunya🤪)


Raheenatu na fita na tashi na miƙe da ƙyar na shiga toilet dan yin Alwalla nayi sallah, ina shiga na duƙa dan kama ruwa naga abinda yai matuƙar bani tsoro, dan ganin wasu kalar ruwa masu uban wari sun zubo man ta ƙasa na sai gundulen jini, jiki a sanyaye na gama kimtsa jikina na na fito, dan gabatar da Sallah, saidai ina kabbara sallah naji Azabar da nake ji da idan zanyi sallah ta yanzun ta linku, da ƙyar da jiɓin goshi na samu nayi, sallah, ina gamawa, na zube nan ina mayar da numfashi,





********************
*Jogu*



Zaune yake wani tamfatsetsan falo na Alfarma, ga waɗansu Alhazawa suma a zaune gefe guda kuma ga Alhaji Naseer, kowane ka kalli fuskar shi cike take da fara'a da annushuwa,


Ɗaya daga cikin Alhazawan da ake kira da Alhaji Yusha'u ya ce "waini kam Jogu ya batun ƙudirimmu ya kuke ganin zamu yi?, danni a ganina bai kamata a ce mace ta zamo shugabarmu ba, kamata yayi musan yadda zamu kawar da ita,"

Na kusa dashi Salmanu, yace "ya dai kamata ku samo mana mafita yanzun, bama son nan da wata huɗu a ce tana nan dan kaga kai ya kamata, yanzun ka ƙara dagewa, muna son nan da wata huɗun mukai wa dodon tsafi yarinyar nan", ya faɗa yana kallon Jogu,


Dogon numfashi Jogu yaja yana faɗin "Salmanu yarinyar ce shegiyar kaya dole sai mun dage mata,babu yadda banyi na hanata sallah ba amma abun yaci tura, amma yanzu, naga ta hau layi, sannan ina jin tsoron ranar da Yarinyar nan zata ƙware a harkar nan, ballantana idan suka yi mu'amula da ita, kaga dole ne a ƙara mata ƙarfin tsafin ta, ina gudun tazo ta hau karagar mulkin ƙungiya," ya ƙarashe zancen da damuwa,



Dogon tsaki Alhaji Naseer yaja yana faɗin "Ni wallahi kuna ban mamaki ku rasa wacce zaku ji ma shakkar aiki sai wannan tatsitsiyar alhakin, to dukkanku ku kwantar da hankalinku na samo mafitar yadda zamu bi komai a hankali,"

Dukkansu Ajiyar zuciya suka saki dan jin Alamar samun nasara,





****************

*Ɓangare guda kuwa*



Dada ce keta masifa wai har ita Salihu zaiyi ma haka, to bari taje da kanta, zata ji idan shi ya hana Huraira ɗin zuwa gidan sunan, Samira, mayafi ta ɗakko ta yafa, ta nufi part ɗin Baba Salihu, tana zuwa ta cigaba da danna door bell ba ƙaƙƙautawa, an daɗe ba azo an buɗe mata ba, da har tayi zuciya zata koma, sai gashi, Aunty Huraira ta buɗe mata,bankaɗe Huraira tayi ta wuce tana faɗin "watakam ke Huraira kin raina ni saboda bani bace uwar da ta haifeki ba ko? har ni zan ta kaɗa maki ƙararrawar sanarwa na iso, amma baki zo kika buɗe min ba, to wallahi kibi duniya a sannu," tafaɗa tana banka ma Aunty Huraira harara,



"Wallahi Dada muna can ciki da baban su Rafi'atu bamu ji ki ba, amma kiyi haƙuri bari na kirawo maki babansu ɗin ta faɗa tana shigewa bedroom d'inta dan kiranshi,"


Da kallo Dada ta bita tana hararar bayanta tana faɗin "kuji man ɓakutar banza shi Salihu ƙwalelen kai ita kuma sai uwar kiba, da uban ƙaton hanci, shi yasa ga ɗiyannan, kamar ɗiyan birai, dan rashin hanci,"


Huraira ta ɗan jima basu fito ba, Dada kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, dan ganin Rainin hankalin da su Baba Salihu su kayi mata, tana cikin haka ne, sai ga Huraira da Baba Salihu da ya fito yana ta faman uwar zufa,



"Kai Salihu waini sa'ar ku ce da zaku tafi ku shanya ni? ka wani fito ranƙwale_ranƙwale da uban ƙaton kai, kazo sai shatata uwar zufa kake, dan baƙar jaraba irin taka baza ka bari ma na tafi ba sannan kayi jarabar taka, amma a ce ina nan zaka raya sunnan ni kabar ni nan shanye," ta ƙarashe zancen da huci kamar wata zakanya,



Huraira ce ta kalleta tana faɗin, "Dada da ki......", katseta tayi da faɗin "kinga Huraira bani son sabon salon wulaƙanci, kin wani tafi ɓakutai-baƙutai wurin miji ni kin barni a shanye, watakam ga kayan wankin kin shanya, idan sun bushe kizo ki kwashe, sai yanzun zaki fito kina wani huhhura min hancinan ki masu kama da gajeren wandon Salihu, to bar kiji ni bazan ɗauki sabon salon iskancin nan naku ba wallahi",






Wannan kenan




*Comments, Share and Like*



Waɗannan sune ƙwarin gwita





*By Mariam sani🌹💗*




✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️





08109554986
[12/18, 3:02 PM] Mmn Minister: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KTIiV2IuK6c8SUvZdVr9P

*RUSHEWAR RAYUWA😓💔*



*NA*
*Mariam Sanee*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


Page 19&20

___________✍️Gashin kanta duk ya barbaje, wata iska ce mai ƙarfin gaske ta zo ta ɗaga ta sama, bushewa tayi da wata kalar shaiɗaniyar dariya wacce da kaji kasan wannan murya tabbas ba ta mutum bace, cikin hargitsatstsiyar murya mai fidda amo da tsawa take faɗin "sai yanzun na ida tabbatarwa ni tabbas Ahalin matsafa ce, kuma jinin tsafi,yanzun ne lokacina, yanzun ne zanci ganiyar mulki da sarauta dan duk wanda yai ƙoƙarin dakatar da ni tabbas sai na bashi mamaki, babu babba ba yaro duk wanda ya shiga shirgina tabbas sai na kai shi kushewa," ta kuma bushewa da wata shaiɗaniyar dariya wanda sai da dajin ga baki ɗayan shi ya amsa.


Suma su Jogu wata shaiɗaniyar dariyar suka saki na samun alamun nasara dan tabbas sunsan yanzu ne lokacin nasarar su, yanzunne lokacin da za suci duniyar su, burin su ya fara cika,suna son su zama shahararrun matsafa wanda babu kamar su duk duniya,



Cikin wata shaiɗaniyar murya Jogu ke faɗin "tabbas Yarinya yanzun ne lokacin da zaki hau ganiyar ki saidai ki sani duk ranar da kika ci Amanar mu sai mun kulle Ruhinki mun azabtar dashi kafin mu kai shi inda ba a dawowa, sannan babu saɓa ma umarninmu, ina son ki sani ki cire burin son zama shahararriyar matsafiya,domin nan dukkanmu muna da wannan burin ki sani tsakaninnmu da ke saidai biyayya, da taya mu ayyuka,kafin ki ida hawa matakin nasara,idan ko kina son hawa matakin nasara to tabbas sai kin shayar da mu jinin ki,wato ina nufin jinin ɗan uwanki ko na Mahaifinki," ya ƙarashe zancen da ƙura mata idanun shi dake cikin mummunar siffar da yazo mata,



Niko tunda yake zancen zani hau ganiyar mulki ta matsafa,na samu kaina cikin farin ciki, saidai abinda ya wanye wannan farin cikin da nake ciki bai wuce jin cewa,wai ni bazan zamo shahararriyar matsafiya ba a tsakanina da su saidai biyayya wani ƙullin takaici naji ya tokare min maƙoshi,abinda ya ƙara tunzira ni bai wuce cewa na basu jinin ƴan uwana da na Abba na,dan duk abinda yake man banjin zan iya sadaukar da jininshi, dan ina jin banyi ma kaina adalci ba,zan ƙara ɗaukar wani zunubin bayan wanda na aikata,


Tsawar da aka buga man ce ta sani dawowa daga duniyar tunanin da na shiga,wani kalar kallo na jefi mai buga man tsawar,wanda ko ban faɗa ba nasan ya razana dashi,cikin wata kalar murya nake faɗin "kar ka sake gigin buga man tsawa dan ni babu mai mani tsawa ya zauna lafiya,ka kiyaye bani son na fara ɗaukar rayukan ƴan ƙungiyar nan," na faɗa da idanuna da ke tsaye a kanshi,


Wannan mummunar halitta ce ta matso kusa dani ta ya watsa man wata powder,wacce ga baki ɗayan ilahirin jikina saida ya ɗauki zafi,wata uwar ƙara na saki dan ganin yadda halittata ta fara komawa da wasu irin gashinan a ciki,cikin hargagi da kururuwa nake faɗin "karku ida illata ni ku barni da wannan ma ya ishe ni amma ina roƙonku ku ƙyale ni hakanan,karku aikata kuskuren da ba zaku iya gyara shi ba,"


Cikin sheɗaniyar dariyar shi da ke nuna zallar sheɗanci yake faɗin "RAIHANATU, babu wani kuskuren da zamuyi ba mu gyarashi ba saidai kisani babu wani mai cetonki a halin yanzun,zamu ida tsafa ki gangar jikinki da Ruhinki ya zama namu,"


Saidai walƙiyar da aka dallaro mai tsananin haske,da tsawa yasa su juyawa bayansu,babu abinda suke gani sama da wani haske mai tsanani sheƙi,a hankali hasken nan ya dinga tunkaro su,yana zuwa daidai Raihana ya tsaya yana haskata da wani madubi,dukkan waɗannan Halittu miƙewa suka yi cikin tsananin tashin hankali dan duk aikin da suka yi na yau ya lalata masu shirinsu, dukkansu ihu suka saki,gashi tabbas wannan yafi ƙarfin su ballantana su ɗauki mataki, ɓacewa suka yi daga su har hasken babu ko ɗaya a cikin su, duƙewa nayi a wurin ina ta rusgar uban kuka na rasa kukan me nake, kukan rusaman shiri da wannan hasken yayi koko kukan cetona da yayi daga zama wannan halittar?



A hankali na dinga buɗe idanuwana har na buɗe su duka,saidai ruwan da naji nabin fuskata ne ya sani taɓa kumatuna, a mamakina hawaye naji nabin fuskata,miƙewa nayi zaune ina gogesu, ɗagowar da zanyi naga Raheenatu na nafila, hawayen na ƙara sharewa, ina jin dama nice ke wannan tsayuwar daren saidai bani da yadda zaniyi, ta farillar ma yaya nake yinta,miƙewa nayi na shiga Toilet nayo fitsari, tattaɓa fatar jikina nayi najita lafiya lau, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke,na koma na zauna bakin bed ɗimmu, na daɗe zaune kafin Raheenatu ta gama salloli da Addu'o'i,

Zuwa tayi ta dafani tana faɗin "sannu Raheenatu kinji,nasan tabbas azzaluman nan baza su barki ba,dan tunda kika kwanta kike waɗansu yaren Aljannu, danni idan bagizau idanuna suka yi man ba har gani nayi kina tashi sama, shiyasa na tashi ina tofa maki Addu'a nayi sallah," ta faɗa idanunta taf da hawaye,

Kallonta kawai nayi na sakar mata murmushi ina miƙewa,duƙawa nayi ƙarƙashin bed ɗimmu na ɗakko wata tsohuwar jikka,buɗeta nayi na ɗakko wani zoben Azurfa mai masifar kyawu, hannu Raheenatu na kamo na saka mata,kallonta nayi ina faɗin "zobennan yana da Amfani a gurinki ki riƙeshi,nasan ke ce kika rusa masu dukan wani aikin su na yau dan tabbas sai sun nemo ki,ki riƙe wannan zoben shi zai hana su ganinki ballantana,su cutar man dake, duk lokacin da kikaji kina kewata ki murza shi zaki ganni," na faɗa ina rungume ta,

Mun ɗan jima muna fira, kafin bacci ya ɗaukemu,


*WASHE GARI*

Duk wasu shiye_shirye mungama su na tafiya,jiran mazajemmu kawai muke su zo ɗaukar mu,mun ɗan jima kafin su zo, duka dai ƴan gidanmu rabuwar kadahan kadaran mukayi da su,Inna Abu ce kaɗai tasha kuka, saidai koda zamu tafi ta bani Adreshin gidan ƙanwar ta a nan ƙauyen Abuja,

Kuka kau na rabuwa mun shashi Ni da Raheenatu kamar ba gobe,haka dai muka rabu zuciyoyimmu na mana ƙuna da zafi,Ni muka ɗauki hanyar Abuja Raheenatu kuwa Lagos,




*Ɓangare guda kuwa*


Koda mommy ta fito taga Dada saida gabanta ya faɗi dan tasan ba Alkhairi ne ya kawo Dada ba,jiki a sanyaye ta ƙaraso, ta duƙa har ƙasa tana gaida Dada,

Wata uwar harara Dada ta watsa mata tana faɗin "sannu Hamshaƙiya sai yanzun zaki wani zo ki gaishe dani,to ki riƙe gaisuwarki bani buƙatar ta,su Harisu dana haifa su ya zama dole suyi man amma kedai ki riƙe gaisuwar ki bani buƙata," ta ƙarashe zancen da buga cinya,


Murmushin takaici mommy ta saki tana faɗin "wllh Dada ban jiki babu yadda za ayi ace ina jinki nayi shiru,kuma cikin su Nuraim babu wanda yaje ya sanar dani,"

Banza Dada tayi da Mommy harta ƙarashe duƙiyarta ta gaji sannan ta miƙe ta zauna,


Sukau su NURAIM da ABDURRAHIM, wani ɗan banzan takaici ne ya tokare su ganin yadda Dada keyi ma Mommy a gabansu,cikin takaici Abdurrahim ya ce "gsky Dada abinda kikeyi ko kaɗan bakya kyauta man.....," Bai ida ƙarasawa ba Mommy ta buga mashi tsawa tana faɗin "kai bansan shashancin banza dana wofi, Dada tsararka ce da zaka dinga gaya mata magana ?kamar wata sa'ar ka ka kiyaye Ni banson rashi tarbiyya," Mommy ta faɗa tana banka ma Abdurrahim harara,


Taɓe baki Dada tayi tana faɗin "barshi faɗima ya gaya man maganar da yake so,tunda yaga makwancina dole ya rainani,idan baiyi sannu ba wllh ko sati baza'ayi ba

Please Login or Register in order to submit comment